Karfe a Wuta Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   23 / 67

66K to 69K   out of 199.8K words

lafiyarka da ta ™wa™walwarka, wannan ba mafita ba ce ba, dan Allah"

"kar ka illata kanka""."

"Liti ya ce ""Zo ki fita, koma uban menene ba ke ce sila ba, uban waye ya ce ki zo, yau ya tashi da"

"'yar walwala kawai kin zo kin kuma tunzura shi""."

"Cike da tsananin damuwa, da tashin hankali ta baro gidan, tana tunanin to ita menene laifinta, da"

suke cewa ita ce sila idan ya ganta yake burkicewa.

***

"Ramma ta zubawa Abdul ido, ya haWa akwatin sa tsaf, ya kalleta ya ce ""˜arfe huWu jirgina zai tashi, dole na shirya da wuri, akwai in da nake son zuwa kafin na tafi"""

"Ta turSune fuska, tayi masa shiru."

"Ya zauna kusa da ita, ya Wago haSarta yana kallon fuskarta ya ce ""Ya dai?"""

"""Ni dai kar ka tafi dan Allah, tsoro nake ji wallahi, nikaWai zan zauna a nan dan Allah"""

"Ya kwantar da murya ya ce ""You start missing me?"" Ta girgiza masa kai alamar a'a."

"""Your excellency, ba iya tsoro ne a idonki ba, missing Wina zaki yi"""

"Ta ture hannunsa ta ce ""Allah ya kiyaye, ni gaskiya tsoro nake ji"""

"Abdul ya ce ""Tafiyar nan dole ce, sannan ina son na je garinku yau, zan ce wa mamanki kina"

"gaisheta"""

"Ta marairaice ta ce ""Dan Allah ka mayar da ni mana"""

"Ya girgiza kai ya ce ""Ba yanzu ba"""

"""Nan gaba zaka mayar da ni?"""

"""Eh to, sai ™ura ta lafa"" tayi shiru tana wasa da yatsunta."

"""Ki yi ha™uri, zan dinga kiranki kullum muna magana, idan da wani abun ma sai ki gaya mini, na"

"ajiye miki komai na amfani a kitchen, ai kin iya girki ko?"" Ta jinjina masa kai alamar eh."

"Ya ce ""Yauwwa your excellency"" ya tashi ya shiga wanka, yana ta shiri, ya zauna a gefen gado"

"yana shafa mai, ta ri™e shirt Win sa tana kuka."

"Nan ya lalace a wurin rarrashin ramma, ""Wai wannan kukan duk dan kar na tafi ne?"""

"""Ni ina ruwana da tafiyarka, tsoro nake ji ne"""

"""˜arya ki ke yi rahama, faWi gaskiya dai"""

"""Ni ba na ™arya"" tayi maganar tana murguWa masa baki sannan ta ce ""Kuma wallahi ka bi mata"

"Allah ya isa"" bai san lokacin da ya ™ya™yace da dariya ba, har sai da ya bata haushi."

"Har ™ofar falon ta rako shi, tana kallonsa, ya kasa gane kallon me take yi masa har haka, yayi"

"mata sallama, ya sanya mukulli ya kulleta, ya ja akwatinsa."

***

"Kan Nabila tamkar zai yi bindiga, ta rasa abun da yake yi mata daWi, haka ta koma jiki babu daWi, kanta fal tunani daban daban."

"Har ta shirya, zata ci abinci, kawai ta tuna kwana biyu ba ta haWu da Nasir ba, kuma ba ya shiga"

"sabgarta, gashi tana son sanin a ina ya tsaya a binciken Viper, saboda duk yadda za ayi ba ta son"

"ya gano Viper ba ta gama na ta binciken ba, idan ya so ko kotu za a shiga, ta shiga da ™warin"

gwiwar ta.

"Gaba Waya mayar da hankali a kan aikinta ya sanya, ba ta shiga sabgar yan gidan, hakan ya rage"

yawan faWace-faWace da suke yi da 'yan gidan.

