Karfe a Wuta Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   62 / 67

183K to 186K   out of 199.8K words

ni, kai ko mutuwa nayi, ina da manya manyan hujjoji a kan sa, da suke a hannun wakilai ne, akwai wanda za su Wora, in sha Allah sai na bayar da misali a Nigeria, an fara hukunta masu ri™e da madafun iko, da iyalansu, ba wai doka a kan"

"talaka kawai ba, everyone is equal before the law"""

"""Haka ki ka ce?"""

"""Hala kurma ne kai?"""

"Ya ce ""To bari mu gani, yaro bai san wuta ba sai ya taka"""

"""Na santa farin sani, tun da na Waukko ˜ARFEN CIKIN WUTA, da ya gagari hannaye da yawa"""

"P.A ya kalleta ya ce ""Me ki ke nufi?"""

"""Zaka fahimta nan ba da jimawa ba"""

"Yana fita tayi tsaki, ta Wauki jakarta ta fita, a nan ta bar motarta, ta hau abun hawa ta tafi gidan"

Viper.

"Yana tsakar gida, daga shi sai Wan mama a gidan, suna hira."

"Sun daWe suna kallon juna, sannan ta ™arasa ciki, ta samu wuri ta zauna ba tare da ta ce masa"

uffan ba.

"Ya samu abu ya zauna, ya ce ""Ya ake ciki, meye labari?"""

"""Ko ka neme ni, kwana biyu ina cikin damuwa da tashin hankali, amma ko a jikinka"""

"Ya tsuke fuska ya ce ""Menene?"""

"""Vi"""

"Ya Kalle ta, tare da Wage girarsa Waya."

"""Ka dubi girman zatin Allah, ka tausaya mini, ina ga ciwon zuciya na daf da kamani, kowa ya ja da baya ya juya mini baya, Abba ya yayyaga hotunan nan ya watsa mini, ya ce naje na nemi ubana na bar masa gida, daga shi har yan gidanmu, babu wanda yake kula ni. Gashi a tsakiyar program sumayya ta hau yi mini tambaya a kanka, yanzu ta ko ina mutane sai attacking Wina suke yi a media, saboda case Winka, client Wina malam garba wai ya yanke jiki ya faWi na je na duba shi, na tarar wai ya samu stroke, yanzu P.A Win Indabo ya bar office Wina da tashi barazanar, kuma haryanzu ka ™i gaya mini dalilin da ya sanya Indabo yake bibiyata. Na rasa ya zan yi me zan yi ne? Kamar na gaza, ba wanda zan je na samu duk na gaya wa damuwata, dan Allah Viper ka gaya mini wacece ta jikin hoton nan, ina jin kamar ina da ala™a da ita, tun da ni dai na san ba ni bace ba, dan"

"Allah idan akwai wani abu da ka sani ka gaya mini, atleast na rage wata damuwar""."

"""Na gaya miki ban san komai ba, 'yan gidanku zaki tambaya"""

"""Na gaya maka ba zasu gaya mini komai ba, so kake sai na mutu ban san babana ba, idan kana da"

"yadda zaka yi ka taimake ni dan Allah, ko hakan ne alfarmar da ya rage da zaka yi mini a rayuwa"" tayi maganar tana haWa hannayenta biyu cikin sigar magiya."

"""Ana kiranki a waya"""

"""Ni ba ta waya nake yi ba, ka taimaka mini dan Allah"""

"""Ki Waga wayarki "" yayi maganar yana kallon ta."

"Ta Waukko wayar, ta ga lambar barrister Habib ce, ta Waga wayar ta ce ""Hello"""

"""Na duba office ba kya nan, Allah ya yi wa malam garba rasuwa yanzun nan"" mi™ewa ta yi tsaye,"

"ta saki wayar, ta tashi za ta nufi hanyar fita, jikinta yana rawa."

"Cikin zafin nama, Viper ya tashi ya ri™e ta, gaba Waya ta gigice, ta ce ""Sun kashe shi, wallahi"

"kashe shi aka yi"""

"Ya ce ""Waye? Waye ya kashe shi?"""

