Karfe a Wuta Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   10 / 67

27K to 30K   out of 199.8K words

mutum zai yi miki ya san a kwanciyar hankali ki ke. Jauhar gyaran gida aka yi miki haka, lokacin da na zo gidan nan kina amarya tsurar bulo ne fa, ikon Allah har da sola, wato a duniya idan Allah yana yinka ko wa ma ya™i ka. Ga Alhaji mu'azzam can Allah ya bar su da shi, matarsa na ta gana wa hafsa azaba, abu har da 'yan sanda, ya ce idan ba zata zauna da matarsa lafiya ba tayi mata biyayya ta tafi gida. Gidanku kuma"

"ana ta tashin hankali, Anty zakiyya ta ce mama ke yi mata asiri"""

"Cikin damuwa jauhar ta girgiza kai ta ce ""Bari kawai Anty lubabatu, lamarin gidan nan namu sai"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, kuma wasu lokutan har da laifin baba, kodayeke shi ma sun"

"mayar da shi sai yadda suka yi da shi, ai da ni aka ce ina yi wa hafsan asiri. Ko gidan ya hanani zuwa, sai idan da daddare ya kaini na gaida baba na dawo gida"""

"""Allah ya taimake ki, ke da suka so su tozarta rayuwarki Allah ya rufa miki asiri, Wan daban da"

"suka aura miki dan ki wula™anta, hakan ba ta faru ba"""

"""Tababs babu abun da zan ce wa Allah sai godiya, Anty lubabatu mijina a maza Wari irnsa Waya ne tak. Daba da shaye-shaye su ne ™addararsa amma, ya ci sunansa amintacce rauninsa mutane"

"suke kallo, basa kallon nagartarsa"" sun daWe suna hira sosai kafin ta tafi."

"Kusan duk bayan kwana biyu zuwa uku, sai hajiya kakar Al'amin ta kira Jauhar ta yi mata ya jiki,"

dan tun wani zuwa da tayi ta fuskanci hakan.

"Tun da ya fita da azahar har bayan magariba bai dawo ba, sai da ta kira shi a waya, ya ce mata"

gashi nan.

"Hnakali a tashe ya dawo mata, dan sai da gabanta ya faWi ya ce ""Master lafiya?"""

"""Nura aka kawo daga Abuja, wai ba shi da lafiya, tun lokacin nan da ya ce mini ba shi da lafiya,"

"yake kwance"""

"Ta ce ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, meya same shi haka?"""

"Ya ce ""Ban sani ba, an dai kai shi asibiti, na je na ganshi a galabaice, yayi magana ya faWi meyake damunsa ya ™i, na ga a galabaice yake sosai, an saka masa ruwa da sauran abun da yakamata gobe"

"in Allah ya kaimu dai zan koma""."

"Jiki a sanyaye ta ce ""Allah sarki Nura, sai da ka ce idan ba zai iya ba ya dawo, wata™ila dan kar ka"

"yi masa faWa ne ya zauna bai dawo ba. Allah ya bashi lafiya"""

Ya amsa da Amin.

Ya ciro mata envelope ya ajiye mata.

"Ta ce ""Menene wannan?"""

"Ya ce ""Duba ki gani mana"""

"Hotunasu ne shi da ita, wanda galibi a wayarta suka yi, ya kai aka ciro su, sai kuma ™atuwar viva,"

"da aka yi frame Win hoton da suka yi na sallar eid Waya an rubuta musu happy marriage life, Waya kuma an rubuta first eid with habibi."

"Tayi murmushi ta ce ""Kamat yayi a rubuta Master weds madara"" duk da a cikin damuwa yake sai"

"da yayi murmushi, ya ce da safe zai kafe a falo."

"Ta kalleshi tana murmushi, bai taSa ce mata yana son ta ba, sai dai actions Win sa, yana tabattar mata da hakan. Da fari kai ba ka ce ya iya duk wani abu da yake da ala™a da kulawa ba, saboda"

"he's always serious, sai dai a hankali ainihin halayensa suke fitowa."

