Chapter 33 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   33 / 106

96K to 99K   out of 316K words

sunanta ban gani ba. Na rude na fara nema hankali na a tashe amma babu, na danna abin searching na saka sunan ta "Zuwaira Abdulkadir Zuzu" amma sai aka ce min no result.

Na fita daga messenger din na yi searching dinta through out facebook amma babu ita sai masu suna irin nata, na daga kai ina kallon sa, shima ni yake kallo amma babu ko alamar tsoro a fuskarsa sai dai tarin damuwa.

Na fara girgiza kaina. "Ya goge, wallahi Daddy ya goge, Aunty ya goge duk sakonnin kuma yayi blocking dinta daga wayata sannan yayi blocking dina daga wayarta"

Ya gyara zamansa "ni? Ni yaushe na dauki wayarki? Ni yaushe na ganki ma ballantana har in dauki wayarki in goge sako?"

Duk suka kalle ni da alamar tambaya nace "Aunty shine ya bude min facebook din dama, shi ya saka min password ni ba ma zan iya tuna mai ya saka as password din ba, ta wayarsa ya bude facebook dina ya shiga ya goge kuma ya fita" na zauna dabas a kasa "innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Wallahi Umar kaji tsoron Allah. Idan su basu gani ba ai Allah ya gani kuma ba zaka taba gogewa a cikin littafin ka ba. Akwai ranar da za'a saka aiyukan ka kamar a TV a gaban kowa ya ga gani, iyaye yanuwa, yaya da surikai. Anan ne za'a ga hotunan daka goge daga wayata"

Daddy yace "Jidda kinsan girman accusations din da kike wa mijinki kuwa? Mun ce ki kawo shaida kuma baki kawo ba sannan kina gaggaya masa magana a gaban mu. Wannan itace tarbiyyar da muke tunanin mun baki?" Na gado kai. "Daddy bani da sauran shaida sai Allah, ya goge wadda nake da ita. Kuyi min duk hukuncin da zaku yi min akan abinda yace nayi, shi kuma Allah zaiyi masa nasa hukuncin akan abinda ni da shi muka san yayi"

Aunty ta sauko ta jawo ni jikinta tana jijjiga ni "tunda babu shaida Jidda babu abinda zamuyi miki saidai mu baki hakuri, mu baku hakuri gaba ki dayan ku dan bamu san wanda yake da gaskiya a cikin ku ba" na da kalle ta sai na ce "akwai wata shaidar Aunty, na tuno akwai wata shaidar" na kalli Umar naga tashin hankalin da naso gani dazu ya bayyana yanzu a fuskar sa.

Aunty tace "mecece shaidar" still ina kallon sa nace "yaya Jamila, yaya Jamilar gwoggo Habibah" yace "what?" Nace "yes, ta gaya min abinda ya faru tsakanin ku lokacin ana saura kwana biyu daurin auren mu. Na karyata ta saboda na bari son ka yayi min yawa, na yarda da maganar ka cewa so take ta raba mu, amma yanzu na yardada abinda tace, tace ka neme ta ita maa bisa alkawarin zaka aure ta"

"Jidda!" Abba ya fada cikin tsawa, na juyo ina kallon sa nace "in baku yarda ba ku kira ta ku tambayeta" sai na mayar da kallona kan Umar sai naga yayi relaxing. "Yes, a kira ta. Ni kuma yarinyar nn tunda tayi min wannan sharrin sai munyi sharia da ita"

Aunty ta fara jujjuya kanta "ni ba xan iya kiran Jamila inyi mata wannan tambayar ba. Kuma ko da gaskiya ne ai ba zata fada ba"

Na mayar da kaina kansa, muka hada ido, of cause bazata fada ba, not to Aunty Afia da take like family, inta fada ba wai Umar kadai ta tona wa asiri ba har da ita kanta, in the society da muke ciki ma ita din ita ce a ruwa ba shi ba.

Wannan shi yasa Umar yayi relaxing dan yasan ba zata fada ba.

Na sunkuyar da kaina kasa na dauko waya ta na lalubi number din Yaya Tahir na tura masa sako "please help me". Sannan na ajiye wayar.

Daddy ya fara fada, wanda duk kusan fadan akaina ne akan wai nadauki wayar Umar na karanta sakon budurwar sa sannan kuma nayi yaji akan hakan.

"Mata hudu aka halasta masa ya aura, kuma ba zai aure su ba sai sun fara fahimtar juna tukunna"

Umar yace "ni Daddy na gaya mata ma babu wani zancen aure a tsakanin mu. Amma taki yarda"

A nan ban iya hakuri ba sai da na dago kai na banka wa Umar wata hararar da sai daya sauke nasa idon kasa.

Suka cigaba daga inda suka tsaya har suka gama ban kuma cewa komai ba, sai da suka kare sannan Daddy yace mu tashi mu tafi, in tashi in bi mijina mu koma gida.