"""Malam garba, wayyo Allahna, meyasa na karSi shari'arsa, na janyo ya rasa raywarsa a banza, bani da sa'a wayyo Allah zuciyata"" wata irin mi™a tayi, kamar zata zare, ta fara kokowar ™wace wa"

"daga hannun Viper, tana kallon hanyar waje."

"Ya ™ara ri™eta ya ce ""Abla, tsaya ki ji, ki nutsu"""

"Magana take son yi, amma numfashinta ya din ga sama yana ™asa, hannunta da ya ri™e, ya din ga"

jin bugun zuciyar ta da sauri-sauri.

"Ya ciro wani abu a jikinsa, ya saka mata a gefen wuyanta, gaba Waya jikinta ya saki."

"Ya kalli Wan mama ya ce ""Ka kira mutanen nan a waya, su aiko da mota, a kaita Asibiti"""

"Šan mama yayi saroro ya ce ""A ina ta ajiye motar tata?"" Viper ya ™ura masa ido, ya ce ""Au,"

"ammm wasu mutanen?"""

"""A tunaninka duk abun da ka ke yi ban sani bane? Zaka kira su ko ni na kira su?"" Šan mama yayi"

"wi™i-wi™i da ido, cikin tsoro da mamaki""."

"""Am talking to you, and you are looking at me"" ba shiri Wan mama ya ciro waya yana kallon"

Viper.

****

"""Abdul yau ka addabe ni, kamar nayi maka dukan tsiya haka nake ji"""

"""Sorry baby, kin san kullum ke ta musamman ce, i so much love the natural you""."

"Ramma ta ce ""Wallahi ka isheni, duk ka dame ni"""

"""Wallahi wani mafarki nayi da bai yi mini daWi ba, ya bani tsoro""."

"Ramma ta ce ""Maganin wanda baya addu'a"""

"""Wallahi ina yi, har karatun Alqur'ani nake sakawa fa"""

"Ta ce ""To Allah ya bada lada, yanzu ka bani wuri na je nayi wanka, zan yi salla""."

"Ya tashi zaune ya ce ""Mu je, daga nan sai ki Wan dafa mana wani abun, yunwa nake ji"""

"Yayi maganar yana Wagota, daga kwancen da take."

"A tsakiyar gado suka din ga ciye-ciye da shi da ramma, suna yi yana tsokanarta, tana gaya masa ba"

™ar magana yana dariya.

"Tamkar ya mayar da ramma cikin sa haka yake ji, kuma ya kasa Soye mata hakan, suka kwanta ya"

"gama damunta, bacci ya kwasheta."

"Juyi ta yi zata gyara kwanciyarta, ta ga Abdul a zaune, ya saka wayarsa a gaba, ya Wora hannu a"

"ka, yana wani irin kuka tamkar Wan ™aramin yaro."

Ayshercool 08081012143

¦ 500 ne via 0009450228

Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne.

90009343

'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

https://whatsapp.com/channel/0029Va9QtrY4dTnBYG1hST2VHADARIN

*BRIGHT PENS SECOND BATCH*

"Ku kasance da littatafan bright pens, second batch."

*˜ARFE A WUTA (AYSHERCOOL)*

*MUTALLAB (NIMCYLUV)*

HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)*

*ZAYTOON (ZEE KUMURYA)*

"Tashi ramma tayi, ta ce ""Abdul, wai menene meyafaru ne?"" Yayi mata shiru ya cigaba da kuka."

"""Dan Allah kayi magana mana, ko mutuwa aka yi muku?"""

"Yayi mata shiru bai yi magana ba, ta kai hannu zata Wauki wayar, amma ya janye wayar ya kashe."

"Kawai ya yin™ura, ya Wauki mukullin motarsa, ramma ta mi™e ta ri™e shi ta ce ""Ina zaka je ne?"""

"""Fita zan yi"""

"""A wannan yanayin da ka ke? Idan wani abu ya sameka fa, dan Allah koma menene kayi ha™uri, zuwa Allah ya kaimu gobe, dan Allah ka ha™ura da fitar nan"" jifa yayi da mukullin, ya koma ya"

zauna ya cigaba da kuka.

"Ta zauna a kusa da shi, cikin damuwa ta cire masa hannunsa da ya rufe idanunsa ta ce ""Abdul,"

"kalleni menene wai?"""

