Karfe a Wuta Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   60 / 67

177K to 180K   out of 199.8K words

kiranye zasu yi mana"""

"""Ka je ka haWa sojojin bakan da muke da su, a basu kuWi, su je su karemu, da da™ile abun, sannan"

"a saya musu fili a kafafen watsa labarai, su shiga su karemu"""

"P.A ya jinjina kai ya ce ""Shikenan, babu laifi za ayi hakan"""

****

"Nabila kusan raba dare ta yi, tana kallon hotunan matashiyar da yake hannunta, ta takura ™wa™ walwarta, wurin yin tunani, ko ita ce a jikin hoton, amma ita dai ba ta san lokacin da aka Wauki hotunan ba, tabbas ta san ta nuna hotunan nan, akwai sabon rikici, sai dai ta shirya karSar duk"

"abun da zai faru, amma sai ta san wacece a jikin hoton."

"Gaba Waya ta Wauki gaba da yan gidan, ba wanda take kulawa, ko abincinsu ba ta ci."

"Ta shirya tsaf cikin uniform Win ta, ta shirya ta fice."

"Nabila ce a tsaye a gaban kotu ta nemi kotu ta bata damar gabatar da shaidun da take da su, wanda"

ba ta gabatar ba a kotun baya.

"Kotu ta bawa Nabila dama, Nabila ta taso wata mata, matar ta zo ta tsaya a gaban kotu Nabila ta"

"ce ""Hajiya ko zamu iya sanin sunanki?"""

"""Sunana hajara wali"""

"""Wacece ke a wurin rahama?"""

"""Ni mahaifiyarta ce, 'ya ta ce"""

"""Ko zaki iya yi wa kotu bayanin meyafaru"""

"Mahaifiyar ramma, tayi bayani tiryan-tiryan."

"""Kin san wannan?"" Tayi maganar tana nuna mata dattijon."

"""Eh, tare da shi muka yi ta Wawainiyar zuwa kai rahama Asibiti"""

"""Shi ne ya dawo ya Wauke ta?"""

"Ta girgiza kai ta ce ""Ba shi bane ba, wancan matashi ne"""

"Nabila ta ce ""Yanzu ina rahama take?"""

"Cikin kuka ta ce ""Ban sani ba, tun da ya Wauke ta ban sake ganinta ba""."

"""Kafin ya zo ya Wauketa meyafaru?"""

"Ta goge hawayenta ta ce ""Wata mata ce ta zo ta ce mu karSi kuWi, a rufe maganar, na ce ban yadda ba, hakkin 'ya ta nake nema, shi ne bayan ta tafi ya zo ya Wauke ta, bayan kwana biyu ya dawo ya"

"ce mini na bashi kayanta, ta zama mallakinsa"""

"""Ko zaki iya gaya mana sunan matar?"""

"lauyan gwamnati, ya nemi kotu ta dakatar da Nabila, tambayoyinta na ™o™arin ™etare iyaka."

"Ya taso zuwa gaban majaifiyar ramma ya ce ""Hajiya wanda ya zo ya tafi da itan, bayan ya tafi da"

"ita, meyasa baki sanar da jami'an tsaro ba?"""

"""Na sanar da su, amma suka ce na je gida za su neme ni"""

"""Da basu nemeki ba kin koma?"""

"""Na koma har na gaji, amma babu wani cigaba"""

"""Sai aka neme ki aka rasa, ko sama ko ™asa"""

"""Bibiyar abi mini hakkin 'ya ta da nake yi, ya sanya aka fara yi mini barazana, shiyasa na bar"

"gidan"" ya yi wa kotu godiya ya koma ya zauna."

"Nabila ta sake komawa gaban kotu ta kalli dattijon nan ta ce ""Baba a kotun baya, ka amsa kai ne"

"ka yi wa rahama fyaWe, shin da gaske kai ne ka yi mata fyaWe?"""

"Ya girgiza kai ya ce ""Cewa aka yi idan na ce bani bane ba, abun da ya samu rahama zai samu"

"'ya'yana""."

"""Meyafaru ranar da abun ya faru?"""

