Karfe a Wuta Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   66 / 67

195K to 198K   out of 199.8K words

ta raya mini maza kafin na farka daga baccin, na je na ga jauhar, ko zan farka dai na ganta."

"Na fara tafiya a duhun nan, har garin Allah ya waye. rana ta Waga, na isa unguwar mu, ban manta hanya ba. Sai dai Abbu ya tabattar mini da jauhar ta mutu, ni na kasheta, na tafi na bar masa gida. Mutanen unguwa suka din ga kallona, har da masu gudu."

"Babu tunanin komai ko tsoro, bayan na je dabarmu, su Walid suka karSe ni, suka kuma tabattar mini da cewar na rasa Jauhar."

"Na burkice musu, amma suka ri™e ni suna kula da ni, kawai sai ga sanarwa daga hukumar 'yan sanda, wai a kamo ni, a raye ko a mace, da fari suka ce na gudu daga prsion, daga baya kuma wai an sake ni ba bisa ™a'ida ba."

"Walid ya ce ""Kome za ayi, ba zasu yadda a sake mayar da ni a kulle ba, sun san ba zan taSa kashe 'yar madara ba."

"Na tarar da su da Wan mama, na san shi tun da na taSa yi masa rauni, shi ne ya bayar da gidan da muke zaune muke Soye."

"Idan nayi kamar na gaya musu, rayuwar da nayi ana bani training, sai na tuna aikin sirri ne, an gargaWemu a kan haka, kuma bani da evidence ni kaina bani da tabbacin cewa a gaske nayi wannan rayuwar."

"Bana iya bacci, bana iya cin abinci, ga azababben ciwon kai, ga nauyin ™irji, kawai na koma shaye-shaye fiye da da, duk da a wurin training ina shan sigari da wiwi, sai dai bana shan miyagun ™wayoyi, ko giya."

"Amma bayan tabattar da mutuwar jauhar, na cigaba da shaye-shaye ina fatan ko haukacewa nayi, na manta da duk wata rayuwa, wadda nake tunanin gaske ce ko mafarki, amma kayan cajin basa W aukata."

"Ganin Wan mama na din ga yi tamkar Nura, dan ba zai fi sa'ansa ba, ya din ga yi mini biyayya,"

"hakan ya sanya nake son sa sosai, saboda su Walid kullum cikin faWa muke, suna hana ni shaye-shaye."

"Shi kuwa samowa yake yi ya kawo mini, a hakan idan na bushi iska, sai na tafi gidana na dura ta katanga, na kan yi iya ™o™arina nayi kuka, amma bana iyawa, sai dai na yi ta jin ™unar rai da bugun zuciya."

"Na kan yi yin™urin zuwa na Wauki fansar abin da madaki yayi mini, amma su Walid su hana ni, suka samo mini waya keypad suka bani incase ina bu™atar wani abu, basa nan, Wan mama shi yake yi mini duk wata hidima, kawai wannan mutumin ya fara kirana, yana ™ara dagula mini lissafi. Kayan shaye-shayen ya zama basa Waukata, sai dai nayi ta tamSele, suna iya ™o™arin su a kaina, amma ba sa yi mini abin da nake so."

"Damuwa shaye-shaye suka ™ara tsunduma ni a wani hali, har nake yin™urin kashe kaina. Ashe duk wannan abun, mutanen nan suna bibiye da ni, da duk wani motsina, na din ga ™o™arin jami'an tsaron kawai su kamani, su yi duk yadda za su yi da ni, amma da nayi laifi, dan goge hanyar da za abi a kama ni."

"Walid ya zo ya bani labarinki, na ce ™arya yake yi, cutata zai yi. Bai ha™ur ba, ya kawo mini ke, kawai ™wa™walwata ta bani cewar, an haWa baki da ke an shirya wani abun ne, dan a kuma yi mini wani mugun abun, hakan ya saka na sanya miki ™arfe ko zan ga ainihin wacece ke, dan na san jauhar ba ta kaiki girma ba, ba ta kaiki waye ba, kuma babu yadda za ayi ta ganni ta kasa gane ni."

