Chapter 95 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   95 / 106

282K to 285K   out of 316K words

kuma na tabbatar idan Umar zaiyi ignoring dina saboda dagewar da nayi na rabuwa da shi ba zai ignoring yayansa ba, what if something bad has happened to him?

Na nemo wata tsohuwar number dinsa wadda yayi amfani da uta lokacin da yake pretending cewa ya daina using layinsa, na kira amma shima not reachable, tunowa da nayi da lokacin da yayi using number din da irin karerayin da ya ringa yi min ya sa nayi tsaki, in ma wani abun ya faru da shi ai yana da iyaye da yanuwa da abokai, ko Bashir ya isa ya kula da shi.

Na tuna rantsuwar da ya dinga yi min cewa ya rabu da Bashir amma Farhan ta gaya min cewa tare da Bashir din suka yi ta yawon nema na kuma babu wata alama ta rabuwa a tsakanin su.

Na jefar da wayar gefena ina jin haushin kaina na damuwa da nayi da sanin dalilin kashe wayar sa. He doesn't deserve that from me does he?

Amma duk da haka ana ya gobe zamu tashi sai na shirya yara na hada su da Amira nace ta kai su gidan su Umar suyi musu sallama. Bata jima ba sai gata ta dawo ita kadai wai Mama tace su zauna su wuni da dare za'a dawo dasu. Kuma zasu je asibiti su duba baban su.

Na tsaya ina kallon ta. "Bashi da lafiya ne?" Ta daga kafada "haka dai naji tace, ni kuma ban tambaye ta ba"

A ranar ne kuma da yamma nayi bakuwa. Surayya. Naji dadin zuwanta sosai na tare da da fara'a muka shiga daki na gabatar mata da ruwa da lemo sannan muka gaisa. Tayi kyau sosai sosai, in ba saninta kayi sosai ba ba zaka gane ta ba saboda yadda tayi fes da ita fatarta tayi kyau sosai. Ba zaka ce da ne take gidan mai kudi ba yanzu kuma take gidan iyayenta masu rufin asiri.

Ta fara min mitar bani da zumunci na daga mata hannu "naji naji, na kuma karbi laifina hannu bibbiyu, amma insha Allah gobe zan yi tafiya in na dawo zaki ganni har gida, nima zan samu ladan. Dama akwai abinda yake rike zumuncin mu amma yanzu tunda ya kau zamuyi zumunci sosai" tace "ban gane ya kau ba, me kike nufi"

Na yi shiru ina wasa da yatsuna sannan nace " baki ganni a gidan mu ba?" Ta gyada kai. "Naje can gidan naki ai tun kwanaki mai gadin ku yace min bakya nan wai kina gida. To yan zu kuma nazo bayan layin ku sai nace bara in shigo in gani ko kina nan"

Na danyi murmushi "mun rabu ai. Mun rabu da Umar" ta bude ido cikin mamaki sannan tayi salati. "Kun rabu fa kika ce Jidda? Umar fa? Umar ne ya sake ki?" Na girgiza kai. "Ni na nemi Umar ya sake ni. He didn't have an option, it was either ya sake ni daga ni sai shi sai waliyyan mu ko kuma in kai shi court ya sake ni a gaban duniya. He chose the first option"

Ta rufe idonta ta bude "innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Allahu ya sa hakan shi yafi muku alkhairi baki daya" nace "ameen. Tare da ke"

Tayi dariya "ni kam alkhairi ne ma alhamdulillah. I have never been this happy. It was hard at first musamman da yake ban samu support na iyayena ba but a hankali sai suka fara fahimtar it was for the best, musamman da wasu daga cikin halayen Bashir suka fara fitowa yanzu a fili, duk da dai nasan ba za'a taba fahimtar how deep yake a cikin harkar ba. Iyayensa ma basu yarda ba sunce sharri ne but ni na san cewa sun sani ko ba su san komai ba sun san something kawai suna pretending cewa basu sani ba dan gaskiyar sai ta fi musu da ci akan karyar"

Na gyada kai cikin fahimta. Sannan nace "ke kuma fa? Me kike ciki yanzu?" Tayi murmushi. "Na koma school. Dama shi ya hana ni kuma I was naive na dauka it doesn't matter ko nayi karatu ko banyi ba tunda ina ganin zai sauke nauyin sa. But now I am wiser" na gyada kai. Allah yasa haka shi yafi mana alkhairi

Da dare su Yasmin suka dawo, tun kafin in tambaye su Asad ya fara bani labari "mommy munje gidan Mama, nace mata ba zan zauna a gidan ta ba tunda tafiya take yi tana barin mu muyi kuka, kuma sai muka je hospital muka ga Daddy bashi da lafiya ana yi masa allura"

Na juya ina kallon Yasmin nace "me yake damun daddyn naku?" Ta zauna tace "nima ban sani ba. Yana kwance muka ganshi kuma baya magana" nayi shiru ban ce komai ba.

