Karfe a Wuta Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   2 / 67

3K to 6K   out of 199.8K words

rabon tallafin karatu ma, a saka mini ita a ciki"""

"Indabo ya ce ""Aminu kenan, shikenan jeka Allah ya taimaka"""

"Ya haWa hannayensa biyu ya ce ""Sa'a dai"" ya fice daga falon."

"Hajiya Bilki ta ce ""Gaskiya honorable, yaron nan yana wuce gona da iri, kamar tsoronsa ka ke ji"""

"Ya ce ""Ba tsoronsa nake ji ba, aikin da yake yi mini yana da yawa, kasada duk girmanta yana W"

"auka. Akwai lokacin da tilas na yakice shi ai""."

"Al'amin bai shiga da kayan gida ba, sai cefane da yayi na abincin dare."

"Ya tarar ta yi dambu tayi wa dambun miyar jajjage, da salad da awara."

"""Ke dai Allah ya yi miki iyayi, dambun da ake sakawa mai, ki ke yi wa miya, har da wata"

"munafukar awara""."

"Jauhar ta ce ""Idan munafuka ce, bamu mu raba da ni da boti, shikenan ba canji, kullum sai dai"

"dambu da mai? Ai gara a din ga upgrading"""

"""Sai dai ya mutu da yunwa kuwa, to ai awarar ce, 'yar kaWan"""

"""Wai master ba ka iya abun 'yan gayu ba? Babu naman da zan saka a cikin miyar, sai na haWa da"

"awara, bai bada ma'ana ba? Ko sai an cika kwanon da awarar passion ce a kai"""

"Ya taSr baki ya ce ""Eh to, gashi nan dai, zoSon ma kamar yayi tsami, amma kwantai ne na jiya ne"

"ko?"""

"""Mmmm, na waccan shekarar ne"" ta bashi amsa tana cigaba da aikin gabanta, na shirya stone."

"Tsoknarta yake yi, ya matsata tayi tsiwa, ita kuma ta™i."

"""Yaushe WAEC Win ku za ta fito ne?"""

"Jiki a sanyaye ta ce ""Ta kusa, har ba na son tunawa da ita"""

"""Saboda ba ki yi abun arziki ba ko?"""

"""A'a lokacin kana tsare, bana iya karatun"""

"Ya Wan rausayar da kai ya ce ""Eyya, abun tausayi, YallaSai dan Allah ku sake shi, ba shi da laifi, laifina ne, wallahi ba shi da lafiya ma, master dan Allah ka gaya musu ba ka da laifi"" yayi maganar"

cikin sigar kwaikwayon yadda ta yi waccan ranar.

"Murmushi ta yi ta ce ""Kada Allah ya kawo abun da ba zai wuce ba, a lokacin nan ji nake a duniya"

"kamar nikaWai aka tsana wallahi. Da aka ce mini an kai ka prison, kawai na sadda™ar ciwon zuciya"

"ya kama ni, kuma wai ka ce kar a kaini na ganka, ai na ji haushi, a duniya ba zan manta da su yaya"

"walid ba, duk da suna taimakawa wurin ™ara ingizaka a shaye-shaye, amma sun tsaya tare da ni a lokacin da kow yake ganin idan ya taimaka mini zai kwana a ciki"""

"Ya ce ""Allah sarki 'yar madara, ba na son in ga kina kukan nan ne, ko kina yi wa 'yan sanda"

"magana, suna wani yan™wana mini ke, raina Saci yake yi shiyasa na ce kar a sake kawo ki""."

"Ta ce ""Gashi ya wuce, duk da lokacin gani nake kamar ba zai wuce Win ba"""

"Ta tashi ta shiga Waki, ta dawo ta tarar da robar alawar madarar da take sayarwa, a gefensa bakinsa"

"kuma yana ta tauna, ta Waga robar ta ce ""Alawata ka ke sha ko?"""

"""Eh, ta guda uku na sha sittin, a rage mini naira goma hamsin kenan"""

"Sororo take kallonsa, ""To ai ba a jikina ake tatso madarar ba, da zan sayar da ita ashirin ashirin,"

"naira hamsin ce fa duk Waya """

"Ya waro ido ya ce ""Ki ji tsoron Allah, har na sha ta Wari da hamsin, gaskiya saba'in zan bayar""."

"Abun da yake so ya gani Win ta fara, shagwaSa tana cewa sai ya biya ta."

