Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
tsaki ina jin zuciyata tana min zafi. Gwara ma in gaggauta barin kasar nan dan a kowanne lokaci zai iya cewa ya mayar da ni tunda minutes kadai bayan saki ya fara min bita da kulli.
Har na ajiye wayar sai kuma na dauka na yi masa reply
"Ba wai ina so inyi proving zan iya rabuwa da kai bane ba. Ina so inyi proving zan iya rayuwa babu kai. And that's what I will do"
Na tura masa tare da jan dogon tsaki.
Yasmin ta bini da kallo.
"Mommy komawar zamuyi gida?"
Na kalle ta ina jin kamar in sharara wa kyakykyawar fuskar ta mari, sai kuma nayi murmushi nace "guess what? Tafiya zamuyi. Jirgin sama zamu shiga muje garin su Muƙaffa" (dan auncle Muhammad)
Ta bude ido cikin murna sai kuma ta fita a guje. Nabi bayanta da kallo sannan na dawo da kallo na kan wayata.
Now I have opened a new chapteri n my life. Page of zawarci. Page din da mata da yawa suke sacrificing rayuwarsu saboda tsoron budewa. Ko menene a ciki? Allahu a'alam. Amma abinda na sani shine zanyi iyakacin kokari na na ganin cewa na karance shi daki daki kuma na bi shi cikin nutsuwa har Allah yayi min jagora in samu kyakkyawan rabo, ko a duniya ko kuma a lahira.
*wannan littafin na siyarwa ne bisa amana, idan baki siya ba kar ki karanta idan kuma kin siya kar ki sharing in kika yi kin ci amana kuma ke da Allah*
*The Divorcee*
Na koma da baya na kwanta akan katifar tare da runtse idona, trying so hard inga cewa ban cigaba da kukan da nake yi ba amma ni kaina na san ba zan iya hana kaina ba, sai dai har cikin zuciya ta ban tantance kukan da nake yi ba, na murna ne? Dan for the past few weeks babu abinda nake so irin rabuwa da Umar, ko kuma na bakin ciki ne dan for the last seven years Umar has been a greatest part of my life. Shi ya saka ni a school da kudinsa da karfinsa da jajircewar sa har na samu aikin da a yanzu shine zai rike ni a zaman zawarcina, ya soni iyakacin so, soyayyar da mata da yawa suke kwadayin samun irin ta a gurin mazajen su, but then ya ci mutuncina iyakacin cin mutunci, yayi min abinda ya sakani tunanin anya kuwa soyayyar gaskiya ce yake nuna min ko kuma ta fatar baki ce? The betrayal, the emotional blackmail, the lies. Some of the things I went through a hannun Umar in na tuna har mamakin yadda nayi surviving dinsu nake yi. Babu wanda zai gane sai wanda ya samu kansa a matsayi na. I mean it is one thing for mutumin da baya nuna maka yana son ka yayi betraying dinka and it is totally a different thing ace mijin da yake nuna duniya kamar babu mace kamar ka ya kuma kwanta da friend dinka, da niece din ka ya kuma kwanta da yar aikin ka a cikin gidan ka.
Tabbas babu wanda zai gane halin da zuciyata take ciki a lokacin sai wanda ya shiga matsayin, bana kuma yiwa kowacce mace fatan shiga wannan matsayin.
Ina cikin tsiyayar da hawayena a cikin pillow naji muryar Abba yana kiran sunana, na mike zaune ina jan hanci sannan nayi kokarin amsawa da dasashshiyar murya ta, "kina ina ne wai? Ko ta zama kurma ne?" Na ja dankwali na na goge hawayena sannan na mike ina kara daga murya ta gurin amsawa, kafin in fita daga dakin sai gashi ya shigo, ya tsaya a bakin kofa yana kallona, da alama ya lura da chanjawar idona. Ya dan dauke kansa kadan yana kallon gefe ni kuma na durkusa a gabansa ina kara jan hanci a kokari na na ganin na rike sauran kukan da yake kokarin sake balle wa. Yace "kiyi hakuri, kiyi addu'a. Sannan kuma ki shirya gobe kuje da gwoggon ki Habibah ki debo muku sauran kayan sawarku ke da yara da kuma abubuwan amfani. Sai kuma ki karasa muku shiri ke da yara tare zaku tafi Ethiopia, kakannin su sunce zasu biya musu kudin jirgi".
Na gyada kai da sauri. Har ya juya ya fita kuma sai ya dawo yana nuna ni da yatsa yace "saura kuma ki kwanta kiyi ta koke koke kamar Aysha ta mutu, in yaso hawan jinin da ya riga ya saka miki ya tashi ki mutu shikenan bashi da asara".
