Karfe a Wuta Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   11 / 67

30K to 33K   out of 199.8K words

yake tafiya ya taimakawa babar Nura ta gyara masa"

"jikinsa, sai dai kullum jikin nasa babu sau™i."

"Ranar na haWu, da ya fito zai fita ta tare shi ta ce ""Master, wai dan Allah laifin me na yi maka har"

"haka ne? Meyake faruwa yakamata ka sanar da ni"""

"Ya ce ""Zan gaya miki idan na dawo"" daga haka ya fice ya bar ta."

"Abun duniya ya ishi jauhar, ta kasa gane meyake faruwa haka yake Soye mata."

"Yana zuwa asibiti ya tarar da mahaifiyar Nura a gefen gadon Nura, ta rufe shi, idanunta sun yi"

jawur.

"Cikin matsanancin tashin hankali ya ™arasa gaban gadon, ya yaye zanin, ya tarar Nura ya cika."

"""Innalillahi wa Innalillahi raji'un"" ya furta cikin matsanancin tashin hankali, ya zauna yayi shiru shiru, ya kasa zubar da hawaye sai wani abu da yake yi masa zillo, tsakanin ma™ogwaronsa da ™"

irjinsa.

"Ya saka gwiwoyinsa a ™asa a gaban mahaifiyar Nura ya ce ""Ki yafe mini saboda girman Allah, ban taSa tunanin abun da zai faru da Nura kenan ba, da na san haka zata kasance wallahi ba zan"

"tura shi ba"""

"Ta share hawayenta ta ce ""Wallahi na sani, kuma ni ban zargeka ba, Yanzu fatana Allah ya sa mutuwa hutu ce a gare shi, Allah ya yafe masa kai ma Wawainiyar da ka yi da mu, Allah ya baka"

"lada""."

"Ya Wauki waya ya sanar da su liti su samo mota, a asubar su zo a tafi da gawar Nura Allah ya yi"

masa cikawa.

"Sun girgiza sun kaWu matu™a da mutuwar Nura, da asubar aka tafi da gawarsa gidan mai unguwa, ta ce ita za ta yi wa Nura wanka, Al'amin ya tayata ya ce ban da su biyu, kar wanda ya je kan"

gawarsa.

"Mai unguwa ya din ga bala'i, yana yayi asara kuwa, ya rasa wanda zai gayyato kan gawarsa sai W"

an daba.

"Maman Nura ta ce ""Ša na bai yi asara ba wallahi, kai ka yi asara, dan da ka kula da shi ka ri™e shi"

"da mutunci da amana, ba zai faWi haka ba. Kuma ba in da aka ce Wan daba Wan wuta ne, ko an haramta masa zuwa kan gawa""."

"Haka suka yi wa Nura sutura, aka sanar da rasuwar sa."

"Duk da ana ganin Nura baya ji, amma ya tara mutane, saboda daga baya duk wani aikin gayya na"

cigaban unguwa da shi ake yi.

"Sai ™arfe goma na safe, Al'amin ya dawo gida, yana zullumin yadda zai gaya wa Jauhar mutuwar"

"Nura, ga zuciyarsa da take wata irin tafasa take raya masa kashe Indabo ya huta da ba™in cikin da ya jefa shi a ciki."

"Cikin matsananciyar damuwa ta ce ""Master wai meyake faruwa dan Allah?"""

"""Allah ya yi wa Nura rasuwa"""

"Gaba Waya sai ta manta waye ma Nura, ta ce ""Waye kuma Nura?"""

"Ya ce ""Guduma Wan gidan mai unguwa"" kamar shashasha haka ta bishi da kallo, daga bisani wani irin jiri ya Webe ta, cikin azama ya ri™e ta, jikinta ya hau wata irin tsuma, ta saka hannu iya ™arfin ta, ta toshe bakinta, dan hana kukan da yake ™o™arin taso mata fitowa amma ta kasa, iya ™arfinta ta din ga maimaita ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Innalillahi"

"wa Innalillahi raji'un. Allah ya sa ba Nuran da na sani ka ke faWa ba"""

"Jiki a sanyaye ya zauna da ita a jikinsa ya ce ""Ba kyau yi wa mamaci kuka fa kin sani, ki yi masa"

"addu'a"""

"Cikin kiWimewa ta ce ""To me zan ce?"""

