Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
sai ya zamanto ko bayan ya koma office din stress baya yi masa yawa kuma yakan dawo gida da wuri.
Wayarsa tana nan har yanzu a gurina, sai dai na dauke ta daga dakina dan kar Mufida ta taba na mayar da ita dakinsa still na ajiye akan mirror ina kuma lura ko zai dauka amma bai dauka ba, duk da bani da tabbas din bai nemi wata a waje ya boye ba amma bani da hanyar sanin hakan inda ba kuda zan zama in ringa bin shi duk inda yayi ba.
Ranar nan Mama ta kira ni tana ta fada "ina Umar? Menene amfanin wayarsa da zai kashe ta ayi ta nemansa ba'a samun shi? Wannan wanne irin shashanci ne?" Ban yi mata bayanin komai ba sai nace bara in kai masa wayata suyi magana tunda yana gida, na same shi a falo na badhi wayar nace "Mama ce take neman ka" ya karba ya saka a kunne, nasan fada take yi masa sai ya jira sai da ta gama sannan yace "Mama wayarce ta fadi, kuma sim dina yana ciki, na sayi wata already amma ban samu lokaci naje nayi welcome back din layi na ba shi yasa ba'a samu na" ya danyi shiru sannan yace "insha Allah, da na samu lokaci zanje in yi"
Na saki baki ina kallon sa ina mamakin yadda Umar yake iya tsara magana a lokaci daya ba tare da tangarda ba. Sai ya dago kai muka hada ido, ya gane mamakin da nake yi sai kawai yayi murmushi tare da kashe min ido.
Na zauna ina jiran sa har suka gama maganar su sannan ya miko min wayata, na karba sannan nace "kasan dai bani na hana ka rike waya ba ko?" Ya daga kafada "nine nayi ra'ayi dan in nuna miki cewa zan iya rabuwa da abinda yafi social media ma"
A wannan zaman da muka yi da Mufida na fahimci wani chanji sosai a game da ita, sai naga yanayin ta yana min kama da yanayin yaya Jamila lokacin da muka je muka kwana biyu a gidan su ni da Farhan. Always busy with her phone, surutun ma yanxu ta rage yi dan in ina so muyi hira sai dai in karbe wayarta. And sau da yawa in tace zata je ta kwanta da daddare sai na shiga dakin sai inga ba bacci take yi ba waya take yi, wayar da in na shiga ake katseta in na fita kuma a cigaba, and I decided cewa zanyi wa Umar magana akanta idan mun shirya, sai dai shiryawar tamu ce na yanke wani decision akanta wanda nasan ba zaiyi masa dadi ba.
Sai da na tabbatar ya wanu, na kuma tabbatar ba zan iya cigaba da kwasar wa kaina zunubi ba dan Allah babu ruwan sa da abinda Umar yayi, zunubin sa daban nawa nima daban. I decided zan koma shimfidar sa, amma for that ina da sabon sharadin da zan saka masa.
A ranar na shiga na gyara masa dakinsa, na wanke toilet nayi duk abinda na saba yi masa kafin mu samu sabani, tun daga nan ya fara saka rai, da dare har da zuwa ya siyo mana kaji muka hadu muka ci a falo da Mufida da yara, sannan kuma da lokacin bacci yayi na bishi zuwa dakin sa na kuma karbi bukatar sa.
Sai da naja ragamar sa ya gama sakankancewa ya gama rudewa shiga kawai yake so yayi daga ciki sannan na ture shi naja baya, ya zaro ido "Jidda, me kike yi haka? Menene kike yi haka? So kike ki kashe ni da raina is that it?" Na sauka daga kan gadon ina kallon sa nace "get your self a condom"
Mamaki ya bayyana a fuskar sa yace "what?" Na gyada kai "kaji ni ai. Nan gurin, baka sake shigar sa sai da condom dan ba zaka kwaso cuta ka kwasa min ba" na fada ina mayar da kaya jikina, ya zamo daga kan gadon yana rike hannuna "haba Jidda, how? Ta yaya zaki ce inyi miki using condom you are my wife for God's sake"
Nace "cuta bata gane prostitute da wife. Jikina hakkin ka ne in baka as long as akwak aure a tsakanin mu, wannan shine ya saka zan baka din. Amma lafiya ta hakkina ne in kula da ita in bawa kaina kariya. Kariyar kuwa a yanzu ita ce condom, get it, sai kazo ka karbi duk abinda kake so"
Ya bata rai, ransa ya baci sosai dan zance ban taba ganin bacin ransa irin na ranar ba "yanzu ni kike tunanin zan dauko miki cuta Jidda, what do you take me for? Stupid or what? Kin dauka bani da hankali ne da ba zanyi using protection a waje ba ko me? Ji nake da cikin Asad ma sai da akayi miki tests har dana std kuma komai negative ne, na kuma gaya miki rabo na da abin nan tun........"
