Karfe a Wuta Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   51 / 67

150K to 153K   out of 199.8K words

shiga, ka jira ni a office Wina,"

"yanzu zan dawo"""

"Viper ya kalli Nabila ya ce ""Koma ciki"" sai ta tsaya tana rarraba ido, tana kallonsa tana kallon"

Alhaji mu'azzam wada.

"Wani irin kallo Viper ya yi mata, da ya tilasta mata barin wurin, tana waiwayawa."

"Viper ya saka hannunsa a hannun Alhaji mu'azzam, ya sauke facemask Win sa yana kallon cikin"

idonsa.

"""Dama ana ganinka, ka yi wa hukuma wuyar kamawa? Ya aka yi na ganka tare da yarinyar da"

"nake so, kuma nake fatan na aura?"""

"Viper ya tsananta ri™on da ya yi wa hannun Alhaji mu'azzam ya ce ""Ka gaya mata wani abu ne?"""

"""Kamar me fa?"""

"""Ka san abun da nake nufi"" yayi maganar yana ™ara tsare shi da ido."

"Alhaji mu'azzam ya ce ""Kana tsoron wani abu ne?"""

"""Ba maganar tsoro bane ne ko akasin haka, gargaWi ne nake yi maka, idan baka furta ba kar ka fara,"

"nike da alhakin kai ™arshen wannan lamarin, idan ka yi wani yin™uri da zai kawo tangarWa ga abun da nake tsarawa, ka san abun da zan iya aikatawa""."

"Alhaji mu'azzam ya yi murmushi ya ce ""Da fari jauhar, na bar maka ita, a wannan karon kuma"

"Nabila, kar ka zama mai......"

"""Jauhar ta wa ce, haka zalika Nabila, muddin zan cigaba da ganin fuskar jauhar a cikin ta Nabila ta haramta a gareka, ba kai ba kowane mahaluki ma"" ya fizge hannunsa daga na Alhaji mu'azzam ya"

mayar da facemask Win sa ya bar wurin.

"Nabila kuwa kai komo ga din ga yi a office Win ta, cike da fargaba da tsoro."

"Kankarofi ya turo ™ofar office Win Nabila ya shigo, ta tsaya tana kallonsa yayi mata murmushi ya"

"™arasa ya ce ""Madam ya na ganki a tsaye ne?"""

"Murmushin ™arfin hali ta yi ta ce ""Bisimillah zauna mana"""

"Ya zauna ya ce ""Ashe tsautsayi ne ya kuma afkuwa haka, ya ™arfin jikin?"""

"Ta ce ""Jiki da sau™i Alhamdilillah"""

"""Amma dai babu wani mummunan rauni ko?"""

"Ta ce ""Eh, gocewar ™ashi na samu a hannuna, amma Alhamdilillah da sau™i"""

"""To Alhamdilillah, na ji daWi ™warai, ya shari'a kuma?"""

"Tayi murmushi ta ce ""Mu na ta fama, sai fatan Ubangiji Allah ya iya mana"""

"""Allah ya yi jagora, kin ga kamata yayi ace har gida na je dubiya, daga nan na mi™a bu™ata ta ga Abba, ayi komai a kan lokaci, kin ga babban mutum ne ni, amma soyayya ta saka sai wahalar da"

"ni ki ke yi, kina sakani sintiri, sai dai na yi ta biyoki office"""

"Ta Wan shagwaSe fuska ta ce ""Wahalar da kai kuma?"""

"Ya kwantar da murya ya ce ""Eh mana, ko ba ayi na ne, ya sanya ake ta bani wahala"""

"""Matanka fa biyu, ni gaskiya..."

"""Ba kya son mai mata ko?"" Ta jinjina masa kai alamar eh."

"""To meyasa?"""

"""Wahala ake sha, kuma nan da nan ake sakin wadda ta zo daga baya, impact ni fa tashin hankali ne"

"ba na so, gidanmu ma uku ne, ina ganin tashin hankalin da ake yi"""

"Yayi dariya ya ce ""Barrister, dabarar mutum ba ta sanyawa ya kaucewa ™addararsa. Da dabara da wayon mutum na sanyawa ya kaucewa ™addara, da wata™ila haryanzu fatima tana raye da ni ta"

"aura"""

"""Wacece hakan?"""