Ya fita yana maganganu kasa kasa. Na mike na koma na zauna a bakin katifa ina cigaba da gitsitstsira strings din dana tsinka a hannun Umar. Sai naji ina mamakin Abba a raina, ban taba tsammanin samun goyon bayansa akan maganar nan ba, I thought ba Mammy ba ko Amira Umar ya nema Abba zai ce ne in koma in cigaba da hakuri ina biyayyar aure. Sai na fahimci abinda Diyam ta gaya min ranar nan cewa Abba yana sona, kuma duk tsaurin sa a tunaninsa yana yi ne for our own good bai san yadda rayuwa ta koma ba, ya dauka mazan yanzu irin na da ne, ko a mafarki bai taba tsammanin Umar zai iya yin abinda yayi ba.
Ina nan zaune aka kira sallar azahar na tashi na koma falon Umma na tarar daga Asad har Yasmin sunyi bacci, sai na tsaya ina kallon su ina lissafin yadda rayuwar su zata kasance, abinda na tabbatar shine their life will never be the same amma gwara hakan sau dubu akan yadda rayuwar tasu zata kasance idan da ace na zabi na cigaba da zama da babansu. Mai zai faru ranar da suka kama babansu in the act a cikin gidan su? Ko kuma su kawo kawarsu gidan ya nema dan tabbas zai iya, ko kuma Yasmin ta zama budurwa shaidan din da yake kwadaita masa sauran mata ya kwadaita masa ita. Dan tabbas idan zina ta ci zuciyar mutum har muharramansa yake sha'awa.
Na girgiza kaina da sauri ina kara tabbatar wa kaina dacewar decision dina. Nayi alwala nayi sallah na gode wa Allah akan niimomin da yayi min sannan na nemi alkhairi a cikin wannan sabon babin na rayuwa da na bude.
Ban jima da idarwa ba Farhan ta shigo dakin, fuskarta fal da murmushi, daga gani bakin ta a cike yake da labari. Ta zauna akan kujera tana kallona nima ita nake kallo sai tayi dariya tana girgiza kai. Na gara zamana ina kallon ta nace "bani in sha" ta sake murmushi. Sai kuma ta tabe baki trying to hide her excitement tace "wai wannan din nan ne, yace wai in na amince yana son ya fito maganar aure" na dan bata fuska "wanene wannan din nan?" Ta juya ido "Sadiq yake ko wa? Wannan dai dan uwan kawar nan ta ki" na dan yi murmushin da bai kai ciki ba duk da ina matukar yi mata murnar samun miji kamar wannan amma kuma zuciyata tana cikin zullumin nima tawa rayuwar nace "munafuka, har da wani nuna kamar baki wani damu da shi ba ko? Har da wani pretending baki san sunan sa ba ko?"
Tayi dariya tana juya ido tace "dallacan, irin jan ajin nan ne fa nake yi" na taya ta dariyar, duk da dai tawa ta yake ce nace "to ai bani zaki ja wa ajin ba shi zaki jawa" ta zauna sosai. "Amma gaya min gaskiya, yayi miki?" Na dauke kaina daga kan ta ina kallon sallayar da nake kai na tuna da sanda nayi mata makamanciyar wannan tambayar akan Umar, sai nace "it doesn't matter idan yayi min ko bai yi min ba, what matters is idan yayi miki tunda ke zaki aure shi bani ba. Mu namu shine muyi muku addu'a, Abba kuma nasa shine ya bincika halayyar sa da nagartarsa. Idan ma nace baiyi min ba bana jin hakan zai hanaki auren sa kamar yadda nima sanda kika ce min Umar bai yi miki ba ban fasa aurensa ba".
Ta sauko daga kan kujerar ta zauna a kusa dani tana girgiza kai tace "noooo. Indai kika ce min baiyi miki ba zan tambaye ki dalili, idan kika gaya min dalilin kuma naji nai karfi ne tabbas zan rabu da shi, I waited for years kafin in same shi and I can wait for more years har in samu wani. It is not as if ina yi masa irin mugun son nan" na gyada kai na cikin fahimta. That was what I lacked a lokacin soyayyar mu da Umar, nayi masa mugun so, forgetting fadin Manzon Allah kan cewa kar mu zurfafa soyayya kuma kar mu zurfafa kiyayya.
