Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
ina son sa, kuma Jidda yarinyar kirki ce daga mu har Umar muna jin dadin zama da ita"
Sai ta fara yin gaba su kuma suka bi bayanta suna cigaba da maganar. ..
Dakin yayi shiru bayan fitarsu. Na rufe idona ina tuno kyakykyawar fuskar da na da na gani a hoto duk da dai har yanzu babu wanda yayi offering min ganin sa.
Kamshin turaren sa naji, na bude idona na ganshi a tsaye a gaban gadon yana kallona as tall and as handsome as ever. Na juya kaina gefe, inajin idonsa tamkar wani mashi ne mai cin wuta da yake sukar zuciya ta. Sai kuma na sake juyowa ina kallon abinda yake hannun sa, jariri na ne, sai kuma na sake juyawa gefe, yace cikin sanyin murya "Asad ne yazo ya gaishe ki. Tunda yazo duniya bai ji dumin mommyn sa ba" ban juyo ba nace "ka ajiye min dana ka juya ka fita, bana son ganin ka".
Sai naji takun sa kamar ya juya, na juyo da sauri sai naga ya ajiye jaririn a gurin da aka tanada dan ajiye jarirai sannan ya dawo inda nake, na sake juya kaina "ka bani dana nace, ai ba kai ne ka haifar min shi ba" ya rungume hannunsa yana kallo na yace "well, technically ni na haifar miki shi tunda ni na ciro shi daga cikin ki"
Ban ce komai ba sai ya cire min ruwan da ya kusa karewa sannan ya fara kokarin kama ni ya tashe ni, ya saka min pillow a bayana sannan ya koma ya dauko jaririn ya miko min shi. Na karba da sauri ina sauke ajjiyar zuciya, sannan na saka babban dan yatsa na na shafa yar mitsitsiyar fuskarsa da idanuwan sa suke a rufe, kirjinsa yana motsawa a hankali yana numfashi, sai naji kamar ban taba ganin jariri kyakykyawa irinsa ba.
Umar yace "sato miki shi nayi kakanninsa basu gani ba, dan nasan in suka ganshi duk sai sun jagwalgwala shi kuma ba'a so ake yawan daukan sa" sama sama na jishi, hankalina yana kan kyakykyawan da na.
Zaman da umar yayi a kusa dani ya saka na dawo cikin hayyacina, na dawo reality din wacece ni kuma wa nake aure, wanene kuma baban jaririn da yake hannuna.
"Ka tashi ka fita nace, bana son ganin ka nace"
Sai ya dora hannunsa akan hannuna da yake rike da jaririn, idona ya sauka akan band dina da yake hannunsa for more than three years, da sauri na kama hannun na zare shi ina jin zuciyata tana kara zafi, nayi jifa dashi ta window nace "I can't even imagine you on top of another woman and still wearing that"
Cikin rashin sa'a sai band din ya daki window frame ya fadi kasa bai fita wajen ba, Umar ya mike ya tafi inda yake ya dauka ya mayar da shi hannun sa sannan ya juyo yana kallo na "bana son muyi wannan maganar yanzu Jidda, baki da lafiya, bana son abinda zai kuma tayar miki da bacin rai dan ni kadai nasan tashin hankalin da na shiga a cikin kwana biyun nan"
Naji raina ya kara baci, it is soooo frustrating wanda ya aikata maka wannan abin kuma ya ke wani nuna kamar yafi kowa damuwa a kan ka, it would have been easier for me idan da ace Umar zai nuna halin ko in kula a kaina, dama da direct zan san gurin da zan ajiye shi amma wannan fuska biyun sai ya kasance ban san ma ina ne position dinsa ba.
Nace "you should have thought about that tun da ba yanzu ba, yanzu is already late na riga na fahimci abinda kayi, ko kuma ince abinda ka dade kana yi, ko kuma ince abinda kake kan yi" ya dawo ya zauna a inda ya tashi sannan ya saka dan yatsa yana shafa hannun Asad,
Yace "really? Bana son muyi maganar nan yanzu kamar yadda na riga na fada miki, amma bara inyi miki wata tambaya guda daya. Na fahimci kin karanta hirar mu da Bashir amma bana jin kin fahimci abinda hirar ta kunsa" nace "na karanta, na kuma fahimci komai, na gane who you really are, dan haka yanzu na dai na tafiya cikin hudu but rather a cikin haske nake, tas nake ganin ka yanzu?"
