Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
sannan ya sake dawowa, daga alama gurin yake gyarawa. Na koma na kwanta, a lokacin ita kuma Yasmin ta farka ta fara tsanyara min kuka kamar zata shide, na gwada feeding dinta amma babu komai a nonon, na chanza mata diaper na sake mata kaya amma bata yi shiru ba. Time din lokacin around 5pm
Ya same dawowa. "Dan girman Allah Jidda ki bude kofar nan" nayi kamar ban ji shi ba sai kuma yace "Okay. Ba kya son ganina I get it, zan fita daga gidan in dai har zaki fito ki ci abinci. Kinji?" Nan ma shiru sai Yasmin da take ta kukan ta.
Jima wa kadan naji fitar sa sannan naji ya tayar da mota duk da dai bana iya hango shi amma naji ya fita daga gate. Na bude kofa na fito da Yasmin a hannuna, ya gyara corridor din, sai jikin bangon daya baci da maiko, na fita falo na ganshi fes, har da jona incense burner ya saka turaren wuta a ciki kamar yadda ya ga inayi.
Na wuce falon na shiga kitchen shima a gyare, sai tukwanen da aka jera su duk sun bushe da indomie sun ki fita. Na harare su na dauko wankakkiya na dora na dafa ruwan zafi na hada tea na koma falo na zauna na sha sannan na dan huta nayi feeding Yasmin sannan na goya ta na koma na dafa taliyana jajjaga attaruhu da albasa nayi sauce na zuba na dawo falo na ci sannan na juye sauran a flask na kai dakina, na dafa ruwan zafi shima na hada da kayan tea na kai dakina. Sannan na shiga na gyara dakin na wanke toilet na kwantar da Yasmin na rufe mana kofa na shiga wanka.
Sai bayan magrib naji dawowarsa. Straight nan ya taho ya gama babatunsa a kofar daki ya hakura ya tafi. Zuwa bayan ishai naga an kira ni da new number kuma jikina ya bani shine dan haka naki dauka. Ya cigaba da kira sai na saka wayar a flight mode na cigaba da game din da nake yi.
Zuwa jimawa ya sake dawowa. "At least ki bani Yasmin in dauke ta, kin san dai nima yata ce ko? Kin san inada hakki a kanta ko?" Na mike zaune.
"Ka tafi gurin Zuwaira ta haifa maka wata yar sai ka dauke ta. Ni tawa yar babu datti a jikinta, kuma zan nesanta ta da daddaudan mutum irin ka"
Daga nan bai kara cewa komai ba kuma bai kara yi min magana ba har nayi bacci.
Da safe ya kara dawowa, ni kaina lokacin zaman dakin ya ishe ni ji nake kamar zanyi dan karamin hauka, ga Yasmin ta ishe ni da kuma. Yayi knocking yace "Jiddo kun tashi? Me kike so kiyi breakfast dashi in soya miki irish ko in hada miki sandwich. Na siyo bread din nan da kike so na Grand Square"
Na juya ido na. Wannan mutumin me ya mayar da nine? Bayan wawiya ya kuma mayar da ni kwadayayyiya? Zuwa jimawa ya sake dawowa. "Zan fita to. Zan zauna a bakin gate ki fito ki ci abinci kiyi kallo ki mike kafar ki dan gidan ki ne kinji?"
Na sake juya ido na, ni mamaki yake bani pretending as abinda yayi is a minor mistake wanda kawai zamuyi kiss and make up mu manta dashi. Tabbas zai sha mamaki na, Jiddan daya sani a da ba ita bace ba a yanzu, wannan ta waye, wannan ya wayarda ita.
Sai bayan ya fita sannan na fito. Na dauko rocker din Yasmin na saka ta akai na bar ya a palo na tafi kitchen, akan dining table na ga an ajiye sandwich a ciki guda biyu a orange juice a gefe, a kasan plate din kuma ga takarda
Baby Dove,
"Please ki ci wannan, For I made it with all my love"
Umarul Faruq
Bansan me yasa ba kawai sai naji hawaye, na dauki takardar na gutsitstsira ta na barbada akan sandwich din sannan na juye lemon akai na barsu a bude, ma wuce kitchen na hada golden morn na dawo falo na zauna ina sha a raina ina tambayar kaina me yasa nake ta buya a daki? Shine yayi abin kunya shi ya kamata ya buya bani ba.
Kamata yayi in fito fili in facing dinsa in nuna masa it really is over between us, in Allah yasa ya gani ya fahimta to in kuma bai fahimta ba sai in saka microphone in sake gaya masa.