"""Ki ce Allah ya ji™an Nura yayi masa rahama"""

"Tari ta fara yi, ya Waga ta yana yi mata fifita, tare da yi mata sannu."

"Sai da ya tabbatar ta Wan samu nutsuwa, sannan ya ri™e hannunta, suka tafi gidan mai unguwa,"

"idanunta sun kumbura sun yi jawur, fuskarta ma tayi ja sosai da sosai."

"Sai dai suna shiga Wakin da mahaifiyar Nura take karSar gaisuwa, suka tarar da hajiya a ciki a"

"zaune, a kusa da Maman Nura."

"Hajiya ta ce ""Al'amin, yanzu nake cewa zan kiraka na ga kamar unguwarku ce nan"""

"Maman Nura ta ce ""Ai wannan ne ubn gidan nasa da ya Wauke shi kamar Wan uwa da nake gaya"

"miki"""

"""To ai Wan wurin Zahra'u ne, jikana ne"""

"""Iko sai Allah, Al'amin da kakarka da mahaifiyata uwar su Waya uban su Waya, Allah bai saka"

"mun san juna ba"""

"Ya zaunar da jauhar, ta zubawa mahaifiyar Nura ido, amma ta kasa magana sai sheshshe™ar kuka, maman Nura ta rungumeta tana ™o™arin rarrashinta, amma ta kasa sai suka cigaba da kukan tare gefe ga ramma da ™aninta sani, da suke uwa Waya da Nura, suma su na ta kuka, hakan ya ™ara"

karya zuciyar Al'amin.

"Har aka gama zaman makoki, Al'amin yana cikin damuwa da tashin hankali, Hajiya da su ramma, a gidan Al'amin suke kwana, har zuwa kwana bakwai, sai dai kafin a gama zaman makoki, mai unguwa ya fara yada maganganu cewar Al'amin ne yayi silar mutuwar Wan sa, Allah kaWai ya san"

"ina ya kai shi, idan abun gaskiya ne, meyasa shi bai je ba ya tura shi."

"Kafin a ™are zaman makokin, sai da maman Nura suka yi kaca-kaca da mai unguwa, ta ce Al'amin"

"babu yadda za ayi ya kai shi in da za a cuce shi, idan ma haka ne, ai Wan uwansa ne ba ruwansa."

"Aka share zaman makoki, amma Al'amin ya kasa cigaba da walwala, tun jauhar na bin sa na"

"tambayarsa ko lafiya? Ta yi rarrashin tayi ban bakin, har ta gaji ta zubawa sarautar Allah ido."

"Zuciyar sa na ta azalzalarsa ya bi Indabo can Abujan, ya halaka shi kowa ma ya huta, amma ya"

daure ya jira ya dawo.

"Sai da Nura yayi sati uku, sannan aka gaya wa Al'amin Indabo ya dawo."

"Gaba Waya baya cin abinci yadda yakamata, idan ya fita baya iya zuwa wurin sayar da shayi, sai ya samu wurin da babu wanda zai takura masa ya kwanta yayi ta tunani, ya din ga jin da ma bai san Nura ba a rayuwarsa gaba Waya da duk haka bata faru da shi ba, ashe duk abun nan ma suna"

da ala™a da juna.

"Hatta jauhar yanzu ba ta iya samun kulawarsa yadda yakamata, dan ko in da take ya daina zuwa, ba ya dawo wa ma sai ta yi bacci."

"Gashi ta shiga wata na bakwai, haki ya sakata a gaba, ga nauyin cikin ya fara damunta, da ™yar"

take iya tafiya.

"Indabo yana zaune a falonsa, yana ganin mutane, ya ga Al'amin ya faWo falon kamar daga sama."

"Cikin sauri ya sallami waWanda suke tare da shi, ya mi™e tsaye ya ce ""Mai zamani lafiya kuwa? Ya"

"na ganka a haka?"""

"KafaWar Indabo ya daka ya hantsila kan kujera, ""Me zamani distinguish senator kamar ni ka yi wa"

"haka, dan na sakar maka na ba dama a kaina?"""

"""Zuwa na yi na gaya maka shukar da kayi tayi huda""."

"""Kamar yaya?"""

