Chapter 52 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   52 / 106

153K to 156K   out of 316K words

ka'ida duk mace sai da saka hannun iyayenta"

"Suka sallami masu film din suka ce a'a su ba zasu saka yar su a film ba, sannan suka lakada mata shegen duka, sai da taji kamar zasu kashe ta sannan ta fadi gaskiyar cewa da saka hannun Umar, shi ya hada ta ma da yan film din a bisa alkawarin ba zata fadi shine ba"

"Haka baban Aunty yazo yayi wa Aunty tas, yace sakacin ta ne, amma da yake masu kawaici ne ko kallon Umar ba suyi ba. Ita kuma Aunty tayi masa Allah ya isa tace babu ita babu shi kuma ba zata taba yafe masa ba. Yarinyar nan Allah kadai yasan abinda ya faru da ita a cikin kwanakin da bata gida, sun ce ma aure zasuyi mata"

Nayi shiru ina tunani, ina tunanin wanne irin cin amana ne wannan? Wanne irin mutum ne Umar? Wanne irin mutum na aura? How Aunty must have felt!

Sai naji kuma ina jin tsoron Allah ya isan ta kar ta dawo ta shafe mu ni da yayana.

Yaya Mubaraka ta yi ta bani hakuri "tabbas nasan kinyi hakuri sosai da sosai Jidda, amma dole zan kara baki wani hakurin, Allah ya kara miki hakuri shi kuma Allah ya shirya mana shi. Kuma gobe insha Allah zan je gida in samu Mama, zan gaya mata komai kuma insha Allahu zata dauki mataki mai kyau, nima kuma zan neme shi muyi magana. Sai ran sa ya baci wallahi. Stufid boy kawai"

Naji dadin yadda yaya Mubaraka ta karbi maganar, sai dai kuma maganar da muka yi da ita sai ta tayar min da damuwa ta na wuni cikin kunci da bacin rai. Ga maganar Ummi da ta zo min a matsayin sabuwa sai abin ya hadu ya saka min rashin lafiya, ciwon kai, daga baya kuma sai zazzabi mai zafi ya rufe ni.

Ina nan kwance a daki da yara suna ta hawa kaina suna wasan su sai gashi nan ya shigo. Ya tsaya yana kallona "are you sick?" Ya fada muryar sa da damuwa, na gyada kai kawai, sai ya hawo gadon ya bude bargon dana rufa da shi yana taba wuyana "subhanallah. Jiddah me yake yi miki ciwo?" "Kaina ne yake ciwo, sai kuma zazzabi"

Ya sauka daga kan gadon yana cewa "kuma shine kika kwanta? Ba zaki kira ni ki gaya min ba? Da kuma ban dawo da wuri ba fa?" Ya fita sai gashi da robar ruwa da magani, ya kamani ya tasar dani zaune sannan ya bani magani "oya sha magani, in bai sauka ba kuma sai inyi miki allura" na karba nasha sannan na koma na kwanta ya gyara min rufa ta sannan ya dauki Asad ya ja hannun Yasmin "ku taho mu bar mommy ta huta"

Bayan sun fita bacci ya dauke ni, sanda na tashi sai na ganshi shi kadai a zaune a gaban gadon da wayata a hannun sa yana daddanna wa, yana jin motsin na juyo yana kallona, fuskar sa da damuwa

"Sannu Baby, bara in samo miki wani abin ki ci" nace "ina su Yasmin?" Yace "nayi musu wanka na kwantar da su a dakina dan kar su dame ki" na rufe ido na, anya kuwa akwai miji a wannan zamanin mai kula da matarsa kamar yadda Umar yake kula dani? Anya kuwa akwai miji mai wulakanta matarsa kamar yadda Umar yake wulakanta ni?

I find it hard to place him, a wanne matsayi yake? Miji na gari ko mugun miji?

Ya mike zai fita sai na rike hannunsa, ya juyo yana kallona sai nace "ka saka an saki Maryam?" Ya juyo yana kallona "kin damu da ita?" Nace "na damu da kai" sai ya hawo kan gadon ya dora kansa akan pillown da nake, fuskarsa kusa da tawa yace "me yasa zaki damu da kamatan da akayi?" Nace "saboda bana so ka dauki alhakin ta, saboda kai mijina ne, duk hanyar da zaka bi zan so ace kyakykyawa ce, in kuma kabi hanya marar kyau zan yi iyakacin kokari na in dawo da kai kan hanya mai kyau, duk abinda nayi ko zanyi dan kai ne, dan nutsuwar ka ita ce tawa ni da yayan mu wadanda muke da su da wadanda zamu haifa nan gaba"

Ya shafa fuskata yana murmushi "Nagode. Kuma an bada bail din ta tun jiya. Ina son kuma ki sani cewa you are the best thing that happened to my life, and I love you too" na rufe idona ina jinjina kalmar love, anya kuwa da akwai sauran ta a cikin zuciyata akan Umar, in ma da akwai bana jin ya kai 30% din yadda yake da, sai dai kyautatawar sa, kulawar sa da nuna damuwar sa akaina su suke rike da wannan sauran 30 din.

Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020

Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020

Please banda kira, WhatsApp only


*wannan littafin na siyarwa ne bisa amana ne idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar kiyi sharing, idan kika yi kinci amana kuma ke da Allah*

*A lesson for all*

Kwana na biyu ina kwance ba lafiya, a karshe Umar bayan yayi min allurai sai ya tafi dani asibiti ya yi min tests, har da cewa "Allah ya sa ciki ne" na kalle shi kawai ban ce komai ba sai yace "kar kiyi mamakin in muka ga shine, kin san condom is not 100% reliable" a hankali nace "I am glad you know that" ya kalle ni kawai sai yayi shiru.

A asibiti pregnancy test din da yayi min turned out negative, babu abinda ya gani sai high bp, tun daga asibitin yake kumbura. "Ni ban san matsalar ki ba Jidda, gabakidaya kin chanja kullum cikin tunanin gashi nan kina neman kiyi wa kanki illa, ni nafi so in kina da problem kiyi min magana, in nayi miki wani abu kiyi min magana mu zauna mu tattauna, bana son wannan bacin ran da kike sakawa kanki akan abinda ni bansan menene shi ba. Yanzu dole in dora ki akan magani"

Nayi shiru kawai ina jin sa, a raina nace pretender, ya kware gurin pretending everything is okay bayan ni da shi munsan it is not. Bansan me ya shiga kansa ba sa da ya nemi Maryam, bansan wacce zuciyar ce ta gaya masa cewa we will continue being okay bayan ya kwanta da kawata, ban san ta yaya yake tunanin zan iya cigaba da enjoying kwanciya da shi ba. Ban san ta yaya yake tunanin zan cire memory din daga zuciyata ba.

Ko da yake shi a ganinsa na yarda da maganar sa cewa Maryam office din sa ta shiga tayi masa sata.............

Sai dai wannan ba shine abinda ya fi daga min hankali a yanzu ba, abinda yafi tashin hankali na shine jiran tsammanin sakamakon aiken da nayi gurin Mama da Baba.

Kamar amsar magana ta naji ya dauki wayarsa "Hello Mama. Bama gida ma yanzu, na kai Jidda asibiti muna hanyar komawa gida. Okay zamu shigo"

Naji zuciyata ta buga da karfi "na juya ina kallon sa naga shima ni yake kallo yace "Mama ce wai take neman mu yanzu, she sounded upset, Allah yasa ba laifi muka yi ba" sai na juya ina kallon side dina, nasan kiran na menene amma ban dauka zata kira mu ne tare ba, na dauka zata kira shine ta bincike shi ko ta saka a bincike shi ko ta gaya wa baba shi ya bincike su tabbatar da gaskiyar ko rashin gaskiyar maganata sannan sai su kira shi suji side dinsa su kuma yi masa fada tunda ni na riga na fadi nawa side din.

Daga nan bamu je gida ba gidan su muka tafi, kowa cikin mu yayi shiru sai Yasmin da take ta surutun ta mostly ita kadai.

Har muka je gidan yayi packing ya zagayo ya bude min ya kuma kama hannuna na fito ina dafe kaina da yake yi min kamar zai tsage "sannu" yace "sannan yayi "da na sani ma gida na kaiki tunda dai na riga na gaya mata ba kya jin dadi" na girgiza kaina "no, muje kawai tunda mun riga mun zo" ya dauko Asad ni kuma na kama hannun Yasmin muka shiga.

Babu kowa a babban palon gidan, na samu guri na zauna shi kuma yashiga dakin Mama. Shiru shiru bai fito ba, a lokacin da za'a sake auna bp na da nasan kadan ya rage ya kai ga ƙwaƙwalwa ta ta buga gabakidaya. Ga dai TV nan a gaba na amma babu abinda nake fahimta a cikin abinda suke yi. Ina ta kallon dakin Mufida wai ko zata fito maybe in tayi min magana zan dan dauke hankali na daga maganar da Umar suke yi da Maman sa a cikin daki.