Ina zaune sai gashi ya shigo, nayi masa kallo daya na dauke kaina. Ya chanza kayan jiya but still ynaa looking rough, ya zagaya da sauri ya dauki Yasmin da take baccin ta ya daga ta sama sannan yayi planting kisses all over her small face "God! I miss you so much my cutie pie"
Ta fara mutsumutsun zata yi kuka sai yayi sauri ya ajiye ta ya fara jijjiga ta, "sorry sweetheart. Daddy ya tashe ki ko? I just wanted to kiss your little face that's all"
Sai ya dawo ya zauna a kujerar datake kusa da wadda nake zaune, idonsa a kasa yana kallon hannun sa yace "naji dadi da kika fito kika zauna gar kika kunna kallo, ina fatan kuma anytime soon zaki yardamu zauna muyi magana"
Na ja kafafuwana saman kujerar sannan nace "ubana ne ya sayi kujerun da kuma kayan kallon, da kudin fansho. Ohh sorry ashe fa ka sani tunda har ka iya bawa karuwa labari"
Ya mike tsaye yana dafe kansa, fuskarsa tayi ja yace "wallahi wallahi ba gaya mata haka ba, you have no idea yadda raina yake baci in kika fadi maganar nan bayan ni nasan ban fada ba" na mike zaune "ohh really? Ashe da ciwo? Ashe sharri da ciwo? Add that to seeing me naked and lying on someone"
Ya taho taku biyu zuwa gaba na, for a second I thought dukana zaiyi sai kuma ya dunkule hannunsa ya rintse idonsa sannan ya juya da sauri ya bar falon ya shiga dakinsa. Na ja dogon tsakin da na tabbatar ya tarar da shi har dakin nasa sannan na koma na kwanta tare da karo volume din tvn da babana ya siya.
Sai dai maimakon maganar da na gaya masa ta sa raina yayi sanyi sai naji kamar zafi na kara wa zuciyata.
Ina nan kwance har around 12, shi kuma yana daki bai fito ba sai jin sallama nayi, Umma da Farhan. Na tashi da sauri na tafi na rungume Umma ina jin kamar zanyi kuka amma na rike shi, Farhan ta tsaya daga gefe tana kallona sannan tace "tashin hankali. Kinga yadda kika rame kuwa? Skeleton!"
Na shaga wuyana, realising wadansu manya manyan kasusuwa da suka yi min sarka. Umma ta zauna akan kujera tana cewa "ko dai tsoron tsotso ne da ke Jidda?" Na zauna a hannun kujerar da take kai nace "menene tsoron tsotso kuma?" Tace "wadansu in suka haihu sai suyi ta rama, shine hausawa suke cewa tsoron tsotso" na daga hannu "ni bana jin wani tsoro Umma" tayi dariya "ai ba tsoron ake ji ba, kawai dai hausar ce haka".
Farhan ta dauki Yasmin tana yi mata rawa "ka ga uwar ubanta, ƴar fara yar dan balarabe" Ummu ta harareta "in kuma yana gidan kuma fa, ke surutu ne da ke"
Nayi murmushi kawai na gaishe da Umma, tace "yayan ki ne jiya ya zo ya saka ni a gaba wai sai nazo na ganki, nace masa lafiya ya ce wai dai kawai inzo in ganki" na sunkuyar da kaina ina iyakacin kokari na akan kar inyi kuka nace "Allah sarki yaya na, ya damu dani ne kawai, yaga na haihu kuma duk kun watse kun barni ni kadai shine ya damu da ni"
Na fada ina kara jaddada wa kaina cewa gaya matan bashi da amfani tunda ba zata iya yi min maganin komai ba, sai ma damuwa da zata shiga ita ma. Tayi shiru tana kallona, da alama bata yarda da ni ba sai na kirkiri murmushi "ko kuma mafarki yayi kura ta cinye ni"
Farhan tayi dariya, nima nayi ina jin stress dina yana raguwa. A lokacin ne Umar ya bude kofa ya fito da murmushi a fuskar sa amma kana gani kasan iyakacin fuskar ya tsaya. Ya kalle ni sannan ya kalli Umma, da akwai alamun damuwa a ransa. Na dauke kaina na tashi na tafi dauko musu ruwa.
Ya durkusa a gaban Umma ya gaishe ta ta amsa masa da fara'ar ta,and I saw his face relaxed, suka dan tsokani juna shida Farhan sai ya tafi hanyar bakin kofa sannan ya juyo yayi kirana "Jidda, zo mana" naji wani takaici ya kama ni, ban amsa ba amma dole na ajiye ruwan hannu na na tafi.
Na tsaya hannuna rike da labule ina kallon sa kamar yadda shima yake kallona. Ya motsa bakinsa ya kai sau uku amma ya magana. Nace "in koma ciki ne? Important mutane suna jirana" ya sake yin kokarin magana "Jidda. Umma ta zo" sai ya kuma yin shiru tare da shafa fuskarsa.