"Al'amin ya kalle shi da jajayen idanunsa ya ce ""Ba na jin magana, amma wallahi ba na cin amana,"

"kuma duk wanda ya ci tawa sai ya biya. Nura guduma ya mutu, na karSi sa™onka ka jira amsar da za ta biyo baya""."

"Ras! Gaban indabo ya faWi, dan ba haka suka tsara ba, ya aka yi ya san Nura ya mutu?."

"""Ban gane Nura ya mutu ba"""

"""Shut up! Ka sam komai, tsohon munafuki algungumi, na san komai, ka lalata rayuwar yaron da nayi niyyar ingantawa. An dawo da shi rai a hannun Allah, na san baka san ya aka yi aka dawo da shi gida ba, bayan ka shirya yayi hatsari idan ya tashi dawowa yadda zaka Satar da abun da ka aikata. Wallahi ka ci amanar Al'amin kuma sai ka biya."

"Ba ka yi mamakin yadda nake yi maka biyayya ba na yi duk abun da ka ke so?, ka zata kawai saboda kana bani kuWi ne? Bari na tuna maka ni yaron dodo ne, dodo babban sarki doodn da yake Wauke da makamin tarwatsaka, ka zata ya mutu da sirrin nan a cikin sa ne? Wallahi ma'aruf na sanka fiye da yadda ka san kanka, a Nigeria ko wajen Nigeria wuraren da ka ke tafka tsiyatakunka."

"Wallahi na buWe bakina a kanka, ka gama kaWewa bar ganin kana da rigar kariya, kuma ku ne ku ke juyar ™asar, dodo ya mutu ya bar ni da babban kundun da zan iya rusa ku."

"Niyyata idan na zo na kashe ka, sai dai hakan ba zai saka na huce ba, saboda yanzu ba irin da ba ne, na ajiye wanda suke bu™ata ta. Akwai dabarun da masu kimiyyar lissafi suke bi, wurin yin solving wato BODMAS. Bracket Open, division, multiplication addition sannan subtraction. To ni upside down nake yi indabo, sai na fara division nake multiplication na yamutsa komai sannan na saka a bracket na rufe."

"Ka rubuta ka ajiye daga yanzu, ni ne babbar barazanar rayuwarka"

"Daga yanzu duk motsin da zaka yi, zaka yi shi a tsakanin tarkunan da zan saka maka, ka daina shan ruwa cikin kwanciyar hankali, ni ne magajin dodo kuma zaka biya cin amanar da ka yi mini"""

ya juya ya fita yana huci.

"Cikin tsananin tashin hankali, Indabo ya tashi, ya Wauki wayarsa ya daddana, ya kara a kunnensa."

"Cikin tashin hankali ya ce ""Ya aka yi Nura guduma ya bar gidan nan, garin yaya? Waye ya dawo"

"da shi kano ban sani ba wane munafukin ne ya rusa mana plan?"""

"Jifa yayi da wayar, ya hau safa da marwa, cikin tashin hankali ""Kenan kallon biri yake yi mini duk"

"tsawon lokacin da muka yi tare? Amma Allah ya tsinkewa dodo albarka, ya ™ara tsine masa cin"

"amanar da ya yi mana kenan?"" Ya kuma Waukko wata wayar ya kira P.A ya ce ""Maza ka ™araso"

"gida ina nemanka""."

Ya ajiye wayar ya cigaba da kaiwa yana komowa.

"Afujajan P.A ya ™araso, ya ce ""YallaSai ya ake ciki ne, meyafaru na ganka cikin tashin hankali?"""

"""Dodo"""

"P.A ya ce ""Me dodon yayi?"""

"""Dodo ya daWe da kashe mu, kafin mu kawar da shi ashe ya gaya wa mai zamani komai? An dawo"

"da yaron nan Nura kano, ya san komai, na yi waya wai an nemi obi an rasa, ya gudu yanzu ya san komai, na kaWe idan yayi magana ya gama rusa ni, Allah ya tsinewa dodo albarka"""

"""Ka kwantar da hankalinka, honorable wai waye wani mai zamani, me aka yi aka yi shi ne? Mutum nawa ka kawar kan mu zo in da muke yanzu? Ba zai tayar mana da tarzoma ba, bayan"

"mun yi nasara kawar da shi kawai zamu yi"""

"Indabo ya ce ""Tayaya wannan yaron mai shegen taurin rai, da ™arfin tsiya, ashe tsawon lokacin"

"nan kallona kawai yake yi"""

"P.A ya ce ""Kwantar da hankalinka akwai abun yi, zan yi maka bayani""."