"Tun kafin a haufi Asad, sai a Zariya. Yes, ka fada min, amma ita ta zariyan na san ta ne? Na san dawa dawa ne suke juye kazantarsu a jikinta kafin kai ka juye taka?"
"Kuma sai na gaya miki da skin dina naje mata?"
"Ban sani ba kuma bana son in sani....ban tabbatar kana using protection din ba ko baka using, dan haka abinda nake so in tabbatar shine ni kayi using on me. Shikenan"
Ya sauko shima "haihuwa kuma fa? Ko shikenan mun daina haihuwa kike nufi?" Nace "Allah ya saka albarka a abinda muka samu, a wannan halin da muke ciki ma ni ba son kara wasi yayan nake yi ba, za kuma mu cigaba da haihuwa a lokacin da komai ya daidaita but not before" nayi kamar zan fita ya finciko ni ya hada ni da bango
"You can't do this. I am your husband kuma ina bukatar ki now. Ina tarbiyyar ki da ilimin ki na addini suke?" Na juya ido na "tarbiyya? Ilimi? Na siyar dasu a kasuwa na siyo hankali"
Sai ya sake ni, na juya na fice daga dakin na koma guest room amma sai na bar kofa a bude na kwanta. Ba jima da kwanciya ba na ji fitarsa sannan naji ya tayar da mota, na mike da sauri na daga labule ina leken sa, kar dai gurin wata zai tafi kuma. Na shiga uku.
Ina kallo ya fita da motar daga gidan sai na zame na zauna a bakin gadon tare da dafe kaina. Ko dai nayi kuskure ne?
Ina zaune naji dawowarsa, na sake tashi da sauri na leka shi. Ya fito ya shigo cikin gidan, nayi sauri na kwanta tare da lulluba sai gashi ya bude dakin ya shigo sannan ya kunna fitila, na mike zaune ina kallon sa sai ya jeho min wani dan karamin kwali da baifi girman na ashana ba, na dauka ina kalla sannan na farke shi ba dauki abin ciki, a raina nace "wannan dan karamin abun shine condom din, but ta yaya yake fitting wannan abin"
Yace "shikenan abinda kike bukata ko kuma akwai saura?" Na gyada kai "shikenan" sai ya yaye bargon da na rufa da shi ya hawo gadon, but still ransa a bace yake, bacin ran kuma har a jikina sai da naji shi dan sai da yayi punishing dina sosai ni kuma na karbi dukkan punishment dina and gave him something in return, something da nasan duk inda zaije, duk gurin wadda zashi ba zai taba samun irinsa ba. Love.
*Forgive the typos please*
Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din
0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank
Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020
Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020
Please banda kira, WhatsApp only
*wannan littafin na siyarwa ne a bisa amana, idan baki siya ba kar ki karanta, in kuma kin siya kar kiyi sharing, idan kika yi kinci amana kuma ke da Allah*
*Maryam*
Ranar Umar ne ya tashe ni sallar asuba "assalatu khairun minal naum" ya fada min a kunne na. Na bude ido ina kallon sa, yayi min murmushi sai na juyar da kaina gefe dan kar in mayar masa da murmushin dan ba wai huce wa nayi ba. Ban ankara ba sai jin cizo nayi a kunnena, nayi kara na rike kunnen sannan na juyo da sauri na dauki pillow zan dake shi da shi sai ya sauka daga kan gadon yana dariya kamar ba shine bacin rai jiya da dare ba. Na nuna shi "wallahi sai na rama" ya daga kafada "sai dai ki rame kuwa ba dai ki rama ba"
Na juya na kwanta tare da sake jan bargo, ya sake zagayowa ta side dina "ki tashi fa, kin san dai sai kinyi wanka ko?"
Na bude ido na again ina kallon sa, sai naga kamar wanda ya sake yin wani kyau na musamman a idona, shima fuska ta yake kallo sannan a hankali ya kai hannun sa ya shafa gefen fuskar yace "kina da kyau sosai Jidda. Ina son ki sosai" sai na rufe ido na ina jin wani irin mixed feelings akan maganar sa, zuciyata tana neman budewa amma kwakwalwa ta tana hanata.
Sanda na bude idona baya dakin sai kamshinsa.
