Karfe a Wuta Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   34 / 67

99K to 102K   out of 199.8K words

aka nemi a mayar da case Win wai sharri muka yi wa yaron."

"Wallahi ™arshe yarinyata fiya-fiya ta sha ban sani ba, yar shekara goma sha huWu ta mutu. Wallahi matar nan azzaluma ce, bamu da wurin da zamu je, mu nemi hakkinmu sai wurin Allah, haryanzu idan zance yayi zance a kan tayar da maganar abun da ya faru da yarinyata, wanda hakan ba ™"

"aramin tsaye mini yake yi ba"" tayi maganar tana kuka mai ban tausayi."

"Nabila ta tashi ta rungume matar, tana rarrashinta ta ce ""Ki yi ha™uri dan Allah, ki kwantar da hankalinki, Allah ya ji™anta, kuma in sha Allah da ikon Allah sai mun kai matar nan ™asa, zan yi iya yi na, in bankaWo duk wani mugun abu da ta aikata muku, kuma sai ta girbi abun da ta shuka, ku yi ha™uri. Yanzu duk zaku bani adress Win ku, zan bi cases Win Waya bayan Waya, na tabattar"

"da abun da ya faru kafin na san abun yi"""

"Jikin Nabila yayi sanyi sosai da sosai, da jin abubuwan da Bunkure take aikatawa, tamkar ba 'ya"

"mace musulma ba, da matan ke i™rarin ciwon ´a mace, na 'ya mace ne."

"Har kuWin mota ta basu, bayan tafiyarsu ta kalli barrister Habib ta ce ""Yaya habib, ka ji wani"

"yahudanci? Ina laifin ta tsaya a kan iya kashe auren an yi wa 'yar auren dole?"""

"""Ke ce baki san wacece ita ba sai yanzu, wannan wata Soyayyiyar a™idarta ce, na bawa mata"

"damar ™in zaman aure da lasisin karuwanci. Tana saye yaran da kuWi, da abun duniya wurin cusa musu wannan mummunan ra'ayin, da koyar da su daidaiton jinsi tsakanin su da maza""."

"""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, amma duk da haka Alhamdilillah, na samu hints a kan yadda zan"

"bankaWo asirin matar nan, and one more thing kuma"" ya kalleta ya na jiran me zata ce."

"""Maganar da muka yi da kai kwanakin baya, a kan case Win Aminu Viper"""

"""Ina jinki"""

"""Naja'atu Bunkure tana cikin tawagar lauyoyin da suka tsaya kai da fata a kan shari'ar da aka yi masa. Kuma ka san ita ungulu ce ba ta jewar banza, dan haka akwai manufa a cikin shiga shari'ar da tayi. Viper ba Wan siyasa bane ba, kuma ba shahararren mai kuWi bane ba, balle ace tsaya masa tayi a shari'ar. Dan haka akwai ayar tambaya a kan charges Win da aka yi masa na kisan kai."

"Take a look at it barrister, an tsare mutum shekara biyar, an yi masa shari'a sau biyar kawai, an kai"

"shi prison an ajiye babu conclusion na shari'ar, is je guilty or innocent? Kwatsam an ce ba a ganshi a prison ba, kuma an cigaba da nemansa, ruwa a jallo, anya akwai gaskiya a lamarin nan kuwa?"""

"Ya tsura mata har ta gama, yayi murmushi ya ce ""Haka kwanyar nan take cike da basira, amma aka ™arar da ita a wurin iyayi da kwalliya?."

"Maganarki gaskiya ce Nabila, amma ina rabaki da case Win Vipern nan, akwai bada™ala sosai a"

"kan case Win""."

"Nabila ta ce ""Me da me ka sani a kai?"""

"""Nothing much, kawai na san dai akwai bita da ™ulli ne a ciki sosai"""

"Ta jinjina kai ta ce ""Haka ne, bari na tafi gida, yau a matu™ar gajiye nake"" tayi masa sallama, ta"

"tafi office ta ™arasa shirinta, ta tafi gida. Ta sake karo da file a office Win."

"Cikin mamaki ta Wauka, ta fara buWewa."