"Amma da ki ka faWi, ciwonki ya tashi, sai na ga kin koma ita sak, duk da ina jin haushin mata wasu lokutan, amma a sanadinta nake tausayin su, saboda tunawa da ita, na sai kayan treatment W in ta na asma, nake ajiyewa ina kallo, ina ganin kamar zata dawo. Shigowar ki rayuwata, ya ™ara rikita mini lissafi, Walid ya ce na sanar miki irin kamannin da ki ke yi da matata, na baki labarina, amma na™i."

"Na cigaba da barazanar kashe ki, saboda na kasa tantance jauhar ce ke ko ba ita ba ce, nayi ta ™o™ arin avoiding Winki, kar na aikata Sarna, saboda babu in da ki ka bar ta, sai kuma daga baya na ga zuwanki wurina, yana rage mini damuwa, kamar ke kin fahimci halin da nake ciki."

"Rigar da ake ta bibiyata da ita, ta wancan aikin ce, dan an tura mini sa™on zasu tafi da ni, na ™i kulawa, sai daga baya da na amince da ke, na ga dole ina bu™atar security ko dan lafiyar ki, na amince zan tafi nayi aikin, amma sai na samu nasara a kotu. Aka ce za a Waukar mini lauyoyi da zasu kare ni, zasu nemi a basu ni, su suyi na su binciken, su yi mini hukunci na ce ban yarda ba, ina da lauya, tsaro kawai nake bu™ata a tsare mini lafiyarki."

"Suka yarda da hakan, amma da zimmar zan fara yi musu aiki."

"Daga nan barrack Win kano, suka zo suka tafi da ni, aka bani kayan aiki, ciki har da tab Win hannuna, da rigar aiki da ki ke ganina da ita, sai dai ba kowa ya san ma'narta ba, ciki har da su Walid."

"A yanzu haka ina karSar salary, kuma ina aiki da NIA, ™o™arin ki ne zai sanya, na yi free na"

"cigaba da aikina, akasin haka kuma, zan iya komawa prison ne, babu ranar fitowata, duk da ba zan ce ma ban yi shekarun nan a prison ba, tun da kauwwame ni aka yi, aka hanani dukkanin walwala."

"Nabila tayi ™uri da ido tana kallonsa, cike da tsantsar mamakin duk wannan rashin mutunci, da cin mutuncin doka, a Nigeria ake aikata shi. Wani abun idan bai zo kanka ya faru ba, sai ka rantse da Allah ™arya ne ba zai faru ba. Har gara shi, da aka fitar da shi daga prison Win, taimakon sa"

"aka yi ta wani fannin, wasu kuwa canza musu gari ake yi gaba Waya, suje su yi rayuwarsu, saboda"

"tsabar masifa, a prsion Win ma bin sa aka yi za a kashe. Gaba Waya rayuwar Viper gaba a baya"

"take, sai dai ita ma tata rayuwar kusan haka."

"""Abla, talk please, jami'an tsaro na nemana, zan je a Wauki statement, kuma dole sai da ke zamu tafi, dan Allah ki daidaita nutsuwar ki, yanzu rayuwata tana hannun Allah, tana hannunki, nayi rejecting support Win da za a bani a hukumance, na zaSi cika miki al™awarin da nayi miki, ba zan"

"ja da baya na barki ba"""

"Ta Wago idanunta da suke tsiyayar da hawaye ta ce ""Wacece ni? Kuma wacece jauhar?"""