"Jikin Nura yayi tsananta, kullum Al'amin cikin sintiri yake, jauhar ce mai lallaSawa tayi musu girki, mahaifiyarsa ce take zaune da shi a asibiti tana kula da shi, gashi an rasa gane abun da yake damunsa, Al'amin har gona ya saka aka sayar masa a ™auye, saboda kula da Nura, dan asibitin ku"

Wi ya saka aka mayar da shi.

"Da daddare babar Nura ta fita, Al'amin ya zo, cikin ™arfin hali ya ce wa Al'amin ""Yau ina Antyna"

"ba ta zo ba?"""

"Ya ce ""Eh, ni na hanata zuwa, tayi nauyi. Nura yakamata zuwa yanzu ka gaya mini menene yake"

"damunka, ana ta kashe kuWi an rasa gane abun da yake damunkaa yayi maganar cikin damuwa"""

"Nura ya ce ""Idan na gaya maka ba zaka yi fushi da ni ba?"""

"""Ya za ayi na yi fushi da kai? Ka gaya mini in san ta in da zan kamo bakin zaren""."

"Ya ri™e hannun Al'amin ya ce ""Na san ba lallai na rayu, amma ba ka da laifi ka taimaki rayuwata ne. Na gayawa mama na ce kar ta gaya maka. Lokacin da na ce maka na fasa tafiyar nan, Honorable ne ya ce sai ya yi Wabi'ar mutanen annabi luW da ni, na ™i yarda, ni kuma na kasa gaya maka, dan ya ce idan na gaya maka, kashe mai unguwa zai yi, amma idan na amince shikenan, ba wanda zai san an yi kuma zai bani aikin."

"Na Wauka daga haka shikenan, sai dai tun da ya tafi da mu, a wani gida aka ajiye mu, abun da suke yi mana kenan, yana da masu kula da mu, babu ta in da mutum zai gudu, kuma ba shikaWai ne yake yi mana hakan ba, akwai wasu manyan mutane a ™asar nan, da duk zan gaya maka sunayensu."

"Kuma kamar tsafi suke yi ta hanyar amfani da mu, bana iya ri™e bayan gida, mama ce take gyara mini kafin mutane su zo dubiya, Indabo ya lalata mini rayuwa amma ka rufa mini asiri dan Allah,"

kuma kar ka zargi kanka! Ina da hujja mai ™arfi da zan baka a kan haka!

Ayshercool. 08081012143

¦ 500 ne via 0009450228

Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne.

90009343

'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724

"Gaba Waya fuskar Al'amin ta sauya takmar ta horo, ta koma Al'amin Win sa na ainihi, tamkar bai taSa sanin wani abu wai shi dariya ba. Wani irin gumi ya shiga tsatstsafo masa, jijiyoyin goshinsa zuwa kansa suka mi™e suka kukkumbura, idonsa yayi wani irin ja mai ban tsoro, bugun zuciyarsa ya ™aru da saurin gaske, jikinsa ya fara Waukar wani irin zafi saboda tashin hankali da tsananin S"

acin rai.

"Ba tare da tunanin halin da Nura yake ciki ba, yayi wa hannun guduma wani irin mugun ri™o, da"

sai da ™asusuwansa suka yi ™ara.

"Nura ya Wora Waya hannun a kan na Al'amin ya ce ""Yaya, kai Wan uwa ne da Allah ya bani rana tsaka a titi, duk wannan abun ka yi ne dan inganta rayuwata, ba ka taSa yin wani abu da zaka cuceni ba, na san da ka san abun da zai faru da ni kenan, ba zaka bari na je ba, dan Allah ka kwantar da hankalinka, ni na san ba zan rayu ba, abun da suka yi mini ya fi na kowa muni da tashin hankali, ban san yaya zan misalta maka ba, amma dan Allah kar ka yi yin™urin yin wani abu, idan ba haka ba za su yi maka illa. Na bar su da Allah ka tayani Addu'a Allah ya yafe mini laifukana, idan na mutu dan Allah ka yi mini wanka kar asiri na ya tonu, ba na son a zargeka da abun da mutane ba su san menene ainihin abun da ya faru ba."