"Cikin dare jauhar na zaune tana lazumi, tayi sallar dare, ta ji shigowar Al'amin, ta Wan jira wasu"

"mintuna, sannan ta bi shi Wakinsa."

"˜wayoyi ta tarar da shi ya haWa zai sha, cikin azama, ta dur™usa ta kwashe ™wayoyin, ta dube shi ta ce ""Akwai abun da ka ke Soye mini master, ba iya mutuwar Nura ce take damunka ba, akwai"

"wani abu a ™asa ka gaya mini. Baka saba ta'amalli da ™wayoyi haka ba""."

Yayi shiru bai ce komai ba.

"""Master ka yi mini magana dan Allah ka gaya mini "" tayi maganar cikin matu™ar rauni."

"""Ki yi ha™uri ki je ki kwanta, dare yayi"""

"""Ka san kwana nawa nayi bana iya bacci, saboda damuwar da ka ke ciki? Kallonka kawai nake yi kar na takura maka ina jiran ka yi mini bayanin menene amma shiru, haba master ka gaya mini"

"dan Allah"""

"Ya juyo ya ri™e hannun jauhar, yana murzawa cikin matsananciyar damuwa, ya sunkuyar da kai ya"

"ce ""Duk da abun a Soye ne, amma bai kamata na Soye miki ba, bai kamata na bar abun a raina nikaWai ba""."

Sai a lokacin ya gaya wa jauhar abun da ya faru.

"""Innalillahi wa Innalillahi raji'un"" tayi ta maimaitawa cikin matsanancin tashin hankali."

"""Master, ka ga irinta ko? Yana Waya daga abun da ya sa nake ta fatan ka nesanta kanka da mutumin nan, ya cucemu amma kansa ya yi wa. Baka yi da niyya ba, Allah ya ji™an Nura ya saka"

"masa"""

"Al'amin ya kifa kansa a kan cinyar jauhar, sai a lokacin ya ji wasu irin hawaye suka zubo masa."

"""Sadik ya mutu a sanadina, Nura yayi wula™antacciyar mutuwa a dalilina, na zama annoba kenan? Mahaifiyar Nura har ta mutu ba zata manta, ni na kai yaron ta, in da ka yi dalilin gurSata masa"

"rayuwa ba"""

"Jauhar ta girgiza kai ta ce ""Dan Allah ka daina faWar haka master, kowa abun da Allah ya rubuta"

"masa yake riska ba kaine sila ba"" tana kuka tana rarrashin sa."

"Tun da Allah Nura ya mutu, Al'amin ya ™ara nutsuwa, babu abun da yake yi masa daWi. Ita kanta jauhar ta kasa daina jin Wacin rashin Nura, dan tun da Al'amin ya ce masa an samo masa aiki a Abuja yake murna, yake bata labarin shi wata yarinya ya gani yake so, kullum sai ya je ™ofar makarantar islamiyyar su idan an taso su ya ganta, yanzu yana fara aiki, idan ya ginawa mama"

"gida a cikin kano, ta dawo sai ya nemi auren yarinyar, amma kar ta gaya wa master."

"Take yi masa dariya ta ce masa ai mamansa aure take yi sai dai ya haWo da mijinta, ya ce ya fasa"

"zai yi aure ya Waukko ramma ta dawo cikin gari, ta baro ™auye."

"Ta ce ""Ban da abunku Nura haryanzu fa da sauran ™uruciyarka, Wawainiyar aure da yawa fa""."

"Ya ce ""Ni dai kawai ki yi mini addu'a, da na dawo, zan fara zuwa wurin yarinyar nan zance"""

"Da haka tayi ta tuna ire-iren hirarsu, da barkwancinsa, ta kasa mantawa da shi."

"Al'amin har tofa ya sake zuwa, ya yi wa mahaifiyar Nura gaisuwa, ya kai mata abun alkhairi, ya"

biya ya gaida Hajiya ya dawo gida.