"""Ki na ji na? Shiyasa tuntuni nake jinjina yadda zan yi miki bayanin nan, ki nutsu ki karSi ™"

"addara a duk yadda zata zo miki"""

"Nabila ta ware masa manyan idanunta, da suka yi jawur, ta ce ""Ba ni ce jauhar ba, to ni wacece? Ko jauhar 'yar uwata ce? Dan girman Allah ka kaini gidansu na ga ko iyayenta ne, wata™ila muna"

"da ala™a"""

"Ya girgiza mata kai ya ce ""Babu tabbacin kina da ala™a da ita, bata taSa gaya mini cewar tana da wata 'yar uwa ba, ce mini tayi itakaWai mahaifiyar ta ta haifa a gidan, ta fita. Amma ke babu abin"

"da ki ka sani game da mahaifiyarki, da ahalinta?"""

"Ta ja wata irin ajiyar zuciya ta ce ""Idan ya kasance jauhar yar uwata ce, kenan ina da 'yar uwa ban"

"taSa ganinta ba, ban rayu da ita ba? An cutar da ni, wallahi an zalunce ni"""

"Viper ya ce ""Kar ki ce haka, ki bari sai mun tabattar tukuna, kuma wannan amsar dole 'yan"

"gidanku ne za su bayar da ita, amma mu fara gamawa da wannan case Win, kiyi ha™uri"""

"Tari ta fara yi, tana kuka ta ce ""Ni gaba Waya baka yi mini adalci ba, ka Soye mini abubuwa da yawa, da yakamata na sani, sai yanzu zaka gaya mini. Ni ka rabu da ni ma ka ™yale ni, ina ga"

"nima haukacewar zan yi"""

"Duk yadda Viper ya sauke jin kansa, yake rarrashinta, ta burkice masa, ta ce idan an ga dama a W"

"aure shi da igiya, case Win nasa ma ta fasa, ™arshe haka ya tashi ya rabu da ita."

***

"""Badi'a, anya ba zan gudu na bar ™asar nan ba, ina daf da yin faWuwar ba™ar tasa, wannan yarinyar ta dage sai ta ga bayana ta kaini ™asa, ya zan yi ne?"""

"Badi'a ta ce ""Naja, wallahi ki ka bari yarinyar nan ta ga bayanki, kin Wuma asara"""

"""Badi'a, kowace hanya ta toshe ta ko ina, duk masu goya mini bayan, sun ce wannan karon"

"lamarin yafi ™arfin su, shi kansa Indabo yana can Abuja, yana fuskantar tuhuma, EFCC sun dakatar da wasu daga cikin kadarorinsa, yana cikin tashin hankali, na rasa yadda zan yi""."

"""Wallahi kina guduwa asirinki zai tonu, ki jira kiga iya gudun ruwansu, tun da haryanzu ba su ce"

"komai ba, ba su tona miki asirin ba"""

"Kamar ta fasa ihu ta ce ""Yanzu jira zan yi sai sun fito sun tona Win? Ke kin san ba zasu bar ni ba, lallai Wan hakin da ka raina, shi ke tsole maka ido, babu ™o™arin da ban yi na kawar da yarinyar"

"nan ba, amma abu ya gagara, amma duk da haka ba zan zuba ido ba, sai na san abun yi""."

***

"Abdul kuwa ya yi sintiri tsakanin Kano da Abuja, babu adadi, amma ya kasa ganin Indabo, hakan ya sanya ya tabattar wa da kansa cewar Indabon ne ya Wauke ramma."

"Duk yadda mahaifiyar ramma, ta bugi cikinta, ramma ta nuna mata babu abin da ya faru, Abdul"

"ajieta kawai yayi, duk da ya ce ya aureta."

"Maman ramma ta ce ""Har na ji sanyi, dole a zo a raba auren nan, dama ba da yardata kawunki ya aurawa wannan tsohon mara mutunci ke ba, saboda kuWi da tsinannen son abin duniya yayi mini haka. In sha Allah yaron nan sai Allah ya tozarta shi kamar yadda ya tozarta mu, sai Allah ya wula ™anta shi, kamar yadda yayi mana"" jin Addu'a ramma tayi har cikin zuciyarta, dan sai da cikinta ya"

"motsa, tayi shiru bata amsa da Amin ba, ta san duk inda yake yana can hankali a tashe."