Aka rubuta continuation a ciki.

"Cigaban tarihin Naja bunkure ne, bayan rape da aka yi mata, cousin brother Win ta, aka rufe case aka ce abu ne na dangi, bayan ta ™ara girma tayi aure, ta sha wahala sosai a hannun mijinta na farko, ya azabtar da ita tamkar baiwarsa, ko haihuwa ba ta yi ba auren ya mutu."

"Yayanta ne ya taimaka mata, ya mayar da ita makaranta, tayi candy, ta shiga jami'a, sai dai bayan rasuwar yayanta, aka rasa mai sponsiring Win ta, ta cigaba. Mahaifiyata na can wani garin tana aure, babanta kuma ya ce ba ruwansa da ita, tun da ta™i zaman aure."

"A lokacin har wurin Wan majalisar su, ta je neman kuWin makaranta, lokacin yana tare da Indabo, indabo ya ce zai bata, amma sai dai ayi bani gishiri na baka manda. Ta amince tun daga nan, ta"

"zama tamkar matarsa su watse ya biya mata kuWin makaranta, babu wani sirri nasa da bata sani ba."

"Ta nemi ya aureta, bayan tayi graduation, amma ya™i, ganin haka ya sanya, ta samu wani suka"

"daidaita ya aureta, sai dai Indabo ya cigaba da bibiyarta."

"Ta fara aiki a matsayin lawyer mai zaman kanta, Naja tana da burin yin luxry life sosai, sai dai mijinta yana da rufin asiri amma ba irin wanda take hange ba, Indabo yayi mata al™awarin haWa ta da manyan mutane, lokacin ya zama Wan majalisa, wanda zata din ga samun alkhairi da damarmaki."

"KwaWayi da buri, ya sanya suka koma ruwa da aurenta, ya din ga kashe mata kuWi, yana kuma haW ata da manya. A wurinsa ta koyi shaye-shaye. Tsakanin ta da mijinta babu ragayya ko kyautatawa,"

duk son da yake nuna mata da kulawar da yake bata sam baya gabanta.

"Ta fara tashe sosai tana shahara, ana programs da ita a kafafen watsa labarai, ta buWe ™ungiyar ta ta kanta, bayan joining Win ™ungiyoyin yahudawa, masu da'awar daidata jinsi, reshen Nigeria, ta"

cigaba da yi musu aiki ta ™ar™ashin ™ungiyar ta.

"Sai dai a haka take miyagun har™allarta, na yi wa manyan mutane safarar mata a birnin tarayya,"

"musamman ™ananan yara, da akan yi amfani da su saboda asiri."

"Red handed mijinta ya kamata, chats Win ta da wani minista, na ™azanta, yayi kuka, amma ko a"

"jikinta, ta ce idan ba zai iya ba ya rabu da ita. Haka ya saketa, ta samu cikakken gashin kanta."

"Ba ta taSuwa, ko da kuwa tayi laifi, yanzun nan ™ungiyoyin kare hakkin Wan Adam zasu shiga"

"lamarinta. Ta din ga binne mutane ta hanyar bayyana musu kyawawan ayyukanta, da Soye na laifin."

"Bayan mutuwar aurenta labari ya bazu, mutane suka din ga tsinewa mijinta, wai ya saki macen"

"kirki, aka yi hira da ita, ta din ga kuka tana yi tsohon mijinta sharri kala-kala."

End the story.... Aka rubuta a ™arshen page Win.

"Wani irin gumi, ya din ga tsatstsafowa Nabila, ta ma rasa abun yi, da tunanin da yakamata tayi, ba ta bari ta takura ™wa™walwarta wurin hasaso waye ya kawo mata file Win a karo na biyu ba,"

kawai ta Wauki jakarta ta fita.

***

"Sumayya ce a tsaye tana kuka wiwi, shi kuma ya zuba mata ido, ko ™iftawa baya yi, sai da tayi mai isarta sannan ya ce ""Kukan ya isa haka, meyafaru?"""