"Ya sake sunkuyar da kai, kamar ita ce baya son haWa ido da ita. A hankali ya kwanta a jikinta kamar ™aramin yaro, ta rungume shi sosai, tana shafa kansa ta ce ""Koma menen kayi ta nanata Innalillahi wa Innalillahi raji'un, zaka samu sassauci in sha Allah"" wata irin ajiyar zuciya ya din ga"

"yi, wanda sai da ya bata tsoro."

"""Rahama"" ya kira sunanta da kyar a galabaice."

"""Dan Allah ko na fuskanci hukunci, kar ki manta da ni, na san koma menene zuwa ki gama"

"karatunki, zan fito"""

"""Tom"" ta faWa a sanyaye, dan wasu lokutan har tausayi yake bata, gaba Waya Abdul ya saduda,"

duk wannan iskancin da rashin mutunci ba ya yin su.

"""Rahama kin ce mini kina da yaya da ™ani ko? Har su ina son in Wauki nauyin su"""

"Ramma ta ce ""Ba na gaya maka yayana ya mutu ba, sai ™anina sani"""

"""Da gaske ki ke fyaWe aka yi masa ya mutu?"""

"Ta ce ""Oho ina na sani, ba ka ce mini ba a yi wa maza ba, ni kamar haka na so na ji an ce, wai za a samo masa aiki, yaje Abuja aka yi masa, amma mama ba ta taSa zama ta gaya mini yadda abun ya faru ba, ko tunawa ba ta son yi, idan ta tuno da shi tayi ta kuka"""

"Yayi ajiyar zuciya ya ce ""Ban san me zai faru ba, amma dan Allah duk tsanani kar ki rabu da ni, ki"

"zama mai yi mini uzuri da tausaya mini dan Allah, Allah ma baya kama wani da laifin wani"""

"Ramma ta ce ""Da bana yi maka uzuri, da bana tunanin zamanmu zai zo i yanzu, ka daina wannan"

"kukan dan Allah kunya kake bani"" tayi maganar da sigar tsokana."

Ya ™an™ameta ya cigaba da sheshshe™ar kuka.

"""To Wan jariri, ya isa haka, cikin dare kawai mutum ya tashi yana kuka, ko ka je ka yi alwala kayi"

"salla""."

"""Ba zan iya ba, ba zan yi karatun sallar dai-dai ba"""

"""Kaga amfanin ibada ko, idan bawa ya tuna da Allah, lokacin da yake cikin yalwa, Ubangiji yana tuna wa da shi lokacin da yake cikin ™unci, ka cigaba da addu'a, Allah ya yaye maka damuwar ka"

"doctor Abdul yasar"" yayi lamo kamar kyanwa a jikinta, ba tare da ya kuma magana ba."

****

"A hankali Nabila tayi juyi, tana ™o™arin gyara kwanciyarta kawai ta ga Viper a zaune a kan kujera, yana danna waya. Ta ™ura masa ido tana kallon sa."

"""Wannan kallon haramun ne, ki daina yi mini wannan kallon"" yayi maganar ba tare da ya kalleta"

"ba. Ko ™ifta ido ba ta yi, ta cigaba da kallonsa."

"Ya waiwayo sosai yana fuskantar ta, ya ce ""Ya aka yi ne? Ya jikin?"""

"Ta Waga hannunta, ta kalli drip Win da yake shiga, ta ce ""Vi"""

"""Mmm"""

"""Ina ne nan?"""

"""Wurin sayar da mutane"" yayi maganar yana cigaba da danna wayar."

"Ta lumshe idanunta ta buWe, ta ce ""Kamar bacci nake yi, kuma kamar a zahiri ne, dan Allah da"

"gaske malam garba ya mutu?"""

"Viper ya ce ""Eh, ya mutu"""

"Ta girgiza kai, tana kuka daga kwance ta ce ""Ai shikenan, ya mutu bai sha™i iskar 'yanci ba, ban cika masa al™awarin da nayi masa ba, da yaya zan kalli iyalinsa? Kullum da shi nake kwana nake tashi a zuciyata, ya mutu da mummunan tabo a zuciyarsa da rayuwarsa, ban cika masa al™awarin"

"da nayi masa ba, na gaza na kasa"" tai maganar tana fashewa da matsanancin kuka."