"Jauhar cikinta yayi girma sosai, kamar kana fita ka dawo zaka tarar ta haihu, ™afafuwan ta duk suka kukkumbura, saboda girman cikin, aka ce yana shiga wata tara ayi inducing Win ta ta haihu ta"

"huta, dan bayan nauyin cikin kullum cikin haki take, a haka kuma take lallaSawa ta je makaranta."

"Wurin shayin Al'amin kuwa, wasu irin kuWi ne suke shiga suna fita, dan tun safe ake aikin Worawa"

"da saukewa, ya zama chamber matasa sosai da sosai, duk da suna sayar da kayan shaye-shayen su a wurin, ba sa cutar Al'amin shi kuma ba ya yi musu mugunta."

"Da safe su yi shayi, da rana indomie shayi, taliya haka suke wuni saye da sayarwar abinci."

"Juahar sun gama haWa kayan haihuwa, dan washegari ne ya kama ranar da za su je ayi mata"

"inducing, tana ta jin tsoro yana kwantar mata da hankali."

"Ta ce ""Master"""

"Ya ce ""Mmm"""

"""Ka ji sai motsi yake yi, kamar ya san gobe in Allah ya kaimu za a fara inducing Win nan"""

"Ya ce ""Ya ™agu ya ga daddynsa, Nuradeenin daddy, in sha Allah sunan Nura zan saka, kamar"

"yadda na yi masa al™awari""."

"Ta ce ""Allah ya ji™an Yaya Nura ya sa ya huta"""

"Ya ce ""Amin""."

"Cikin shagwaSa ta ce ""Amma a gabanka zan haihu master, tsoro nake ji, an ce haihuwa akwai"

"wahala fa"""

"""Ba wata wahala in sha Allah, ina kusa da ke, ina yi miki addu'a zaki haihu, Ni zai fara gani kafin"

"ya ganki "" yayi maganar yana sumbatar cikin nata."

"""Ni dai na fuskanci ba a so na, ta babynka kawai ka ke yi"" tayi maganar cikin shagwaSa."

"""Ni na isa? Dukkanku ina sonku madarata"""

"""Ba wani, ni baka taSa cewa kana so na ba""."

"Yayi murmushi ya ce ""Amma kina gani a aikace ai""."

"""Baka taSa faWa ba"""

"Yayi dariya ya ce ""Ai ke da ruwan zinari aka rubuta sunanki a zuciyata. Ina sonki madarata, ina ™"

"aunarki ™auna mai tsanani ya fi ubban shadidan"""

"Ta ce ""Wayyo Allah daWi. Wallahi har cikin tsakiyar zuciyata na ji kalaman nan, ba ka taSa gaya"

"mini ba, ka cigaba da gaya mini, da daWi"""

"Ya ™ara rungumeta ya ce ""I love you madarata"""

"""I love you too babyna, kuma baban babyna, masterna abun ™aunata"""

"Har mamakin irin kalaman soyayyar da suka din ga musaya take yi, da ba ta taSa tsammanin jin su"

daga bakin mastern ba.

"Cikin matsanancin shau™in so da ™auna, suka kasance cikin farin ciki. Suka yi wanka, ya"

rungumota daga toilet tana takawa a hankali da ™aton cikinta a gaba.

"Ya taimaka mata, ta saka rigar bacci, sannan suka kwanta, ta kwanta a jikinsa, tayi balance da ta"

motsa sai yayi mata sannu.

Wani irin nannauyan bacci ne yayi awon gaba da ita.

"Ji tayi kamar ana kokowa a falo, ta laluba ba ta ga Al'amin ba, ga wani irin ™aurin taba ya cika ko"

ina.

"Hasken fitila ta hango an kunna ™wan falo, ta saukko ta fito falon tayi arba da wasu matasa"

"hannunsu ri™e da miyagun makamai, madaki ta fara ganewa gabanta ya faWi."

"Sun rirri™e Al'amin, suna sha™a masa wani abu, jikinsa ya saki yana ta layi."

"Madaki ya bushe da dariya ya ce ""Ka ce baka ji, dama ka ce da ni da kai sai wani ya kawo ™ arshen wani, to ni zan kawo naka ™arshen yau ina dodon da kake ta™ama da shi? Duk da zuwan ba nawa bane ba, na uban gidanka ne Indabo, amma

11 / 67