A ranar bayan yaje office ya dawo yake gaya min cewa anyi approving annual leave din da ya nema. "Da ina da isashshen kudi ma da waje zamu fita, mu je mu shana" na danyi masa murmushi "su shanawa manya" yace "Allah kuwa. But zan fara tanadi next year Dubai zan kaiki" nace "Allah ya kaimu. To yanzu ina zaka kaini din?"
Yace "Abuja nake so muje, amma kuma ina so mu fara zuwa Lagos first ki je kiga gidan mu, baki taba zuwa gidan mu ba fa?" Na juya ido "to laifin waye? Kai ne baka kaini gidan naku ba ai" yace "zan kai ki yanzu to, and I will show you around ki ga birnin ikko"
Tun daga nan muka fara shiri, ninda shi da yara, Mufida tace zata ni mu tunda suna hutu a lokacin sai yace ba zamu je da ita ba gida zai mayar da ita, sai a lokacin yake gaya min cewa ta samu spill over a makaranta, nayi mamaki sosai dan bata gaya min ba ko da wasa.
A daren ranar ne kuma na bashi labarin abinda nake tunani game da ita "Mufida fa ina tunanin samari ne suke haa ta karatu, ka ga yanzu chats din dare taje yi da phone calls kuma bata yi a gaba na sai taga bananan, sannan kuma nayi kokarin in bugi cikinta tayi min hirar saurayin amma taki kulani kamar boye shi take yi. Gaskiya ya kamata a saka ido sosai a kanta"
Yayi shiru yana sauraro na kamar mai tunani sai yace "dan tayi saurayi a yanzu bana jin akwai matsala tunda ya kamata ace tana da saurayin by now" na gyada kai nace "yes, amma ba saurayin da zata ke boye shi ba, ba kuma saurayin da zai hana ta karatu ba" ya gyada kai "haka ne. Abinda za'a yi shine idan munje Lagos zanyi magana da Baba a kanta sai a saka ta fito da miji a hada auren ta dana Muhsina"
Kwana biyu bayan nan muka ajiye Mufida a gida gurin Mama muka zarce airport muka tafi Lagos din. Sati daya muka yi a can, naga gidan su Umar naga gurare da yawa mun kuma shana kamar yadda yace zamuyi, kusan kullum ba gida muke wuni ba, kullum da akwai inda yake so in gani ko kuma wanda yake so mu hadu dashi.
Sai dai matsala daya dana fuskanta a Lagos din itace Aunty wadda ita muka tarar a gidan dama mun bar Mama a Kano, Aunty gabakidaya ta chanja ta zama kamar wata stranger, auntyn da na sani mai kirki da fara'a wadda ta mayar dani kamar wata kawarta Umar kuma kamar wani abokin wasan ta amma sai ya zama tunda muka je gaisuwa ce kawai take hada ni da ita, sai na lura shi umar din ma ko gaisuwar bata shiga tsakaninsu tunda muka je.
Dakin da yake matsayin nasu Mufida muka sauka, shima ba ita ta bude mana ba Umar ne da kansa yaje dakin Baba ya dauko key din, dan da cewa yayi mu zauna dakinsa, ni kuma ina ganin akwai kunya tunda Aunty tana nan kamata yayi mu sauka a cikin gidan tunda shi dakinsa a waje yake, amma sai ta shanya mu a falo muka yi ta zama tayi tafiyarta dakin ta, sai mai aikinsu ce ta kawo mana abinci da lemo.
Sai da Umar din ya shigo sannan ya dauko key din ya bude mana dakin kuma ya saka mai aikin ta gyara mana, na dauka zaiyi magana ko yayi mita akan abinda tayi musamman saboda nasan yadda ya raina ta amma sai naji bai ce komai ba, bayan an gama gyaran dakin ya taya mu shigar da kayan mu sannan ya jaddada min duk abinda nake so a kitchen in shiga inyi kar in jira komai.
Sai naji babu dadi a raina tunda an saba ba haka ake ba, Aunty idan ita ce a kano ma nafi son zuwa gidan su Umar saboda nafi sakin jiki da ita akan da Mama duk da dai itama Maman ba wai tana da problem bane ba.
To yake ma dai bama wuni a gidan sosai ya saka abin bai dameni sosai ba, mostly har mu fita bana ganinta sai ace min tana sama, ni kuma ban taba hawa saman ba, in mun dawo ne sometimes zamu same ta a kasa, shima gaisuwa kadai zamuyi ko su Yasmin bata yiwa wasa yadda ta saba a da.