Na dan dafa ta "wasa nake yi miki ke. Personally yayi min. Ban ga wata makusa ba a tare da shi a zahiran ce. Ina ganin ki fada masa ya fito din. Allah yasa albarka a ciki"
Sai ta zagaye ni da hannayenta cikin murna tace "ameen summa ameen sister. Nagode. You are the best sister in the whole world" nayi dariyar yadda tayi maganar dramatically sannan ta tashi da sauri zata fita sai na kira sunan ta. "Farhan" ta juyo tana kallona sai na ga ta yar da jakar hannunta ta tana kallona. "Lafiya?" Na sunkuyar da kai na ina jin mugayen hawayen nan suna kokarin dawowa nace "dazu Umar yazo, tare da iyayensa. Ya rubuta min takarda. Saki daya. Mun rabu da Umar Farhan"
Ta zauna dabas a gaba na. Na danyi murmushi tare da saka gefen hijab dina na goge hawayen daya taru a idona nace "babu komai. Haka rayuwa take. A ranar da ake haifar wani a ranar wani yake mutuwa. A ranar da wani yake warkewa daga ciwo a ranar wani yake kwanciya. A ranar da wani auren yake mutuwa a ranar ake dasa foundation din wani. Fatana shine Allah yasa hakan ya kasance alkhairi a gare mu baki daya".
A ranar da dare na kira Umma na gaya mata abinda ya faru. Na kuma kira Aunty Afia itama. Sai dai dukkan su baji dadin yadda suka karbi maganar ba dan har yanzu suna nan kan bakansu na cewa dadai na xauna na cigaba da hakuri da zai fi.
Maganganun damuka yi da su ya saka naji duk zuciyata tai babu dadi, nafara questioning decision dina. Ina bukatar someone to assure me cewa akan dai dai nake. Sai na kira Diyam da number din ta ta canada data kira ni da ita ranar nan.
Sai bayan da kiran ya shiga sannan na fara adduar Allah yasa time din is convenient tunda ban san time difference din dayake tsakanin mu ba.
Luckily sai gata ta dauka. Muka gaisa. And I told her abinda ya faru. Kamar yadda nasaka rai sai ta kwantar min da hankali ta kuma jajanta min tare da fatan alkhairi. Na kuma gaya mata fear dina na tsoron rayuwar da take gabana, rayuwar zawarci. Sai ta kwantar min da hankali da cewa babu komai.
"In dai kin saka Allah a gabanki to kin wuce fargaba. Kin samu support din Abba, a hankali kuma sai kiyi kokarin fahimtar da Umma itama. Kuma ke kinji dadin ki ma kin yi karatun ki kina aikin ki kina samun albashin ki ba zaki tagayyara ba, babu wanda zaki dorawa responsibility sai dai maki rage musu nasu responsibilities din, dama shine amfanin aikin ko sana'ar. A shawarce kuma yanzu ko kin gama idda ki ajiye batun aure a gefe in dai ba karfin sha'awa ne dake ba kina gudun fadawa halaka, ki bari kiyi healing sosai ki nutsu kuma kiyi addu'a sosai kar kiyi rushing sai kiga Allah yayi miki jagora ya baki wanda ma baki taba tsammani ba. People will talk, no matter what you do, just let them talk, zasu yi su gama ne dan kansu. In da kin tsare mutumcin ki shikenan. Shi Allahn dakike yi da shi yana ji kuma yana gani".
Washegari kamar yadda Abba ya fada sai ga gwoggo Habibah tazo a motar babban danta yaya Kabiru. Na samu na bar su Asad a tare da Amira saboda bana son zuwa gidan su dasu dan kar su zama emotional, musamman idan suka hadu da Umar a gidan. Sai muka tafi tare da Farhan da yayana Abbah. A hanya ina ta addu'a da kuma fatan kar Allah ya hada ni da Umar a gidan kuma cikin ikon Allah bamu same shi ba sai maigadi shi kadai a bakin gate, yana ganina ya taho da murnar sa "Hajiya! Sannu da zuwa. Ina su uwar masu gida (Yasmin)" nayi murmushi kawai sai Farhan ce ta bashi amsa da cewa suna gida. A rufe muka tarar da falon, da yake da akwai key jaka ta sai na bude mana, muna shiga sai ga mai gadi da kayan sharar yana wai yazo zaiyi mana, gwoggo Habibah ce tace masa ai ba zama zamuyi ba kaya muka zo diba, sai ga shi yana sharar kwalla.
Na jima a tsaye ina bin gidan da kallo, gidan dana yi tunanin nanne zan kare rayuwata tare da mijina da yayana, gidan da nayi tunanin sai dai a fitar da gawata daga cikin sa yau gashi ni da kaina na zabi fita daga ciki. Na bude corridor na shiga dakina, kayan Umar ne duk a barbaje a dakin, wannan yasa nayi tunanin anan ya dawo da zama.