"""Gaskiya bani da kuWi yanzu, zo ki shanye abarki"" ya fito mata da harshen sa."

"Ta harare shi ta ce ""Bana so, kuma idan na zo yi maka wanki na tsinci kuWi, sun zama nawa"""

"""Eh ai dama kin saba kwashe mini 'yan canjina, da kayan cajina shiyasa ki ke yi mini wanki ba dan Allah ki ke yi ba"" ya tashi kamar zai tafi, amma ya ri™eta, yayi kissing Win ta, ya ce ""To kin ga tare muka shanye, yanzu talatin ma zan baki"" ya saka hannu a aljihunsa ya ciro dubu biyu ya Wora"

"mata a wuyanta ya ce ""Gashi nan, uwar son kuWi"""

"""Ai talatin ka ce zaka bani, saura dubu Waya, dubu uku yakamata ka bani"""

"Ya ce ""Biyoni Waki ki karSa"""

"Ta ce ""A'a na yafe maka sauran, amma kar ka sake"""

"Sosai wani bond mai ™arfin gaske ya shiga tsakaninta da shi, har mamakinsa take yi, duk da mai hali baya fasawa, idan miskilancinsa ya motsa, ko kuma ya cake, ba ya sarrafuwa ta daWi, amma haka take jurewa. Ga babban abun da yake ci mata tuwo a ™warya yanzu, wasu lokutan idan ya dawo daga shaye-shayen sa, da ™aurinsa da komai yake zuwar mata, gashi ba abu ne mai sau™i ba,"

"ta nuna masa hakan ba, dole sai ta cikin hikima da dabara."

"Haka zata zauna, komai daren da zai yi sai ta jira dawowarsa, ta saka shi yayi wanka, ya canza"

kaya.

"Yau bayan ya bar Wakinta, bayan ta idar da salla ta je ta same shi, a zaune a kan katifa."

"Ta Wauki kwalin sigarin gabansa, ta ciro guda uku ta bashi ta ce ""Wannan ta isa, kar a sha sama da"

"haka dan Allah"""

"""Bani in je ™ofar gida in sha"""

"Ta ce ""A'a ai shan nake so ka rage sosai da sosai, wannan ta isa"""

"Ya juya mata baya ya shanye, tana zaune tana jiransa, ta bubbuWe window, saboda haya™in ya fita."

"Jira yake ta fita ya kuma kunna wata, amma ta cire masa shirt Win jikinsa, ta ce ya kwanta, ya"

"kwanta yana jiran ta fita, amma ta kwanta a jikinsa, a hankali ta din ga karanto azkar Win safiya."

"Babbar salla na ta ™aratowa, jauhar hada-hadar neman kuWi, ta cigaba da kankama, Al'amin bai ta Sa saka ido a kan abun da take samu ba, dan yanzu iya ™o™arin sa yake yi, ya yi cefanensa, duk da kuWin da take Wan samu, in dai ya ji kuWi a jikinsa, a kaso Wari tamanin, ita zai kashewa, bai fi ya"

"™arar da kaso ashirin ba, goma ya rabar goma ya yi shaye-shaye."

"Idan ta fuskanci da kuWi a hannunsa, ta din ga lallaSa shi kenan, ayi wani abu mai muhimmanci,"

"idan ba haka ba, ba zai sai abubuwan da suka fi bu™ata ba."

"Kuma babbar hanyar samun kuWinsa, wurin Indabo, ya din ga tatsarsa kamar mai, duk da yana"

"samun hanyoyin samun kuWi yanzu, tun da kakar siyasa ce."

"Ana jibi salla, ya ba wa jauhar kuWi, wai tayi kitson salla ita ma, ta je ayi mata zane a hannunta."

"Ta dawo ta tarar da kaya a kan gadonta, ta zazzage taga kaya na alfarma duk an Winka su, har da"

takalmi da turare.

"Mamaki ya cikata, yana dawowa ta fito falo ta ce ""Master kayan waye a kan gadona?"""

"""Na kishiyarki ne"""

"""Wace kishiyata?"""

"""Ban sani ba, ko ina da wata matar ne bayan ke"""

"Gaba Waya ta rikice ta ce ""Master wai nawa ne Gaba Waya?"""

"Ya ce ""Naki ne babyn roba"""

"Har ™asa jauhar ta dur™usa tana yi masa godiya, ta rasa ma wace kalar godiya za ta yi masa, har"

da matse ™walla.