Kamar daga sama ya bude kofa ya fito, sai ya tsaya yana kallo na da handle din kofar a hannun sa, mun jima muna kallon kallo sannan na sunkuyar da kaina kasa ina ambata "innalillahi wa inna ilaihir rajiun"

Maganar Mama naji tace "sannu Jidda" yadda ta fadi sannun da gatse ya saka nayi saurin dago kaina ina kallon ta, ta wuce Umar tazo ta zauna akan kujera tana kallona da wani irin expression a fuskarta dana kasa fassara wa. Na gaishe ta "barka da fitowa Mama"

Bata amsa ba tace "daga farko dai ina son inji bayan Mubaraka wa kika gaya wa maganar nan" na dago kai na kalle ta na kuma sunkuyar da kaina, automatically hawaye yana tahowa ido na, "ban gaya wa kowa ba Mama, dama so nayi ta gaya muku tukunna....." Ta katse ni "to alhamdulillah. Tambaya ta biyu da zanyi miki ita ce, menene Umar ya rage ki dashi? Menene kike so wanda bai yi miki ba?" Na sake dago kai tare da kokarin bude baki zanyi magana amma voice din sai yaki fitowa, ta daga murya "ki fada min mana ina jin ki? Meye bai yi miki ba da zaki bishi da wannan sharrin?"

Na fara kuka sosai, Umar ya karaso da sauri ya durkusa a gaban Mama "Mama dan Allah ki bar maganar nan, na gaya miki sabani ne muka samu kuma zamu daidaita, bata da lafiya kinga dan Allah kar kiyi mata fada"

Ta kai hannu kamar zata doke shi, "matsa daga kusa dani tun kafin in targada ka, yanzu lalacewar taka Umar har ta kai haka? Har ta kai yarinyar da ta dubi idona ta kala maka wannan sharrin ita kuma zaka zo kana karewa a gaba na? Anya kuwa Umar ba sai na hada ka da addu'a ba? Anya kuwa wannan soyayyar ta Allah da Annabi ce"

Ta juyo kaina ta nuna ni da dan yatsa "wallahi Jidda kiji tsoron Allah. Yaron nan babu irin fadi tashin da bamuyi akan sa ba babu irin ilimi da tarbiyyar da mu bashi ba, kuma idan baki sani ba bara in sanar da ke, babu irin yammatan da basu so shi ba, wadanda kuma suka fiki komai da komai amma shi ya nace ya dage sai ke, mu kuma muka bi son da muka ga yana yi miki muma muka so ki sosai muka dauke ki daya da dukkan yayan mu, ashe ke din ba yar goyo bace ba"

"Kullum na ganki sai nayi tunanin menene yake hana ki kiba, ke ba rashin ci ba ba rashin sha ba, ke ba kishiya ba kuma ke babu abinda kika nema kika rasa amma sai bushewa kike yi a tsaye, ashe shegen kishi kika dauka kika saka a ranki."

"Shikenan kuma dan ya aure ki sai aka ce mikin a zai kula kowacce mace ba kenan? Shi kenan sai aka ce miki duk macen da kika ganshi da ita neman ta yake yi? Ita wannan yarinyar da kika yi magana akanta ba Mufida ta gaya min cewa kawarki bace kuka yi fada, sai ta shirya masa sharri to gate back at you? A tsakanin ku waye ya kamata yaji haushi? Shi da akayi kokarin batawa suna akan ki ko kuma ke da idan da zaki saka kishi aside zaki fahimci cewa sharri ne?"

Naji hannayen Yasmin a bayana ta zagaye ni da su tana dan jijjiga ni kamar mai rarrashina. Naji Umar ya sake magana "Mama dan Allah ki bar maganar nan haka. Rashin fahimta ne muka samu a tsakanin mu kuma zamu warware matsalar a tsakanin mu insha Allah. Ki bar mu mu tafi gida kawai, ki manta ma da cewa hakan ya faru"

Tace "ai ni bani na shigar da kaina maganar ku ba ita ta shigar dani tunda ita ta aiko takanas azo a gaya min, maganganun fa su a da yawa data shishshirya wadanda ni ina ji na fahimta cewa shiri ne, raina ya baci ne kawai saboda banyi tsammanin haka daga gareta ba, shi yasa na nuna mata bacin raina dan ta kiyayi gaba kuma ya zama warning a gareta cewa ni ba zan bar dana guda daya a duniya ya zama bawan mace ba, tunda duk abinda ake mata bata gode Allah ba yanzu kam sai mu saka kafar wando daya ni da ita mu gani, dan halak ka fasa"

Ya sake cewa "Mama please" tace "kasan Allah in ka kara yi min magana sai na fasa bakin ka, banza shanyayye. Ni bansan yadda akayi ka koma solobiyo ba wallahi, ina zafin ka yake ina zuciyar ka take da har mace zata samu uwarka ta gaya mata wadannan maganganun amma ka zauna kana kare ta kuma"

Haka ta cigaba da fada sai da ta wanke ni tas a gaban Umar, wai Umar ni ma mai bada hakuri, karshe sai ta hada dashi tayi masa fadan me yasa yake kare ni. Sai da tayi ta gama dan kanta sannan tace mu tashi mu tafi. Yazo ya kama hannuna ya mikar dani tsaye, ban musa mishi ba dan na tabbatar in na tashi faduwa zanyi dan jiri kawai ne yake dibana, sai daya kai ni mota na shiga sannan ya saka yara a baya ya tashi motar muka tafi.