Farhan ta shigo muka sauke akwatinan saman wardrobe muka fara zuba kaya, ina yi ina tattare wa Umar na sa, ignoring kamshin sa da yake jikin kayan. Sai da muka gama kwasa tsaf, na zagaya sauran dakunan gidan ma na daukar mana abinda nake tunanin zamu bukata. Sauran kuma duk muka jirge su muka hade su waje daya, kitchen ma duk muka zuba kayan a cikin kwalaye da buhunhuna. Furnitures ne nace da gwoggo Habibah "shi ya siya wadannan, nawa sune yanzu a dakin Umma" ta daga kafada "sai menene kuma? Ai tunda ya siya miki sun zama naki" yaya Kabiru yace "a'a kar a taba masa saboda gudun wulakanci, duk abinda shi ya siya a bar masa kayansa idan ya bar mata ne to shi da kansa zai aiko da su ko kuma yace azo a dauka"
Kusan wuni mukayi, sai yamma muka gama kuma har muka gama Umar bai zo gidan ba, muka hade duk kayan da suke nawa a cikin bedroom dina muka rufe, sauran kuma muka bar komai a inda yake. Na dauki suturar sa dana tarar a bedroom dina na kai masa nasa, sai na tsaya ina kallon dakin, zuciyata tana bugawa da karfi my head blank, sai kuma na ajiye da sauri a bakin gado na kife frame din family picture din mu na fito da sauri daga dakin.
A bakin gate gwoggo Habibah tace da mai gadi "idan mai gidan yazo ka gaya masa mun zo mun debi kaya mun kuma hada sauran, za'a aiko da mota ta kwashe" yace "ai Hajiya tun jiya da safe da ya fita har yanxu bai dawo ba, ina ta tunanin ma ko lafiya dan kwanakin nan kullum a gida yake kwana yake wuni babu inda yake zuwa" gwoggo Habibah ta tabe baki "lafiya ce ai take yin shiru, in da wani abu ai dole za'a sani. Allah ya kyauta" daga haka muka koma gida.
A ranar da daddare Hajiya ta shigo har daki tayi min jaje, tana ta sussunkuyar da kai, na amsa mata babu yabo babu fallasa, sannan kuma yanuwana suma kusan kowa yayi min waya ya jajanta min wasu daga ciki ma har gida suka zo, ban sani ba ko har zuciyar su suke alhinin abin ko kuma munafunci ne oho, amma ni ban damu ba dan nasan bana nufin kowa da sharri a zahiri ko badini, kuma na yarda da cewa duk mai nufi na da shi kansa zai koma kamar yanda wancan sharrin da suka kulla ya kwance a tsakiyar kansu.
Babu bata lokaci shirin tafiyar mu ya kankama, dama rashin isassun kudin da zan tafi da yara ne ya saka nake ta delaying abin amma yanzu tunda an dauki nauyin mu bani da stress, na sami Yaya Tahir da Abba na roki ina son mu tafi da Amira dan itama ta ga yan uwa kuma naci sa'a Abba ya bari.
Kayan da na dauko wanda zamu tafi dasu kawai na diba sauran na jibge su a dakin Umma. Na san maganar mutuwar aure na a yanzu ta gama zagaya yan'uwa da makota, na san da cewa masu zuwa gidan da yawa suna kallo na da abin but I don't care, zasu yi magana na sani, zasu yi surutu na sani, kamar kuma yadda na sani cewa abinda ya faru dani halal ne ba haram na aikata ba, na san kuma cewa mutuwar aure ba'a kaina aka fara ba ba kuma a kaina za'a kare ba, kamar yadda babu wanda yasan ranar mutuwar sa haka babu wanda yasan makomar auren sa.
Matsala ta farko da na fara fuskanta kuma dama ita ce matsalar da na saka ran zan fuskanta ita ce matsalar yara na. Kullum zancen baban su, musamman da suka ga alamar munje gidansu mun debo kaya. Kullum sai sun ce in kira musu shi a waya ni kuma sai in ki in kuma yi musu tsawa su rabu da ni. Shima kuma bai ta taba kira ba.
Ranar nan sai ga Yasmin ta sako kaninta a gaba sun zo gurina. "Mommy tunda ke ba zaki kira Daddy ba dan Allah in dauki aron wayarki in kira shi?" Na lura tsoron yadda ranar nan da ta kira shi na kusan dukanta take yi. Na bude mata wayar na mika mata "kira shi" da sauri ta karbi wayar ta nemo number dinsa ta kira ta saka a kunne, sai kuma ta bata rai tana kallona tace "wayar ta ki yi mommy, ko ta lalace?" Na karba ina kallon sunansa "Umarul Faruq" sai na shiga edit na chanza sunan zuwa "daddyn Yasmin" sannan na kira amma sai naji wayar a kashe. Na ajiye nace "wayar sa a kashe take Yasmin" sai suka bata rai amma kuma suka hakura.
Sai dai ni a nawa bangaren ina jin babu dadi a raina. Duk da babu aure tsakani na da Umar amma shi din wani bangare ne na rayuwata,