Karfe a Wuta Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   6 / 67

15K to 18K   out of 199.8K words

safe bayan sun karya, ya bata magunguna ta sha, tana ta lallaSa jikinta, za ta yi"

"aikace-aikacenta, ya hanata ya fito ya yi mata share-share, har tsakar gida ya wanke mata."

"Kayan da ta cire yake wankewa, aka buga ™ofa, ya je ya buWe hafsa ya gani a tsaye, hannunta ri™e"

da leda.

"Ya bata hanya ta shigo, a tsorace ta kalli Al'amin fuskarsa a haWe ta ce ""Ina kwana"""

"""Lafiya ™alau""."

"""Dan Allah wurin jauhar na zo"" da hannu ya nuna mata falo."

"Daga falon ta ce ""Muryar wa nake ji kamar Yaya hafsa"""

"Ta ce ""Nice"""

"Ta tashi ta taro hafsa ta ce ""Sannu da zuwa""."

"Hafsa ta ce ""Yauwwa sannu ya jiki?"""

"""Jiki Alhamdilillah, ya aka yi ki ka gane gidan?"""

"""Yaya saifu ne ya gaya mini hanya, kuma direbana da yayi tambaya aka nuna masa gidan ba"

"wuyar ganewa""."

"Ta ce ""Allah sarki yaya hafsa tun ina Asibiti nake tambayar kina ina, aka ce mini kina umara, na"

"ce baki gaya mini ba muna chat, ai da na jero addu'a ayi mana ni da mai gida"""

"Tayi murmushi ta ce ""yanzun ma an yi miki, wai jauhar Sarin da wahala ne, na ga kin rame haka"

"kin yi fari?"""

"""Kai da wahala mana, jini na zubar sosai shiyasa na yi haka, amma kwanaki ai ™iba na yi sosai,"

"ashe ciki ne ban sani ba"""

"""Allah sarki, Allah ya kawo mai amfani, sannu"""

"""Yauwwa ai na warware """

"Al'amin ya shigo falon, jauhar ta ce ""Master ba ka ganeta ba ne? Yayata ce da muka je gidanta fa,"

"ba ka ga muna kama ba?"""

"Kai tsaye ya ce ""Na gani, kin fita kyau"""

"Jauhar ta ce ""Kai fa ka fiye son kai ta ina?"""

"""Ta ko ina"" yayi maganar yana shigewa Wakinsa."

"Hafsa tayi murmushi ta ce ""Aikam kin fi mu kyau ai duk gidan nan"""

"Jauhar ta ce ""Rabu da shi, shi ma faWa kawai yayi"" suka cigaba da hira, ya sake fitowa ya shirya"

tsaf zai fita.

"""To yau me ki ke so? Kayan cikin ko ganyen wanne ki ke so?"""

"Ta shagwaSe fuska ta ce ""Kai"""

"""Ni ki ke so?"" Ta Waga masa gira tana murmushi."

"""Aikuwa zaki kwana da yunwa, me ki ke so?"""

"""Komai ka samu na gode"""

"Ya ce ""Abun da zai ™ara miki jini aka ce ai"""

"""Jininka zan sha"" ta yi maganar tana dariya."

"Yayi murmushi ya ce ""You are not serious, ki yi addu'a Allah ya sa na samu kuWi, na sayo miki"

"kaza""."

"Hafsa ta ce ""Ai ga miya ma na yi miki, da kazar a ciki"""

"Jauhar ta ce ""Ashe zaku yi faWa da master, tun da ki ka riga shi kawo mini kaza"""

"Murmushi ya sake yi, wanda ya bawa hafsa mamaki, take bin su da kallo, gwanin burgewa."

"Har zai fita ta ce ""Master"""

"Ba tare da ya juyo ba ya ce ""Kar na yi shaye-shaye da yawa, kar na yi faWa da kowa, banda rigima da mutane"" ta kwashe da dariya ta ce ""Au ka haddace ma kenan, addu'a zan yi maka ai, Allah ya"

"iya maka, ya goyi bayanka yayi maka jagora ya wadatamu da halal ya nesanta mu da haram"""

"Ya waiwayo ya ce ""Amin ya haiyyu ya ™aiyyum, 'yar aljannata"" ya juya ya tafi."

