Karfe a Wuta Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   65 / 67

192K to 195K   out of 199.8K words

take halalina ma, sai da. Sai kuma ya yi shiru."

"Ya cigaba da cewa ""Kamar yadda na gaya miki, duk wata mace idan ba jauhar ba, namiji ce a"

"idona"""

"""Katako kake gani ba namiji ba"" tayi maganar cikin ™un™uni."

"""Ban taSa ganin abin da ya raina ni ba kamar ke? Amm dama zan gaya miki, ina ganin zan canza lawyer, saboda na lura baki da sa'a ko kaWan, gashi baki wani goge ba, nafi son wanda zai din ga abin da nake so. Idan na biye miki, sai na koma prison, kuma ™ila nima a bini a kashe a can,"

"kamar yadda aka kashe wannan mutumin, dan haka zan canza lauya""."

"Šagowa tayi tana kallon Viper, cikin tsananin mamaki da takaicin abin da yake fitowa daga"

bakinsa.

"Fuskarsa a Waure, alamar da gaske yake yi."

"""Bayan duk wannan wahalar da na riga na sha? Ka san zaka Wauki wani lauyan, amma ka wahalar"

"da ni, nake ta dagewa ina ™o™ari a kan shari'ar ka na kasa zaune na kasa tsaye?"""

"Viper ya ce ""Eh, muddin zaki cigaba da yi mini rashin kunya, tabbas zan sake saka miki ™arfe"

"wataran, kamar yadda na saka miki da farko, na gaji kin kasa kawo ™arshen lamarin, kullum sai surutu da shirme ki ka iya"""

"Tamkar ta kwaWe shi, haka wani abu ya cunkushe mata ™irji, kawai ta kifa kanta a kan gwiwarta."

"""Abla, Wago ki ga"" banza tayi masa ta™i Wagowa."

"""Kin san magana Waya nake yi"" ta Wago idanunta, da suka yi sharkaf da hawaye."

"Ya ajiye mata takarda a gabanta, takardar umarnin kotu ce, da ta hana kama shi, Wagowa tayi ta kalleshi, ta rasa ihu zata yi na murna ko kuma me? Kawai ta cukuikuye takardar, ta jefa masa a ™"

"irji, ta sauka daga kan gadon tana cigaba da kuka"""

"Murmushi ya yi ya tashi ya bi bayanta, cikin kuka ta ce ""Amma a haka kake cewa zaka canza"

"lauya?"""

"Ya ce ""Sorry, am just kidding"""

"""A haka ake wasa Vi?, fuska a Waure ana zare ido? Tayaya zan gane wasa kake yi?"" Tayi maganar"

tana kuka cike da shagwaSa.

"Ya ce ""Viper baya manta halacci, ba kuma ya saSa al™awari, ko da zaki yi failing sau dubu, ba zan"

"taSa barin ki ke kaWai ba, al™awari ne da na Wauka"""

"Nabila ta ce ""Look at you, i even save your life, amma da haka zaka yi mini albishir da 'yar ™ aramar nasarar da nayi"" ya girgiza kai ya ce ""Ba ™aramar nasara ba ce Congratulations, and barrister Habib ya yi miki message, Civil defense sun Waukko rahama"" a take ta waro ido ta ce"

"""Dan Manzon Allah, da gaske?"" Ya jinjina mata kai, alamar eh."

"Rikicewa tayi, ta dur™usa tayi sujudu shukur, ta tashi, ta shiga kaiwa tana komowa ta ce ""Alhamdilillah, ko yanzu na mutu, na cika wani sashe na al™awarin da nayi, Allah sarki malam"

"Garba, Allah ya yi masa rahama, ni me ma zan yi ne dan daWi Vi?"""

"Murmushi take yi, tana kuka, tana ta zarya a Wakin, kamar zata zare, shi kuma sai bin ta yake da"

"ido. Ta je ta tsaya a jikin bango, ta jingina tana sauke numfashi."

"Ya sake takawa, ya ™arasa in da take ya saka hannunsa Waya ya dafe bango, yana cigaba da"

tsareta da ido.

"""Thank you for saving my life 'yar suga"" duk da ta takura, amma bai hanata yi masa murmushi ba."

"Kallonta yake yi, yana tunanin a yaya zata Wauki ™addarar da take bibiye da ita? Ko zata iya jurewa, ko zata gaza kamar yadda yayi? A hankali ya ce ""Wannan babbar nasara ce ki ka samu, kamar yadda nayi tsammani, ba kya gori, kamar yadda Jauhar take, na zata da na ce zan canza lauya, zaki yi mini gori, amma ba ki yi ba."