"""Ni ba irin wannan godiyar nake so ba, a she™a mini girki, a yi wa fankata caji, in sha iska sosai"""

"sunkuyar da kai ta yi, cikin matsananciyar jin kunya."

"""Allah ya ™arawa fankata gudu, tana ba da iska sassanya, ™arfin gudunta, bai sanya tana bada"

"iska mai cutarwa ba"""

"""Amm bari na je na yi jajjage"" ta juya ta nufi Waki."

"""Dama a Waki a jajjagen"" ko waiwayowa ba ta yi ba, ta shige."

"Ranar idin babbar salla ma, tare suka tafi sallar idi."

"Ta sha kwalliya, tayi kyau sosai da sosai, a abun da bai fi wata guda ba, ta yi ™iba fatarta ta ™ara"

fresh.

"Ta sha Waurin Wan kwali, hannunta yayi kyau da zanen lalle ja da ba™i. Su liti suka din ga kiransa a waya, suna jiransa, ya™i fita, sai da suka zo har gida sannan suka fita da shi, bayan sun kwashi"

wainar masa da sinasir da miyar agushi.

"Bayan la'asar sosai, ya dawo gida da nama kaya guda, har da karfatar sa, ga kayan ciki da uban"

nama.

"Kamar tayi kuka ta ce ""Master, aiki daf da magariba ya zan yi?"""

"""Ke da aiki ba ya yi miki wahala, Wan wannan aikin zaki yi raki?""."

"""To aikuwa sai ka tayani, kuma ba ka sayo itace ba"""

"Ya kalleta ya ce ""Ba a yi a gas, an hanaki shiga haya™i""."

"""Gas Win dubu nawa za a zuba? Dole sai a itace"""

"Ya kalli naman, ya ce ""Ki shiga ciki, bari na aika nura ya sayo itacen, su walid suna waje, sai su"

"shigo mu yayyanka"""

"˜arshe dai haya™in da ba ya so, sai da ta shiga, har sha biyun dare suna aiki ita da shi."

"Duk da haka aikin bai ™are ba, sai washegari, ta ce masa tana son zuwa gida, ya ce sai ta gama yi"

masa kwalliyar salla kan ta fita.

"Ya samu dambun nama da cin-cin, ya din ga tumurmusa, jauhar ta ce ""Ni ban gane wannan"

"lamarin ba, gaskiya rabawa za ayi. Kana ta ci idan cikinka ya Saci babu ruwana""."

"""Ke ki ke da ruwa kuwa""."

"Sai huWu ga salla, sannan ya bari ta je gida, ya kaita da kansa."

"Aka yi sa'a Hafsa ma ta je gidan, tun da ta jauhar ta je, suke kallonta da kayan jikinta."

"Sai da mama ta magantu ta ce ""Jauhar wannan leshin fa?"""

"""Mama kayan salla ne"""

"""Kin san kuWin leshin nan kuwa?"""

"Ta girgiza kai ta ce ""A'a shi ne ya kawo mini"""

"Ta kalleta ta ce ""Wai sana'ar me yake yi haka ne?"""

"Tayi murmushi ta ce ""Yana sana'oin sa, kuma kin san yana tare da 'yan siyasa""."

"Hafsa ta din ga kallon jauhar, yadda take komai nata cikin walwala, kamar ba ta da wata damuwa,"

duk da tana auren Wan daba.

"Bayan jauhar ta ba su nama, dambun nma da cincin, aka din ga gaya wa jauhar, ai mijin hafsa rago"

ya kawo.

"Ta ce ""Masha Allah, Allah ya saka da alkhairi"" Duk yadda Hafsa ta so mazewa, sai da yanayin ta"

ya nuna akwai damuwa.

"Sai yamma Al'amin ya dawo, ya ce ta fito su tafi, babu yadda ba ta yi da shi ba, amma ya ce ba zai"

shiga ba.

"Gidansu ma da ya kaita, a waje ya tsaya, a gurguje jauhar ta shiga ta gaisa da Rahila, ta bata"

"naman sallar sai dai ita ma, kayan jauhar kawai take kallo."

"Ana gama bikin salla, aka shiga hada-hadar zaSe."

"Hankalin jauhar ya kasa kwanciya, saboda yawan shige da ficen da yake yi yawa."