Ya mike tsaye yana kallona, his calmness yana kara irritating dina yace "really? In dai har kin fahimta kenan kin fahimci dalilin da yasa na dawo gida kafin lokacin dana gaya miki zan dawo yayi" nace "sosai kuwa, ka dawo ne ka wanke najasar jikinka sannan ka sauke sha'awar daka dauko ta dalilin kallon tsiraicin wata a kaina"
Yace "in har kin fahimci haka kin fahimci banje ba kenan, kin fahimci banyi abinda kike tunani ba kenan" nace "dan baka yi ba ranar hakan ba ya nufin ba ka yi, yanayin maganganun ku kawai ya tabbatar min da cewa kun saba aikata haka ko kuma ma abinda yafi haka, Allah ne kadai yasan irin girman kazantar da kuke aikatawa"
Ya runtse idonsa ya bude "to kin tambayi kanki dalilin da yasa banje din ba?" Nace "you clearly said it ai a wajen, saboda baka da kudi kuma shi shugaban yan iskan duniyar yace ba zai biya maka ba"
Ya daga gira "really? Ke kin yarda cewa bani da kudin da zan biya? Ke kin san nawa ne a cikin account dina a yanzu haka kin san kuma idan da naso yi din zan iya biyan ko nawa ne inyi din, ke kinsan haka amma Bashir bai sani ba, na gaya masa bani da kudi saboda bana son yi din, ba kuma na so in gaya masa hakan saboda wani dalilina"
Na juya kaina gefe ina jera numfashi. Tabbas akwai isassun kudi a account dinsa dan last week yayi wa Baba complain din motar sa tana bashi problem kuma ya turo masa kudi masu yawan gaske yace ya chanja, a yanzu haka ma lissafin motar da zai siya da kudin yake yi kuma kudin suna cikin account dinsa, plus kudin da yake tarawa na shirin haihuwar Asad.
Ya saka hannu ya juyo da fuskata muna kallon juna yace "yes, ya turo min hoton da ya tayar min da hankali na a matsayi na na namiji, wannan shi yasa na taho gida, na taho gurin ki ke Jidda matata. Idan da naso zan iya biya ya kirata ta dawo idan da naso zan iya cewa ya kira wata ko da ita ba zata zo ba amma ban so yi din bane shi yasa nace bani da kudi na kumace ya biya min saboda nasan in yaji shi zai biya min he will stop nagging me"
Ya saki fuskata ya mike "zamuyi maganar kamar yadda na fada amma sai kin samu lafiya, ba lallai ki yarda ba saboda ni yanzu a gurin ki makaryaci ne kuma nasan nayi deserving duk abinda zaki kira ni da shi and more, amma ina son ki sani cewa Umar have changed alot for you, ba lallai ki fahimci how much na chanza din ba amma ina ki sani cewa fiye da tunanin ki ne. I have changed for you. Because I love you"
Sai ya juya ya fita.
Na runtse idona hawayena ya zuba akan yar mitsitsiyar fuskar jariri na.
Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din
0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank
Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020
Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020
Please banda kira, WhatsApp only
*wannan littafin na amana ne kar ki karanta idan baki siya ba, idan kuma kin siya dan Allah kar kiyi sharing, in kika yi kin ci amana kuma ke da Allah*
*Zahra*
Ban daga kai na kalle shi ba har ya fita ya rufe min kofa. Na sake bin hawaye na da yake zuba akan dan jaririn da bai ji ba bai kuma gani ba da kallo, sannan na saka hannu na dangwali hawayen na kalla kamar ban san menene ba.
Kwakwalwa ta ta toshe, kaina ya cunkushe ya kasa yi min tunanin komai. Duk abinda Umar ya fada sounds right and it sounds good ga zuciya ta da dama neman abinda zata yi masa uzuri da shi take yi. But har yanzu akwai wani abu daya chak da yake tsaye a cikin kwakwalwa ta ya kasa kwanciya. Na rufe idona na sake jingina da jikin pillown da ya saka min a bayana ina jujjuya maganganun sa ina kuma yin filla filla da su ina so in samu inda zan samu wani rami da zan fake a ciki amma babu, ko ina a toshe yake babu hanyar bullewa.
Na sake tariyo hirar su da Bashir a kaina,na kuma hada ta da bayanin Umar na sake fahimtar cewa komai ya zauna kamar yadda ya so ya zauna din. Sai dai yaki zama a kaina. A ina matsalar take ne......
Tun farkon haduwa ta da Umar zuwa wadannan shekarun da nayi tare da shi na fahimci abubuwa da dama a kansa amma wani abu guda daya yafi komai girma, he is smart, in nace smart ina nufin smart, kwakwalwar sa is very sharp dan har mamaki yake bani in yayi wani abu a lokuta da dama dan kansa yana ja fiyeda yadda nake tunani.
