Chapter 6 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   6 / 106

15K to 18K   out of 316K words

kuma na gamsu.

Sai dai kuma da dare bayan mun kammala komai munyi shirin kwanciya sannan na zayyanawa Farhan labarin Umar, yadda muka hadu da yadda nake ji a zuciya ta game da shi, abinda ya gaya min shima da kuma yadda mukayi da Mufida. Sai kuma na bata labarin abinda Abba yace min da shawarar dana yanke akan Umar. "Kinga in ba da gaske yake ba sai yayi tafiyar sa kawai"

Sai kawai naga tayi dariya, na tsaya ina kallon ta dan ni banga abin dariya a cikin magana ta ba, sai da ta gama dariyar ta sannan tace "lallai Jidda kin tabbata yar boarding school wadda bata san abinda yake faruwa a cikin gari ba. Ai in dai dan yaudarar ne kamar yadda kanwarsa uwa daya uba daya ta fada to kuwa zuwa gurin Abba ba zai hana shi yaudarar ki ba. Rikakkun yan yaudara su kan kawo kudin aure ma kuma har zuciyarsu ba da gaske suke ba. Ke dai kawai muyi ta addu'a muna neman zabin Allah tare da neman tsari daga hatsabibai kuma mugayen samari"

Nayi tagumi da hannu daya ina kallon ta, ina jin duk farin ciki na na samun solution yana tafiya. Ta dan baya rai "ke ni har cikin raina ma sai naji bai yi min ba duk da ban ganshi ba. Yadda kike tsara shi sai nake ganin kamar kinyi masa kankanta, irin su manyan yammata suke so wayayyu yan jami'a"

I was so into my problem har na manta da maganar da tun ina makaranta take cewa zata gaya min. Sai da ta tuna min "baki tambaye ni labarin da zan baki ba?" Na juya barin da take ina kallon ta, sai naji kunyar mantawar da nayi, nace "okay, ina ji. Bani labarin new catch din" tayi murmushi mai sautin da ya saka nan take na fahimci cewa ita ma duk a cikin jirgin da nake a nan take ita ma, jirgin soyayya.

"Kinga, sunan sa Sulaiman, lokacin da muna waec shine yake mana invigilation, to shine fa ranar nan mun taso na fito neman mota zan taho gida sai gashi yazo wucewa shine ya dauko ni"

Na bude ido "a motarsa? Baki ji tsoro ba? Da Abba ya gan ku fa?" Tayi murmushi "nima naji tsoro ai, but kawai na daure, kuma dai rabon zamu dai dai ta ne. That was how it started" na dan dake ta kadan ina dariya "to a ina zata yi ending?" Ta juya ido "a inda zaku yi ending ke da Umar din ki" na dauki pillow na na doke ta ita ma ta dauki nata ta rama, muka yi tayi sai da muka gaji dan kanmu sannan muka kwanta muna haki, sai kuma muka cigaba da hira, planning our lives, but Allah shine the greatest of planners duk namu tatsuniya ne.

Kwana na biyar a gida, a cikin kwana biyar din nan Sulaiman yazo, dama already ya samu amincewar Abba, kuma naje mun gaisa da shi ya kuma kwanta min a rai, mutum ne mai faran faran da wasa da dariya.

Malamin makaranta ne shima kamar Abba, sai dai bai kai Abba dadewa a system din ba kuma bai kai Abba matsayi ba. Kuma daga ganinsa ba karami bane ba sai dai yana da karamin jiki kuma yana da kyau dai dai gwargwado da saurin shiga zuciya and I didn't blame Farhan for falling for him.

A daya bangaren kuma tunda na dawo gida kullum idan wayar Umma tayi kara sai inyi sauri in duba, a raina ina tunanin ko Umar ne, dan nasan a gurin Mufida zai nemi hanyar samuna kuma nasan number din Umma take da ita. Sai dai the call never came through.

Haka zalika a duk lokacin da naji yaro yayi sallama sai inyi tunanin ko za'a ce ana sallama da Jidda ne amma shiru. Sai a ranar da nayi five days a gida ne aka aiko kira na

"Salamu alaikum, wai ana sallama da Jidda" na dago kai daga karatun littafin hausan da nake yi ina kallon Umma, ita ma ni take kalla, sai muka ji Hajiya ta amsa wa yaron tare da cewa yaje ya tambayo waye mai sallamar. Na mike zaune ina wasa da band din hannuna. Zuciya ta tana bugawa da tsananin karfi a kirjina har naji motsin yaron ya dawo yace "wai inji Musa" naji zuciyarta tsaya da bugawar da take yi sai kuma hawaye ya taho zuwa idona. Nayi saurin tsayar dasu tare da sunkuyar da kaina kasa dan kar Umma ta ga kuka na.