"Ta share hawayenta ta ce ""A gaskiya sir, ni na gaji da aikin nan, na samu matsala da ni da Nabila, ni Nabila ba ™awata ce kawai ba, ´ar uwata ce, ta riga ta yi fushi, ba zata saurare ni ba, ni ban san wanda ya gaya mata ina bibiyarta ba, ga wancan honorable Win ya addaba mini, duk motsina sun sani, sai kuma sun tambaye ni, me tayi me take ciki, banda barazana da suke yi mini ba yau ba gobe, ni dai dan girman Allah ka yi wani abu a kai, kar ni ko ita ayi wa wani illa, indabon nan fa"

"ba imani ne da shi ba"" ta ™arasa maganar tana sake fashewa da kuka."

"Yayi murmushi ya ce ""Haba ´ar jarida, ya da kuka wiwi haka da karaya nan da nan? Da kin sanni, kin san zan taimake ki? Baki san ya aka yi na gane Indabo yana yi miki barazana ba. Har na shigo lamarin ba, dan haka ba zan bari a cutar da ku ba, dukkaninku a kan gaskiya ku ke, sai dai ita naga buyaginta yayi yawa."

"Ki yi ha™uri ku daidaita, da haka zan cigaba da yi mata supplying abubuwan da take bu™ata a"

"harkar shari'ar nan"""

"""Sir yanzu fa ka gama cewa buyaginta yayi yawa, sai ce mini munafuka take yi, babu yadda"

"tsakanunmu yanzu"""

"Ya ce ""No, tayi fushi ne kawai, and ki ™ara kiyayewa sosai da sosai, ki daina bari tana gane kina"

"bibiyarta""."

"Sumayya ta ce ""Yanzun ma, wallahi ina kiyayewa, ban san yadda aka yi ba"""

"Ya din ga rarrashinta, sannan ya saka aka Wauke ta a mota, aka mayar da ita gida."

***

"Nabila da ™yar ta isa gida, ta watsar da kayan a kan gadonta, ta fara kiran wayar Viper, amma a kashe, ta kira ta Walid amma baya Wagawa, haka ta ha™ura ta shiga banWaki tayi wanka ta yi alwala ta fito."

"Har washegari da safe, Nabila tana neman layin Walid, hankalinta ya ™ara tashi, tayi tunanin ko"

wani abun ne ya same shi.

"Tana saka kayan abinci a motarta, Nasir ya fito."

"Ta ce ""Yaya ina kwana?"""

"Ya amsa da ""Lafiya ™alau, wai ina ki ke zuwa da kwanukan abinci kwana biyun nan ne?"""

"Ta Wago ta kalleshi ta ce ""Ci nake yi mana, wataran ai wuni nake yi bana gida"""

"Ya Wage kafaWa ya ce ""Ban sanki da dakon flask ba, saboda haka kin gwammace ki ci biscuit da"

"sauran kayan ciye-ciye"""

"""Haba yaya, yanzu ba mota ce da ni ba? Kuma zan je in ta cin abinci nikaWai duk ga mutane ne a"

"wuri?"""

"Ya girgiza kai ya ce ""A'a, amma yanzu ™arfe bakwai saura kwata, har shida da rabi kin fita, saS"

"anin da har goma saura sai ki kai a gida"""

"Ta tsaya sosai ta dube shi ta ce ""Yaya me kake nufi ne? Ka daina Soye-Soye ka fito fili ka sanar"

"mini cewar, tuhumata kake yi, da aikata rashin gaskiya mana"""

"Yayi murmushi ya ce ""Ai ba a tuhuma sai an tabattar da zargi my dear"""

"""Da ka daina zargin, dan wahalar da kanka kawai zaka yi, ko kuma irin abun naku zaka yi mini na"

"masu kaki"" tayi maganar tana murmushi."

"Shi ma murmushin ya yi, ya ce ""A sauka lafiya"""

Ta amsa da Amin ta tafi.