"Yana fita Hafsa ta ce ""Innalillahi, jauhar dan Allah ya aka yi ki ka canza mutumin nan, dariya fa yake yi miki, kalli yadda yake yi miki, dan Allah jauhara ya ki ka yi ki taimake ni"" tayi maganar"

cikin tsananin damuwa.

"Jauhar ta ce ""Ban fahimci in taimake ki ba yaya hafsa, meyafaru? Wannan ai normal ne tsakanin"

"ma'aurata, kodayeke shi ya koya mini rashin kunya, da ko kallonsa bana iya yi a gaban mutane"""

"Idon hafsa ya cika da hawaye ta ce ""Jauhar, wallahi tun da na auri Alhaji mu'azzam hankalina bai kwanta ba, bai taSa bani awa biyar cikakkiya ba. Sai abun da matarsa take so yake yi, bai tare a W akina ba sai da matarsa ta amince. Ga kuWin yana da su, yana kashe mini ya sakar mini amm ba su"

"nake so ba, kulawarsa nake so da lokacin sa""."

"Juahar ta ce ""Yaya hafsa ba fa abun da ki ke kalla a film ne soyyaya ba a ™asar hausa da wurin mijin bahaushiya, dole ki fara kallon wane irin mutum ne shi, kin ga mijinki mutum ne mai hidindimu da yawa, ba zai yiwu ace kullum yana da lokacinki ba yakamata ki din ga yi masa"

"uzuri"""

"""Uzuri jauhar, yana da lokacin matarsa da yaransa, gaba Waya auren ya fita daga kaina, na je na gaya wa anty, wai wallahi na Waga maganar nan, sai ta yi mini Allah ya isa, wai zan saka ayi mata dariya, na zama kamar hoto a wurinsa, ko Wan abun Wokin nan na amarci, duk fa ban san su ba. Ke da ki ka auri wanda ake yi wa kallon sai a hankali, babu imani da tausyai a zuciyarsa kalli abun"

"da yake yi miki fa. Ni dai dan Allah idna wani malamin ne da ke, ki haWa ni da shi"""

"Cikin damuwa jauhar ta ce ""Yaya hafsa ni wallahi ban san in da ake ganinsu ba ma, canza mutum daga wani abu da baka so zuwa wani, ba abu ne mai sau™i ba. Kin san ni irin wahala da gwagwarmayar da na sha kafin mu zo wannan matakin kuwa?"

"Da fari nima damun kaina na din ga yi, daga baya na kama addu'a babu dare babu rana, na haWa da biyyaya da kuma ha™uri."

"Master mutum ne, kallon da mutane suke yi masa daban, wanda nake yi masa daban, biyayya da addu'a ne suka canza mini shi. Alkhairin da yake yi mini nake kalla kullum, nake yi wa laifukansa uzuri, har gara ke kina da uwa a raye, ni daga ni sai Allah, da na san bani da wata mafita, na bi abun da ™addara ta zaSa mini, na rungumi abuna hannu bibbiyu. Kuma Allah ya shiga lamarina Alhamdilillah, mijina talaka ne, amma ba kowace mace take da ikon da nake da shi a gidan aurena ba. A zahiri shi nake bawa girman, shi ne jagoran amma a baWini ni ce sitiyarin rayuwarsa, ina"

"fatan kasancewa da shi har aljanna. Ke ma ki nutsu ki gano menene kurakuranki, sai ki gyara""."

"""Ba wani kuskure, ina kyautata zaton asri aka yi mini wallahi """

"""A'a yaya hafsa, ki daina faWar haka, ki mi™a wa Allah lamuranki, wallahi zaki ga canji """

"Duk yadda jauhar ta so nusar da Hafsa muhimmancin ha™uri da juriya, da dagewa a kan addu'a"

amma ta™i ganewa kuma ta™i yadda.

"Zuwa azahar ta tafi, ta yi wa jauhar uban farfesun kaji, da abinci, ta kuma ajiye mata kuWi ta tafi."

Har a lokacin ba ta yadda har da hakkin jauhar a abun da yake faruwa da ita ba.

"Al'amin ne zaune a gaban Abbu, tun da ya gaishe shi, yayi shiru."

"Abbu ya ce ""Ya jikin 'ya ta?"""

