Chapter 90 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   90 / 106

267K to 270K   out of 316K words

bacci na.

*Baba*

Tunda yaji zancen Mama tana asibiti hankalin sa ya tashi, babu abinda yake sai innalillahi wa inna ilaihir rajiun a haka har suka zo asibitin da take din. Sai da ya yi komai ya kammala da jikarsa da dansa ya tabbatar ya hada su da doctors din da zasu gansu sannan ya nemi Mubaraka a waya ita kuma ta kai shi dakin da Mama take. Mufida tana kofar dakin da Mama take ciki ta hada kai da guiwa, sai yaga ta juye masa gabakidaya ta zama kamar ba mufidan da ya sani ba, duk ta firgice ta rikice.

Ta gaishe shi, yayi mata fadan dalilin da yasa bata daga wayarta ba duk kiran da akeyi mata kuma bata fada cewa Mama ba ta da lafiya ba tun azahar sai dare. Sai tayi masa karya da cewa ta bar jakankunan su ne a mota kuma wayoyin suna ciki kuma ba zata iya fita ta dauki ba tunda babu kowa a gurin Maman. Daga yadda take maganar ya san karya take yi amma bai musa mata ba sai ya shiga ciki.

Kamar yadda Mufida ta chanja haka ya ga Mama ta chanja masa, yaga kamar tayi wani tsufa tayi kamar wadda ta shekara babu lafiya duk kuwa da cewa idonta a rufe yake. Ya tambayi Mubaraka abinda Doctors suka ce sai ta maimaita masa abinda ta fadi a waya "sunce kamar ta tsorata ne kawai, amma lafiyar ta kalau, sai jininta da suka ce ya hau itama. Kuma tunda nazo take ta fitgita tana kiran Umar wani lokacin kuma ta kira Mufida, in ta farka kuma sai ta kama kuka. Dazu data farka kuma kai take nema tace in kira ka"

Baba ya zauna a gaban gadon yana kallon fuskar ta tare da ambatar sunan ta "Maryam. Maryam gani nazo. Menene ya faru?"

Ta dan bude idonta a tsorace ta kalle shi sannan ta kalli dakin "ina Umar? Ina Mufida?" Baba ya kalli bayasa shima a dai dai lokacin da Mufida ta juya da sauri ta fita daga dakin, ya dawo da kallon sa kan Mama yace "ba sa nan. A kira wo miki su?" Sai ta mayar da idonta ta rufe tare da girgiza kai sai kuma tayi wa yaya Mubaraka magana "jeki waje ki bamu guri", sai bayan da ta fita sannan ta dawo da hankalin ta kan Baba da ya riga ya gama rudewa tace "magana nake so muyi, ina so in nuna maka irin tarin nadamar da take tare da ni akan kuskuren da nayi a tarbiyyar yayanmu, wanda kuskuren nawa shi ya jawo tarbiyyar su ta gurbata, gurbata kuma mafi muni" ta fada hawaye yana zuba a idonta.

Sai ya rike hannunta yace "uhm uhm, ba laifin ki bane ba. Ni nafi kallon abin a matsayin laifina. Da ace na zauna tare da yayana na taya ku tarbiyyar su na taya ku saka ido a kansu da Umar bai zama abinda ya zama yanzu ba. Ana gaya min kin fadi a gidan biki dama maganar dana kawo a raina kenan, na san wani abu ne da ya danganci halayyar Umar kika ji ko kika gani. Ki gaya min Hajiya Maryam, mai kika ji? Mai kika gani?"

Ta rufe idonta tana kokarin cire munanan hotunan yayanta daga zuciyarta tace "abinda na gani ina fatan kar Allah ya nuna maka shi. Abinda na gani ina fatan babu wata uwa da zata kuma ganin irinsa a duniya, ko da kuwa uwa ce irina mai take laifin yayanta saboda son zuciyata" Baba yace "inna lillahi wa inna ilaihir rajiun. Maryam ki gaya min abinda kika gani" tace "har abada bakina ba zai furta abinda na gani ba, zan tafi da shine zuwa kabari na. Kafin mutuwa ta kuma Zan dauki abinda na gani a matsayin darasi, babban darasi a gare ni da zai saka in gyara halaye na, in sauka daga kan hanyar da nake kai ta son kai da son zuciya in koma kan hanyar gaskiya ko Allah zai dube ni ya taya ni gyaran yayana"

Baba yace "ƴaƴan ki? Ko dai dan ki kike so ki ce?" Ta girgiza kai. "Yayan mu Alhaji Muhammad. Yayan mu. Zina tayi naso a cikin zuriar mu. Dole sai mun tashi tsaye dan ganin mun dakile ta in ba haka ba zata mamaye mu gabaki daya ba tare da mun sani ba"