"""Ke, wai baki da tawakalli ne? Shikenan ke ba zaki mayar da lamarinki ga Allah ba? Wani ya ce"

"ke ki ka kashe shi ne?"""

"˜ara sautin kukan ta yi, ta ce ""Ya ka ji da aka kashe matarka, ya zuciyarka tayi da aka ™ala maka laifin kisanta? Haka iyalan malam garba suke ji, da wannan Wacin da ba™in cikin ya mutu, kuma ni ban yadda da wani stroke ne ya kama shi ba, wani abun suka yi masa"" Viper ya janyo kujerarsa gaban gadon sosai, ya matsa daf da ita, ya ce ""Ki yi ha™uri"" ta kalli cikin idonsa ta ce ""Kai yakamata na bawa ha™uri nayi al™awarin saka kotu ta wanke malam garba, a gurfanar da ainihin wanda yayi laifin, amma ya rasa rayuwarsa ina kan ™adamin aikin, na fara tsorata kamar ba zan"

"iya ba Vi"""

"Ya girgiza kai ya ce ""Zamu cigaba da ™o™ari, ba zamu gaza ba, ba zamu sare ba, zamu yi nasara"

"in sha Allah, idan kina cewa kin karaya, nima karaya nake yi"" ta ja wata irin ajiyar zuciya ta kalli rigar jikinsa."

"""Vi"""

"""Mmm"""

"""Me kake Soye mini ne? Ba irin wannan rigar ka yaga lokacin kana Asibiti ba, mai tambarin"

"dragon Win nan ba?"""

"""Ki daina saka ido, kina ™irga mini kaya, son rigar nake yi"" hararsa tayi ta ce ""Am not kid"""

"""You are"" yayi maganar very serious."

"Wani ne ya shigo Wakin Nabila, yana shigowa ya ce ""Viperrr"" ya kira sunan yana jan sunan, tare"

"da dun™ule hannunsa, ya mi™awa Viper, Viper ya dun™ule nasa suka haWa."

"Ya ce ""Ya madam, ta tashi? Barrister ya ™arfin jiki?"""

"""Ba sau™i"" ta faWa tana tura baki."

"Duka suka kalleta, ya ce ""Subhanallah, ba sau™i fa, garin yaya meyafaru?"""

"Ta nuna Viper, ta ce ""Baya son na warke, bai iya jinya ba sam"" dariya ya yi ya ce ""Maza gumbar dutse, ina Viper zai iya jinya dama, ki manta da shi, zaki samu sau™i in sha Allah, meyake"

"damunki yanzu?"""

"Ta girgiza kai ta ce ""Babu komai, ™irjina ne yake nauyi kawai"""

"""To ki cire damuwa daga ranki, zai daina in sha Allah"""

"Ta ce ""Ok sir, na gode sosai"" yayi rubuce-rubuce a file Win hannunsa ya fita."

"""Vi"""

"""Mmm"""

"""Wai ina ne nan? Kuma waye wannan Win?"""

"""Asibiti da likita"""

"Nabila ta ce ""Ai na san asibitin ne, ina son tafiya ne, zan je na ga malam garba"""

"Viper ya kalleta ya ce ""Kina da abun gaya wa iyalinsa ne?"" Jiki a sanyaye ta girgiza masa kai."

"""To sai ki daina maganar zuwa"""

"""To ina son na gaya wa yan gidanmu ina Asibiti, kar a neme ni"""

"""Wa zaki kira? Wanda ya ce ki bar masa gida ki je ki nemi babanki, ko kuma yayanki da yake yi miki bita da ™ulli? Ko kuma sauran yan gidan da suke yi miki kallon yar hana ruwa gudu? Ba wanda ya damu da ke, mutum Waya ne, kuma a halin yanzu an gurSata masa tunani, na taSa tsintar kaina a cikin wannan halin. Mata guba ne mai masifar dafi da saurin kashe wanda suka hara. Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yayi gaskiya, da ya ce Bai bar wata fitina a bayansa da take cutar da maza ba a bayansa sai mata, banda haka me zai sanya mace ta raba Wa da uba?"" Yayi maganar jijiyoyin kansa na kumbura, idanunsa suka yi ja, suka ciccika da hawaye, tuna mahaifinsa"

da ya yi.