"""Da sau™i"""

"Abbu ya ce ""To Alhamdilillah yarinyar kirki, 'yar aljanna Allah ya ™ara mata lafiya, matso ka haW"

"a shayi ga kayan breakfast nan"""

"Sai da Al'amin ya kalli Abbu, ya girgiza kai ya ce ""Na ™oshi"""

"""Too, yau kai ne ka ™oshi da abinci kuma?"""

"Ya bashi amsa da ""Eh na ci a gida"""

"Abbu ya yi murmushi ya ce ""Na manta ne, ashe fa magidanci ne, ya aka yi?""."

"""Sonake a sayar da gadona, zan ja jari, sana'oin da nake yi, ba sa iya ri™e mu sosai, gashi ina so ta koma makaranta, babu isasshen kuWi a hannuna."

"Sai kuma ina son ka bani full adress Win hajiya, zan kaita ta gaisheta ta matsa a kan haka"""

"Abbu yayi shiru yana ™arewa Al'amin kallo, duk ya Wan yi sanyi daga wani rashin mutuncin, babu uwar sumar da yake tarawa da faratan da yake bari za™o-za™o, gashi yadi ne a jikin sa saS anin da, da idan bai ga dama ba da 3quater yake yawo da shirt damatsansa a waje, ya wani nutsu sosai."

"Abunka da uba da Wa, wani irin shau™i ya ji yana kama shi, a yadda ya ga tarin sauye-sauye a"

tattare da Al'amin.

"""Kai amma 'yar nan tawa ta kyauta, amma wace sana'ar zaka yi?"""

"Al'amin ya ce ""Da wurin buga bulo nake so, ko wurin yin buredi, amma ban gaya mata ba tukuna,"

"ban sani ba ko tana da wata shawarar"""

"Abbu ya numfasa ya ce ""Kana ji na Al'amin, tsawon shekarun nan, filayenka sun yi daraja sosai da sosai, idan ka bari suka ™ara kwana biyu sai sun fi haka sosai. Ka je ka rubuto business plan Win ka kawo mini, tare da list Win abun da za ayi mata na makarantar, sai na baka kuWin, idan Allah ya dafa maka, aka samu cigaba, sai a sayar da ko gona ce a garinsu a ™ara, ka san kana da wasu"

"kadarorin a tofa"""

"Al'amin ya ce ""A'a ni ba na son ka yi mini abu, daga baya azo a saka ka din ga yi mini gori, kawai"

"dai a bani wanda na san nawa ne, kuma ma ni na fi son registration nayi mata da kuWina da kaina, sai na fi alfahari da haka"""

"Abbu ya ce ""Gaskiya ne, kamar ba a nan ka zauna kana ce mini, ba ka son auren ba"""

Al'amin yayi shiru yana basarwa.

"""Ka rubuto business plan ka kawo mini, zan san abun yi, ka je ku yi shawarar ina jiranka."

"Gaba Waya haushi ya cika Al'amin, kawai ya ji ba shi ne ba zai yi ba, ya ce ""Ina ne gidan hajiya a"

"tofa"""

"Abbu ya kwatanta masa, ya tashi ya fita."

"A waje suka yi karo da Rahila, bai ko kalli in da take ba ya fice."

"Ta shiga gidan da sauri, ta samu Abbu ""Yanzu na ga Aminu ya fita, Allah ya sa ba wani abun ya"

"aikata ba?"""

"Abbu yayi murmushi ya ce ""Al'amin ai rigima ta ragu yanzu, duk da wata rigimar ya zo yayi mini ya tafi. Wai gadonsa yake son a bashi, saboda yayi sana'a ya kula da matarsa"" gabanta ya faWi, Wan kuwa ba ™aramin harin filayen nan take yi ba, manyan filaye ne awon gwamanti ga gidaje guda"

uku. Ko da Abbu ya samu karayar arziki bai taSawa Al'amin su ba.

"""Wace irin sana'a kuma, wallahi kar a sayar, ba shi da shi a ina ya samu kuWin sayen leshin dubu tamanin ya bata ta saka, kalli a asibitin da ta kwanta fa na kuWi, kalli uban kaji da naman da aka kawo gidan nan da salla, duk ba shi da kuWin yayi haka? Ni ban taSa zaton zai iya zama soko har"

"haka ba a kan mace wallahi, yanzu saboda kula da itan ne za a sayar da wannan wuraren?"""

"Abbu ya ce ""Ba dai nasa bane ba, shi ya ga zai iya ai"""

"Jauhar ta lallaSa ta cigaba da sana'oin ta, yanzu tana iya aikace-aikacen ta, ta gama aikin, ta idar da"

"sallar magariba, ta ji bugunsa."