Jirgin mu da safe zai tashi dan haka da wuri muka fita. Muka je airport muka gama komai muka zauna jiran lokacin tashin mu. But hankalina was somewhere else. I want to know yanayin jikin Umar da kuma abinda yake damunsa, nayi tsaki ya kai cikin charbi. A karshe dai na dauko wayata na kira number dinsa still switched off. Na sake wani tsakin na ajiye wayar. Mintuna kadan kuma sai na sake dauka na nemo number din Mufida na kira. Remembering cewa tunda na bar gidan Umar bamu yi waya da ita ba.

Sai da kiran ya kusa katsewa sannan ta dauka. Muryarta sounds far away kamar wadda ta tashi daga bacci ko kuma wadda take cikin damuwa. Na lumshe idona na bude. She was and still is a very good friend of mine. Tun ranar da muka hadu Allah ya hada jinin mu but now? Now I don't even know menene a tsakanin mu.

"Mufida?" "Na'am Jidda. Ya kike? Ina mamana da babana? (Yasmin da Asad) nace "lafiya lau suke. Ya kike? Ya mai jiki?" Ta danyi shiru "da sauki" nace "uhmm. Me yake damunsa ne?" Tace "some kind of a heart problem" na lumshe idona na bude "Allah ya bashi lafiya. Dama yau zamu tafi ne, muna airport already. Shine yara suke so suyi sallama dashi and his phone is not going through. Ko zaki hada su suyi magana if that is possible?"

Tace "bana gari ai. Ina Kaduna. Sai dai ki kira Mama ko Yaya Mubaraka. Na san daya tana tare da shi" nace "ohh okay. Shikenan babu komai. Thanks. In kunyi waya kawai kya ce muna duba shi ni da yara"

Sai na katse wayar na rike ta a hannuna ina jujjuya ta. Ciwon zuciya? Umar? Nayi ajjiyar zuciya. Allah ya bashi lafiya.

Mintuna basu fi biyu ba sai ga kiran Mama ya shigo wayata. Kamar ba zan dauka ba kuma sai na dauka na gaishe ta. Ban tambayi mai jiki ba. Tace "Mufida ta kira yanzu tace in kira ki wai kin kira kina tambayar jikin Umar ko? Jiki da sauki Jidda. Alhamdulillah jiya da dare ya farka. Yana ta neman ki da yara. Ban dauka zaki kula shi ba shi yasa ban neme ki ba. Bara in bashi wayar ko a waya ne ku gaisa"

Na juya ido na. Did I say ina son magana da shi?

Some part of me wanted to cut the call but sai na kasa. And I heard muryar Mama "Umar Umar Umar. Jidda ce a waya. Ta kira zata duba ka ne"

And I asked myself "ni na kira da ma?"

Sai kuma naji muryar sa. Can kasa "Jidda?"

Sai nayi magana cikin sauri

"Hello Umar ya jikin? Ashe baka da lafiya. Dama muna airport ne zamu tafi sai su Yasmin suke son yi maka sallama. So, ba wai ni na kira ba. But ina maka fatan samun sauki"

Na dan jira kadan, kamar ba zaiyi magana ba sai kuma murya can kasa yace "ina zaku je?" Nace "baka sani ba? Na dauka ka sani tunda su Baba sun sani. Zamu je Ethiopia ne. Muna airport ma already. Ga yara zasu yi maka sallama. Allah ya baka lafiya" ban jira amsar sa ba na mikawa Asad da Yasmin da suka saka ni a gaba suna jin abinda nake cewa. Nan da nan suka fara rige rigen yi masa magana yayin da ni kuma na rufe idona ina jin tawa zuciyar tana yi min nauyi. Ban san ma sun gama ba sai gani nayi sun miko min wayar. Na saka ta flight mode sannan na saka a jaka ta. Mintuna kadan aka kira jirgin mu.





*Wannan littafin na siyarwa ne bisa amana idan baki siya ba kar ki karanta idan kuma kin siya kar ki sharing idan kika yi kin ci amana kuma ke da Allah*

*The New Life*

**

Sai dana tabbatar Asad da Yasmin da kuma Amira sun zauna properly sannan nima na zauna na saka seat belt na kwantar da kaina na rufe idona, all I can see a idona shine Umar a kwance a kan gadon asibiti thinner than last ganin da nayi masa, na'urori a zagaye da shi. Sai da naji jirgin ya fara tashi sannan na bude ido na ina kallon kasa har muka daga cikin sararin samaniya ina kallon garin kano, and I thought, tabbas abinda na fada gaskiya ne, tabbas rabuwa da Umar itace jarabawa ta ba wai zama da shi ba.