Na bata rai "kana da abin cewa ne? Akwai maganar da zakuyi da umman ne?" Ya girgiza kai. Na daga kafada "then Allah ya kiyaye hanya" sannan na saki labulen na rufe kofa na koma ciki.
Ga mamaki na bayan tafiyar sa sai naji zuciyata tayi min dadi, muna ta hirarrakin mu da Umma da Farhan, daga baya ma muma shiga bedroom suna ta taya ni sorting kayan barkan dana tara ana ware wadanda ba yanzu Yasmin zata yi amfani da su ba ana adanawa, sannan Umma tana ajiye min wadanda nima zan ke yin barka da su in anyi haihuwa, sannan kuma ta ware wa Farhan, Amira da kuma Hajiya atampopi masu kyau tace in basu, amma ita sai taki dauka tace bata so, ni kuma sai na dauki wasu nace ta kaiwa Aunty da Aira.
Farhan ce ta shiga kitchen tayi mana girki, tazo tana tsokana ta wai in nuna mata food warmer din da zata zubawa Umar abinci, kar ta zuba a wani abun da ba zai ci a ciki ba. Ban kula ta ba har ta gama ta fita. Sai Umma ta tambayeni. "Lafiya dai ko?"
Na kalle ta ina kirkirar murmushi "Lfy lau Umma, kinga wani abu ne?" Tace "duk kin rame Hauwa'u, annurin fuskar ki duk ya kau" na daga kafada "kawai stress ne Umma, ga rigimar Yasmin ga hidimar gida ga karatu da zan koma next week" tace "to a samo miki mai aiki mana? Yar dattijuwa haka da zata ke kula da gidan tana kuma taya ki rainon Yasmin"
Na girgiza kai, ni a raina sam bani da sha'awar yar aiki ko dan ina da muguwar tsafta ne? Gani nake yan aiki zasu yi min kazanta a gida ne ko suyi min wani abun ba dai dai ba. Nace "babu komai umma, zan saba in na kwana biyu, babu komai" tq cigaba da kallo na sai na tashi na shiga toilet duk da babu abinda zanyi a ciki.
Sanda na fito bata nan, sai na fita falo na tarar da ita ta goya Yasmin suna maganada Farhan. Nima na zauna muka cigaba da hirar. A lokacin ya shigo falon da sallama, da ledo ji a hannun sa yana rarraba ido a tsakanin mu sannan ya sake gaishe da umma sai ya tafi kitchen da ledojin.
Banyi niyyar binsa ba na cigaba da zamana sai naji Umma tace "Jidda....." Kafin ta karasa yakira ni "Jidda" na mike ba tare da nace komai ba sai Umma ta kama fada "shashancin banza kenan. Mijinki ya shigo baki bishi kinji me yake bukata ba kuma yayi kiranki ba zaki amsa ba?" Kafin inyi magana ya sake kirana "Jidda"
Na amsa "gani nan na taho fa" na shiga na same shi da ledojin a hannunsa sai ya miko min, ban karba ba ya ajiye a kasa "uhmm, dama naga bamu da kaji a freezer ne, shine na siyo wa Umma gasassu, irin wadanda nake siyo mana din nan masu laushi, na ga kina son su maybe zata so su itama"
Na bata rai "shikenan abinda ya saka kake rafka min kira?" Yayi shiru bai ce komai ba. Na ja karamin tsakin da nasan Umma ba zata ji ba na koma falon. Bai jima ba shima ya fito, sai ya sake yiwa Umma sallama sannan yace min "Jidda zan dan fita, idan su Umma zasu tafi sai ki kira ni inzo in kai su gida"
Yana sane, yasan cewa nayi blocking number dinsa, wato so yake yi in bude shi in kira shi. Umma tayi saurin cewa "a'a doctor, ina za'a taso ka daga gurin aikin ka saboda kai mu gida? Mun gode amma kayi zaman ka wallahi zamu tafi ma da kan mu, muna zuwa bakin layi zamu samu abin hawa"
Ya sake cewa "ai ba office zan koma ba, nan bakin layi zan je, tana kira na zan dawo, menene amfanin mota ta in ban kai ki gida ba Umma?" Tayi masa godiya ya fita ni kuma na bishi da harara.
Yana fita Farhan ta mike,"me aka kawo mana a leda? Na san dai sakon mu ne" nace "to shigabar kwadayayyu, je ki dauko ki gani" ta shiga sai gata ta fito da kaji manya guda biyu da kuma apples a wata ledar da ban.