"Ta buWe ta kalle shi, ta ce ""Malam lafiya ka ke yi wa mutane wannan bugun haka?"""

"""Zance na zo"""

"""A me ka zo"""

"Ya ce ""˜afata"""

"Ta ce ""Ko keke ba ka da shi ma?"" Ta fito ta zauna a kusa da shi, a kan barandar gidan malam"

"lawan ta ce ""To me ka kawo mini """

"Ya ajiye ba™ar leda ya ce ""Gata nan gyaWa ce marau, suyar yau mai zafi"""

"""Ka rasa me zaka kawo mini sai gyaWa, anya ka na so na din ga fitowa zancen nan"" ya saka hannu zai Wauke ledar, ta riga shi Waukewa ta ce ""Allah ya shiryeka, Allah master da da kanka a ka bari"

"ka samo matar aure, za a sha wahala kan ka samu"""

"""In ji wa? Farinjini fa zan yi """

"""A hakan kana muzurai da zare idon? Kan na saba da kai fa na daWe, tsoro ka ke bani da sosai """

"Ya ce ""To yanzu fa?"""

"""You are my best friend ever, sau™in kai ne da kai fiye da yadda ka ke tunani, miskilanci ne kawai"

"matsalarka wuyatta na dafa abinci mai daWi shikenan an wuce wurin """

"Suka kwashe da dariya tare, a kan barandar gidan, suka cigaba da hira, suna cin gyaWa,"

"kasancewar a cikin duhu ne, babu wuta, yake ba gaya mata yadda suka yi da Abbu."

"""To yanzu wanne zaka yi a ciki, wace sana'ar zaka yi?"""

"Ya ce ""Rabu da shi, idan muka je ™auye zan saka a nuna mini gonakin, a sayar da wata na karSo"

"kuWina"""

"""A'a kar ka yi haka master """

"""Haka fa za a yi, wallahi ba zai taimaka mini ba muddin shegiyar matar nan ta sani, ban da ina"

"duba darajar amintar da suka yi da marigayiyya, wallahi da sai na tsinke mata laka"""

"""A'uzibillah, wannan wace irin magana ce?"""

"""Mu bar wannan maganar, Waukko key ki rufo gidan mu fita yawo "" ta ce to."

"Ta rufe gida, ya goya ta a babur, suka tafi ya din ga zaga gari da ita, ya kaita gidan su, ya ce ta"

"shiga ta gaisa da baba mintuna goma ta fito, saboda ya lura shi ne kullum yake kiranta a waya, yana tambayarta ya jiki."

"Baba ya din ga murna, ganin ta warware, baba da kansa ya rakota, suka gaisa da Al'amin, ya yi ta yi musu fatan alkhairi, da fatan samun wani rabon mai amfani jauhar ta yi shiru, shi kuwa ya amsa"

da Amin.

"Ba su da wurin zuwa, ya cigaba da zagaye da ita, suna tafe suna shan iska, ya saya mata kayan"

"ciye-ciye, su rake, awara, dafaffen ™wai kasancewar dama ba iya cin abinci take yi ba."

"Har wurin sha daya sannan suka koma gida, ya ci abinci."

"Ganin yana ta kaiwa da komowa tsakanin falo da tsakar gida, bayan sun yi shirin kwanciya, ya"

sanya ta gane shaye-shaye yake son yi.

"Ta kalleshi ta ce ""Master ka je ka sha, amma kaWan dan Allah, ba da yawa ba, kar ka bugu"" ya ce"

"""To"""

"Ya fita tsakar gida yayi abun sa ya gama, tana jin sa ya shiga Wakinsa yana wanka, ya fito ya saka turare ya nufo Wakinta, duk da yana Wan warin sama-sama amma ™amshin turaren ya hana warin"

yin tasiri.

"""Ba ki yi bacci ba?"""

"Ta ce ""Ban yi ba jiranka nake, na san ko na yi sai ka tashe ni"""

"""Allah sarki madarata"" yayi maganar yana rungumeta, ya kwanta da ita a jikinsa."

"""Wace sana'ar ki ke ganin zan fara?"""

