Karfe a Wuta Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   26 / 67

75K to 78K   out of 199.8K words

dai? Tara ko bashi, ki ka tsaya mini a ™ofar office"" tayi murmushi ta ce ""Babu Waya, nemanka nake yi ruwa a jallo ne"""

"Ya saka mukulli ya buWe, suka shiga, ya ce ""Allah ya sa ba wata shirirtar ba ce? Nima ina nemanki"

"dama"""

"""Haba barrister, sai ka ce wata 'yar yarinya, is a very serious issue"""

"Ya dubeta ya ce ""To yanzu dai, ki yi ha™uri, na fara karyawa tukuna"""

"No™e masa kafaWa tayi, tare da girgiza kai."

"Ya ce ""Ke, kwanan nan fa nayi mata ta biyu, da na sani ma da ke nayi ta biyun nan, wannan"

"shagwaSar taki ai sai ki hanani karyawa"""

"""TaS matarka ta daka ni kenan, ni dai ka zauna Please muyi magana"""

"Ya zauna ya ce ""Na zauna Nabila menene?"""

"Wayarta ta ciro ta kunna masa voice message Win nan, cikin mamaki ya kalleta ya ce ""Waye ya"

"turo miki?"""

"Ta girgiza kai ta ce ""Ban sani ba, shiyasa na zo na nuna maka"""

"""To ai tun jiya naso na kira ki, na je garinsu yarinyar da kaina, har gidan su na je, amma ban tarar da kowa ba, ma™wabta sun tabattar mini da ta shafe kwanaki ba su san in da take ba, kuma ba ta yi wa kowa sallama ba"" Nabila tayi turus ta ce ""Ban gane ba, uwar ta Sata kenan? Ko kuma guduwa"

"tayi saboda gudun abun kunya?"""

"""Shi ne dai ban sani ba"""

"Nabila ta ce ""Na kasa gane kan lamarin nan, to waye ya turo mini voice Win nan, an ce shi wanda"

"yayi mata fyaWen, ya zo ya Wauke ta, to ya aka yi da uwar, waye ya naWi wannan recording Win?""."

"Barrister Habib ya ce ""Gaskiya dai abun tunani ne, lamarin akwai Waure kai, amma kar ki damu,"

"koma waye sau™a™a miki aiki yayi"""

"""Amma abun da mamaki fa, kuma wanda yayi hakan ba shi da wata manufa ta yin hakan, ya"

"bayyana kansa mana idan yana da gaskiya koma waye"""

"Barrister Habib ya jinjina kai ya ce ""Yauwwa, ya ku ka yi da Alhaji wada M karofi?"""

"Ta yamutsa baki ta ce ""Soyaya muke yi """

"""Soyayya kuma? Cewa yayi yana son ki shiga cikin lawyoyinsa, masu kula da dukiyarsa fa"""

"Ta ce ""A'a gaskiya, ce masa nayi a'a, sai ya ce to shi na din ga kula da shi, shikenan"""

"Habib ya ce ""Innalillahi, wallahi baki da lissafi Nabila, kin san waye mutumin nan kuwa? Kin san"

"kuWin da muke samu a wurinsa kuwa? Babban mutum ne fa a ™asar nan"""

"Ta tashi ta ce ""Oho, a hakan ma ai yana bani kuWi, bana son dai ya zo gidanmu, naga he's very"

"serious, kar ya zo suyi magana da Abba ace sai na aure shi, dan yasin bana son tsoho""."

"Ya girgiza kai ya ce ""˜uruci dangin hauka, Allah ya shiryeki"""

"""Amin, ayi aiki lafiya"" ta fice daga office Win."

***

"Ramma na zaune tana ta gyangyaWi, ta ji ana murWa ™ofar falon, Abdul ya shigo da akwatinsa."

"Suna haWa ido ya sakar mata murmushi ya ce ""I am back"" murmushin ita ma tayi masa."

"Ya ™arasa ya zauna tare da rungumeta, yayi kissing Win goshinta ya ce ""Kina zaune baki yi bacci"

"ba kina jirana?"""

"""˜arfe tara fa ka ce, amma sai sha biyu, Club ka je ko?"""