Muna fita daga gate din gidan na juyo ina kallon sa nace "gidan mu zaka kaini" yayi banza dani kamar bai jini ba, na sake maimaita wa ganin ya dauki hanyar gida, "Umar ka kaini gidan mu na gaya maka, wallahi ko ka kaini gidan ka sai na fito, yau a gidan mu zan kwana"

Ya juyo ya kalle ni, fuskar sa da alamar bacin rai yace "da iznin waye zaki je gidan? The last time I checked ni mijinki ne kuma sai na baki izni sannan zaki je ko kofar gida ne" nayi shiru na kwantar da kaina a jikin kujerar mota amma a raina ina lissafa ko sama da kasa zasu hade sai naje gida gida sai dai ayi wacce za'a yi. Ai nima ina da iyayen kuma nima iyayena suna sona.

Sai dai su suna da kawaici da sanin ya kamata. Ko kuma ince suna ganin suna da sanin ya kamata bayan ba wai kamatar yayi ba.

Sai naji ya cigaba da magana

"Why Jidda why? For God's sake what were you thinking? Ta yaya zaki samu mahaifiya ta wadda ta kawo ni duniya ki fada mata wannan maganar" na juyo ina kallon sa nace "kasan dalilin da yasa na gaya mata? Saboda ita ta kawo ka duniya kuma ita ya kamata kake kunsawa bakin cikin ka bani ba, na gaya mata ne dan zuciyarta ta buga maybe in bakin cikin ka yayi ajalinta sai kasan cewa ba daidai kake yi ba"

Yayi saurin yin packing a gefen titi ya juyo "what????" Na dauke kaina "in kaji haushin abinda nace ka kaini gidan mu, ka hada min da takarda ta" yayi shiru yana kallona sannan yace "okay, ranki a bace yake I get it. Ni kuma ba zan kula ki ba, sannan kuma gida nace ba zaki je ba" ya sake tayar da motar ya cigaba da tafiya.

"Maybe sanda kika gaya wa yaya Mubaraka maganar nan you though you were doing the right thing, but yanzu na tabbatar kin fahimci cewa it was not the right thing. Gashi kin jawo wa kanki fada a gurin Mama, na tabbatar baki san halin fadan Mama ba amma yanzu kin sani. But ni abinda ba gane ba shine; na dauka mun gama maganar nan tuntuni,  just because I confessed to you cewa da ina neman mata doesn't mean yanzu ina yi, ba na gaya miki na daina ba? Sau nawa ina gaya miki na daina wai? Me yasa ba zaki yarda dani ba wai Jidda? Abinda yafi komai kona min rai shine rashin yarda dani da kika yi kuma har zaki nuna min kin yarda da abinda nace sannan ki zagaye ki gaya wa Mama. Kina tunanin Mama zata yarda......"

Nace "zata yarda, da ace ka gaya mata gaskiya da zata yarda. Zata yi bakin ciki tabbas amma ba zatayi disowning dinka ba kuma zata yi maka abinda nake yi maka kwadayin samu wanda dalilin sane ya saka na gaya mata din, zata yi maka addu'a. Za ta kuma iya sakawa shima Baba yake yi maka addu'a. Tare da support din su da addu'ar su zamu ga karshen matsalar nan. Wannan shine dalilin da yasa na gaya mata"

Sai kuma ya saukar da murya kasa "Jidda wai addu'ar menene Mama zata yi min ne? Me yasa wai ke baki yarda cewa na daina din ba?" Na girgiza kaina "saboda baka daina ba. Saboda karya kayi min da kace baka nemi Maryam ba. Na sani ka neme ta"

"What?....... How...... Ta yaya ma zaki ce haka? Bayan ga bayani nayi miki kuma har police sun kama yarinyar nan ta kuma yi accepting laifin ta shiga office dina tayi min sata kuma na gaya miki a lokacin ne ta chanja band din bansan kuma me kike so in ce miki ba. Ban san me yasa baki yarda ba"

Nace "guilty look din daya ke kan fuskarka a lokacin da kayi min wannan bayanin shine dalilin da yasa ban yarda ba, kuma look din shine yanzu ma akan fuskarka. Abinda baka sani ba Umar shine

52 / 106