"Akwai tambayoyi da ki ka yi mini a baya, da wasu wanda nake son na yi miki."

"Da fari meyasa nayi yin™urin kashe ki karon farko da na ganki? Meyasa ki ka ga ruWewa a fuskar liti da walid da suka ganki? Meyasa na din ga korarki idan ki ka zo wurina, nake yi miki barazanar"

"mutuwa? Meyasa su liti suka amince su kawo ki wurina, duk da babu mahalukin da suke bawa damar hakan? Meyasa Indabo ya ke ™o™arin yi mini tarko da ke? A yanzu ko a baya, ba za a rasa mutanen da suka nuna miki sanayya ba, alhalin baki san su ba right?"" Ta tsare shi da ido tana jiran"

amsohin tambayoyin.

"""And as my lawyer, akwai abubuwan da yakamata na sanar da ke, but before then, Abla ni da ke ™"

"addara ce mai ™arfin gaske ta haWa ni da ke, dan haka dole mu yi ha™uri, mu karSeta a yadda ta zo mana, saboda pain Win da zaki shiga, zai iya fin wanda ni na tsinci kaina a ciki"""

Tayi tsuru tana kallonsa.

"Ya zaro wani hoto a aljihunsa, ya mi™a wa Nabila."

"Hannunta na rawar rashin sanin wace ™addarar ce, ta sanya hannu ta karSi hoton, wata 'yar ™ aramar ™ara ta saki, ta saki hoton a ™asa, jikinta yana rawa, ta kalleshi ta ce ""Soka ke sai na haukace sannan zaka daina yi mini wasa da hankali, menene wannan? Ni bani bace wannan, ni yaushe na sanka har muka yi wannan hoton tare?"" Tayi maganar a firgice, tana neman ta raSa shi ta wuce, amma ya ri™eta a jikin bango, idanunsa suka cika da hawaye ya ce ""Matata ce a jiki, ita ce jauhar, 'yar madarata, mace mafi soyuwa a gare ni, matar da ba zan manta halaccinta ga rayuwata ba, matar aljanna da kullum nake fatan na farka daga mummunan mafarkin da nake yi, na farka na ganta a kusa da ni, Nabila meyasa ki ke kama da matata?"" Jikinta ne yake wata irin"

"rawa, ta zazzaro ido tana kallon sa."

"BuWe ™ofar Wakin aka yi, suka waiwaya gaba Waya suna kallon ™ofar, Alhaji mu'azzam ne ya"

"shigo tare da barrister Habib, da kuma Wan mama, da yake laSewa a baya, yana le™owa."

"Cikin mamaki Viper yake bin Alhaji mu'azzam da kallo, ba tare da ya saki Nabila ba."

Ayshercool 08081012143

¦ 500 ne via 0009450228

Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne.

90009343

'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

*BRIGHT PENS SECOND BATCH*

"Ku kasance da littatafan bright pens, second batch."

*˜ARFE A WUTA (AYSHERCOOL)*

*MUTALLAB (NIMCYLUV)*

HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)*

*ZAYTOON (ZEE KUMURYA)*

"""Bana iya gane ina ake, saboda a matu™ar galabaice nake, amma naji a jikina, yakamata ace idan asibiti ne ya ci ace an je, duk da bana sanya ran zan rayu, a maganar da mutanen motar suke yi, jini nake ta fitarwa ta hancinca, ga azabar yunwa da datti, na gidan yari, tufafina tamkar mahaukaci, dan a mazaunin da aka ajiyeni kenan."

"Aka yi parking Win motar, aka canza mini wata, wadda nake kyautata zaton ambulance ce, dan a ciki aka toshe hancina da bandeji, saboda jinin da nake zubarwa, aka saka mini ruwa, muka cigaba da tafiya. Tun ina jin maganganun da ake yi a motar, tafiya ta™i ci ta™i cinyewa, har na daina gane komai, na buWe ido na ganni a wani wuri, a kan gadon asibiti, an tuSe kayan jikina, sai gajeren wando, na tashi a gigice cikin matsananciyar kiWima, ina ihu saboda ban san meyafaru da ni ba, na farka ina zaton zan ga madaki da jauhar, ina hana shi cutar da ita, wani Sangaren ina tunanin ko ina prison ne, wani yayi galaba a kaina. Sai dai na ji ni a Waure da ankwa dukka hannayena, na din ga ihu saboda yadda naman jikina yake yi mini wani irin azababben zugi, kamar ba zan rayu ba."