"Tana tafe a hanya sai ga kiran wayar Walid, ta Waga wayar ta ce ""Oga Walid, sai kiranka nake yi a"

"waya, shi wayarsa ba ta shiga, wayarka kuma baka Wagawa"""

"Walid ya ce ""Bari kawai, kin san halin mutumin naki sai a hankali ai, jiya bayan tafiyarki, ya kafa mitar sai an sallame shi daga Asibiti, da mu da likita muka din ga rarrashin sa, yayi mana banza, mun fita salla ya gudu, baki ga yadda hankalinmu ya tashi ba, na ce musu kawai mu koma gida, dama ya saba irin haka, ko lokacin da ™anwata take raye, haka take fama da shi, idan aka kwantar"

"da shi, da Wanyen ciwo haka zai bar asibiti sai dai ta ™arasa masa dressing a gida ya warke""."

"Nabila ta ce ""Allah sarki, Allah ya yi mata rahama, shi kuma ya bashi juriya. Kana ji na, zan shigo dan ga abinci ma nayi, yayana ya fara saka mini ido ne, dole na canza takuna, zuwa azahar zan bar"

"motata a chamber, zan zo in sha Allah"""

"Ya ce ""To Allah ya kawo ki, dan zuwan naki yana da amfani, ya™i cin abinci ya ™i shan magani,"

"yana kwance kawai tun jiya"""

"""In sha Allah zan zo, ayi masa sannu"" ta ajiye wayar tana murmushi, rigimar Viper tana da yawa,"

idan ba ka da ha™uri ba zaka iya da shi ba.

"Har ta fara neman lambar sumayya, sai kuma ta fasa kiranta, dan har ta manta sun yi faWa. Kawai ta din ga jin ta wani iri, akwai abubuwa da dama da take son gaya wa sumayya, saboda kusancinsu da sha™uwarsu, ta musamman ce. Sai dai haryanzu tana mamakin dalilin da zai sanya a din ga"

"bibiyarta ta hanyar sumayya, kuma waye yake bibiyar ta ta."

"Sai dai ta fara zuwa courts Win da take da trials, ta gabatar da shari'oi, sannan ta koma asibitin da"

"aka kai ramma, lokacin da aka yi mata fyaWe."

"Ta nemi a bata copyn report Win da aka yi confirming rape case Win, aka ce an bawa ´an sanda."

"Ta nemi ganin likitan da ya kula da ita, aka ce ya tafi ™aro karatu, a bata lambarsa nan ma aka cigaba da yi mata yawo da hankali."

"Sai da ta gama zagayenta, sannan ta ajiye motar a wani wurin parking, ta karSi pass, ta tafi wurin"

su Viper.

"Yau a tsakar gida ta tarar da shi, sun shimfiWa masa tabarma, yana zaune yana ya danna wayarsa,"

"sai dai idanunsa sun Wan yi wuri wuri ya faWa, gabansa kuma kwalin sigari ne da lighter."

"Tayi sallama duk suka amsa, ya Waga kai ya kalleta ya mayar ya sunkuya."

"""Ohhh masha Allah, the most handsome man ever saw, kaga yadda ka yi kyau sosai da sosai"" ta nemi wuri ta zauna a gabansa ta ce ""Manya gatan wasa, fisabilillahi mutum sai ya gudu daga"

"Asibiti ba a sallame shi ba? Idan kuma bai warke ba fa, ni gaskiya ban ji daWi ba"""

"Ba ta saka ran zai kulata ba, ta ce ""Ina wuninku, ya mai jiki kuma?"""

Suka amsa da sau™i.

"Walid ya ce ""Ba yadda bamu yi da shi ba, amma sai nemansa muka yi muka rasa"""

"Tayi dariya ta ce ""My, ya kake haka ne, duk muna ta taka, amma kai ko a jikinka. Wannan sigarin ina fatan ba sha aka yi ba, kaga an ce jininka ya hau, kuma kana smoking ba zai sauka da wuri ba, an ce mini baka cin abinci, duk ka rame ai ba zan ji daWi ba"" ta janyo ledar abinci ta ce ""Ka yi ha™ uri ban kawo abinci da wuri ba, Yaya Nasir ya fara saka mini ido"" ta ™arasa maganar tana mi™a"

"masa plate, da cup Win da ta zuba masa kunun alkama."

"Ya saka hannu ya karSa, ya fara ci."

"Liti ya ce ""Wato mai zamani mune dai ba ma yi maka gwaninta ko?"""