"Ta fito falo, dan ta gaji da zaman Waki, abubuwa duk sun dameta, sai ga Nasir yayi sallama a falo,"

"ta amsa sallamar tana kallon sa, amma ya basar da ita ya nemi wuri ya zauna."

"Ta ™arasa ta zauna a kusa da shi ta ce ""Sannu da zuwa"""

"""Yauwwa"" ya amsa mata a ciki."

"""Wai me na yi maka ne ka ke wani share ni?"" Tayi maganar a shagwaSe."

"Rasa me zai ce mata yayi, yai shiru, ya kawar da kansa gefe."

"Ta zagaya in da ya kawar da kan ta ce ""Me na yi ne?"""

"""Bakomai"". ""To ka kula ni mana""."

"Nasir ya ce ""Na gaji, kar ki dame ni dan Allah"""

"""Sai na gaya wa Abba kana hantarata"""

"Ya ce ""Sai kin dawo"" ta rausayar da kai ta ce ""To ni dai ka yi ha™uri, dan Allah"" ya kalleta ya ce"

"""Ya wuce"""

"""Yauwwa DSP, to ya ake ciki ya aikin?"" Ya gyara zamansa ya ce ""Alhamdilillah, mu na ta fama ya"

"naki?"""

"Ta kwaSe baki ta ce ""Babu daWi, duk na gaji, da fa ajiye aikin zan yi, aka bani ha™uri"" Nan ta bashi"

labarin abun da barrister Kabir yayi mata.

"Nasir ya ce ""Ke baki da ha™uri ne, shiyasa wasu lokutan ba kya cin ribar abubuwa, ki daina"

"gaggawa"""

"""Ai abun ne ya bani mamaki, daga zuwana wurinta, har an kira barrister Kabir an gaya masa, baka"

"ga abun da ya yi mini ba, da cewa na yi sai na gaya wa Abba ma""."

"Nasir ya ce ""No, ba za ayi haka ba, duk abun alkhairin da yake yi miki, sai a kan laifi Waya ki yi"

"fushi"""

"""To meyasa zai yi mini tijara a kan wata Naja""."

"Ya ce ""Hakan yana alamta miki cewa, kin Waukko gagarumin abin da sai kin yi kyakywan shiri na"

"gaske""."

"Tayi ajiyar zuciya ta ce ""Haka ne, ya ake ciki da naka aikin, yaya batun case Win Viper, akwai"

"cigaba kuwa?"""

"""Wallahi ba wani cigaban kirki, ina da ta fafutuka, gashi sai hura mini wuta ake yi"""

"""Kai abun babu daWi, but you can do it, na yarda da kai ai""."

"Mama ce ta fito fuska a haWe ta ce ""Nasir menene haka?"""

"Ya ce ""Mama a ina?"""

"""Ban sani ba, uban me ka ke zaune a nan ka ke yi? Ka dawo gida tun Wazu, amma ka gagara shiga"

"inda nake?"""

"Nasir ya ce ""Wallahi nayi tunanin bacci ki ke yi, shiyasa na yada zango a nan muke magana da"

"Arfa, yi ha™uri"""

"Nabila ko a jikinta, ta sake gyara zamanta ta kwanta sosai a kan kujerar tana danna waya."

"Mama tayi mata wani mugun kallo, ko a jikinta, sai ma wani irin murmushi da tayi."

"Messages aka din ga turowa Viper, da private numbrn nan, da ake kiransa da ita."

"""Muddin ka cigaba da biyewa yarinyar nan, asirinka zai tonu, kuma zata iya rasa rayuwarta a dalilinka, ba ka da sa'a wasu lokutan, kar ka bari ta zama raunin da ma™iyanka za su yi amfani da ita, wurin cimmaka har maSoyarka"" Ya din ga jujjuya wayar, yana sake tunanin waye wannan, kowaye ya sanshi, ya kuma san in da yake, kuma yana ankare da duk abun da yake yi, amma"

meyasa ya™i bayyana kansa?.

"Kiran Nabila ne ya shigo wayarsa,"

"tana zaune hannunta ri™e da waya a kunnenta tana kiran lambarsa, babu tsammani ta ji ya Waga."

"Ta kalli agogon Wakinta, ™arfe goma daidai na dare."