"Yau ake zaSen sanatoci, dan haka tun kan ta tashi daga bacci ya fice."

"Har yamma shiru bai dawo ba, kuma wayarsa ba ta shiga."

"Gaba Waya jikinta a sanyaye yake, jikinta ya din ga bata akwai matsala, har bayan magariba bai"

dawo ba.

"Jin ana knocking Win gate, gabanta ya faWi, ta saka hijjabi ta fito, ta ga Nura guduma a tsaye ta ce"

"""Yaya wannan karon me kuma yayi?"""

"Ya ce ""Ki sako hijjabinki mu tafi"""

"""Mu tafi ina?"""

"""Asibiti!"""

"""Innalillahi wa Innalillahi raji'un!"""

Ayshercool 08081012143.

¦ 500 ne via 0009450228

Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343

'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724

"Muryarta na rawa ta ce ""Meyafaru? Wani abun ne ya same shi, ko ya yi wa wani?"""

"Ya ce ""Ni ma ban sani ba, oga walid ne ya ce ""In zo mu tafi tare """

"Jikinta a sanyaye, ta kulle gidan, ta bi Nura guduma suka tafi, suna tafe tana ta addu'a a ranta."

"Wani private clinic suka je, emergency suka nufa, ana ta kai komo da matasa, da aka ji wa raunuka daga wurare daban-daban na harkar zaSe, kasancewar an yi tarzoma sosai da sosai a wasu wuraren,"

kuma nan asibitin ne mafi kusa.

"Da ™yar take iya Waga ™afarta, wani irin yammmm haka jikinta yake yi mata, saboda tsoro da"

tashin hankali.

"A ™ofar wani Waki, ta tarar da Walid hankalinsa a tashe, yana kaiwa yana komowa."

"""Yaya walid, meyasame shi? Ko mutuwa yayi?"""

"Walid ya ce ""Ki nutsu ba mutuwa yayi ba, yana ta kiran sunanki ne kafin mu zo nan""."

"""To meya same shi, yana ina?"""

"Ganin likita ya fito daga Wakin da yake facing Win su, ya sanya ta saka kai ta shiga ita ma."

"Gigicewa ta yi, ganin Wu™a a kwiSin Al'amin a tsaye tsororo, jini baya zuba, amma tana jikinsa, ga gefen kansa, an naWe shi da bandeji. An saka masa oxygen, gefe ga oxymetre na reading vitals"

Win sa.

"Cikin kuka ta ce"" Innalillahi wa Innalillahi raji'un, meya same shi haka? Waye yayi masa haka, Master dan Allah ka tashi, kar ku ce mini mutuwa yayi"" tayi maganar tana rirri™e hannunsa cikin"

tsananin tashin hankali.

"Kukan jauhar ya janyo hankalin likitoci, da m'aikatan jinya, suka ce meyasa aka bari ta shiga?"

"Da ™yar aka fito da jauhar ana rarrashinta, aka tabattar mata da yana da rai, tiyata za a shiga da shi"

"a cire masa wu™ar, sai a duba kansa."

"Cikin tashin hankali ta ce ""Dan Allah likita zai rayu?"""

"""In sha Allah, da kun biya kuWin za a shiga da shi"""

"Ta kalli Walid ta ce ""Yaya Walid, nawa ne kuWin?"""

"Walid ya ce ""KuWin da yawa, P.A Win Indabo muke kira, su biya kuWin, hannunmu kuWin ba za su"

"kai ba ayi masa aikin"""

"""Ka gani ko? Sun ma ™i Waga wayar, su suna can hankalinsu a kwance, suna jiran sakamakon zaS"

"e, ni kuma an kassara shi, wannan tashinsa ai sai Allah"""

"Liti ya ce ""Ki yi ha™uri, in sha Allah zai tashi"""

"""Nawa ne kuWin?"""

"""Da Wan yawa, ki bari kawai"""

"Ta girgiza kai ta ce ""Ni ku gaya mini dan Allah, a nema tun da wuri, wu™a ce fa a cikinsa"" tayi"

maganar tana wata irin ajiyar zuciya mai ban tsoro.

"Suka din ga rarrashinta, amma ta™i saurarsu, Liti ya ce ""Bari na yi gaggawa na je na samu wannan"

"banzan mutumin P.A, ko dai a san yadda za ayi a biya, wallahi ko mu ji™a musu aiki"""

"Jauhar kamar za ta yi hauka, ™arfin Addu'a ne kawai ya saka mata nutsuwa, ta din ga kaiwa tana"

"komowa, gashi an ce ba zata sake shiga ta ganshi ba."