"""Wallahi ban je club ba, abubuwan da na tarar da yawa a can, Shiyasa na kuma samu matsala ne"

"da flight Win shiyasa, gudowa fa nayi saboda ke"""

"Tayi ajiyar zuciya ta ce ""To sannu"""

"""Yauwwa sweetheart """

"Ta ce ""TaS babu daWin ji"""

"Ya ce ""Wallahi da daWi, rantse baki ji daWi ba da na ce sweetheart"""

"""Wallahi ban ji ba"""

"Abdul ya ce ""˜arya ki ke yi, santaleln mutum kamar ni, na kira ki da sweetheart, ki ce ba ki ji"

"komai ba"""

"""To waye kai Win? Sai ka ce wani mutum na musamman"""

"Ya kaWa ™afa ya ce ""Ke kin san matan da suke crushing Wina kuwa?"""

"""To ina ruwana?"""

"""Kina da ruwa mana, na gaji fa sosai Saboda na san maybe kina nan kina jirana, ko abinci ban tsaya na saya ba, yanzu zan yi wanka, sai ki rakani mu duba in da suke 24hrs, mu ci abinci"""

"Ramma ta ce ""A'a, na yi girki ai tun magariba ma na gama, tun da nan gidan ba mak aiki, kayi"

"wankan ka ci"""

"Ya ce ""Iyee zan ci jagwalgwalo yau, bari nayi wankan"" ya ja akwatinsa, ya shiga bedroom Win da"

take.

A falo ya tarar ta ajiye fulasai.

"""Rahama kayan miyan cikin fridge Win ba su lalace ba kenan?"""

"Ta ce ""Eh, har fruit Win, na iya reserving Win su ai"""

"Yana cin abincin yana murmushi, ya ce ""Yanzu har sakwara ki ka yi, gaskiya kina ji da ni, ga"

"shayin ma yayi daWi sosai"""

"""Ba wani ji da kai da nake yi, tunani nake ina ma da guba a ciki, ka ci ka mutu"""

"Yayi dariya ya ce ""Koma dai menene, idan ma da gubar na ci, ba mutuwa zan yanzu ba, sai kin haifa mana babies, kuma fa zama zaki yi kiyi kuka idan na mutu. Anyway abinci yayi daWi sosai,"

"yaya aka yi ki ka iya girki haka?"""

"Ramma ta ce ""Aikina kenan a gidan Anty maijidda, ta ce ba ta taSa yar aiki kamata ba, sai gashi iftila'i ya faru da ni a gidanta, amma ta kware mini baya, saboda kai Wan Wan uwnta ne, ni kuma bata da ala™a da ni, ko ganin idonta ban yi ba, wai sai ma umarnin idan mun zo kar a bari mu shiga da ta bayar, aka canza masu gadi.shikenan bakomai, shi talaka ai Allah yana son abun sa"""

tayi maganar tana share hawayenta.

"Sai jikin Abdul yayi sanyi, ya ce ""Rahama duk laifina ne, nayi kuskure, kuma duk sharrin giya ne da ruWin shaiWan, amma na rage shan giya ma, kuma wallahi rahama na daina bin mata, da Win ma sharrin giya ne da kuma abokai"" tashi ta yi ta bar masa wurin, saboda tuno hanyar da ya bi ya ci"

mata zarafi da yayi.

"Shi ma gaba Waya sai jikinsa yayi sanyi, duk da irin zaluncin da yayi mata, tana da matu™ar"

"tausayi da imani, duk da yana shan zagi da tsinuwa, amma wasu lokutan sau™in hali ne da ita."

"A zaune ya tarar da ita a kan gado, tana ta uban kuka, bai ce mata uffan ba, ya rungumeta yana shafa bayanta, a hankali yake furta ""Am very sorry for what i did, ki yi ha™uri"" ya din ga rarrashinta, har suka kwanta, yana ta magana, amma tunani ne daban-daban a cikin kanta, babu"

"tsammani ya ji ta ce ""Abdul yasar"""

"""Your excellency"""

"""Wai dan Allah da gaske ana yi wa maza fyaWe?"""

"Ya ce ""A'uzibillah, wannan wace irin magana ce?"""

"""Shekarun baya, kan yayanmu ya mutu, kamar haka na so naji an ce, wani ne ya ce zai samo masa aiki a Abuja, shi ne yayi masa fyaWe yayi rashin lafiya ya mutu, kullum mama ta tuno da shi, sai ta kusa kwana tana kuka, sai ta daina cin abinci, kusan shekara shida fa, amma ta kasa mantawa. Kuma dama ba a hannunta yake ba, shi yana wurin babansa a birni. To ni haryanzu ban taSa jin an ce an yi wa namiji fyaWe ba sai mace, shi ne nake tunanin, ko wani abun suke nufi daban ban gane"

"ba""."