"""No kar ki damu, kawai dai misali nake yi miki, wata yarinya ce da na taSa ™allafa raina a kan"

"aurenta, Allah bai yi ba"""

"""Baka aureta ba, sai ka auri mata biyu, yanzu da sai ka yi ta uku da ita ni ta huWu?"""

"Sosai ta bashi dariya, saboda yarinyata da kishinta da suka gaza Suya."

"""Karki damu, labarin ne akwai sar™a™iya, idan ya zo ™arshe zan baki. Amma matana ba matsala bane. Uwargidana tana Abuja, amaryata kuma na kano, ke kuma sai in da ki ke so zaki zauna"" No™e kafaWa tayi, tana Wan tura baki, har ya gama yi mata hirar, bai yi mata magana akan Viper ba, duk da ta so ta tambaye shi ko ya san shi, amma ta ja bakinta tayi shiru, dan da Viper yakamata su"

tattauna wannan maganar.

****

"Naja'atu Bunkure ce zaune a office Win Abdul yasar, ya hakimce a kan kujera yana saurarenta."

"""Abdul, yarinyar nan fa dole ka fito da ita, even for your own safety, idan fa aka wanke mutumin"

"nan, akwai cakwakiya, bamu san ya shari'ar nan zata kasance ba, taurin kan nan da kake yi, babbar barazana ce gareka da mahaifinka Shari'a saSanin hankali ce"""

"Abdul ya ce ""Ba wata barazana, ai ba yau ki ka saba goge laifi ba komai girmansa, wannan karon"

"ma ki yi wani abu"""

"""Nayi iya yi na, da kai da mahaifinka ne kuka Sata komai, Abdul idan lamarin nan ya kwaSe fa,"

"zaku shiga matsala mussaman ma kai. Kuma an gaya maka shaida kawai zata bayar a kotu shikenan ba wani abu ba"""

"Abdul ya yi murmushi ya ce ""Naja'atu Bunkure, na sanki fa, na kuma san waye mahaifina, na san abun da zaku iya na san wanda ba zaku iya ba. Idan aka kuma cutar da yarinyar nan a karo na biyu, ba zan yafewa kaina ba, ke da kanki kin san kura tayi lafiya, duk da a duk lokacin da zan shiga Asibiti ina ajiye duk wani iskanci a gefe, in shiga a nutse, amma ke kin san yanzu na nutsu sosai"

"da sosai, albarkacin rayuwa tare da rahama"""

"Naja ta tafa hannu ta ce ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Abdul kidnapping fa kenan, bayan fyaWe"

"ka saceta kana rayuwa da ita, wani laifin fa kake aikatawa a kan wani"""

"""Babu wani laifi da nake aikatawa, da na barta to da tabbas kun yi mata wata illar, barinta a wurina"

"shi ne zata zauna safe"""

"""Shikenan, zamu Wauki duk wani mataki da hukuncin da muke ganin ya dace"""

Ya Wage kafaWa alamar ko a jikinsa.

***

"Indabo kuwa gaba Waya ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya rasa abun da yake yi masa daWi, tun yana"

"™irga adadin shigarsa banWaki, har ya sare lissafi ya ™wace masa."

"Gudawar tsoro da fargaba kawai yake yi, tun bayan da Viper ya kira shi a waya."

"Embassy Win Nigeria na Mexico ya kira, domin a bincika masa da maganar da Viper ya kira shi ya gaya masa, idan gaske ce."

"Ya ma rasa wa zai kira ya gaya wa maganar, ashe da gaske yana sane da cewa, da shi yake sakawa ayi exchange a duk lokacin da jafar ya aikata laifi, to ko da sanya hannunsa aka kama masa Wa?"

"Amma ya za ayi common Wan daban gari, ya saka a kama masa Wa a ™asashen ™etare?."