Awa biyu ta kaimu garin addis ababa, Mun tarar da auncle Muhammad da matarsa sun zo airport daukar mu daga nan muka tafi gidan sa inda acan Umma take a lokacin.

Murnar ganin Umma da yanuwana ya saka naji duk tunane tunanen da na kwashe entire journey din ina yi sun dakata, na fara murmushi da dariya tare da karbar kulawa da soyayya daga yanuwana duk da dai ban samu hakan daga gurin mahaifiya ta ba wadda tayi kicin kicin taki kula ni sai Amira taje yiwa magana da kuma su Yasmin.

Na fahimci har yanzu ni mai laifi ce a gurin ta, na fahimci yaki na ba'a cire Umar completely daga zuciyata kawai yake ba, yaki na ya hada da kokarin samun goyon bayan mahaifiya ta. Dan a matsayin ta na uwa ta fushin ta a gare ni masifa ne.

Kwanan mu biyu da zuwa na fahimci target din ta, she was set on making my life miserable maybe a ganin ta hakan ne zai saka in zabi komawa gidan Umar. Duk motsin da nayi sai ta gaya min magana. And I realized ita a gurin ta kamar zinar da Umar yake yi ba wani babban laifi bane ba wanda ya chanchanci a rabu da shi, a ganinta sauke hakkinsa da yake yi a gare ni ya shafe wannan zinar da yake yi. She kept saying

"Mata nawa ne suke neman samun irin naki? Wata matar in dai zata samu miji kamar Umar to babu ruwanta da bin kwakwkwafin sai ta san abinda yake aikatawa kuma ko ta sani ma ba zata daga hankalin ta ba ballantana har ta nemi saki. Bana so inyi miki baki Jidda, amma ina jiye miki irin mijin da zaki aura nan gaba sai kin yi kukan rashin Umar"

And I remembered some of the comments na mutane lokacin da na nemi shawara a social media, I realized ba ita kadai ce take da irin wannan tunanin ba matan mu da yawa na hausawa suna da irin wannan tunanin. Su a ganin su indai miji yana basu ci da sha da sutura shikenan ya gama musu komai, wannan kuma shi yake kara bawa maza masu halin Umar license na cigaba da halin su, matan sun mance cewa aure is beyond wadannan abubuwan, far beyond.

Dan ni dai a yanzu personally I rather marry wanda baya wadata ni da wadannan abubuwan amma zai kiyaye mutuncin sa da nawa a zahiri da kuma badini than to marry mai irin halin Umar, in har rashin wadata ne sai mu hadu mu rufa wa juna asiri, in kuma rowa ce sai in dauke kaina daga abinda kake dashi in nemi na kaina.

Tunda naje ban ma saka layi a waya ta ba saboda ina bukatar quietness and peace, da wayar Umma muke gaisawa da mutanen gida, but ban manta da rashin lafiyar Umar ba kuma ina yi masa addu'a sometimes kuma ina saka yayansa suyi masa addu'a duk sanda suka yi sallah kamar yadda nima har yau ban daina addu'ar zabin alkhairi a rayuwata ba da neman Allah ya sassauta min abinda nake ji a zuciyata ya sanya min nutsuwa.

Satin mu daya a Addis Ababa muka tafi garin Nazret inda nan ne tushen su Umma daga tribe din Oromo anan kusan dukkan yanuwansu suke auncle Muhammad ne kawai da few suke a Addis Ababa suna aikin gwamnati. Sai da na bar inda Umma take sannan na samu nutsuwa na huta da maganganun da take gaya min kullum, sai a lokacin hankali na ya kwanta na fuskanci halin iddar da nake ciki. Wannan yasa sanda Amira zata dawo Addis Ababa sai na hado ta dasu Yasmin ni nayi zamana can gidan auntyn su Umma wadda take a matsayin kamar kakarmu kenan a can. Daga gidan ta kuma sai gidan yarta Nuru wadda take cousin din su Umma kenan kuma tana da yaya da yawa maza da mata ciki har  da babban danta mai suna Salem da kuma yarta mai suna Aida da take kusan sa'a ta kuma muka saba da ita, dan haka nafi jin dadin zaman gidan ta

A haka time yayi ta tafiya har na kammala idda ta kuma a lokacin ne muka fara shirye shiryen dawowa Nigeria musamman saboda sakon da aka aiko min dashi daga gurin aiki cewa ana bukatar ko dai in dawo bakin aiki na ko kuma inyi resigning, wanda a gare ni is not an option a yanzu dan ina tsananin buƙatar aikina. Wannan ya sa muka fara shirin dawowa gida.