Wannan shi ya saka ya iya tsara magana, ya kuma iya tsara karyar da zai kare kansa a duk lokacin da yayi laifi, irin karyar da ya ringa yi min a lokacin case din mu akan Zuwaira har sai da abin ya kai karshen bango sannan ya fito ya bude min gaskiya sannan muka samu nutsuwa ni da shi.
Wannan kuma shine abinda ya kasa fahimta, the more da zaiyi karya in dai har akwai an ounce of doubt a raina to zuciya ta ba zata yi settling ba har sai na gano gaskiya. And right now everything seems perfect except for one thing, and that thing is yanayin yadda suka yi magana da Bashir, normalcy din maganar su, tabbas ba ranar suka fara ba kuma ba wai sun jima ba suyi bane ba. They talked like suna magana ne akan normal thing like shopping ko office stuffs. Abinda ake yi yau da gobe.
Yes, baiyi ranar ba kamar yadda ya fada kuma na tabbatar, amma hakan ba yana nufin baya yi bane ba, sai dai bani da yadda zanyi proving hakan to myself and to him.
Na goge hawaye na ina kallon fuskar da na, Umar yana so ya kashe ni ne da raina ba wani abu ba, kullum zaiyi fata-fata da zuciyata sannan kuma ya zauna ya dinke ta da kansa only for him to break it again. How much longer zan iya cigaba da tolerating this emotional turture? How much longer kafin in gane gaskiyar waye Umar kuma in samu solution din zama da shi?
But no one will understand ballantana har ya bani shawarar yadda zan bullowa lamarin, kowa kallo yake min kamar wadda nake aljanna yayin da sauran mata suke a wuta, babu wanda zai gane position dina sai idan ya samu kansa a cikin irin yanayin, abinda bana yi wa kowa fatan shiga.
Da daren ranar Bashir suka zo duba ni shida Surayya. Sai na fahimci cewa Umar bai gaya masa abinda ya faru ba in kuwa har ya gaya masa to kuwa tabbas shi din ba karamin marar kunya ba ne ba. Ban gaishe shi ba, Yace "ya jikin?" Sai dana dauki seconds biyar sannan nace "da sauki" sai naga yanayin sa ya chanja, mun saba magana freely da dariya, sai ya fita yace matar in ta gama ta same shi a waje.
Ta dan jima min kadan sannan ta tafi, sai naji a raina ina tausayin ta, ina tausaya mana ni da ita amma ko kadan tunanin in gaya mata abinda na gani bai zo kaina ba.
Ba'a sallameni daga asibiti ba har sai ranar sunan Asad, a can gidan su Umar akayi masa yanka aka rada masa sunan Baba, Muhammad kamar yadda Umar ya riga yayi masa huduba da hakan. A cikin kwanakin nan na warke sosai, tun daga jikina har zuwa zuciyata ta dan sarara min, musamman saboda yadda Umar yake tsaye a kaina da kulawa da kalamai da nuna soyayya kamar wata gimbiyar mata. Kawaye na da yan uwana duk wanda yazo duba ni sai yayi min murna na samun miji kamar Umar, marasa aure suna yiwa kansu fatan kasancewa kamar ni, a cikin su babu ya Maryam, wadda zuwanta hudu a asibitin kuma duk zuwasai ta saka ni a gaba da zancen Umar tun ina murmushi har ta fara annoying dina sai da na samu Mufida ranar nan ta wanke ta tas sannan tayi fushi tace ba zata kara zuwa ba tayi tafiyar ta.
Bayan an sallame ni mun koma gida Abba ya sake turo Hajiya ta zaunada ni, ita kuma kamar wancan lokacin ta taho da Mammy suka zauna tare, farko banji dadin zuwan nata ba amma sai na lura wanda banji dadin ba saboda shi ko a jikin sa, babu abinda yake hada shi da ita sai gaisuwa, ita ma kuma saboda lokacin tana zuwa makaranta basu yi hutu ba sai ya kasance ba zaman gida take yi ba, in ya dawo daga office shi kuma baya zaman palo saboda Hajiya, a dakin sa yake cin abinci anan kuma yake kallon sa.