Bata ce min komai ba sai ga Hajiya ta zo ta daga labule, Jidda ana kira a waje, ko ace masa ba zaki zo ba? In ba kya son zuwa sai ace masa ba kya nan shikenan"

Umma tace "tana zuwa, mai zai hana ta zuwa?" Hajiya ta saki labulen tare da cewa "wai da" na mike na shiga cikin daki na zauna a bakin gado, ni dai har ga Allah bana son zuwa, mai zan je inyi? Ni akwai wanda nake jira..

Umma ta shigo tana kallona, "yana jiran ki fa" bance komai ba na mike ina neman hijab dina, ta cigaba da magana "baban ku yayi min maganar sa dama, Musa ne dan gidan Malam Magaji na bakin layi, yaron kirki ne ya gama karatun sa har ya samu aiki koyarwa a makarantar su Amira" na saka hijab dina still bance komai ba, tace "ki bude muku sitting room din baban ku, baya son ake tsayawa da samari a titi" na tsaya a gabanta nace "to Umma na tafi" tace "a dawo lafiya Allah ya bada sa'a" bance ameen ba dan bana jin akwai sa'a a fitar tawa.

Ta kofar cikin gida na shiga sannan na bude kofar waje, yana tsaye a cikin railer ya juya bayansa, bude kofar da nayi ya saka ya juyo, na sunkuyar da kaina ban yarda mun hada ido ba nace "bismillah" sannan na koma ciki na zauna a kan kujerar da take ta can karshe wadda daga ita sai kofar da za'a koma cikin gida. Ya shigo da sallama, ya ajiye ledar hannunsa a kasa sannan ya zauna shima, bance komai ba duk da nasan ya kamata in gaishe shi.

Yace "ina wuni Jidda?" Sai naji babu dadi, ko babu komai ya girme ni nesa ba kusa ba. Na dan russuna nace "sannu da zuwa. Ina wuni?" Yace "lafiya lau. Ya bakunta?" Bance komai ba, ya cigaba "ke yanzu kin zama bakuwa anan ko?" Still no answer

Ya zauna yana ta shafa kai sannan yace "nasan zaki yi mamakin ganina a gidan ku, musamman da kika ji gurin ki nazo, amma hakan ba abin mamaki bane ba musanman in kika yi la'akari da ke din wacece......."

"Ban yi mamaki ba, Abba ya gayamin zaka zo, ya kuma gayamin abinda zai kawo ka"

Ya danyi shiru, sai kuma ya yi murmushi mai sauti yace "Allah sarki Abban mu, ya kyauta min sosai kuma ya taimaka min ya hutacce da ni daga dogon bayani, yanzu abinda ya rage mana shine....."

Na dago kai da sauri nace "ba cewa yayi ya baka ni ba ai" ya daga hannu "ni ma bance ya bani ke ba, amma at least na taka wani stage mai kyau a maganar mu ko?" Na girgiza kai, "kawai dai kaidar sa ce hakan, ba wai yana nufin wani abu bane ba" yayi shiru yana kallona yayin da ni kuma nake kallon gefe na hade girar sama da ta kasa, yayi ajjiyar zuciya "okay. Maybe na yi raising expectations dina sosai, maybe nayi wa maganar shigar sauri, maybe Jidda zata fi so ace ita na fara samu da maganar kafin Abba. Amma har yanzu ma bata baci ba, ki gaya min abinda kike so inyi, kiyi min magana ki saki jikinki mu fahimci juna ni kuma zanyi duk abinda kike so"

Na juyo da idona ina kallon sa, sai naji zuciyata tana comparing dinsa da Umar, nayi saurin kawar da tunanin daga raina sannan nace "daga farko ina son inyi karatu" ya danyi shiru, ina jin a jikina kamar kallo na yake yi, sai naji yace da alamar mamaki a muryarsa "karatu kuma?" Na daga kai kawai, yace "I thought Abba baya bari" nace "Abba baya bari ba yana nufin mu bama so ba, dan Abba bai bar yayye na ba ba yana nufin ni ba zai barni ba"

Yace "duk na fahimci wannan kuma na amince, zan kuma so hakan ta kasance, ni malamin makaranta ne dan haka na san darajar karatu ba kuma zan so ace matata bata da ilimi ba, amma ina tuna mana cewa biyayya ga iyaye wani babban abu ce a rayuwa, idan Abba bai bari ba ina so mu dauka a haka, ba sai lallai kinyi karatu a waje ba, zaki iya yi daga ciki hankalin ki a kwance" na dago ina kallon sa a raina ina tunanin ko wannan shine maganar da mazajen sisters dina suke yi musu kafin aure.