"Nabila ta yi murmushi ta ce ""Ka san wani abu?"" Ya girgiza mata kai alamar a'a."

"""Ni fa na gaya wa Sumayya, na san tana bibiyata, duk da jiya ta kawo mini wasu mata, da suka yi mini complain a kan Bunkure, amma mun yi faWa da sumayya."

"Sannan an sake ajiye mini file a office Wina, na ™arashen labarin Naja'atu Bunkure."

"""Ku ka yi faWa ba ™awarki ba ce ba?"""

"""Eh, amma meyasa zata ci amanata?"""

"Ya kalleta ya ce ""Ya aka yi ki ka tabattar da cin amana ne ya sanya take bibiyarki?"""

"""Saboda kai ka gaya mini"""

"""Ban ce tana bibiyarki dan ta ci amanarki ba, kuma baki da tabbacin da gaske nake ko akasin"

"haka"""

"Ta gyara zamanta ta ce ""A labarinka da na ji, baka ™arya dan ka ci amana, kuma bana tunanin"

"zaka fara a kaina"""

"Ya jinjina kai ya ce ""Bani wayarki"" ta Waukko wayarta ta bashi, ya nutsu sosai yana ta daddanawa."

"""Yayanki ma na ™o™arin yi wa layinki kutse, sai dai na rufe damar hakan. Yana zarginki a kan da shi kansa bai san menene ba. Yayanki ya ga Indabo yana yi masa aiki a kaina, yana kuma gargaWin sa a kan abun da ki ke yi a kan bunkure, na san zuwa yanzu ya matsa miki lamba a kan ki rabu da"

"ita"""

"Ta waro ido ta ce ""Ya aka yi ka sani? Anya yayan kuwa?"""

"Ina bibiyar kiran wayarsa ta hanyar amfani da wayarki, hakazalika duk wasu maganganu da yake yi, recording Win suna kan computer ki. Wayarsa da Indabo kawai nake bibiya, ba ruwana da"

sauran harkokin sa.

"Ta ce ""Subhanallah, amma yaya ya bani kunya, shiyasa yake ta uzzura mini? Amma nima ka yi"

"hacking Win wayata kenan? Kana jin duk wayar da nake yi da samarina?"""

"Tsaki yayi, ya jefa mata wayarta. Ya ce ""Ina magana serious kina yi mini shirme?"""

"Ta ce ""To ai kar ka ji ina kalamai ne, ka zo kana kishi, nifa duk ba son su nake yi ba, kai kawai"

"nake so"" tayi maganar da niyyar sake kunna shi."

"˜o™arin tashi yayi, tana dariya ta ce ""Yi ha™uri, dan Allah ka duba mini ™arashen labarin nan, na"

"Najar bunkure ka gaya mini menene opinion Winka""."

"""Mu yi aiki kawai, ki daina yi mini wannan shirmen"""

"""Ba shirme bane ba fa, ni da gaske nake"" ya karSi file Win, ya cigaba da duddubawa."

"Ya Waga kai ya kalli walid ya ce ""Mai laya"""

"""Mai zamani""."

"""Yakamata ku je ku daba mini mahaifiyar Nura, tun da na fito yakamata ace na je na ganta, amma ba zan iya ba, ban san wace irin karSa zata yi mini ba, maybe ita ma irin kallon da ake yi mini,"

"take min"""

"Liti ya ce ""Haba maza, babu lallai gaskiya"""

"Nabila ta ce ""Ina kakarka to? Wadda oga walid ya bani labarinta?"""

"""Ta mutu ina prison"""

"Walid ya ce ""Har tare da ita mun je prison, sau biyu ba a bari mu ganshi. Baiwar Allah nan tashin"

"hankali da damuwa ne, suka haWu suka kasheta"""

"Jiki a sanyaye ta ce ""Allah sarki, Allah ya yi mata rahama, ya sanya sun huta baki Waya, da yar"

"madara, da Hajiya, da mamana da sauran al'ummar musulmi baki Waya"" suka amsa da Amin."

"Walid ya ce ""Mamanki ta rasu?"""

"Ta jinjina masa kai ta ce ""Eh,

34 / 67