"""Barka da dare, duk da ba amsawa zaka yi wa ba. Amma ina fatan kana lafiya?"

"Na kasa jurewa ba zan Soye maka ba, ban ji daWin yadda na baro ka ba, muna cikin magana ka tashi ka tafi, kuma ka je ka na yi wa kanka allura, gaba Waya ban ji daWi ba, dan girman Allah ka rufa mini asiri kar ka yi wa kanka illa, ka bari mu yi nasara mu kamo bakin zaren. Na san maybe ka raina gogewa ta, kuma kamar ba zan iya ™wato maka hakkinka ba, amma na san Allah yana tare da mu, dan Allah ka daina shan abun da zai yi maka illa, ba na jin daWi, na san yayata ma 'yar"

"madara ba zata ji daWin hakan ba, dan gaskiya sai ta matsa mini na shigo, daga ni sai a rufe. Saboda son da nake yi mata make son mu kasance tare, idan na shiga gidanta, kaga gani ga ta, in ™ara koyon halayenta, in ™ara sonta, amma gaskiya ayi mana adalci, saboda kishi ne da ni sosai da sosai fa, kuma alamu sun nuna mini kana sonta da yawa"""

"Kamar mai sauraren karatu, haka ya nutsu yana jin ta, Wan mama da yake kusa da shi, har kuma le"

"™a idonsa yake yi, ya ga reaction Win da zai yi, tare da jinjina rawar kan Nabila, a gaban Viper ko"

"™wa™waran motsi ba ta iya yi, amma ta sameshi a waya, sai karairaya take yi tana shagwaSa."

"Ta sauke numfashi ta ce ""Bari na ™yaleka, amma yakamata na san ™arshen labarin nan, saboda na san yanayin shirin da zan yi, kuma kar sai na gama za™ewa 'yar madara duk kirkinta ta ce ba zan shigo mata gida ba, dan ni gaskiya idan ba gidanta ba sai rijiya. Sai da safe take care"" tayi maganar tana ajiye wayar, cikinta na kaWawa saboda ita kanta ta san ba ™aramar kasada take yi ba, abun da take yi. Amma hanyar da matarsa ta bi ta iya samun kansa da farko, dole ita ma ta bi,"

"domin cimma nasara, saboda gaba Wayansa hukuma ne, sai da rarrashi."

***

"Sanye yake da face mask, yana tu™i a hankali, saboda yadda hanyar ta ™ara lalacewa, a ™ofar gidan su ramma yayi parking, ya fito ya tsaya a waje yayi sallama, amma shiru, ya shiga cikin gidan sai dai tsakar gidan babu kowa, ™ofofin Wakin duk a buWe."

"Ya Wan jira ko za a shigo, ko fita tayi, amma shiru, ba ta dawo ba."

"Ya fita ya tambayi ma™wabta, suka sanar masa kwanaki huWu kenan, su ma ba su san in da ta tafi"

"ba, ba ta yi wa kowa sallama ba."

"Yanayin gidan ya tabattar masa da ba fitar nutsuwa tayi ba, ya lissafa shi yanzu kwanaki uku kenan, da mahaifinsa ya kira shi yai masa magana a kan batun ramma balle ya ce ko mahaifinsa"

ne.

"Yayi shiru yana tunanin to garin yaya haka, ya za ayi ta fita ta bar gida a buWe haka babu kowa, tsawon kwanaki huWu, ba ta yi wa kowa sallama ba, lallai akwai wani abu a ™asa, yanzu me zai"

cewa ramma? Ya tambayi kansa.

"Lallai akwai wani abu a ™asa, gashi lokaci na nema ya ™ure masa, ™arfe huWu zai tafi."

"Saif ya kira a waya, ya sanar masa halin da ake ciki, saif ya ce ""Kuma baka tunanin ko guduwa"

"tayi, ko kuma daddy ne yayi mata wani abun?"""

"Abdul ya ce ""Bana tunanin haka, shekaranjiya yayi mini zancenta, da shi ya saka aka Wauke ta zai"

"gaya mini, na rasa wani lissafin ma yakamata na yi"""

"Saifu ya ce ""Ka tafi kawai, zan tsaya na sake bincikawa, in Allah ya yadda ba wani abu""."