Suna nan guri na har bayan laasar sannan suka ce zasu tafi, nace su bari ayi magrib amma suka ki. Umma tace "kar ki kira shi dan Allah ki rabu da shi, ni ba zan ma iya shiga motar sa ba" Farhan ta bata rai "haba Umma, ki bar mu mu shiga raɓa mana" Umma tace "sai dai ki shig ke kadai ni ba zan shiga ba" ni dai inajin su suna tayi har suka gama ban tanka musu ba dan na riga na gama yanke shawarar in sun ce in kira shi ma zanyi faking kiran ne in ce network babu kyau.
Sai bayan magrib ya shigo. "Yanzu shine kika bar su Umma suka tafi a motar haya?" Na tashi zaune "ai kasan sun saba da ma, ko ka manta a cikin motar hayan suka zo? Tun muna ciki muke yawo a motar haya dan haka one more babu abinda zai yi musu"
Ya zauna yana kallona. "You won't stop, will you?" Na girgiza kaina "never" yace "you won't let me explain ko?" Na sake girgiza kai na "bana bukata" yace "saboda me? Idan banyi miki bayani ba ta yaya zamu samu fahimtar juna?"
Na mike tsaye "bana bukatar fahimtar ka, na riga na fahimci duk abinda ya kamata in fahimta. Bana bukatar jin wani bayanin ka, dan bana jin zan kuma yarda da duk wata kalma da zata fito daga bakin ka"
Zan wuce sai ya mike da sauri ya rine hannu na. Na juyo ina kallon sa muka hada nayi saurin dauke nawa idon, ban taba ganin jikinsa yayi sanyi irin na yau ba. Nace "sakar min hannuna" bai musa ba ya sake ni na shige daki, sai dana kwanta na kifa kaina a pillow na fara hawaye sannan na tuna na bar Yasmin a falo.
Na mike ina goge hawaye na na koma falon sai na ganshi ya durkusa a gaban ta ya dora fuskar sa a jikin ta ta, nazo na saka hannu na ture fuskarsa na dauke yata. Ya bini da kallo bai ce komai ba har na shiga daki na rufe kofa ta.
Kusan kwanan mu biyar a haka, a lokacin na fara kokarin komawa school dama kuma already ina shirye shiryen project dina, sai dai yanzu sam mind dina baya kan karatun ko na dauka ma ba iya wa nake yi ba. Na saba most of the times tare da Umar muke yi kuma shi yake koya min duk abubuwan da ban gane ba. Yanzu kuwa magana ma sai dai yazo yayi ta yin abarsa in bakinsa ya gaji ya yi shiru.
A wannan ranar ma ina cikin dakina da laptop a gaba na ina ta danne danne wai ni a lallai karatu nake yi duk da babu abinda nake ganewa. Naji anyi knocking kofar, a bude take kuma nasan waye dan haka na share shi. Ya turo kofar ya tsaya yana kallona. Na dauke kai pretending to be busy.
"Kinyi bakuwa a falo" na dago kai kna kallon sa, wani barin na zuciya ta yana aiyana min Zuwaira a matsayin bakuwar da tazo, "Zuwaira ce?" Na tambaya ina kallon sa, sai yazo ya zauna a gefen gadon, na mike tsaye da sauri tare da nuna masa hanyar fita "go away" na fada da dan karfi, ya mike tsaye shima da sauri yana min alamar in yi a hankali, na kara daga murya "ka fita min a daki nace" da sauri ya je ya rufe kofar sannan ya jingina da jikin kofar "Bashir ne yazo tare da Surayya da kawarta, Surayya ita ce wadda zai aura, ya kawo miki ita ne ku gaisa"
Na koma saman gado na na zauna tare da harde kafafuwana "kaje kace musu ba zan zo ba, bani da lokacin ka ballantana na abokin ka da budurwar sa balle wata kawarta" ya bude hannu "na riga na gaya musu cewa kina nan Jidda, cewa nayi bara in je in kirawo ki. Me zan ce musu kuma yanzu?" Ya fada kamar zaiyi kuka, na daga kafada "oho, ka fini sanin abinda zaka fada ai tunda kai gwani ne gurin iya tsara magana wadda akayi da kuma wadda ba'a yi ba, tabbas zaka san abinda zaka gaya musu"
Ya rintse idonsa ya bude "Jidda please. Ni fa mijin ki ne. Dan Allah ki je ku gaisa ko minti biyu ne sai ki dawo ki cigaba da abinda kike yi dan Allah" sai na dauko ear piece na saka ajikin laptop din na kuma saka a kunne na na fara gyada kai duk da cewa babu kidan da nake ji.
Ya hawo kan gadon, na nuna shi da hannu "ko ka sauka ko in yi maka ihu" ya sauka ta tafi bakin kofa, ya jima a tsaye yana kallo na sannan ya bude kofar ya fita. Na bi bayan sa da harara sannan na zare earpiece din daga kunnena.
Amma kuma sai