"Wurin bayan gidana ya riga ya Saci, kowa ya gani zai gane meyafaru dan Allah kar wani ya je kan"

"gawata idan ba kai ko mama ba"""

"Al'amin ya ri™e hannun Nura gam, amma ya kasa magana sai wani irin numfashi mai haWe da huci,"

ya sunkuyar da kai yana sauke numfashi.

"Yanayin yadda mahaifiyar Nura ta tarar da Al'amin, ya sanya ta gane ya gaya masa."

"Ta ™arasa gaban gadon, jiki a sanyaye ta ce ""Al'amin, ka kwantar da hankalinka dan Allah, zan iya dafa Alqur'ani na rantse, ba zaka kai mini nura in da za a cutar da shi ba, na san da ka san me zai faru kenan ba zaka yadda ya je ba, a irin yadda yake bani labarin zamanka da shi. Iya W awainiyar da ku ka din ga yi da mu kai da matarka ya ™ara tabattar mini da haka. Cuta ce an riga"

"an cuce mu, amma mun bar wa Allah, ni ba zan zargeka ba"""

"Ya saki hannun Nura a hankali, ya tashi ya juya ya fice."

"Nura yayi ajiyar zuciya ya ce ""Allah ya sa kar ya ce zai Wauki wani mataki, dan mutanen nan sun"

"wuce duk yadda yake tunani, ni dai ku cigaba da yi mini addu'a da fatan cikawa da imani"""

"Duk da juriya da mahaifiyar Nura take yi, sai da ta kasa ta zubar da hawaye, cike da karaya, dan magana kawai Nura yake yi, amma komai sai an yi masa, gashi buni-buni jininsa ya ™one, sai an saka masa wani, dan bayan bayan gidan, har da jini ne yake zuba daga wurin, jini sosai ba kaWan"

"ba, a tunaninsa da na mahaifiyarsa Soye wa likitocin ainihin abun da ya faru shi ne rufin asirin su,"

"dan babu wanda zai fahimce su, cewa za a yi shi ya kai kansa, saboda kwaWayi da son abun duniya,"

dan Nura ya yi girman da ya fi ™arfin ace dole aka yi masa.

"Ikon Allah ne kawai ya kai Al'amin gida, dan ko me za ayi masa bai san ya aka yi ya isa gidan ba."

"Jauhar har ta yi bacci, dan 'yan kwanakin nan bacci take yi sosai da sosai, duk in da ta ji kwanciya"

ta yi mata daWi sai bacci.

"Ba ta farka ba, sai bayan sha biyun dare, shi ma dan taji ta gaji da kwanciyar ne, a hankali ta tashi"

"jikinta duk yayi tsami, ta kalli ™ofar Wakin Al'amin, ta tashi ta nufi Wakin, ta Waga labule ta shiga."

"Yanayin kwanciyar da ya yi, ya tabattar mata da yayi shaye-shaye ya bugu, dan wata irin kwanciya"

yayi.

"Jiki a sanyaye ta ™arasa gaban katifarsa ta zauna a hankali ta ce ""Haba master yau kuma?"" Dan bai fiye shan abun da zai gusar masa da hankali gaba Waya har haka ba, yana yi amma ba sosai ba, ya fi ganewa busa haya™i. Kuma kwanakin nan da Allah ya taimaketa tayi galaba a kansa, bai fiye shan abun buguwa ba sai shan sigari, wiwin ma ya rage shan ta sosai, amma ta zo ta tarar da shi a"

wannan yanayin.

"Da ™yar tana haki, haka ta gyara masa ™afarsa da hannunsa, ta shafi sumar kansa, sai wani irin gumi yake yi, naman fuskarsa yana Wan yi rawa lokaci zuwa lokaci ga ajiyar zuciya da yake ta yi"

a kai kai.

"Ganin ba ya hayyacinsa, balle su yi magana, ya sanya ta tashi ta tafi Wakinta, cikin zullumi da"

tunanin me aka yi masa?.