"Wasu mutane da ban san suwaye ba, suka zo kaina, da allurai suka yi mini, Waya daga cikin su ya ce ""A cigaba da kula da shi mu gani, will he survive the poison, duk yadda zaku yi, ku yi ™o™arin ceton rayuwar sa"" haka na sake fita hayyacina na farka, sai dai a wannan karon, ban ji wannan raW aWin ba."

"Aka cire mini ankwa, aka tashe ni zaune, aka kawo mini abinci, kamar mayunwacin kare, haka na dirarwa abincin nan, kamar zan haWa da kwanon saboda yunwa, ina ci ina jin kamar ana yayyanaka kayan cikina da wu™a, amma azabar yunwar da nake ji, ya sanya na™i daina ci, sai dai ban gama ci ba na din ga amai, haWe da jini, wai duk cikin side effect Win allura da aka yi mini ne, kashe ni aka so ayi."

"Ba a sake bani abinci ba, sai ™arin ruwa da allurai, mutanen wurin ba kowa ke jin hausa ba, ni kuma bana magana, suna bani damar yin salla, aka fara koya mini cin abinci."

"Ba wanda na tambaya dalilin kai ni wurin nan, kuma babu wanda yayi mini bayani, a haka har na shafe wata guda cif."

"Duk yadda suka so nayi magana, bana yi, sai dai wasu lokutan ina rasa tunanina, na din ga ganin madaki da jauhar a zahiri, na din ga yin™urin sha™e duk wanda yake kusa da ni. Sai da na Wan samu nutsuwa, aka aske mini gemuna da sumar kaina gaba Waya, aka kuma saka mini ankwa, aka rufe mini ido, aka sakani a mota, aka bar wurin da ni."

"Wani wurin aka sake kai ni, mu huWu ne a wurin, kowa da wurin da ake ajiye shi tamkar ceil. Na fauskanci nikaWai ne musulmi babu bahaushe, sai ™abilu, kullum bayan nayi sallar asuba, da sassafe haka za a kaimu wani wuri, ana bamu training na azabatarwa, wanda ka iya zama ajalin mutum."

"Idan muka gama, zamu saka wasu riguna, masu tambarin dragon, za a kaimu wani wuri, in da ake bamu darasi, malamanmu turawa ne, class Win mu huWun nan ne, kowa da computer sa, ayi mana darasi ta online. WaWanda suke kula da mu, wasu irin zaratan ™artin sojoji ne, sun kai su goma sha biyu, a kan mu huWu kawai."

"Azaba ta ishe ni, ban ga alamar za a mayar da ni gida ba, na gaji, gaba Waya na rasa ina rayuwata"

"ta dosa, bani da wani burin da ya wuce na mutu na huta. Za a bamu abinci mai kyau, a bamu abin sha mai kyau, amma azabar da ake mana ta ishe ni. Wataran ana tsaka da bamu training, na fizgi bindigar wani, nayi yin™urin kashe kaina, suka ri™e ni, aka Wauke ni aka kai ni wani Waki, da ban zaci zan fito da rai ba. Sai da na kwana bakwai a Wakin, ko class bana zuwa. Ranar na takwas, ogansu ya zo ya same ni, yake tambayata meye matsalata na yi yin™urin kashe kaina."

"Na ce masa su mayar da ni garinmu, ina son ganin matata."

"Ya ce mini muddin ina son komawa gida, sai na basu haWin kai, na yi wa ™asata aiki, sun san ni yaron dodo ne, kuma akwai amfanin da zan yi musu, dan haka dole na mayar da hankali a kan training da kuma karatun da nake yi, kuWi aka ware masu nauyi, saboda mu yi wannan karatun."

"Na ce ni ba zan yi ba, su kasheni kawai su daina wahalar da rayuwata."

"Ya ce ba zasu kashe ni ba, in yi abin da suka umarceni, idan ina son na ga matata. Sai na tambaye shi, matata na raye? Ya ce tana raye, zan ganta idan na daina taurin kai, nayi abin da ake so. Kuma ko ina so ko bana so, ubangidana ne ya nema mini wannan aikin, tun kan ya mutu, dan haka sai dai na mutu a process Win, tun da na san sirruka masu muhimmanci da zasu taimaki ™asa. Na din ga tunanin, wane irin laifi na yi wa dodo, zai zaSa mini wannan azabar, sai dai tsananin Woki, da daWin bakin zan ga matata, ya sanya na saduda, gashi suka saka mini ido sosai da sosai, saboda suna i™irarin bani da lafiyar ™wa™walwa, kuma bana ji."

"Wata makaranta muke yi a russia, ilimin na'ura mai ™wa™walwa kawai ake bamu, duk da na san abubuwa da yawa ni, ta online muke makarantar, a training Win nan aka koya mana duk wani nau'i na haWawa da wargaza bindiga, ilimin makamai, le™en asiri, da duk wani nau'i na abin da ya shafi harkar tsaro."