Ya saki hannunta ya dafe nasa kan yana jujjuya shi kawai cikin tashin hankali. Ta sake kamo hannunsa tace "ni yanzu alfarma nake nema a gurin ka. Dan Allah. Ina so ka samo wani babban mutum mai mutuncin wanda ka san yana ganin darajar mu kuma zai rike mana amanar mu, ina so ka daura wa Mufida aure a cikin satin nan"

Ya bude idonsa yana kallon ta tashin hankalin sa yana karuwa yace "Mufida? Hajiya mai kika gani? Mufida kika gani da Umar?" Ta girgiza kanta "Mufida na gani da Umar, amma ba irin ganin da kake nufi ba. Ni dai dan Allah kayi min wannan alfarmar, ka samu tsayayyen namiji wanda ba zata gagare shi ba. Ka daura mata aure a cikin satin nan".

Ya sunkuyar da kansa kasa, baya bukatar ta gaya masa cewa abinda ta gani yana da dangantaka da cewa Mufida ita ma ta bi layin Umar.



Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020

Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020

Please banda kira, WhatsApp only

*wannan littafin na siyarwa ne bisa amana, idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar kiyi sharing, idan kika yi kinci amana kuma ke da Allah*

*The Letter*

Da asuba da na farka Umar baya dakin, sai na tashi nayi alwala nayi sallah, ina cikin adduoi na ya sake shigowa, nayi shiru ina jin haushin dalilin da yasa zai ke shigo mana daki bayan nasan shima an bashi na sa.

Ya sake komawa kan kujerar da nake tunanin akai ya kwana, ya zauna tare da kife fuskar sa a kusa da ta Yasmin, sai na gyara zamana akan sallayar na cigaba da azkar dina sai kuma naji muryar Yasmin tana magana cikin tsoro "mommy! Mommy" na mike da sauri na tafi gurinta a lokacin da shima Umar yake mikewa daga zaunen da yake yana rike ta. "Mamana! Mamana! Daddy is here. I am here"

Ta zagaye hannunta a wuyansa tana jera ajjiyar zuciya, na karasa kusa da su ina shafa bayanta ina tofa mata duk adduoin da suka zo bakina. Sai kuma ta dago kai tana kallona sannan ta saka kuka "mommy! Ni ba zan koma gidan Mama ba tunda tafiya tayi ta bar mu kuma Asad yake ta kuka wai zai taho gurinki, shine na ce ya zauna inje in kira daddy ya kai mu gurin ki, shine kuma ban ga daddyn ba shine na fita waje ina neman sa, shine wani yace inzo ya kaini gurinsa, kuma bai Kai ni ba sai ya kaini want guri kamar gidan dodo, Ni kuma nayi kuka nace ya kaini gurinsa daddy na, shine ya ke dukana wai in daina kuka, kuma... kuma...kuma shine ya daure min hannuna, shine nake kuka ina kiranki kizo ki hana shi duka na, kuma baki zo ba, kuma daddy ma bai zo ba....kuma ni ban san me nayi masa ba, daddy me nayi masa?"

Ta fada tana kallon Umar, ya saka hannu ya goge mata hawayen fuskarta yace "Babu abinda kika yi masa daughter, shi din azzalumi ne kuma sai Allah ya saka miki kinji?" Ta gyada kai tana kallona kamar mai jiran taji abinda ni ma zance sai na shafa kanta nace "ba zai kuma kama ki ba kinji, Allah ba zai bar shi ko wani azzalumin ya kuma kama ki ba kinji? Zamu ke yin azkar kullum da safe da kuma da yamma, Allah ba zai bar wani ko wata halitta ta mutum ko aljan ya kuma taba ki da niyyar zalunci ba kinji?"

Ta sake gyada kai tana sauke ajiyar zuciya, har yanzu fuskarta cike take da tsoro. Ina lura da Umar yana ta kokarin ganin bai bari ta ga hawayen sa ba, ya taba ciwon goshinta ta danyi wincing tare da rike hannunsa. Ya juyo yana kallona yace "in an zo duba ta ki ce su sake duba ciwon na, naji kamar yayi tauri kuma gurin yayi duhu, ina tsoran kar ya zama infected" na gyada kai kawai. Sai shima ya sunkuyar da kansa sannan yace "kin duba ta? Ko su suka duba ta? Me suka yi mata a gurin mai suka ce?"

Nace "me zasu yi mata banda suyi mata dinki su bata magani?" Ya rintse idonsa tare da dafe kansa yace "innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Wanne wacce irin masifa ce ta saukar mana Jidda? Yarinyar nan is just a baby, how can they?"