"""Ka yi tunanin ko kala uku ce, sai mu yi addu'a Allah ya zaSa mana mafi alkhairi """

"Yayi ajiyar zuciya ya ce ""Babu laifi"""

"""Masterna, kai zaSin Allah ne a gare ni, na gode Allah da bai sanya ni cikin masu yi masa butulci"

"ba""."

"Ya ce ""Ni Win?"""

"Ta jinjina masa kai. Nan ta bashi labarin hafsa, ya ce ""Allah ya ™ara, alhakinki ne ai, daga har ke"

"turin jeka ka mutu suka yi mana mussaman ke, Allah ya ™ara"""

"""Master yayata ce fa"""

"""Koma wacece, ai Allah ba ya barin zalunci""."

"""Duk da haka master"""

"""Ni yanzu dan Allah da gaske kina jin daWi rayuwar da muke yi a haka?"""

"Ta ce ""Gaya mini matar da aka taSa goyawa a tarihi, aka yi tafiyar da aka yi da ita a baya, saboda"

"ba ta da lafiya? Gaya mini matar talakan da ake ajiyewa masu kula da ita? abubuwa da dama da mata suka rasa a gidan aure ni na samu""."

"""To ai wannan duk ba wani abu bane ba a kan wanda ki ka din ga yi mini, dan Allah kina jin daWin"

"zamanmu a haka? Just recently kin kusa rasa ranki saboda ni?"""

"Ta ce ""Ba laifinka bane ba ai"" ya yi murmushi cikin jin nishaWi, yake ™o™arin canza hirar zuwa"

"wani abu daban""."

"""Master"""

"""Mmm"""

"""Ban taSa jin ka ce kana so na ba, ko dai kara kawai ka ke yi mini, saboda halaccin da kake i™"

"irarin na yi maka?"""

"""Nima baki taSa gaya mini ba, kuma ina yi a aikace ai, ba dan haka ba, babu wanda ya isa ya saka"

"na zauna da ke ai""."

"Tana dariya ta ce ""Sai abinci"""

"""Ki kiyayeni da abincin nan, kina takura mini fa"""

"Ta shafa bayansa cikin shagwaSa ta ce ""Ba ka ce ba"""

"""Me?"""

"""Ka na so na"""

"""Yanzu dai jirani tukuna, na gama caji, koma menene ya biyo baya""."

"""Ba zaka yi cajin ba, sai ka gaya mini"""

"""Yanzu na tashi na yi waje, zan je na yi wanda na saba, na manta komai, yanzu zaSi Waya"""

"""Ni zaka yi wa wayo ko?"""

"""A'a ba wayo zan yi miki ba, zaSi na baki""."

"Da safe jauhar ta fito falo, ta tarar da Al'amin a kan kujera, ta ce ""Master da me ka yi wanka ne a"

"banWakina?"""

"""Sabulu"""

"""Wanne?"""

"""To ai abubuwan naki ne da yawa, kuma kina bacci kawai na Wauki na wata roba, na zuba a soso"""

"""Master feminine wash ne fa"""

"Ya kalleta ya ce ""Me ke nan?"""

"""Abun kama ruwa ne, dan Allah yayi kama da abun wanka?"""

"Al'amin ya ce ""Kai, wallahi tsirfarki tayi yawa, kama ruwan ma, sai an yi masa wani abu, to sai ki"

"din ga rubutawa a jikin robar"""

"Cikin shagwaSa ta ce ""Gaskiya sai ka saya mini wani, dubu uku fa na saya""."

"""Iyee dubu uku, ke fa wasu lokutan kin iya damfara, dubu uku, wannan abun ne dubu uku, car"

"wash ne fa"""

"""Morning fresh ne, wai car wash kuma yasin sai ka biya ni, ina jin daWin amfani da abuna fa, kai"

"da ba a gyarawa ka din ga lallaSowa"""

"""A daina gyarawar, a bar mini abuna a haka, ko kuma ki karSi car wash"""

"""Sai fa ka biyani, wuyatta na soya maka wainar fulawa da zoSo mai sanyi, sai ka zazzage mini"

"komai na aljihunka"""

"""Ai dama kin saba cin zalina, ki kwashe mini kuWi"""

***

"Tun sassafe jauhar ta shirya, kasancewar yau za su tafi tofa, gidan Hajiya, duk da ya ce wuni kawai za su yi da yamma su dawo gida, ba ta damu da hakan ba, tun da dai ya

6 / 67