"""Ni ba guba bace ba, idan ka yi wa dukkan mata ka kira mu da guba, baka yi mana adalci ba, yakamata ko albarkacin jauhar mu ci, ka din ga kallon wasunmu ne gurSatattu, kamar yadda kuma"

"a jinsinku yake da akwai gurSatattu"""

"Yayi shiru tare da sunkuyar da kai, saboda sake soso masa wurin da yake yi masa ™ai™ayi."

****

"Indabo yana zauna yana karyawa, tare da matarsa, kawai Abdul ya faWo tsakiyar wurin da suke cin abincin."

"""Meye haka Abdul, baka iya sallama ba baka iya gaisuwa ba"""

"Indabo ya ce ""Ko giyar ka je ka sha, ka yi shaye-shaye ne?"""

"""Na daina shan giya da miyagun ™wayoyi, tun bayan da rahama ta shigo rayuwata, ta haskar ba™ ar bayahudiyar rayuwar da kuka tarbiyyantar da ni a kai, kodayeke gara ma ni shan giya ne da neman mata kawai, but am so much disappointed on you, nayi dana sanin kasancewar ka mahaifina. Dama a tsatson talakawa na taso, talakawa futuk sai ya fiye mini wannan mummunar"

"rayuwa da iftila'in kasancewar ka mahaifina"""

"""Abdul, uban naka ka ke gaya wa haka? Duk iya ™o™arin da yayi na ™arar da rayuwarsa wurin"

"ganin ya gina ku, ka zo gabansa kana gaya masa wannan maganar?"""

"""Mummy! Wace irin gina rayuwarmu, gangar jikin da aka gina da zunzurutun haramun da jinin mutane? Haba mummy da alama mafitarki kawai ki ka nema, ya sanya ki ka auri Daddy, wallahi mu 'ya'yanki baki yi mana adalci ba, kuma a yau ba sai gobe ba, zan bar ™asar nan, na nesanta kaina da ku, tun kafin asirinka ya tonu a idon duniya abun da ka yi ya shafe ni, gara in kalli duniya a hukunta ni da laifin fyaWe da nayi, da a hukunta ni da mummunan laifin da ka aikata, ga waya"

"nan ka karSa ka saurari sa™onka"""

"Yayi maganar yana mi™a masa wayarsa, Indabo ya saka hannu ya karSa, yana dubawa."

"Wani audio ya fara buWewa, sai dai jin muryar wanda yayi message Win kawai, ya rikita masa"

"lissafi, ya fara gumi hannunsa ya hau rawa."

"""Wanna sa™on ba naka bane ba, na mahaifinka ne. Duk da ina da access na yadda zan same shi, amma yafi dacewa na tura masa sa™on ta hannunka, sai yafi karSar sa da muhimmanci. Lokaci yayi da zamu daina buga wasan 'yar Suya da kai indabo, zamu yi wasa na ™e™e da ™e™e, saboda ina daf da barin ramina da nake Soye, na cigaba da addabar rayuwar ka ta kowane hali. Idan ka muzgunawa Nabila, tamkar jauhar ka taSa mini, taSa jauhar kuwa taSa zuciyata ne kai tsaye. Dan zan yi wasa irin wanda ka ke so ayi."

"Ka so ta zama tarkon da zaka yi amfani da shi ka kamani, shi kuma Allah ba azzalumin sarki bane ba. Šanka ya yi wa rahama fyaWe ™anwar Nura, da ka lalatawa rayuwa ka kashe, ka Worawa wani daban, kuma ka bishi ka saka an kashe shi. Abun da baka sani ba shi ne, ina da cikakkiyar shaidar mummunar Wabi'ar da ka ke aikatawa, ta lalata rayuwar matasa da sunan sama musu aikin yi."

"Sannan ni na saka aka kama Wanka Jafar, a Mexico in da ya gudu neman mafaka bayan yayi kisan kai, haka zalika yanzu ma da saka hannuna a mayar da shi amurka."

"Yanzu haka miyagun ™wayoyi da hodar iblis Win da aka loda maka a jirgin ruwa, za ayi safararsu"

"ta ruwa, za a kama

62 / 67