Muka tashi Umar ya fita ta kofar waje ni da Aunty muka yi cikin gida sai Daddy ya kira ni na dawo na durkusa a gaban sa sai yace

"Kiyi hakuri Jidda, jikina ya bani kina da gaskiya amma bani da hujjar dazan kama mijinki da ita, kiyi hakuri ku tafin amma ki bani sunan yarinyar da kika ce yana nema din, zanyi bincike a kanta halayyar ta ita zata tabbatar min da abinda kika ce, daga nan kuma sai in dauki mataki"

Nayi mamakin cewa ya yarda din amma bai nun a gaban Umar ba ballantana yayi masa fada.

Nace "ni bansan komai a kanta ba sai sunan da take amfani da shi a facebook" ya dauko wayarsa "bani sunan in duba, na gaya masa ya saka ya duba ya nuna min profile picture din ta yace "wannan ce?" Na gyada kai. Yace shikenan kar ki damu. Zanyi bincike akai".

Na tashi na shiga ciki. Ina shiga Aunty ta kira Afia tace ta karbo Yasmin a hannun Baba Dije ta kuma dauko mana jakar kayan mu ta kai mana mota, ta hau ta sauko da jakar da kum Yasmin a hannun ta ta fita, jimawa kadan ta dawo amma babu Yasmin din, nasan shi ya karbe ta.

Aunty ta fara yi min nasiha

"Jidda, nasan kina da gaskiya amma babu yadda zanyi ne, kiyi hakuri, ki sani kowacce mace kika gani a gidan mijinta to hakuri yake zaune da ita, kadan daga cikin mata ne suke jin dadin auren su a wannan zamanin"

Na dago kai "yanzu Aunty kuna nufin duk kun yarda da abinda nace amma ba zakuyi komai a kai ba?" Tace "to me kike tunanin zamuyi akai Jidda? Muce ki dawo gaban mu ki zauna? Na yarda shi ya goge sakon cikin wayarki amma kin san dalilin da yasa ya goge?"

Nace "saboda ya kare kansa mi kuma ya dora min laifi" ta girgiza kai "saboda mu bashi ke ku tafi. In muka ga hoton ba zamu bashi ke ba, ko zamu bashi ba yanzu ba. Kin san saboda me yake son mu bashi ke din yanzu" nayi shiru amma amsar a raina ita ce saboda mu koma gida ya cigaba da kunsa min bakin ciki, ita kuma sai tace "saboda yana son ki, yana son cigaba da zama da ke"

Na girgiza kaina "baya so na Aunty, da yana sona da ba zai ci min mutunci har haka ba" tace "idan akwai abinda nake da tabbas akansa Jidda shine son da Umar yake miki. Men are very funny akan harkar so." Na sake cewa "ita yake so Aunty, tunda har ya kasa rabuwa da ita duk kuwa da abinda tayi" tace "sai kuma ya kasa auren ta ya aure ki? Saboda me?"

Na danyi shiru sannan nace "saboda ya lalata ta a waje, shi yasa ba zai aure ta ba" tayi murmushi "to saboda menene ya lalata ta a waje ke kuma bai lalata ki ba?" Nayi shiru ban ce komai ba.

Tace "wannan shine banbancin, ke yana son ki ita kuma baya sonta sha'awar ta kawai yake yi, ta san da haka, wannan shine dalilin da yasa take jin haushin ki kuma take son taga ta raba ku. Kar ki bata wannan damar. Ki rike mijinki kiyita hakuri kina ta yi masa addu'a wata rana sai labari"

"Yanzu a zamanin nan kusan 80% na maza haka suke. Amma in kika yi hakuri duk abinsa zaiyi ya gama ne da kansa zai daina. Bara in baki wani labari wanda daga ni sai umman ki muka sani, nima kaina da kike gani na din nan I was once in your shoes amma yanzu fa? Komai ba ya wuce ba sai labari? Gashi ina cin ribar hakuri? Kema watarana haka zaki zama"

Nayi shiru ina tunanin abinda tace. Watarana sai labari? Yaushe kenan? Sanda Umar ya tsufa instruments dinsa suka daina functioning well sannan zai daina, meanwhile ni kuma ina zaune ina ta hakuri?

Na duba maganar da tace namata da yawa suna cikin irin problem dina suna hakuri, but why? Me yasa ba zamu hada kai muce "enough is enough ba?"

In ance kusan kowa haka yake ai kamar ana kara musu kaimi ne, kamar ana nuna musu cewa wannan xinar da suke yi ita ce identity dinsu dan haka it is okay zasu iya cigaba. Wanda ma baya yi in yaga wani yana yi kuma babu abinda yake faruwa sai yayi joining club din shima.