"Waya ya Wauka ya kira IG, ya din ga masifa, a kan jan ™afar da ake yi, wurin kama Aminu Viper,"

"tare da jadadda idan har ba za su yi abun da yake so ba, zai shiga ya fita a Wauke shi daga garin"

"kano, a canza wani IG. Tun da suka kasa kama mutum Waya, alhalin yana yawonsa a gari, da"

aikata abun da yake so.

"Yayi ta bashi ha™uri, tare da bashi tabbacin suna iya ™o™arin su, amma komai ya kusa zuwa ™"

"arshe. Ya ajiye wayar yana mamakin ya za ayi, ace senator guda ya tayar da hankalinsa haka a kan"

"Wan daba guda Waya tal har haka, ya din ga Sata lokacinsa a kansa."

"Yadda indabo ya kira shi, ya tayar masa da hankali, haka shima ya kira Nasir a waya, ya ce masa nan da kwanaki talatin, idan babu improvements a aikin nan, zasu karSi aikin daga hannunsa su"

"bawa wani, kuma hakan ka iya janyo masa demotion, da rasa wasu damarmaki."

"Shi ma ha™urin ya din ga bayarwa, tare da bada tabaccin zai kama Aminu Viper."

***

"Abdul da la'asar ya koma gidansa,ya tarar rahama na wanka, ya kwanta ya yi Wai-Wai a kan gado."

"Ta buWe ™ofa ta fito, ta tarar da shi ta Sata fuska ta ce ""Abdul meye haka?"""

Ya buWe ido ya kalleta.

"""Na gyara gadon, kawai ka hau ka ajiye mini shirginka, wata uwar jaka kamar wanzami, kalli"

takalmi har bedroom ba a wancan Wakin nake ajiye maka ba?

"Lumshe idanunsa ya yi, ta ™arasa ta kwashe kayan, ta hau kan gadon ta kwance agogon hannunsa,"

"dan ta san ™arshe ya cire, ya yar da shi a wani wurin, ya zo ya isheta da nema."

"Ya kai hannu ya fara shafa bayanta, tayi masa banza, tana cikin Salle masa labcourt ya cigaba da shafa gashin kanta, sai da ya kai hannunsa kan towel Win ta, ta buge hannunsa da ™arfi ta ce"

"""Tashi kayi sallar la'asar na san baka yi ba"" ya buWe idonsa ya kalleta."

"""Eh kana wani manne ido, ka tashi kayi sallar la'asar"""

"""Zan yi in anjima, yanzu na gaji"""

"Ramma ta buWe baki ta ce ""Wace anjiman? Kai ke da anjiman? Waye ya baka guarantee kai wa anjiman? Abdul wallahi wutar duniya ma ba zaka iya da ita ba, balle ta lahira, kai a wuta kala nawa kake so a saka ka ne? Sa™ara fa, wutar marasa yin salla, ita ka ke so ka shiga ko? bayan ta shan giya da neman mata. Ba shiri ya tashi ya ajiye labcourt Win ya ce ""To naji, ai dama ban ce ba zan yi ba, zan yi Astagfirullah in sha Allah ba zan shiga wuta ba, shan giya da neman mata ai kin"

"san na daina"" yana maganar ya nufi banWaki."

"Sai da tayi dariya, Abdul ga tsoro ga iskanci, ta tabatta da ya samu kyakkyawar tarbiyya, da"

"isashshen ilimin addini, da bai aikata wasu abubuwan ba."

"Taje gaban mudubi ta zauna, mudubin fal da turaruka, da kayan gyaran gashi da na fata, wasu"

"abubuwan duk shi ya koya mata amfani da su, har wasu supplement yake bata tana sha. Ita kanta ta san tayi ™iba ta yi kyau. Tayi ajiyar zuciya ta fara shafa man."

"Ya fito ya tayar da salla, ta ce ""A kyautata niyya da nustuwa idan ana salla, yadda ka yi ta haka zata zo maka a kabari"" ta shirya cikin doguwar riga, yana idar da sallar, ta Waukko masa azkar ta ce ""Ungo, ka san shi yawan ambaton Allah, yana hana mutum aikata alfasha, abu ne mawuyaci kaga wanda yake da kusanci da Allah, yana aikata Sarna kala-kala"" haka ta saka shi a gaba, ya"

idar suka je ya ci abinci.