"""Amma ramma, kin tabattar ba abin da ya haWaki da mutumin nan? Mutumin da yayi miki fyaWe"

"shi ne zai aure ki kawai ya ajiye ki?"""

"Cikin tsoro da rashin gaskiy, ramma ta ce ""Eh, Soye ni yayi saboda kar asirinsa ya tonu, cewa aka yi da ya kashe ni ma, shi ne bai kashe ni ba. Kuma wai ya biya mini kuWin makaranta na cigaba"

"har jami'a"""

"""Allah ya kiyaye, ba ma bu™atar duk wani abu daga hannunsa, da haka zai yaudaremu, in sha Allah sai an hukunta shi, barrister nan tayi mini wannan al™awarin, sai an gurfanar da shi, ya girbi abin da ya shuka, ga kisan kan da suka yi wa wannan tsohon, da suka ™alawa sharri, Allah dai ya"

"watsa shi, daga shi har wanda suke goya masa baya"""

"Ramma ta kawar da zancen, ta hanyar cewa ""Mama wai a nan zamu yi ta zama?"""

"Ta ce ""A'a, nima wannan Alhajin ne ya saka aka Waukko ni wai idan aka bar ni, nima za a iya cutar da ni, ban san zuwa yaushe zamu zauna a nan Win ba, amma ina ga da komai ya daidaita sai"

"mu tafi"" Ramma ta jinjina kai."

"Maman ramma ta bi ta da ido, ganin yadda duk jikinta yake a sanyaye, ta kalli fatar ramma yadda"

tayi haske take ta she™i.

"""Rahama"""

"""Na'am mama"""

"""Wai me ki ke ci ne a hannun nasa, na zata a wahale zan ganki, ki gaya mini tsakani da Allah idan"

"akwai wani abu"""

"""Mama babu komai fa, nifa tun da ya ajiye ni baya ™asar, sai masu kula da ni"" mama ta jinjina kai"

"kawai, ba ta sake magana ba."

"Viper ya ha™ura da azabar kishin da yake Wawainiya da shi, aka yi zama na musamman da shi da Alhaji mu'zzam, da shugabannin sa, aka sake jaddadawa Al'amin, Alhaji mu'azzam tainakonsa yayi, kuma tare da haWin kan Alhaji mu'azzam komai ya tafi daidai, kasancewar sa babban mutum a Sangaren harkar tsaro."

"Sai kuma aka yi masa al™awarin ba shi duk wata kariya, da shi da Nabila, tun da haka ya zaSa,"

"amma muddin suka yi failing a shari'a a kotu, babu wani abu da za a kuma sake yi masa. Ya ce ya amince, babu gudu babu ja da baya Nabila ce lauyar da zata tsaya masa."

"Sai dai Nabila gaba Waya ta hargitse, Viper ya kasa gane kanta, gashi an gayyace shi hukumar yan"

"sanda, ya je ya bayar da bayani, amma Nabila fafur ta ce ba zata je ba."

"Sanarwa kuma ta fita, muddin Viper bai kai kansa ba, order kotu zata koma arrest order."

"Nabila na zaune, zuciyarta a cunkushe ta rasa abin da yake yi mata daWi, lallai tana bu™atar ganin"

"Abba, ko ta halin ™a™a Viper ba shi da niyyar yi mata bayanin abin da take son ji."

"Ta ga wayarta a gefen gadon da take kai, tayi sauri ta Wauka, ta kunna tana dudduba sa™onni."

"A What's app ta tarar da message, wai gari ana ta yaWa rumors, cewar Viper ya saceta, ba a san in"

"da take ba, wasu suna Allah ya ™ara, wasu suna yi mata addu'a."