"""A ranar aka Waukko ramma daga ™auye, akwai ™anin matar gidan ya zo a buge, ya tambayeni matar gidan sun dawo, na ce masa a'a, amma ya shiga, bayan wani lokaci ya fito ya Wauki motarsa ya tafi. Sai bayan zulai ta dawo daga sayayya, ta fito tana ihu, ta ce na zo na gani, muka tarar da"

"ramma a kwance a Wakin girki, cikin jini"""

"Nabila ta ce ta gama tambayoyin da zata yi, mai shari'a ya Waga shari'ar zuwa sati biyu domin"

yanke hukunci.

"Suka fito tare da barrister Habib da mahaifiyar ramma, da yaran dattijon, ta ce ""In sha Allah, mune"

"ke da nasara, hukuncin da kotu zata yanke zata yi mana adalci"""

"Barrister Habib ya ce ""In sha Allah, komai ya kusa zuwa ™arshe"""

"Nabila ta ce ""Zai dai zo, burina kawai a wanke baba, daga nan mu Wora da cigaban shari'a"" iyalan"

dattijon suka din ga yi mata godiya.

FEW DAYS BACK

"Cikin tsananin mamaki, kankarofi yake kallon Nabila. Ya ce ""Barrister, ke ce da kanki a office W"

"ina? Ya aka yi ki ka san wurin nan?"""

"Tayi murmushi ta ce ""Ba abun mamaki bane ba, matambayi ai baya Sata, yau gani a ofishin masu"

"™asa"""

"Ya ce ""Allah ya sa ba laifi nayi ba aka zo kama ni?"""

"Ita ma murmushin ta yi masa ta ce ""Yan sanda ai su ne suke kama mutum"" ya bata izinin zama."

"Ta samu wuri ta zauna ta ce ""Na yi sa'a, kana kano baka tafi Abuja ba kenan?"""

"""Eh, ina hutu ne, amma haryanzu mamaki nake yi, yadda aka yi ki ka tako da kanki, ki ka zo har"

"in da nake"""

"Ta numfasa ta ce ""Ka san komai dalili ne yake kawo shi"""

"""Haka ne, bari na saka a kawo miki abu mai sanyi"""

"Ta ce ""A'a, Alhamdilillah tambayoyi ne nake da su a gareka YallaSai"""

"""To gimbiyata ina jinki"""

"""Case Win da nake yi, na yarinya da aka yi raping, ashe a gidanka aka yi. Na sake komawa na lura da sunan street Win sunanka ne, kuma na tambaya aka nuna mini gidan aka ce naka ne. Abun ya W aure mini kai, sai dai na jajje amma ban samu abun da nake so ba, matar gidan ta koreni, kusan"

"sau biyu ma, yaya aka yi haka yallaSai?"""

"Yayi murmushi ya ce ""Waye ya ce miki gidana ne?"""

"""Sir gidanka ne mana, Mu'azzam wada kankarofi street, kuma aka nuna mini gidan aka ce gidanka ne, sir ban yi tsammanin haka daga gareka ba, Soye mai laifi a Worawa wanda bai ji ba bai gani"

"ba mai gadinka?"""

"""Nabila, ina iyakar ™o™arina, am even supporting you, baban yaron nan abokin adawata ne,"

"matata kuma akwai yara a tsakanin mu, bai kamata na tona mata asiri haka anyhow ba"""

"""Amma yarinyar mutane da aka zalunta fa? Maigadinka da aka rufe ba da laifinsa ba fa? Wannan"

"ba hujja ba ce ba, what if Wanka aka yi wa haka? Haba yallaSai"""

"""Nabila, lamarin ™asar nan ya wuce duk in da ki ke zato? Dole sai mutum yana lissafi, amma in tambaye ki mana? Waye ya ajiye miki tarihin Bunkure a Office Win ki? Waye ya tura miki message Win babar ramma? Duk kina tunanin wannan, ko kuwa kawai sabgarki ki ke yi?"" Waro"

ido ta yi tana kallonsa.

"""Mayar da idanun madam"""

"Cikin mamaki ta ce ""But how?"""

"""Through barrister Habib my dear. Ba zan tona wa yaron asiri kai tsaye ba, saboda ubansa ne tushen lalata shi, ba kuma nayi haka ne dan na Soye laifinsa ba, ina jan ™afa a lamarin ne, saboda ki gano komai a sannu, yadda babu mai zargina, duk da akwai ji™a™™iya tsakanina da ubansa."