Na dauke kaina gefe nace "exactly ta yadda ake yi ta haka akayi, ko in bude maka ka gani?" Ya girgiza kansa sannan ya dafe kan da hannu biyu yace "I can't, I can't" ya juyo yana kallona yace "did you?" Na gyada kaina a hankali bance komai ba, yace "how bad is it?" Na sake yin shiru ban ce komai ba sai ya mike tsaye tare da kwantar da ita a hankali, Ina lura da yadda yake lallabata, sai ya jawo drawer din magunguna ya dauko allurar pain relief din da suka sako mata a ciki, probably saboda ciwon goshinta, yazo ya bude cannula din hannuta yayi mata sannan ya juyo yana tambaya ta in akwai abinda muke so. Shiru na sake yi masa sai kuma yafita, yana fita na bi bayansa na rufe kofar sannan na dawo naci gaba da lallaba Yasmin.

Ranar da wuri Amira tazo tare Asad da Abba, Abba ya duba jikin Yasmin ya tambayi ko muna da abinda muke nema nace masa babu komai sai ya tafi ya bar Amira da Asad a gurina, Asad yana ta murna tare da kuma complain din duk mun tafi mun bar shi shi kadai yana ta kuka yana neman mu, na lallabashi tare da bashi fruits a cikin ledar da saurayin Farhan ya kawo mana, sai kuma na tashi Yasmin na bata abincin da Amira ta kawo mana kuma na samu taci sosai ta sha ruwa har suna ta hirarsu da Asad.

Sai kuma ga mufida ta shigo tare da aunty suma sun kawo mana abinci, aunty tana ta murnar ganin jikin Yasmin yayi kyau har tana tsokanar ta, Mufida kuma na lura da yadda tayi wani irin chanjawa kamar ba ita ba ta zama kamar mutum mutumi, na tambaye su jikin Mama suka ce da sauki, na san ya kamata inje in duba ta amma ban je ba har suka gama zamansu a nan suka tafi.

Basu jima da fita ba Diyam ta zo itama tare da Subay'a, itama ta ji dadin ganin Yasmin tana magana har da dariya duk da dai tana complain kanta yana mata ciwo. Wannan yasa muka saka Amira ta dauki yara suka fita dan kar su dame ta, basu jima da fitar ba kuwa sai tayi bacci.

Bayan tayi baccin ne muka samu muka yi magana sosai na vata labarin abinda ya faru da kuma hukuncin da na yanke na boyewa Umar gaskiyar abinda ya faru dan ina so ya cigaba da dauka cewa anyi din  dan ya kara samun regret, duk da nasan nan gaba zai iya sanin gaskiyar magana amma Ina fatan kafin ya sani din yayi nisa a cikin nadamar sa. Sai kuma na gaya mata fear dina na cewa wannan attack din on Yasmin kamar somin ta bi ne, bisa la'akari da irin tarin laifuffan babanta a wannan bangaren.

Sai ta yaba wa idea ta ta boye wa Umar gaskiya amma kuma sai ta kwantar min da hankali ta hanyar bani misalai da yawa akan mutanen da suke lalatattu sannan kuma sai Allah ya fitar da shiryayyu daga gare su, kamar yadda yakan iya fitar da Yaya masu munin hali daga jikin iyaye tsarkaka. Ta kuma sake encouraging dina akan dagewa da addua akan kaina da kuma yayana, amma kuma sai tace "amma kuma ba kya ganin kamar babanta wannan karon da gaske ya gyaru?" Na tabe baki nace "ban sani ba, Umar is very unpredictable, a duk sanda na kama shi da laifi yana irin haka ai, jiya da dare har da su tashi yayi sallar dare, amma ya kan yi hakan dama a lokuta da dama kuma daga baya ya cigaba da halayyar sa, dan haka a yanzu ma bani da tabbas and I am not going to take chances gaskiya, dan naga kamar kina son kiyi min magana ne akan komawa gidan sa" tayi dariya "Ni va haka nace ba, mayar da wukar, kawai dai ji nayi na fara jin tausayin sa musamman da kika ce min ya fadi. Yana son yarsa sosai kuma for him to think anyi raping his five years old daughter gaskiya dole a tausaya masa" na bata rai "kafin zancen Yasmin ma something has happened, something related to him da kuma Mufida duk da bansan ko menene ba amma nasan yana da dangantaka da dalilin da yasa maman su take asibiti a yanzu. Kuma ya gaya min wai ya hadu da wata masifa bayan ya bar gidan mu jiya ".