Tsakani na da Umar tun da na dawo gida babu yabo babu fallasa musamman ta bangare na, na kasa sakar masa fuska kamar da duk kuwa da kokarin da yake ta yi min, nakan zauna inyi hawaye saboda takaicin haka, ina son mijina ina kuma son rayuwar mu ta dawo kamar da amma na kasa, na kasa cire maganganun sa da Bashir daga zuciyata. Sometimes I hated myself, ina fatan ina ma akwai wata addu'a da mutum zai iya yi wanda zata goge masa wani memory daga ransa, da ace da akwai dakuwa tabbas da nayi dan in manta dan kuma in mayar da mijina cikin zuciyata da kuma cikin jikina kamar yadda yake a da.
It wasn't funny on Umar as well, gradually ya fara loosing wannan calmness din nasa da ya saka a kansa tun ranar dana farka na ganni a asibiti. Ba wai masifa nake masa ba ko kuma magana nake gaya masa ba, a'a ignoring dinsa kawai nake yi kamar baya duniyar. Zan hada masa abinci zan kuma gyara masa dakin sa da duk abinda nasan yana bukata daga gare ni, amma ba zanje dakinsa ba zanyi kwanciya ta a dakina, sai dai hakan shi bai hana shi biyoni zuwa nawa dakin ba, bana kuma hana shi idan ya shigo din kamar yadda bana hana shi dora hannunsa a jikina sai dai ko kallon sa bana iya yi idan ya dora din, shi kuma wannan shi yake frustrating dinsa kuma duk maganar da zaiyi ba zan juya in kalle shi ba pretending nake yi as if I was made with stone, yakan hakura ya rabu dani.
A haka har nayi wata daya da haihuwa, na warke sosai kuma nayi tsarki, a lokacin ne kuma Hajiya da Mammy suka tafi aka bar mu daga mu sai yayan mu.
A cikin ranakun da suka biyo bayan nan ne kuma Umar yakai limit na frustration din sa, ya same ni a daki na kamar yadda ya saba kullum ya hayo kan gadon yana laluba ta, nayi kamar ban san yana yi ba sai naji ya finciko ni da karfi ya zaunar dani yana kallona.
"Jidda menene yake damun ki ne wai? Me kike so ne wai? So kike ki kashe ni ne wai?" Na cigaba da kallon sa ba tare da nayi komai ba kuma ba tare da nace masa komai ba. Ya girgiza ni kamar mai kokarin dawo dani cikin hayyacina "idan kina da wata magana da kike so ki gaya min talk to me, nasan ba zai wuce akan maganar Bashir ba kuma na riga nayi miki bayani na kuma dauka cewa kin fahimta, idan baki fahimta ba ki yi min magana sai in sake yi miki bayani, idan akwai wani abu ne kuma na daban ki fada min shima in na rashin fahimta ne in fahimtar dake in kuma na laifi ne in baki hakuri. Please Jidda talk to me"
Na hadiye abin da naji ya tsaya min a makogwarona yana kokarin karya min zuciya akan sa amma sai na daure "ni nace kayi min wani abu ne? Kaji nayi maka wani complain ne? Babu abinda kayi min kuma ni ma babu abinda nayi maka"
Ya kama hannuna "then what is the problem?" Na sake cewa "mai ka gani, wani abu ne?" Ya sake kama hannayena ya zagaye su a bayansa "then hold me, touch me, kiss me" ya fada kamar zaiyi kuka. Sannan ya dora bakinsa a saman nawa yana kara jayoni jikinsa tare da saka hannunsa cikin rigata yana shafa kirjina, na saki hannayena da ya saka a bayan sa da niyyar in rike shi suka sauka a gefe na trying hard not to feel his touch ina kallon sa, yayi breaking kiss din shima yana kallon na still hannun sa a rigata, "damn it Jidda" na kalli hannun nasa nace "sai dai kayi hakuri, basu kai girman wadanda kake so ba"
Ya zare hannunsa fuskarsa tana nuna bacin rai "damn it Jidda, damn it. Kiyi magana ki fadi abinda yake ranki" nace "gashi na fadi abinda yake ran nawa? Hakuri na baka ai, hakuri ya taba zama laifi ne? Basu kai girman wadanda kake so ba and I can't change that sai dai kayi hakuri" Ya dafe fuskarsa "damn it. Ni nace miki ina son wadancan din bana son naki? Ko na taba nuna miki cewa bana son naki din, eh? Ai nasan da Zahran amma na tsallake ta na aure ki saboda bana son ta ke na ke so"
Naji wani abu yayi clicking a mind dina "Zahra?" Na fada, ya bude fuskarsa yana kallona and the blood seemed to have drained from his face, "zahra? Na maimaita "wato ashe ka santa kenan, not only ka santa but ka santa so well that kana ganin tsiraicin ta za