"Mahaifiyar ramma na tare da ni, ni na saka aka Wauketa, tun kan a illata ta saboda case Win nan. Zan haWa ki da ita, zata yi miki bayanin komai, amma ki daina zargina a kan Soye mai laifi, am supporting you, program Win ma da ki ke yi am supponsoring the program sweetheart, ki daina zargina please, tabbas a gidana aka aikata laifin, kuma ina iya ™o™arina a kai madam. Ki je ki"

"cigaba da aikinki, zan cigaba da ™o™arina in taimaka miki"""

Saroro tayi tana kallon kankarofi kamar sokuwa.

"""Akwai alamar gajiya a tare da ke, ki je zan saka Habib ya kai ki in da take"""

"""Amma duk tsawon wannan lokacin, kuka rufe ni ka ke yi mini yawo da hankali?"""

"""Akwai dalili ne, amma ki yi ha™uri dan Allah, a dalilin haka aka saka miki wuta a office, aka kusa taka ki da mota, duk dan ina tsayawa ina tsawatar wa ne, akwai hatsari a abun da ki ke yi nesa ba kusa ba, shiyasa nake taimaka miki ta ™ar™ashin ™asa, amma kiyi ha™uri"" ba ta ce masa"

"uffan ba, ta Wauki jakarta za ta fita."

"""Ina ba™onki kuwa? Idan kun sake haWuwa ki ce ina gaishe shi"" ta tsaya ta waiwayo ta ce ""Wane"

"ba™on kuma?"""

"""Viper"" ya amsa mata kai tsaye."

"""Ka san Viper?"""

"Kankarofi ya ce ""Na san shi, akwai labari mai sar™a™iya ne, amma kar ki matsa, ki bi a hankali, zai kawo ™arshen labarin, kamar yadda ya faWa, a sauka lafiya abar ™aunata"" ba ta iya magana ba, ta murWa ™ofar ta fice."

"Tun a hanya ta kira barrister Habib, take yi masa masifa, a kan abun da ya yi mata, ya din ga yi"

mata yawo da hankali da nuna bai san komai ba.

"Sai da suka haWu, yayi ta bata ha™uri, yana ™ara yi mata bayani, kankarofi yayi mata kwarjinin da"

"bata tsigale masa ba, amma ta yi wa Habib ta tas."

****

"Nabila tana tafe tana kallon hotunan hannunta, ta kira Viper ya Waga ta ce ""V ina wuni?"""

"""Lafiya ™alau, ya ake ciki?"""

"""Ina hanya zuwa zan yi"""

"""To, Allah ya kawo ki lafiya"""

****

"Ramma ta tsurawa Abdul ido, ya ce kunun gyaWa yake so, yana sha yana waya, ya ajiye kofin kunun ya ce ""Daddy ni dai dan Allah ka yi ha™uri, wallahi ba zan iya fito maka da rahama ba"""

"Ashariya Indabo ya din ga zabga masa, ya ce ""Wallahi zan saka jami'an tsaro su kama ka, su ci ubanka, uwar yarinyar nan ta bayyana a kotu, an ambaci sunanka, duk da ba a faWi cikakke waye kai ba, ga maganar kuWi na yi maka, duk ka yi kunnen uwar shegu da ni, Abdul kana son ka gama"

"da duniya lafiya kuwa? Dole sai ka tozarta ni?"""

"""Daddy ba tozartaka zan yi ba, makomar rahama nake dubawa ita ma...."

"Wata ashar Win indabo ya lailayo, kamar ba babba ba, ya gama masifar, Abdul ya ajiye wayar ya"

dafe kai.

"""Kai ma da naci kamar me, ka fitar da ni mana, ko ma me za ayi mini ayi mini, sai Soye ni ka ke yi kamar ciwo, ni kaina tun ina masifa har na gaji, haba dan Allah"" tsaki ya ja, ya tashi ya bar mata"

dining Win.

***

"""Abba ya yi tafiya, yau nake saka ran dawowarsa, zan nuna masa hoton nan, na ji mai zai ce, tun da kai ka™i gaya mini wacece?"""

"""Yaya shari'ar ta kasance?"""

"""Alhamdilillah, babar ramma ta je kotu ta bayar da shaida, ina jin alamar nasara in sha Allah"""

"""Mhmm, a ina aka ganta?"""