Na rike "na shiga uku ni Halima, kar dai garin dauke dauken sa aka dauko masa kanwarsa. Kin san kin gaya min dama itama kamar ta fara daukan hanyarsa?" Na daga kafada "I don't know, and to be frank with you I don't want to know gaskiya. Ni yanzu bani da interest akan duk wani abu da ya shafesu interest dina kawai akan yayana ne. Da kuma fatan zai bani takarda ta ba tare da an kai ruwa rana ba. Fatana kawai in samu in tsayar da hankali na guri daya in bawa yayana tarbiyya"

Ta yi shiru tana kallona sannan tace "you are innocent Jidda, you don't deserve all this mess" nayi murmushi tare da girgiza kaina "no am not. Akwai laifuffa na a cikin abubuwan da suka faru. I was warned akan Umar tun farkon fari amma soyayyar sa ta rufe min ido na kasa ganin gabana, ko bayan auren mu ma I should have acted faster than I did, amma na cigaba da zama da kuma cigaba da bashi uzuri da kuma cigaba da bashi chances ina gaya wa kaina cewa hakan da nake you shine dai dai bayan in reality still soyayyar sa ce take sawa har nake bashi wadancan madammakin. Dan haka I deserve all what has and is still coming my way"

Sai tayi kokarin lightening mood din ta hanyar tambayata game da auren da Umar yace za'a daura masa da Asabe "an daura din kuwa?" Na yi dariya "ni ban sani ba fa, bai sake yi min maganar ba kuma babu wanda yayi min maganar a yanuwansa. Ban sami ba ko an daura din" tayi dariya "kuma haka ake kishiyar babu kayan fadar kishiya balle a gaiyace mu mune dannar kirji?"

Nima nayi dariya "sai dai a gayyace ku diban kaya ba wai dannar kirji ba" tace "ke kuwa ki bar mata kayan ki mana, a matsayin ki na uwar dakinta ai dama ke ya kamata kiyi mata kayan daki" nace "kinga kuwa dama kayan sun dace da ita, sai ku rakani in debo mana kawai sauran kayan sawar mu da sauran kayan amfani, sai ta samu ma ta tare sosai tunda bedroom dina shi yafi dacewa da ita a matsayin ta na matar gida, kinga wannan kawar tata shikenan buri ya cika sai take zuwa gidan a matsayin gidan kawarta"

Sai kuma Diyam din ta koma serious tace "ni fa wasa nake yi, amma har a raina bana son auren nan, ke kuma sai nake ganin kamar babu abinda ya dame ki" na daga kafada "kamar kin sani kuwa, babu abinda ya dame ni, in fact na ma ji dadi da za'a yi auren dan ya zama darasi ga Umar"

Da zata tafi ne tayi min sallama akan cewa zasu tafi Canada gurin surikan ta tare da maigidan ta da Subay'a da twins, na  rakata har bakin mota suka tafi tare da alkawarin zamuyi waya

Kwanan mu uku a asibitin aka sallame mu, a cikin kwana ukun nan kullum Umar a gurin mu yake kwana amma da rana bana ganinsa kuma ban taba neman sa ba. Kwanan mu biyu a asibitin naje na duba Mama sai dai na lura da yadda take ta kokarin kin hada ido da ni, ban san dalili ba kuma ban tambaya ba tunda na gaishe ta tayi shiru nima nayi muka jima a haka sai na tashi na tasa Asad a gaba muka tafi.

A ranar da aka sallame mu ne bayan naje gida Abba ya kira ni yake gaya min cewa ya kira waliyin Umar yayi masa maganar takarda ta "ina ta daga musu kafa ne saboda ina ganin mutuncin iyayen sa kuma gashi uban babu lafiya" na dago kai nace "har maman ma tana asibiti" yayi shiru "amma bana son zaman ki da aure a kanki, kuma vana

So nake da zan samu in karbi takardar sai ki tafi gurin ummanki kiyi idda a can"

Nayi shiru bance komai ba ina jin kalmar idda tayi min nauyi a zuciyata. Sai yace in tashi in tafi. Na dauka zaiyi min magana akan zancen da na gaya masa akan Hajiya amma sai naji bai ce komai ba.

A ranar da dare Umar ya kira ni, ina ganin kiransa na fahimci cewa yaje dakin da muka zauna kamar yadda ya saba zuwa da daddare ya tarar bama nan. Sai na amsa kiran amma sai na sakawa Yasmin wayar a kunnenta ina kallon yadda murmushin ta ya fadada tace "Daddy mun dawo gidan Abba, yaushe zaka zo ka dauke mu mu koma gidan mu?" Sai kuma naga ta bata rai ta miko min wayar. Na karba wata zuciyar tana ce min in katse kiran in ajiye wayar amma dai sai na saka a kunne na nace "hello?" Yace "yanzu saboda Allah ace an sallame

90 / 106