"Gaba Waya rayuwa da ramma ya sanya ya ji tamkar an canza shi, zuwa wani na daban, haka"

kurum yake jin wata nutsuwa a tare da shi.

"Mussaman saita shi da take yi a kan ibada, da yawan tsoratar da shi a kan yin ta, haka yana saka masa nustuwa da kwanciyar hankali, kuma ya rage aikata tsageranci da rashin ta ido. Hakan ya"

"sanya yake ™ara jin raba shi da ramma, tamkar raba shi da rayuwar sa ne."

"System ya kunna ya ce ""Your excellency zo ki ga wani abu"""

"""Wanke-wanke zan yi na Wora abincin dare"""

"""Karki damu, zan yi mana takeaway"""

"""Sai dai idan zaka yi wanke-wanken"""

"Abdul ya ce ""Na ji zan yi"""

"Ta ™araso ta zauna, ya rungumeta a jikinsa, sannan ya buWo wani form ya ce ""Kin san na menene"

"wannan?"""

"""No"""

"""Form Winki ne na makaranta"""

"Ta kalleshi ta ce ""Makarnta kuma?"""

"Ya ce ""Eh mana, ko ba kya so?"""

"""Ina so, amma gida zaka mayar da ni?"""

"""Eh, zaki je ki ga gida, daga nan sai school, boarding ce, mai kyan gaske, saboda sonake ki nutsu ki yi karatu da kyau, yadda babu wanda ya ganki, balle yayi miki gori, da kin gama karatu kuma, ™asar waje zaki tafi jami'a, shiyasa nake tambayar ki me ki ke son zama, na biya komai, na yi"

"rubutu, yadda ko bayan raina ba zaki tozarta ba in sha Allah, ko bana raye karatunki ba zai tsaya"

"ba sai kin kammala in sha Allah"""

"""Yar uban wace ni da zaka yi mini duk wannan hidimar haka?"""

"""Ba yar kowa ba ce, amma komai zan yi miki, ba zai kai nauyin laifin da nayi miki ba, ba zai biya budurcinki da na karSa ta ™arfin tsiya ba, da kuma rashin darajar da naje gidanku nayi ba, ba zan gaji da cigaba da neman afuwar ki ba rahama"" ta sunkuyar da kai ta yi shiru, hawaye na zubowa"

daga idanunta.

"Ya saka hannu yana share mata hawayenta ya ce ""Ki yi ha™uri, na san na cutar da ke, dan Allah ki yafe mini rahama, soyayyar nan kawai da Allah ya jarabbe ni da ita, ta isheni, baki san tarin ™ alubalen da yake a gabana nake ta ™o™arin karewa a waje ba, amma dai ki yi ha™uri dan Allah"" a"

"hankali ta zare hannunta daga nasa, ta tashi ta bar falon tana kuka."

***

"Nabila kuwa da file Win Viper ta tafi gida, ta kai shi Wakinta, ta cigaba da duba shi daki-daki, tana picking Win kurakuran da aka tafka a cikin shari'ar ta sa. Kai da ganin fasalin shari'ar ka san cewa cike take da mugunta da zunzurutun zalunci."

"Zafi ne ya isheta, babu wuta, ga solar sai ™ara take yi, kasancewar ranar ba ayi rana sosai ba."

"Ta Waukko system Win ta, da wayoyinta, ta fita gareji, ta shimfiWa sallaya, da kayan ciye-ciyenta,"

ta zauna ta cigaba da aikinta.

"Nasir ne ya fito yana waya, ba ta san da wa yake yin waya ba, sai dai yanayin yadda ya fito yana"

"wayar, bai san tana wurin ba."

"""Eh dan Allah, duk yadda za ayi a samo mana hotunansa, ko guda Waya ne, nima na daWe da wannan tunanin, ban aiwatar ba, amma a yanzu naga hakan ne kawai mafita, a samo hoton nasa, dan IG ya kira ni Wazu, shi kansa distinguish sai da ya kira ni, ni duk na ruWe, nayi mamakin yadda aka yi mutum Waya ya gagari hukuma. Duk wata hanya da na bi da zan sameshi, sai ta kuS"

uce mini.