"Jauhar ba ta san yadda aka yi ba, liti da Nura guduma suka dawo da kuWi, suka biya."

"Ake ce ana bu™atar jini, dan da yiwuwar ana cire wu™ar, jini ya Salle."

"Haka suka din ga zirga-zirga, jauhar itakaWai a cikin su, babu wani daga danginsa, babu daga nata."

"Nura guduma ne ya bayar da jininsa, dan shi ne yayi dai-dai da na Al'amin, aka shiga da shi tiyata."

"Hawaye suka kasa barin idanunta, zuciyarta ta din ga wani irin zafi, ba ta taSa tsanar wani abu ba, tsana mai muni sai yau duk da ba ta taSa ganin indabo ba, tsananin haushinsa take ji, dan shi ne"

musababbin wannan tashin hankalin.

"Ta kai ta kawo, ta tsuguna tayi kuka, aka shafe sama da awa guda, ba a fito da shi ba, tayi alwala ta shimfiWa Wan kwalinta, ta tayar da salla, sai dai tana cikin sallar sai ta hau wasi-wasi, da tunanin"

me zai faru ta kasa nutsuwa.

"Babu tsammani likitocin suka fara fitowa, dan team Win tiyatar sun kai su biyar, gaba Waya suka"

"nufe su, suna tambayar yaya?."

"Jagoran tiyatar ya ce ""Alhamdilillah, an cire wu™ar, kamar yadda muka yi tsammani ya zubar da jini sosai, amma an saka masa jini, zamu kai shi Wakin hutu, amma ba ma son a din ga shiga ana fita da sunan dubiya, kafin a kai shi Wakin hutun, za a yi masa hoton kai, duk da saran da aka yi"

"masa a ka bai yi zurfi ba, amma akwai bu™atar a duba""."

"""Alhamdilillah ala kulli halin, Doctor mun gode Allah ya saka muku da alkhairi, ya ji™an"

"magabatanku, Allah ya sa ku gama da duniya lafiya ku bar aiki lafiya, ka da Allah ya wulakanta rayuwarku bayan ajiye aiki""."

"Cikin farinciki suka din ga amsar addu'a jauhar, da Amin, tare da ba ta ™warin gwiwa a kan zai"

tashi ya warware gaba Waya.

"Bayan an yo hoton, suka tabattar da babu internal injury, jauhar ta zauna ta zuba masa ido, ga jini"

yana shiga jikinsa a hankali.

"Walid ya ce ""Ina ganin ki koma gida, ko ni sai na kwana da shi a nan, kin ga idan ya tashi ba abun"

"da zaki iya yi masa"""

"""A'a idan na koma ba zan iya zama bama, hankalina ba zai kwanta ba, ni kawai ku bar ni""."

"""To ai dole sai da namiji, ko zaki iya Waga shi, idan yana bu™atar hakan?"""

Cikin ™warin gwiwa ta jinjina kai alamar eh.

"Duk da alhini da suke ciki, sai da suka yi murmushi."

"Walid ya ce ""Bakomai, ki kwana da shi, sai na kwanta a waje ni, idan ana bu™atar wani abun sai ki"

"kira ni, yanzu bari na sayo wani abun, ki ci""."

"""Bana jin yunwa"""

"Haka suka kwana da Al'amin, amma bai farfaWo ba."

"Ta din ga kallon wayarta, tana tunanin wa za ta kira, kamata yayi ace tana da wanda za ta kira, a kawo mata abun da zata bu™ata saboda zaman asibiti, amma ta san ko za ayi mata sai an yan™"

wanata ko gaya mata maganar da zata Sata mata rai.

"Kwana suka yi likitoci na kaiwa da komowa a kansa, ™arfe shida ta kira Abbu a waya, ya dawo"

"daga masallaci kenan, ya ga kiran jauhar. Ya Waga a nitse suka gaisa."

"Ta gaya masa abun da ya faru, dumm ™irjinsa ya buga, duk da ba wannan ne karon farko da"

Al'amin yake kai kansa in da ake cutar da shi ba.

"Abbu ya ce ""Shikenan, ki yi ha™uri ki daina kuka, in sha Allah zan

2 / 67