Now; Tunda muka je na fahimci kudurin da Umma da yanuwanta suke shiryawa, suna so ne su hada aure a tsakanin mu mu yan Nijeriya da kuma yanuwan mu da suke Ethiopia dan su karfafa zumuncin tsakanin su.

"Idan ba'a samu auratayya ba duk ranar da mu iyayen muka mutu to yayan mu ba zasu yi zumunci ba"

Wannan burin nasu sun dora shine akan Amira, inda suka samo mata responsible samari har guda biyu,  daya cousin din su ne mai suna Djimon (pronounced as Jah-moh) sai kuma Salem dan Aunty Nuru. Daga baya kuma sai wani family friend a Addis Ababa shima ya fara nemanta. Sai dai kuma inda aka samu matsalar shine ita hankalinta yafi karkatuwa akan shi family friend din su kuma su Umma sunfi son dan uwa dan dama saboda zumunci suke son hadin. Wannan yasa Amira a tsaka mai wuya, ni kuma na bata shawarar neman zabin Allah duk da nima nafi son ta da Salem dan na yaba da tsarin sa da yanayin sa, kar kuma ma ayi zancen kyau dan dama mutanen Ethiopia duk duniya ta shaida baiwar kyawun halitta da suke da ita mazan su da matan su.

Sai bayan da na gama idda ne sannan maganar mutuwar aure na ta fara fita a cikin yan'uwa, da yake tun zuwan mu kadan ne suka sani, sai nan da nan cousins din Umma suka fara mata suggesting "ga Jidda nan itama? Ba sai a gwada duk biyun ba mu ga wadda Allah zai tabbatar mana?" Inji Aunty Nyala matar auncle Muhammad da tazo ta tarar muna ta shirye-shiryen kayan mu.

Na rufe ido na ina ambaton Allah a raina da fatan kar idea din ta shiga kan Umma sai kuwa naji tace "wacce Jidda? Rufa min asiri. Indai wannan yarinyar ce ba za'a gyara zumunci da ita ba sai dai a kara bata shi, wanda ta aura ma tana son sa yana sonta ta matsa ya sake ta saboda kaddarar da Allah ya dora masa ballantana wanda aka hada su? Ai ina jin in an hada da ita ko shiga yayi wadda bata yi mata ba cewa zata yi sai ya sake ta"

Na ajiye kayan hannuna ina jin hawaye yana taruwa a gefen idona. Sai ta fara bawa Aunty Nyala labarin irin soyayya da kuma kulawar da Umar yake yi min amma na guje shi, sai kuma ta rufe laifinsa ta kira abinda yake yi da sunan kaddara. Aunty Hajar ta juyo kaina tayi ta yi min fada tana girmama laifina musamman saboda su din mutane ne masu rikon aure sosai. Na yi shiru ina jinta hawaye yana zuba a ido na. Ban san me yasa mutanen mu suke yiwa kaddara wata irin fahimta ba, ba komai ne mutum zai aikata bisa son zuciyarsa sannan ya kira shi da kaddara ba.

Kamar yadda Diyam ta fada min ranar nan kuma na amince, idan har komai mutum yayi kaddarar sa ne me yasa akayi wuta da aljanna? Idan har mutane zasu ke yin sata, kisan kai, rape, kuma suna jingina shi da kaddara then me yasa muke da shari'ar da take yanke hukuncin ga mai laifi? Me yasa ba za'a barsu ba kawai ace ai kaddarar su ce babu yadda zasu yi su kauce mata?

Idan har zinace zinacen da Umar yayi shekara da shekaru yana yi mai yasa a shariance za'a jefe shi da ransa a musulunce?

Life is all about the choices we make. Shine ake kira da jarabawa. Allah zai jarabce ka da son abun wani dan yaga zaka sata ko kuma zaka fi karfin zuciyarka. In case of Umar kuma jarabawar sa shine sha'awar mata, dan Allah ya ga zai iya daurewa yaci jarabawar sa ko kuma zai bi bodily cravings dinsa ya fadi jarabawar? And he chose to fail, his choice, babu ruwan Allah, babu ruwan shaidan, babu ruwan kaddara.

Bayan ta tafi ne sai na sauko daga kan kujerar da nake zaune na durkusa a gaban Umma. Tayi kamar bata ganni ba ta dauko wayarta ta kira Aunty Afia a Nigeria ta na bata labarin maganar Aunty Nyala da kuma amsar da ita ta bata, suka cigaba da kushe maganar tare da kara girmama laifina. Ni kuma ina durkushe ina fama da zafi a zuciyata.

Ba wai hadin da suke magana akai nake so ba har nake jin haushin kin amincewar su, a'a ni idan da sun karbi hadin ma zanyi iyakacin kokari na gurin tsayar da maganar saboda babu aure

95 / 106