"Kiran sallar farko ya farka, sai dai zuciyarsa cike da tsananin ba™in ciki da Sacin rai, ya san ko ya je gida ba zai samu indabo ba yana Abuja, kuma ba zai iya tafiya Abuja ba, cikin fargaba zai tafi"

kar yana matsawa wani abun ya samu Nura.

"Alwala yayi ya fice, a hanya yayi sallar asuba, ya ™arasa Asibitin, maman nura na ta kokowar"

"yadda zata Waga shi, ta saka masa pampers, yayi mata girma."

"Al'amin ya bubbuga ™ofar, ta ce ""Waye?"""

"Da ™yar ya iya magana ya ce ""Al'amin ne"""

"Nura ya ce ""Mama buWe masa"""

"Ta buWe masa ya shigo, Nura ya gaida Al'amin, jinjina kai kawai yayi, suka gaisa da maman Nura,"

"da ™yar yake iya magana, saboda tsananin Sacin rai da tashin hankali."

"Ya taimaka mata, suka canzawa Nura pampers, jinin da Al'amin ya gani a pampers Win ya Waga"

"masa hankali, gaba Waya halittar duburar Nura ta fito waje, babu ™yan™yami babu komai, ya taimaka mata suka gyara shi, suka saka masa pampers uku, kamar yadda take saka masa, sai kuma ta kawo zannuwa ta tuttura masa ta toshe ko ina, ta fesa masa turare, ta kunna turaren wuta, ta"

shiga banWaki ta wanke kayan da aka cire mas.

"Al'amin ya rasa me ma zai cewa Nura, abun duniya ya ishe shi, ya ji ya tsani kansa, komai baya yi"

masa daWi.

"A hankali ya kalli Nura ya ce ""Zan gaya wa likitoci, su duba idan da abun da za a iya yi, ayi maka"

"babu dabara a Soyewa likitoci wannan lamarin"""

"Da sauri Nura ya ce ""Dan Allah kar ka yi mini haka, ka rufa mini asiri, wallahi babu wanda zai"

"yadda dole aka yi mini, na san ba zan rayu ba, lokaci kawai nake jira, dan Allah yayana wannan ce alfarmar ™arshe da zan nema a wurinka, dan Allah kar ka gaya wa kowa"""

"Cikin matsananciyar damuwa Al'amin ya ce ""Nura ka yafe mini, wallahi ban san abun da zai faru"

"ba kenan, na zata hakan zai taimaki rayuwarka ne... Sai ya kasa ™arasawa muryarsa ta fara rawa."

"Guduma ya ce ""Wallahi na sani, kai mutumin kirki ne yayana, dan Allah idan na mutu ku din ga yi mini addu'a, na san sauran jama'ar gari babu lallai su yi mini, saboda ban shuka alheri ba, amma na san kai zaka yi mini kai da mama, da Antynmu. Dan Allah idan ta haihu, idan namiji ne, ka"

"saka masa Nuraddenni ka din ga tunawa da ni"" yayi maganar yana murmushi."

"Al'amin ya haWiye wani abu mai tsananin Waci, ya kalli Nura, amma ya kasa magana."

"Nura ya sunkuyar da kai, yana share hawayen karaya."

"Maman Nura ta fito ta gama wanke kayan Nura, muryar sa na fita a hankali, ya kalli maman Nura"

"ya ce ""Me za a sayo muku ne? Da me zaku karya ba ta tashi ba na taho"""

"Mama ta ce ""Kar ka damu Al'amin, ™anwata suna nan tafe, da wuri za su zo, ai da ™annensa ma su duba shi, baiwar Allah ai tana ™o™ari Allah dai ya raba ta da cikin nan lafiya, ta sauka lafiya ™ alau. Ai ta ce tuwon dawa zan yi mata, da miyar Wanyar kuka da man shanu idan ta haihu, in sha"

"Allah kuma ana ce mini ta sauka, zan dafo na taho kano, yajin daddawa ma ni zan yi mata""."