"""Ta gudu ne wani wuri ta Suya, daga baya da taimakon barrister Habib, muka ganota"""

"Viper ya jinjina kai ya ce ""ya nawa, ni ya ake ciki?"""

"""Shiyasa na zo ai"""

"""Ok"""

"""Kamar yadda na fara gaya maka jiya, dole ina bu™atar su oga walid, da wannan bugaggen a kotu"

"su bayar da shaida"""

"""Wane bugaggen?"""

"""Oho ni na san sunansa ma? Amm sannan sai ka yi ha™uri, duk wasu rashin ji da ka yi, sai mun yi"

"exposing Win su a kotu"""

"""Rashin ji kamar yaya?"""

"Ta kalleshi ta ce ""Kamar yadda ka yi mana, sara suka, ™ulla wiwi black market duk da ka yi"""

"HaWe rai yayi ya ce ""Amma ba prison zan koma ba ko?"""

"""Idan ta kama ai dole ka koma"""

"Ya ce ""What? Gaskiya ki yi yadda zaki yi, ba zan koma prison ba, wanda nayi 5yrs fa?"""

"Ta zumSura baki ta ce ""Ni na Waureka, sai abun da ya kama kawai, bari na je gidan, na ji wadda"

"zamu yi da su, sai anjima"""

*****

"Nabila ta tafi Wakin Abba, domin amsa kiran da yayi mata, ta tafi bakinta Wauke da addu'a, ta"

"shiga Wakin da sallama, suka amsa ban da Abba da yayi shiru ransa a Sace."

"Ta je ta dur™usa ta ce ""Abba gani"""

"""Nabila ban isa na gaya miki magana ki ji ba ko?"" Tayi shiru ta sunkuyar da kai."

"""Dole sai kin nuna wa duniya cewa ban haife ki ba ko Nabila? Kin nuna mini iyakata, ban isa na"

"nemi alfarmarki ba kenan ko Nabila? Sai kin tozarta ahalin nan gaba Waya ko Nabila?"""

"Ta girgiza kai ta ce ""Abba bani da wannan burin, kuma wallahi ba zan taSa aikata wani abu da zan janyo maka zagi ba. Amma dan Allah Abba a yanzu, ka yi mini wani taimako, saboda zatin Allah"

"kar abun da zan nema ya Sata maka rai"""

"Ta mi™a wa Abba hotunan, da Viper ya bata, ta ce ""Dan Allah Abba wacece wannan? Ni dai na san"

"ba ni ba ce ba, dan Allah Abba ko kana da masaniya a kan ta jikin hoton nan."

"Abba ya saka hannu, ya karSi hotunan yana dubawa."

"Ya gama ™arewa hotunan kallo, ya ce ""A ina ki ka samu hotunan nan?"""

Ayshercool 08081012143

¦ 500 ne via 0009450228

Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne.

90009343

'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

https://whatsapp.com/channel/0029Va9QtrY4dTnBYG1hST2VHADARIN

*BRIGHT PENS SECOND BATCH*

"Ku kasance da littatafan bright pens, second batch."

*˜ARFE A WUTA (AYSHERCOOL)*

*MUTALLAB (NIMCYLUV)*

HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)*

*ZAYTOON (ZEE KUMURYA)*

"Ta Wan yi shiru sannan ta ce ""A office Wina na gansu"""

"A take Abba ya fara yayyaga hotunan, cikin kuka ta ce ""A'a Abba, dan girman Allah ka gaya mini idan ka san ta jikin hoton, Abba ba ka ga yadda kamaninmu suka Saci ba, dan Allah Abba ko sau Waya ka nuna mini wani a dangin mahaifina dan Allah Abba"" ™arasa yayyaga hotunan yayi, ya watsa mata cikin matsanancin Sacin rai ya ce ""Ki koma in da aka baki hotunan, su gaya miki koma wacece, ubanki kuma ga hanya nan, ki bar mini gida ki tafi yawon nemansa, yayi miki abun da ban yi miki ba, tashi ki bar gabana kan na tattaka ki, da uban naki ya damu da ke, da zuwa"

"yanzu shi ya nemi in da ki ke""."