"Shiru ya yi, lokacin da ya lura da ita a wurin a zaune, ya ™ar™are wayar ya saka a aljihunsa."

"""Dama har zuwa yanzu baka taSa ganinsa ba, baka san kamaninsa ba?"""

"""Eh"" ya bata amsa a ta™aice."

"""Hmm"""

"""Ko zaki bani hoton nasa ne?"""

"""Ni a su wa?"""

"""Ke a 'yar kankamba mana, samunki da hotonsa ai ba abun mamaki bane ba"""

"Nabila ta yi murmushi, kawai ta cigaba da aikin da yake gabanta."

****

"Mutumin da yake zaune a cikin ofishin sa, ya kalli P.A Win Indabo ya ce ""Šan sake duba na da kyau mana malam"""

"P.A ya ce ""Na kalleka"""

"""Shekaru huWu rak idan Allah ya bani aron rai, suka rage mini nayi retire, a tarihin aikina, ban taSa karSar cin hanci na aikata son zuciya ba, ban ™i ba wasu lokutan ina karSa in yi abun da ya dace, duk da hakan ma saSa doka ne. Ba za a haWa kai da ni ayi rashin albarka ba, a tozarta harkar shari'a ba, idan na ci amana na tsayawa ™arya a duniya, wa zai tsaya ni a kotun Allah idan zai yi mini hisabi, a cikin kai da uban gidanka, waye zai ™wace ni? Tambayarka nake yi, na ce waye zai ™wace ni? Kotun Allah saSanin tunanin Wan Adam ce, kuma wallahi dukkanin mu, sai mun tsaya a wannan kotun, kotun da bata bu™atar lauya, Wan sanda balle ka yi tunanin bayar da cin hanci."

"Duk da na san bada™alar da ake tafkawa a cikin harkar shari'a, na yi mamakin wasu abubuwan da yarinyar nan ta din ga faWa, yar cikina ce amma ina sauraron programs Win ta, kuma ko kaWan ban ji haushin yadda take tsigalewa aikinmu ba, yadda ake amfani da mu, ake aikata abun da ake so. Babu wani rashawa da zaku bani na karSa, zan yi abun da ya dace ne kawai, idan kuma aka sake zan yi abun da rai zai Saci. Kai in ta™aice maka doguwar magana zuwa gajera, daga sama aka yi mini magana a kan lallai nayi abun da ya dace a kan shari'ar nan, ba a bu™atar kuskure a ciki,"

"kuma ko ba haka ba, ni sonake na gama aiki na ajiye shi lafiya"""

"P.A ya jinjina kai ya mi™e tsaye, ya ce ""Hakan ma babu laifi, muna godiya sosai"" ya juya ya fita"

daga office Win.

***

"Missed call kusan uku Nabila ta yi wa Viper, amma bai Waga ba, sai da ranta ya sosu, ta rasa irin wannan murWaWWen hali nasa, gashi ko zata yi fushi da shi, na Wan lokaci ne, ana jimawa ta manta."

"Viper kuma fitowar sa kenan daga wanka, ya kalli wayarsa ya ga missed calls Win ta, har guda"

uku.

"Bai kula ba, ya fara ™o™arin neman kayan da zai saka, wayar Walid ta far ringing."

"Walid ya Waga yayi sallama, ta amsa ta ce ""Oga walid barka da wannan lokaci"""

"""Yauwwa barkanmu barrister, ya aiki ya jama'a"""

"""Alhamdilillah, ina ta kiran Viper ya ™i Wagawa, wai ni ko wani laifin nayi masa ya tsane har"

"haka ne?"" Walid ya kalli Viper, sannan ya ce ""Wanka yake yi yanzu ya fito"""

"Ta ce ""Ai dama kai kare shi zaka yi, baka taSa yadda yayi laifi, ko yayi laifin sai ka kare shi, dama"

"magana nake son mu yi da shi, kuma na ma fasa barshi kawai, sai anjima"""

"Da sauri Walid ya ce ""A'a ba za a bari ba, ko na haWa ki da shi?"""

"""Ba

51 / 67