"Nura ya ce ""Mama ni dai ki tayani ro™o, na ce a saka sunana idan an samu Wan saurayi"""

"Suna yin hirar ne, dan Al'amin ya kwantar da hankalinsa, sai dai fuskar nan tamau ya kasa yin"

fara'ar.

"˜arfe takwas da mintuna, wata yarinya ta shigo Wakin, 'yar ba™a mai kyau, da siririn billenta, a"

gefen fuskarta.

"Babu ko sallama ta faWo Wakin ta ce ""Mama mun zo"""

"""Baki iya sallama ba ne?"""

"Ta ce ""Assalamu alaikum, yaya wai da gaske ka je Abuja?"" Tayi maganar tana ™arasawa gaban"

gadonsa.

"Nura ya ce ""Eh ramma, ya gida ya makaranta?"""

"Ramma ta ce ""Lafiya ™alau, yaya wai to ka ga shugaban ™asa?"" Ya girgiza mata kai alamar a'a."

"""To idan ka koma zaka ganshi? Ka ce masa dan Allah a gina mana burtsatse, wurin Webo ruwa da"

"nisa sosai"""

"Ya shafa kanta ya ce ""To zan gaya masa, ina Sani?"""

"""Babanmu ya ce ba za a zo da shi ba, ya tafi makarantar Allo, nima da ™yar ya bar na biyo innar"

"su jafarun muka taho""."

"Mama ta ce ""Ke baki iya gaisuwa ba, balle ki yi wa yayan naki yaya jiki ba?"""

"Ta kalli Al'amin ta dur™usa ™asa ta ce ""Ina wuni?"""

"Ya jinjina mata kai kawai, ta ce ""Yaya sannu ya jiki?"""

"""Jiki da sau™i Alhamdilillah"""

"""To Allah ya baka lafiya"""

"Wata mace ce tayi sallama, tana faWin ""Ke kuwa ramma an yi ´ar bantan uba, ina can ina bulayin"

"in da aka kwantar da ku, kawai na nemeta na rasa shashasha ba zaki yi hankali ba"""

"Ta zauna suka gaggaisa, Mama ta nuna mata Al'amin ta ce ""Atine ga uban gidan Nura, shi ya samo"

"masa aikin nan, yake ta Wawainiya da mu"""

"Atine ta ce ""Allah sarki, ni wallahi kama yake yi mini da mai gyaWa, yana kama da 'yar nan ta ta"

"da ta rasu wadda tayi aure a birni, zahra'u"" da sauri Al'amin ya kalleta Mama ta ce ""Wallahi kuwa, mun yi waya da ita ma, ta ce zata zo duba Nura""."

"TaS yana da ala™a da Nura ne, ko kuwa kawai dai hasashe ne, ko abun su na mutanen ™auye, da"

"kowa ma Wan uwan su ne? saboda tsabar miskilanci bai yi musu magana ba, ya tashi ya tafi."

"Ya je gidansa ma, ya kasa kawai ya tafi ya samu wani kango, yayi zamansa, abun duniya ya ishe"

"shi, bai ma san ta ina zai fara ba."

"Bai koma gida ba sai can bayan la'asar sannan ya koma gida, ba ta ce masa uffan ba, tayi masa"

"sannu da zuwa, ita babbar godiyarta ga Allah, dawowarsa lafiya, ba tare da wani abu ya faru da ita shi ba."

"Sai dai ta haWa abinci ta bashi, amma ta ga ya daWe bai motsa ba, daga baya ya Wauki cokali ya din ga tura abincin da ™yar, kamar mai tura magani, ya gama ya nemi wuri ya kwanta bai ce mata"

uffan ba.

"Duk da yanayin hakan bai yi mata daWi ba sam, amma ta daure ta Wan bashi lokaci, amma taga a jere, kusan kwana uku, ba ya ce mata uffan, kuma kullum sai ta yi bacci zai dawo, da asubar fari kuma yake ficewa. Idam ya fitan nan, asibiti

10 / 67