Jin nayi shiru yace "look Jidda daga kallon da kike min da kuma yadda kike amsa min magana na fahimci cewa banyi miki ba, and I understand that, amma ba wai na hakura bane ba yanzu ma na fara insha Allah, abinda nake bukata daga gareki kawai shine dan Allah kar ki rufe zuciyarki ki bar min ita a bude ni kuma xanyi iyakacin kokarin ganin na shiga cikin ta a hankali. Ki daure, ba dan ni ba kinji Hauwa'u?"

Na gyada kai na a hankali ina jin a raina babu dadi saboda yadda nayi masa, amma kuma sai zuciyata ta ji haushina akan damar dana amince zan ba shi, yayi murmushi, "Nagode. Insha Allahu ba za kiyi nadamar yin hakan ba" ya fada yana gyara zama, sai na mike tsaye da sauri nace "am sorry zan koma cikin gida, dama ina yin wani abu ne aka yi kirana" fuskarsa ta nuna rashin jin dadin hakan amma baiki ba sai ya mike tare da miko min ledojin daya shigo dasu a hannunsa yace "shikenan, Nagode sosai da kika fito kuma kika saurare ni, ga wannan a bawa Amira" na girgiza kai na, "ka barshi kawai" ya matso "ai ba ke na bawa ba, Amira nace ki bawa" na sake girgiza kai "ka barshi kawai" sannan na juya na koma cikin gida.

A falon Umma na same ta tare da Abbah da Amira suna hira, Umma tace "ya akayi? Ya tafi?" Na gyada kai kawai ina jin kamar zanyi kuka, na kwanta akan kujera na juya musu baya duk da ina jin Abbah yana tsokana ta wai na fita zancen farko a rayuwata "ya kamata in dauke ki a hoto in ajiye miki tarihi, sai kin haihu in nuna wa yayanki"

Amira tayi dariya "na ganshi ai a sitting room, Yaya Musa ne yayan kawata Saddika, dama kullum muka hadu sai ya bani wani abu ashe yayata yake so" suka sake yin dariya tare da Umma, Umma tace "ni ma muna haduwa da babarsa a islamiyya, ranar nan ma har take bayar da labarin cewa ya samu aiki ta bada sadaka tace ayi masa addu'a" naji kamar zan tashi in bar musu gurin sai mukaji yaro yayi sallama a tsakar gida

Amira ta mike tana amsawa a lokacin da Hajiya itama ta fito daga nata dakin tana amsawa, banji me yaron yace sosai ba sai da Amira ta dawo hannun ta da ledojin da naki karba daga hannun Musa tana murna, suka zauna suna budawa, daya kayan kwalliya ne da turare a ciki dayar kuma fruits, na tashi na shiga ciki dan haushin su nake ji kuma babu yadda zanyi dasu, su kuma duk sai suka dauka wai kunya nake ji, ina ciki naji yaya Tahir ya shigo shima amma naki komawa duk da cewa inaso ayi hirar dani nayi kwanciya ta a daki.

Sai dare bayan mun kwanta ni da Farhan sannan na samu na bude abinda yake zuciyata. "Bana sonsa" na fada mata. Bata nuna mamaki ba tace "saboda me?" Na gyara kwanciya ta ina neman dalili, ba zan hada shi da Umar a kyau ba amma kuma ba zan kira shi da mummuna ba, yana kuma da hali mai kyau dan kowa a unguwa ya shaida, babansa abokin Abba ne, maman sa kawar Umma ce, kanwarsa kawata ce, daya kanwar tasa kuma kawar Amira, yana da ilimi na addini dana boko dai dai gwargwado. What else nake bukata kuma?

Na yamutsa fuska nace "yayi min gajarta da yawa, da kadan fa ya fini tsaho, sannan sunan sa babu dadi" Farhan ta kwashe da dariya har da rike ciki sannan tace "Allah da gaske? Wannan dalili ne? Ki fadi gaskiya, ko dai kina nufin ki ce Umar ya cika ko'ina babu gurin da Musa zai zauna?"

Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020

Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020

Please banda kira, WhatsApp only


Episode Five : The Visit

Free Episode

Ranar dana kwana goma a gida ne na gaji da jiran kiran wayarsa nayi deciding zan kira Mufida watakila ko zan samu wani labari a kansa a gurinta, duk da dai nasan cewa pride dina ba zai barni in tambaye ta shi ba. Na dauko slum book dina na nemo number din ta na kira a wayar Umma, bugu biyu ta dauka "Hello?" Nace "hey Mufida" sai tayi dariya cikin murna tace "Jidda? Wow. Ko da yake nayi fushi, ke da mukayi da ke cewa kina zuwa gida zaki kira ni amma sai da muka kwana goma sannan zaki kira?" Nayi murmushi "kiyi hakuri yammata, ko da yake ai bai kamata in baki hakuri ba tunda kema ai kina da number din Umma mai yasa baki kira ni ba? Dan haka laifin ba nawa bane ba ni kadai" sai tayi dariya kawai.