"Suka ce mini ™wazona, shi zai bayar da damar komawata garinmu, har naga matata, na ro™e su ko a waya, a haWani da matata tun da sun ce tana raye, suka ce ba zasu haWamu ba, zan Sata musu aiki."

"Na zage damtse, lokutan jarrabawa, ina cikin overollers, ina tashi da points masu kyau, na fara sabawa da wahalar training, jikina duk ya murWe, sai dai babbar matsalata bana cikakken bacci, bana iya bacci, da na rufe idona, zan ganni a falo, tare da jauhar madaki zai kasheta, gaba Waya sai na tubure musu, na hau ihu. Ko abincin da nake ci, bana cin sa ta daWin rai, saboda damuwa da tunani. Abokan karatuna a kan basu damar shan giya, har mata a kan kawo musu, amma ni duk ba wannan a gabana."

"Tun ina lissafi da sanya ran ™arewar wannan wahala, naga babu rana babu wata, na zauna nayi tunani, babu yadda za ayi, jauhar na raye a gurfanar da ni a gaban kotu, a tuhume ni da laifin kisan kai, naga kawai raina mini hankali suke yi, sai kuma wata zuciyar ta ce mini ai mafarki nake yi, sai dai na rasa wanne ne mafarkin wanne ne zahirin?."

"A haka na shafe shekaru a wurin nan, ban taSa barin kewayen in da muke ba, na rayu da matsanancin ™unci da damuwa a zuciyata, wasu lokutan sai an yi mini allurar bacci nake iyawa."

"A haka muka kammala karatu, sauran ukun aka ce, za ayi posting Win su, in da ake son su gabatar da ayyukansu, ni kuma sai an yi settling issue Wina. Mun zama sojojin le™en asiri."

"Ni dai jinsu kawai na din ga yi, sauran suka din ga murna, aka shirya mana walima, sauran duk sun saba da su, ni duk yadda aka so ja na a jiki, a yi raha da ni, a saba ban yadda ba, dan ni kaina na san rabi mai hankali rabi mahaukaci nake. Abokan karatuna kuwa, basa shiga harkata, dan duk lokacin da ™wa™walwa ta ta haska mini fuskar madaki, a jikin Waya, sai na kusa kashe shi, dan duk da training Win da aka bamu, na fi su ™arfi nesa ba kusa ba, kuma ba addinmu Waya ba, ba ™"

abilarmu Waya ba.

"Sai da na ji haushin dodo, duk da baya raye, na ji ya sakani a masifa, duk da ina fatan sanya indabo, biyan bashin abin da ya aikata ciki har da kisan dodo."

"Ana gobe za a mayar da ni kano, ina ta murna zan koma naga jauhar, naga Wana, dan na san a lokacin ya yi wayo, ban san meyafaru ba, ko me suka yi mini ba, sai farkawa nayi, na ganni a prison. Hakan ya ™ara burkita ™wa™walwa ta, na fara tunanin wani mafarkin na kuma yi, na din ga kiran sunayen shugabbaninmu da suka bamu training, ina cewa su zo su cika mini al™awarin da suka yi mini, su haWa ni da jauhar Wina da Wana kamar yadda suka yi mini al™awari, gashi ko za a kashe ni, ban san sunan garin da aka kaini ba."

"Gandirobobi, suka yi mini dukan tsiya, wai na cika musu kunne da hauka, matar da na kashe da hannuna, bayan na sha na bugu, na amsa hakan a kotu, yanzu kuma na zo na ishe su da shirme. Suka yi mini dukan tsiya, amma na kasa daina kururuwar kiran sunaye da magiyar su haWani da jauhar, gaba Waya na zama mahaukaci, ni kaina a lokacin na yadda ni mahaukaci ne. Wasu lokutan idan na buWe jikina, ina ganin tabon raunuka da wahalar da na sha a wancan garin, amma fafur aka nuna hauka nake yi, da sambatun ™arya."

"Tun da suka tabattar mini ni na kashe jauhar, na ™ara rasa tunanina, damuwa da tashin hankali suka koma sabbi fil."

"Kusan watanni uku, cikin dare ina kwance, dama Wakina daban, aka tashe ni aka ce na fito, na fita na bi bayan wanda suka kira ni, aka fitar da ni wajen gate, wai an karSi court order na tafi."

"Na tsaya ina kallonsu, ina mamakin wane mafarkin kuma na sake shigowa, suka rufe gate Win prsion Win, suka bar ni a tsaye."

"Zuciyata

65 / 67