Shigowar yaya Tahir ce ta katse min tunani na, na mike da sauri na rungume shi ina cigaba da kukan da na dakatar da.

"Me ya faru? Ya fada yana kallon Aunty, ta harare shi "ina ruwan ka? Wa ya kirawo ka? An riga an gama magana kuma ba za'a dawo da ita baya ba saboda kai"

Ta nuna ni "wuce ku tafi" na cika shi sannan na goge hawaye na nadauki waya ta na fita ba tare da nayi masa sallama ba. Ina fita Umar yayi sauri ya fito daga mota da Yasmin a hannunsa ya bude min kofar gaba, na wuce shi na bude baya na zauna tare da rufe kofar da dukkan karfina, hopping glass din motar zai tarwatse at least nima in rama ta wani gurin.

Yaya Tahir ya fito yana kallon mu, sai naga Umar yaje gurinsa ya mika masa hannu sun gaisa, sannan naga suna magana amma bana jin abinda sume cewa duk da dai na tabbatar karya kawai Umar yake shirya masa, maybe har da sharri yake kara yi min.

Sai naga sun taho tare, Tahir ya shiga seat din driver Umar kuma ya zauna a gaba, Tahir ya tayar da motar muka bar gidan ni kuma na hada kaina da kofa na cigaba daga inda na tsaya a abin da nagi iyawa fiye da komai, kuka.

Yaya Tahir ya kira sunana "Jiddo?" Na dago kai ina kallon sa ta mirror sai yace "ki daina kuka kinji. Allah yana kallon duk wanda ya zalunce ki kuma zai saka miki" sai ya kalli Umar yace "Doctor Umar Maijidda amana ce a hannunka, in kaci amanar ta Allah ba zai barka ba"

Bai ce komai ba kuma banyi tunanin zai ce komai din ba.

Sai naji shigowar message waya ta. Na dauka da sauri hoping ko wata shaidar na samu amma sai naga sako daga Umar

"Baby dan Allah ki daina wannan kukan. Ko kina so ne zuciyata ta buga in mutu a motar nan?"

Na dago kai nace "yayana" Tahir ya amsa, nace "ya ake blocking number yadda ko message ba zai shigo ba? Nayi blocking wata number naga bata iya kira na amma gashi ana turo min message da ita" yace "ki yi installing true caller, in kika yi blocking ta can shikenan" nace "Nagode, yanzu kuwa."

*wannan littafin na amana ne, idan baki siya ba kar ki karanta idan kuma kin siya kar kiyi sharing, in kika yi kinci amana kuma ke da Allah*

*The Confession*

Shiru ne ya sake biyo baya a motar, a haka har muka har buk road sai yaya Tahir yayi packing yace anan zai sauka zai shiga school. Ya fito daga motar Umar ma ya fita bude inda nake ya miko min Yasmin, na karbe ta ba tare da na kalle shi ba sai ya rufe ya koma seat din driver.

Yaya Tahir ya leko ta window yace min "Jiddo? Zamuyi waya kinji?" Na gyada masa kai sannan ya gangara mu kuma muka yi gaba.

Babu wanda yayi magana sai Yasmin da take yan korafi irin na jarirai har muka je gida. Yana packing sai yai sauri ya bude min kofa ya miko hannu zai dauki Yasmin na janye ta na matsa na fita daga kofar da ba ita ya bude ba, ya rufe kofar sannan ya bude booth ya dauko mana jakar kayan mu sannan ya biyo bayana bakin kofa inda nake ta kokarin nemo key a cikin jakar hannuna, ya ajiye jakar hannun sa yace "kawo Yasmin din sai kiji dadin daukowa" nayi banza na bawa iska ajjiyar sa, ya sake miko min hannu sai na matsa na cigaba da abinda nake yi, sai ya koma mota da sauri sai gashi dawani key din ya dawo ya bude gidan sannan ya matsa yace min "bismillah" na ja dogon tsakin danasan da ace zare ne da sai ya kai bakin gate sannan na shiga. Ya biyo bayana da kayan mu a hannun sa.

Falon kacha kacha kamar anyi yakin badar a ciki. Yace "am sorry for the mess, yanzu zan gyara miki gidan gabakidaya, kamar sabo zan mayar miki dashi. Kin san dai ai na fiki iya gyaran gida ma ko? Yanzun ma....." Banji karshen maganar ba na wuce shi na tafi dakina, ina shiga na rufe kofa na murda key sannan na kwantar da yarinya ta nima na kwanta.

Hawayen ya tsaya yanzu a idona, amm zuciyata tankar garwashin wuta haka nake jin ta acikin kirjina. Wato Umar ya dauki wuka ya daba min a cikin zuciyata ta hanyar cheating on me, sannan kuma hakan bai ishe shi ba sai ya debi gishiri ya barbada a kan yankakkiyar zuciyar ta wa ta hanyar rufe laifinsa da kuma yi min sharri a gurin iyaye na.