Muka yi ta hirar mu, kowa yana bayar da labarin abinda ya faru bayan zuwan mu gida, a lokacin ne take bani labarin zasu tafi Lagos suyi hutu gabaki dayan yan gidan su "banda yaya doctor tunda shi yana aiki" a wannan statement din ne kawai ta ambaci sunan sa, ban nemi karin bayani ba kuma nima ban ambace shi ba har muka yi sallama. At least dai naji cewa he is fine, sai dai wannan ya saka na sake shiga wani tunanin, tunanin dalilin da yasa bai neme ni ba har yanzu.

A ranar ne kuma da yamma muna cin abinci tare da Umma da Amira, sai ga Abba ya shigo falon, ya zaro kudi daga aljihunsa ya ajiye akan kujera yana kallona yace "ki shirya gobe da safe ki tafi ki zagaya gidajen yan uwanki, mazan kowa kiyi masa kwana biyu matan kuma kwana daya, sannan ki je gidan Aunties dinki Habiba da Afia suma kiyi musu kwana dai dai. Na amsa da "to" kaina yana kasa ina jin babu dadi a raina, duk yayyen nawa ba wani jin dadin juna muke yi ba dan haka ba dadin ziyarar zanji ba, Umma ta gyara zama tace "amma da an barta tayi wa Afia kwanaki da yawa, yaushe rabonta da ita? Ba ka taba barinsu suje su kwanar mata ita kuma nata yayan duk hutu sunanan gidan. Dan Allah ka barsu suyi sati ita da Amira. Ita kadai su ke da ita a matsayin dangin uwa" direct yace "kwana daya nace, kuma ita kadai, idan kwana dayan bai yi ba to tayi zaman ta" ya juya ya fita. Duk muka yi shiru kowa ransa babu dadi sai kuma muka ji shi ya dawo yana kwalla wa Farhan kira yace "ki shirya ki bi Jidda zaku zagaya yan'uwa" sai kuma ya sake fita.

Umma tayi dan karamin tsaki. Wato ya hada ni da Farhan dan kar in ki yin yadda yace. Amma ni sai naji dadin hada ni da Farhan din da yayi, at least zan fi jin dadin tafiyar akan ace ni kadai ce.

Umma ta dauki kudin daya ajiye tana kirgawa sai ta sake wani tsakin "wannan ai ba zai ishe ku ba, tunda ku biyu ne yanzu, sai dai inya dawo ita sai ta je ta karbi nata tunda wannan ke kadai ya bawa" Amira tace "gashi inda zasu je babu mai basu kudin mota, sai dai ko gidan Aunty Habiba da gidan Mami" Umma ta tabe baki tace "su samu abinda zasu saka a cikin su first kafin suyi tunanin a basu kudin mota. Su kansu nema suke ballantana su bawa wani".

Ban kuma tabbatar da maganganun Umma ba sai da muka je, gidan Mama Sa'a muka fara zuwa, ƴaƴan ta shida, Mammy ce babba kuma tana jss3 a lokacin, amma sai da muka kirga yaya sunfi ashirin a gidan, duk yayan kishiyoyi da mijin yake aura yana saka ana tarawa Mama Sa'a su, ita ma kuma abinda muke tunanin ya saka take gidan har yanzu shine saboda yadda take daukan duk wani wulakancin sa dan tasan in ta mayar masa ya sake ta to bata da gurin zama a gidan mu ita kanta ballantana ƴaƴan ta, ita kuma yadda take sane da yanayin gidan ba zata iya tafiya ta bar yayanta a cikin wannan halin ba.

Mugu ne na karshe, daga matan har yayan tsoronsa suke ji kamar wani dodo, sai dai jin dadin su daya shine basu rasa ci ba ba kuma su rasa sha ba, ba dai za'a ce suna da komai ba amma basu da yunwa. Sai dai yawan yayan da kuma rashin kulawa daga uban ya saka rasa tarbiyya. Idan kaji yaran suna zabga ashar zaka dauka yayan maguzawa ne, basu kyale kowa ba har matan uban zagi suke yi uban ne kadai basa zaga shima kuma dan sun san jikin su ne zai gaya musu.

Kallo daya zaka yi wa Mama Sa'a ka fahimci cewa ba jin dadin zaman take yi ba, bakin ciki ne fal a zuciyarta babu wanda zata iya budewa zuciyarta.

Da safe cikin bacci muka ji shi ya shigo ya balbaleta da masifar bata gama sallamar yara da wuri sun tafi makaranta ba har sun makara. "Kina cen kina shegen bacci sai

6 / 106