"Ya ce ""To shikenan, ina saurarenka dan Allah"" ya ajiye wayar yana cigaba da tunanin lamarin."

***

"Abdul yana sauka a Abuja, sai da ya kira Ramma, ya ce mata ya sauka, sai dai ba ta amsa masa ba sai cewa tayi ""Yaya ka baro mini mama? Tana nan lafiya? Ta tambaye ka yaya nake?"""

"""Ni ba zaki tambayi ya na sauka ba, sai mama kawai?"""

"""Dan Allah ka gaya mini, ko na ji daWi"""

"Abdul ya ce ""Zan gaya miki da daddare idan na huta"" ya katse wayar yana fargabar ranar da"

"ramma ta san halin da ake ciki, bai san ya zai yi ba. Ya san duk laifin shi zata Worawa."

***

"Katafaren falo ne, ya sha ado da kayan alatu na zamani, manyan mutane ne su uku, zaune a falon wanda kaf Win su sanannun fuskoki ne da su a ™asa."

"Kayan shaye-shaye ne a gaban su, suna sha suna hira, gefe ga kayan marmari."

"""Distinguish ma'aruf Indabo, ya ake ciki ne gaba Waya baka walwala?"""

"""Komai ma ya dame ni ne, Abdul sai so yake yi sai ya watsa mini lissafi, da ™yar na ya™o shi, ya"

"tafi Abuja, zaman taron nan, nima gobe in Allah ya kaimu zan tafi birnin tarayyar"""

"""Ya salam, wai meyasa Abdul yake haka ne? Ya san wahalar da muka yi kuwa kafin mu zo nan,"

"shi me yake damunsa ne?"""

"Indabo ya kora ruwan lemon da yake cikin kofin hannunsa, ya ce ""Oho masa, gaba Waya na kasa gane kansa, ina tsoron Allah ina tsoron ya aikata wani abun da zai yi dalilin takarar nan, amma ina"

"nan na kafa na tsre ina monitoring activities Win sa""."

"""Ohh Allah ya kyauta, ya batun wannan yaron ne da ake nema?"""

"Indabo ya girgiza kai ya ce ""Hmm honorable kenan, wallahi kullum da shi nake kwana nake tashi, kamar wani iblishi, ya gagara kamuwa, na rasa uban da yake tsaya masa, sai dai na samo wata yarinya da nake son ayi masa tarko da ita, to ita kanta yarinyar ba ta da cikakken saiti, wata barrister ce, 'yar wani tsohon soja, idan na matsa zata iya tona mana asiri, na saka ana yi mini monitoring Win ta, ta hanyar ™awarta. Saboda wani furuci da tayi. Duk dai na ga hanyoyin ba sa yi mini sauri, na san dole yaron nan bakam yayi mini, at any cost sai na canza dabara, wadda za ta"

"Sulle mini da wuri, na kashe Aminu na huta"""

"Haka suka cigaba da jimantawa, tare da tattaunawa da neman mafita, suna yi suna shaye-shaye."

"Ramma tana du™un™une a cikin bargo, karnukan estate Win, da na gidan sai haushi suke yi."

"Video call suke yi da Abdul, ta ce ""Ba ka ce mini komai a kan mama ba"""

"""Mama tana lafiya, ta ce a gaishe ki"""

"Ta ce ""Hmm, to ya take, tana cikin damuwa ko? Tayi kuka?"""

"Ya ce ""A'a, na bata tabbacin kina nan lafiya, har hotonki na nuna mata"""

"Ramma ta ce ""A'a hankalinta ba zai taSa kwanciya ba, ka manta rashin Wa'ar da ka yi mata, ranar da ka je ka tabattar mata da kai ka keta mini haddi, kuma ka tafi da ni, ai a yanzu idan akwai"

"wanda ta tsana bai wuce ka ba, kodayeke akwai wanda suka yi mata wasu laifuffukan"""

"Yayi shiru jiki a sanyaye ya ce ""Laifin da suka yi mata irin nawa ne? Ai na nemi afuwarta"""

"""Ta ina ka nemi afuwarta? Hmm ta ce ta yafe maka ne? Kai baka ganin girman laifin da ka aikata fa saboda mu talakawa ne kana da kuWi."