"Anty ta ce ""Haba major, dan Allah ka yi ha™uri kar ka yanke wannan tsatstsauran hukuncin a kan"

"ta, kayi ha™uri dan Allah "" gaba Waya jikin Nasir yayi sanyi, ganin yadda take ta uban kuka."

"Cikin tsawa Abba ya ce ""Ki tashi daga gabana, ki tafi ki bar mini gida, ki je ki nemi ubanki, amma"

"ki bar mini gida kar na sake ganinki a gidana"""

"Wata irin ajiyar zuciya ta din ga yi, ta yin™ura ta tashi da kyar, ta bar Wakin, ta koma Wakinta ta kifa a kan gadonta, ta fara sabon kuka, shi kuwa Abba wace irin zuciya ce da shi haka? Ko menene a tsakanin sa da mahaifinta, yakamata ace ya wuce, ta san ya gama yi mata komai a rayuwa, yayi playing role Win uwa, yayi na uba a rayuwarta, amma duk da haka gurbin ido ba ido"

bane ba.

"Baba magajiya ce tayi sallama, ta ™arasa kan gadon, ta dafa kafaWarta ta ce ""Haba Arfa, ke a rayuwarki ba zaki iya ha™uri da tawakalli ba, tun da ya nuna miki baya son zancen nan ba sai ki ha"

"™ura ba, shekara nawa ana abu Waya kin ™i ki gane ki ha™ura""."

"Nabila ta tashi zaune, idanunta sun yi jawur ta ce ""Baba magajiya"""

"""Na'am arfa"""

"""Kema laifina ki ke gani?"""

Baba magajiya ta yi shiru tana kallonta.

"""Ki bani amsa mana, laifi nayi dan na nemi sanin in da mahaifina yake na ganshi ko sau Waya?"

"Baba magajiya mahaifi fa, a duniya na san Abba ko baki yayi mini, sai ya kamani, bana nufin yi"

"masa butulci ko tozarta shi, amma ina son sanin babana, baba magajiya dan Allah ina da wata yar uwa ne? Ke kin san komai, hoto aka bani da wata a jiki irina Waya da ita sak, ko yar uwata ce, dan Allah ki gaya mini. Ni idan kin san in da zan ga babana ki gaya mini, ko sau Waya na je na ganshi"

"na dawo dan Allah"""

"Baba magajiya ta girgiza kai ta ce ""Ni ban san komai ba, lokacin da na zo gidan nan, an gama"

"dambarwar da za ayi, na zo, ni bani da wani labari a kan mahaifinki"""

"Nabila tayi murmushi mai ciwo, hawaye na bin fuskarta ta ce ""Haryanzu kallon yarinyar da ki ka raina ki ke yi mini ko, shiyasa ki ke tunanin bani da wayo ko? Shekaru ashirin da biyar a doron duniya, ai na girmi ki yi mini wayo baba magajiya, amma shikenan, ai Abban ya ce na je ne nemi"

"babana, zan neme shi kuwa in sha Allah """

"Baba magajiya ta waro ido ta ce ""Baki san gatse ba Arfa?"""

"Nabila ta jinjina mata kai alamar eh, ta mayar da kai ta kwanta."

"Baba magajiya ta ce ""Arfa na san har da damuwar matsi da takura da ake yi miki a gidan nan, ya sanya ki ke damuwa da son ganin mahaifinki, ni dai ro™ona da ke, ki yi ha™uri idan da rabo zaki haWu da mahaifinki ko danginsa, amma dan Allah dan Annabi, kar ki bari ku samu saSani"

"da maitama"""

"Nabila ta yi mata shiru, dan gani take yi babu wanda zai fuskanci halin da take ciki."

"Tamkar zuciyarta Abba ya yaga, haka take jin zuciyarta, idan ta tuna yadda ya yayyaga hotunan"

"nan, sai dai har a lokacin tana ganin hotunan yarinyar mai kama da ita a cikin idanunta."

****

"Duk da Nabila bata jin daWin komai na duniyar, jin ta kawai take yi gata nan dai, haka ta cigaba da up and down a kan muhimman abubuwan da ta saka a gaba."

"Ta sake shigar da koke gaban hukumar'yan sanda, ta nemi su kama madaki da wasu daga cikin"

"yaransa, bisa zargin kisan

60 / 67