"Ta buWe message Win Nasir, ta saurari voice message Win da ya turo mata."

"""Haryanzu wanda ki ke i™rarin karewa, bai bayyana a gaban hukumar yan sanda ba, idan ya wuce wa'adin da muka bashi, order kotu zata sauya, ga shela da ake ta yi, na cewar ya sace ki, ba a san in da ki ke ba, ko a nan sunanki ya Saci, am did on you."

"Knocking aka yi, tayi shiru, dan ta zata Viper ne, ta ajiye wayar."

"Wani narkeken mutumi ne ya shigo, tare da barrister Habib, da sumayya, da kuma Walid."

"Zama tayi sosai tana kallonsu, sumayya ta ™arasa ta zauna a kan gadon ta ce ""Nabila, ya kike kina"

"cikin ™oshin lafiya?"" Nabila ta jinjina mata kai."

"Mutumin ya ce ""I salute you barrister, kallabi tsakanin rawuna"" yayi maganar cikin gurSatacciyar"

"hauss, amma da alama ya ji hausa."

"Ta Wan yi murmushi ya™e, ta kalli Walid ta ce ""Oga walid"""

"""Na'am barrister, ya ki ke ya ™o™ari?"""

"""Alhamdilillah"" ta din ga bin su da ido, dan bata san dalilin zuwan su duka ba."

"Walid ya ce ""Barrister, na san mun yi miki laifi, tun da fari na so Viper yayi miki bayani, amma ya ™i, kin san shi wasu lokutan da taurin kai, kuma na san kin yi ha™uri da shi, amma dan Allah ki janye batun cewar ba zaki tsaya masa ba, ki yi ha™uri dan Allah, ba zamu iya jure ganinsa ya koma prison ba, kiyi wani abu a kai, wanda kuke ™alubalanta, suma ba zasu zauna haka ba, dole zasu yi"

"™o™arin yin wani abu suma, ki taimaka"""

"Šaya mutumin ya ce ""Duk wani support da zamu ba shi a hukumance, ya™i yarda, ke kaWai ce"

"hope Win sa, kar ki ce a'a, kiyi ha™uri, a ™arasa wannan case Win, sai koma menene ya biyo baya"""

"""Meyasa ya Soye mini abubuwa irin wannan?"""

"""Tsarin aikinmu ne a haka, haryanzu ke kaWaice lauyar sa, ke ki ka sani, su kansu yanzu da muka zo tare ba komai suka sani ba, ga abokin aikinki, dole kina bu™atar sa, ga ™awarki kina bu™atar ta,"

"ga abokansa da sun san komai"""

"Barrister Habib ya ce ""Ga case Win ramma ma"""

"Mutumin ya ce ""Yess, ke fa yanzu idon duniya yana kanki, ba laifinsa bane, kin san ba mai yawan"

"magana bane ba, kuma tsarin aikinmu ne, yanzu abin nan da ya gaya miki, zai iya zama da hukuncin kisa a kansa, banda mun san a situation Win da yake"""

"Walid ya ce ""Yana asibiti ma, ciwon cikin nan da yayi kwanaki ya kuma tayar masa, hantarsa ta kumbura, yana asibitin sojojin nan da aka Waukko ki"""

"Nabila ta numfasa, ta ce ""Muje zan ganshi, kuma ina son zuwa office Wina, zan koma aiki"""

"Mutumin nan ya ce ""Is ok, zaki koma bakin aikinki, amma a ™ar™ashin kulawar mu, ™asarmu na"

"san rayuwar Viper"""

"""Amma ku ka bari ya kusa haukacewa, aka Sata masa suna"" mutumin yayi murmushi ya ce ""We"

"are trying our best now"""

"Sumayya ta ce ""Nabila ina son magana da ke fa"""

"""Ni da nake kare Wan ta'adda, me ki ke so a wurina?"""

"Sumayya ta yi murmushi ta ce ""Arfan Abbanta,

66 / 67