Har nayi kamar zanyi shiru dai amma sai na kasa na tambayi Umar "ni kuwa Aunty, nace ko fada kuka yi ne da ita?" Ya yamutsa fuska "fada kuma? Wanne irin fada ana zaune kalau?" Nace "a'a nasan yadda kuke ne kamar abokai amma kuma yanzu sai naga kamar duk lamarin ya chanja, bata kula ka bata kula mu, ni kuma bansan wani abu ya faru ba shine dai nace bara in tambaye ka"
Sai yace "wai da gaske bata kula ku? Ai ni ban lura ba? To me yasa?" Na saki baki ina kallon sa, tabbas ba zai ce wai bai lura ba sai dai in baya son yin maganar, sai kawai nayi shiru ban kuma cewa komai ba, na dauka zai bar maganar shima amma sai maji yace "kuma babu wani abu da kika yi mata? Ko kuma kinyi mata wani abu ne ba ki sani ba?" Na dauke kaina gefe nace "ni babu wani abu da nayi mata fa" ya daga kafada "maybe she is just moody, waya sani ko period take"
Ya karasa yana dariya, na juyo na harare shi "auntyn? Auntyn kake gaya wa haka?" Yace "ita din fa, gabakidayan ta nawa take auntyn na tabbatar tana yi bata daina ba, maybe ma nan kusa ki ga twins sun samu kanwa ko kani"
Sai nayi murmushi kawai, Aunty tana da burin haihuwa dan in dai kuka zauna sai tayi maka hirar haihuwa da babies da sauransu, na tabbatar shi Baba ne baya so zai ce sun ishe shi haka ko kuma dai wani abu. Ganin ya shashantar da maganar sai na bar ta ni ma.
Ban samu munyi wata magana sosai da Aunty ba sai ana gobe zamu tafi na same ta a kitchen tana aiki, na gaishe ta na fara tayata sai na tambaye ta "Aunty ina Ummi kuwa? Gashi tayi candy ballantana ince ko tana school kuma naga bata Kano na dauka tana nan sai da nazo na tarar bata nan" sai naga ta kalle ni, for a second sai naga kamar kallon tausayi take min sannan tace "Jidda Ummi ta koma gidan su, tana gida" na ajiye wukar hannu na na bude baki "gida kuma Aunty? Ganin gida taje yi amma ko?" Tace "no, ta koma can da zama gabaki daya"
Na girgiza kai "ayyah, Allah sarki Ummi, amma ko sallama bata yi mana ba da zata tafi, at least dai ai musan ta tafi din, babu dadi wallahi duk an saba da ita" naji har raina ina jin babu dadi duk da yarinyar ba wani sonta nake sosai ba. Sai Aunty tayi murmushi tace "kar ki damu, in auren ta ya tashi za'a gayyace ku ku je har Adamawa ku saka ta a lalle"
Da zamu tafi sai gashi ta debo kaya da yawa ta bawa yara, na yi mata godiya sosai na kuma nuna wa Umar sai yace "ta kyauta" kawai. A raina sai na tabbatar sun samu matsala ne amma tunda baya son maganar sai na barta ban kuma yi masa ba tare da fatan Allah zai daidaita su.
Daga Lagos Abuja muka tafi kamar yadda yayi min alkawari, dama already yayi using phone dina yayi mana reserving daki a hotel muka sauka, sai kuma ya nemi wani friend dinsa a can ya karbi aron mota tunda a jirgi muka je bamu da motar fita yawo. Sai da mukayi sati biyu a Abuja, Umar ya kashe kudi masu yawa a zaman nan namu kuma yayi mana hidimar sosai ni da yara komai mume so mun samu a gurinsa, anan na fahimci ma'anar shanawar da yake yawan fada dan duk wani gurin shakawata munje duk wani gurin wasan yara mun kai yaran mu duk wani gurin hutawa munje mun huta, 24/7 muna tare baya dauke idonsa daga kanmu, in mun dawo hotel din mu kuma mu huce gajiyar mu a jikin juna, sai gani na ina yiwa umar murmushi, daga nan sai gashi muna dariya tare, kafin mu dawo kano in ka ganmu ba zaka ce wani abu ya faru ba a zahiri, amma a badini zuciya ta bata manta da komai ba.
Bayan mun dawo Kano ne muka je gidan su zamu gaishe da Mama, sai muka tarar shima Baba yazo garin, anan ne ya zauna ya wanke Umar tas akan rashin samunsa da ba'a yi a waya "wannan ai sakarci ne da rashin hankali, kana namiji magidanci kuma ace babu waya a hannunka? Akan wanne dalili ne