Daya abin kuma daya kara rura wutar zuciyata shine yadda Aunty da Daddy suka tabbatar cewa Umar ne marar gaskiya amma suka kasa yi masa fada sai ni da suka san ni ce mai gaskiya ni kuma suka yi wa fada. Ni akayi wa laifi, babban laifi, sannan akayi min sharri, sannan kuma akayi min fada kuma aka bashi ni yadawo dani gidan sa.

Saboda me??????

Saboda shi namiji ne ni mace? Saboda an haife shi da jela a tsakanin kafafuwan sa ni kuma babu??? Wannan shine dalilin????

Kuma ma wai dan gidan Aunty nae ba gidan mu ba. Maybe da gidan mu naje da bayan fada Abba sai ya hada da duka.

It was a bitter experience but I learnt something, something din kuma shine ba zan sake fita daga gidan Umar da niyyar yaji ba, duk kuwa ranar da na fita to tabbas na gama aurensaa ranar ba zan sake dawowa ba har abada. Duk kuwa da tsananin son da nake masa.

Tunowa da soyayyar Umar da take kwance a cikin zuciyata shi ya taso min da bakin cikin abinda yayi, ya dawo min da hotunan pictures dinsa shi da zuwaira cikin zuciyata, hotunan da duk da ya goge su a waya ta ba zasu taba goguwaba daga cikin kaina ba for as long as akwai ƙwaƙwalwa a skull dina.

Na dauki Yasmin da ta fara rigima nayi feeding dinta ina kallon fuskarta, shin anya kuwa nayi mata zabin uba na gari? Anya kuwa?

Bayan ta gama na kwantar da ita sannan nima na kwanta na jawo pillow kirjina na rungume ina jika shi da hawaye, ina hango rayuwar da take facing dina, ina hango challenges dina wadanda a lokacin ma ban san dukkan su ba dan babu wanda yasan abinda gobe zata kawo sai Allah.

Daga dakin nake jiyo shi yana ta butuntu a falo da kitchen, har da su karar blender najiyo daga kitchen din, zuwa jimawa kadan kuma naji kamshin turaren wuta. Ni dai ina nan a kwance ban tashi ba kuma bani da niyyar tashi in dai har yana gidan. Ni da shi mu zuba mu gani, dan halak ka fasa.

A haka bacci mai nauyi ya dauke ni, exhausted from my cries. Cikin baccin naji ana kwankwasa kofa, na yi mika tare da salati dan baccin mai nauyi ne nayi sannan na kalli agogo naga around 3pm. Nayi sauri na kalli Yasmin naga har yanzu bacci take yi dan su jarirai basa gajiya da bacci.

Aka sake knocking. "Jidda, ki bude ga abinci ki ci" Na sake tsaki ma koma na kwanta ina rufe idona da kunne na, hoping zan daina jin muryar sa. "Jidda" ya sake kirana. "Nasan kina jina. Please don't punish yourself da yunwa, ni nayi laifi ni za'a yiwa dukkan hukunci ba ke ba. Ki fito ki ci abinci. Ni na dafa miki da kaina"

Takaici ya kama ni na taso da sauri nazo bakin kofar na rike kugu "go away please. Ko ba zaka tafi bama please ka daina magana kana ambatar sunana, muryar ka tana saka ni jin amai" ya danyi shiru sannan yace "naji, zan tafi. Amma ina zanje?"

Nayi tsaki "oho maka. Go and hang your self or something I don't care" yace "okay. Naji, you don't care. You are angry I know kuma you have absolute right to be angry. Ki ce min komai kiyi min komai but Please ki bude kici abinci"

Ban ce komai ba na koma na kwanta ina jin haushin kaina dana kula shi ma. Zuwa anjima kadan sai naji motsinsa ya same dawowa naji kamar ya ajiye wani abu a bakin kofa sannan yace "ga abinci, ki bude ki dauka"

Nayi sauri na mike na sauka daga kan gadon sannan na bude kofar, yana tsaye bai bar gurin ba, a kasa ga tray nan da flasks guda biyu babba da karami da robar lemo data ruwa.

Ya dan fara murmushi nervously yana jujjuya hannun sa "Jidda" na durkusa na bude abincin, taliya ce da miya, daga ganin miyar kasan ko gama dahuwa kayan miyan basuyi ba ballantana su fara soyuwa. Har da nama zuku zuku a ciki.

Na daga kwanon taliyar na watsar a corridor din sannan na bishi dana miyar, miyar ta bata har jikin Umar da kuma jikin bango, sannan na bude lemon na daga shi na tuttular a kasa na kuma jefe shi da robar a fuskar sa, naja kofa ta na rufe.

And I was so happy with myself duk da dai banga irin bacin ran da nake fatan gani a fuskar sa ba.

Naji ya fita

33 / 106