"Mama ta sha wahala sosai, gashi duk mun WaiWaice, kaga ™anina sani daka je?"""

"Ya girgiza mata kai ya ce ""Ina ga yana makaranta"""

"""Shikenan, sai da safe, bari na rintse idona ko zan yi bacci, haushin karnukan nan ya isheni"""

"Ya ce ""Ni kuma sanyi ne nan ya dame ni, da muna tare da kin bani Wumin jikinki"""

"Cikin tsiwa ta ce ""Saboda gani heater ko?"""

"Ya ce ""No, jikinki akwai Wumi sosai, da duk ba zan ji wannan sanyin ba"""

"""Sai da safe"""

"""Dan Allah ki tsaya ban gama ganinki ba"""

"ta ce ""Sai kuma ka yi ai"""

"""Mi™o bakinki na yi miki kiss"""

"""Ba na so"" tayi maganar bacci yana kwasarta, tana lumshe ido."

"Ya ce ""Rahama"""

"""Na'am"" ta amsa tana buWe ido da kyar. Sai kuma yayi shiru yana cigaba da kallon fuskarta, har"

"bacci ya kwasheta, yana kallonta, tausayinta ya din ga ratsa zuciyarsa."

***

"Yau weekends, Nabila tana gida, tana kai komonta, ta bayar da wankinta ayi mata, ta fito harabar"

"gidan tana zagawa, Nasir ya fito da shirin fita."

"""DSP sai ina? Ko zance za a tafi rana tsaka"""

"""Wurinki zan zo zancen"" tayi dariya ta ™arasa gabansa ta ce ""Ina zuwa yanzu?, La'asar ta kusa?"""

"Ya kalli agogon hannunsa ya ce ""A kan Viper ne"""

"Cikinta yayi ™uuu, amma ta maze ta ce ""Ya ake ciki?"""

"Ya ce ""Eh to, na canza dabara ne, a yanayin neman nasa, mun riga duk mun yi connecting da mutanen unguwar su, an ce yana zuwa gidansa da ya zauna, to kwana biyu bai je ba. Abokin faW ansa da na kama kwanaki madaki, an ce ya dawo yana cikin gari, akwai ™ishin-™ishin na zai iya zuwa unguwar, neman rigima da shi madakin, duk mun baza komar mu, akwai wurin shayin yaransa, an ce ma wurin nasa ne, zuwana biyu wurin cikin fararen kaya, an kwatanta mini wani yaronsa Walid, na haWu da shi a wurin, amma ko kaWan ba sa zancensa a wurin. Da na so na zunguro zancen daba ma, na kama sunansa, cewa suka yi na tashi na fita. Ina kyautata zaton wannan Walid Win ya san in da yake, motsinsa zan sakawa ido sosai, ana ta yi mini binciken ina yake da zama, da a unguwar suke zaune, amma tun da Viper ya bar prison, sun daina kwana a unguwar sai idan za su yi aikin rabawa ™anan dealolinsu wiwi. Ba zan motsa da wuri na kama shi Walid Win ba ba, kar shi ma ya zille mini, kuma an tabattar mini da Wan amanrsa ne, ina dai ta bibiyar su ta hanyar mai unguwa, da wasu daga mutanen unguwa. Wanda nake baki labarin nan ma Wan mama, ya daina zuwa arear da aka gaya mini kai kayan shaye-shayen na su, abun ne dai"

"duk sai a hankali""."

"Tayi ajiyar zuciya ta ce ""Wani aiki sai mai shi, Allah dai ya ba da sa'a, sannu da ™o™ari DSP"""

"""Yauwwa arfan Abba, bari na tafi"""

"""To yanzu can Win zaka tafi?"""

"""Eh, zan je in sake zaSar yarana su shiga unguwar su madakin a farin kaya"""

"Ta ce ""Shikenan,

23 / 67