"Dummm haka Abdul ya ji kansa yayi, ita kanta kalmar ga mace ma babu daWin ji, balle ga namiji, sai yanzu ya ™ara tabattar da in dai zancen ramma gaskiya ne, ya zalunce su. Hakan ya saka ya ji dolensa ya ™ara ™aimi, ya nemo mahaifiyarta, ya nemi afuwarta, amma bai ji a ransa zai iya"

mayar mata da ramma ba.

"""Abdul ka yi shiru, ka gaya mini mana"""

"""Ke kin ga alamar in da za a yi wa namiji fyaWe ne? To ban sani ba ko ana yi, tun da nima yaro ne"

"haryanzu, ban sani ba ko ana yi"""

"""Waye yaron?"""

"""Ni mana"""

"""Ka fiye abun haushi, da takaici, a'a mahaifa ne kai"" murmushi ya yi yana sumbatar ta."

***

"""Mai zamani"" Walid ya kira sunan Viper."

Ya Waga ido yana kallon Walid.

"""Da gaske ka haWu da madaki? Ko kuma yaransa ne suka yi maka wannan raunin na damtsenka? Na ji an ce an neme shi an rasa, kuma ban ji labarin yan sanda sun kama shi ba. Abun duk ya W aure mini kai, daga majiyarmu ta dabarsa, hatta su yaransa ba su san a inda yake ba. Kuma na san abu ne mawuyaci ku haWu ace iya illar da yayi maka kenan, bai kashe ka ba, tun da ya san nemansa ka ke yi, kuma kai ma da ka kashe shi da an ji labari, kuma bana tunanin zaka iya kashe"

"shi a yanzu""."

"Viper ya gyaWa kai, ya Waga russia da take hannunsa yake ta goge ta, yana shafa mata mai."

"Ya mi™awa Walid ita, ya karSa. Ya ce ""Meyafaru?"""

"Al'amin ya ce ""Duba da me aka ™erata?"""

"Mamaki ne ya kama Walid, tun da suke bai taSa yi masa wannan tambayar ba, ya karSa ya"

"dudduba ta, ya ce ""˜arfe ne"""

"Viper ya ce ""Duba dai"""

"Ya sake dubawa ya ce ""˜arfe ce Viper"""

"Viper ya haWa tafukan hannayensa biyu ya Waga ya ce ""Allah ya ji™an maza"""

"Walid ma ya haWa ya Waga ya ce ""Amin, dodo babban sarki"""

"Viper ya ce ""Shi ya saka aka ™era mini russia. An yi amfani da ™ashin ™waurin zaki ne, a samanta, ™asanta kuma azurfa ce haWe da ™arfe, sai kuma aka yi amfani da magunguna wurin ™ arasa haWa aikinta. Shiyasa ba ko yaushe nake amfani da ita ba. Ya saka an ™era mini ita, ita ce"

makarin taurin da madaki yake amfani da shi.

"Sai dai a lokacin ban ji cewar ya dace na kawar da madaki farat Waya, na kashe shi ba, na cigaba"

da ajiyeta.

"A wannan karon naga yakamata na nu na wa madaki, talala kawai nayi masa. Saboda shi aka ™era russia, na gwada aikinta ne a kansa, kuma tayi tasiri, dan kuwa ta huda shi, ya kuma zubar da jini. ˜afar da na soka masa, ta tashi daga aiki har abada, ba zan kashe shi farat Waya ba, sai na gama sabauta rayuwarsa, Indabo ya watsar da shi a dalilin Rashin amfanin da ba zai yi masa ba. A lokacin da sauran waWanda yake cuta, za su farga asirinsa ha karye ya daina tasiri, su ma su fara far masa da kai masa hari. A haka zan cigaba da yi wa gaSoSinsa yankan ™auna, har sai na fara jin"

"sanyi a zuciyata""."

"Walid ya ce ""Kan uba, yanzu duk tsawon lokacin nan, kana da makarin tsafin madaki, ka zauna"

"muke bulayi? Har yayi maka illa ta biyu?"""

"Ya sunkuyar da kai sannan ya Wago ya ce ""Tun a baya, nayi niyyar Waukar fansa, amma daga cikin alfarmar da matata ta nema a wurina, ya haWa da na bar madaki da Allah, kar na kashe shi, ba ta son nayi kisan kai, sunana ya ™ara Saci, hatta gabarmu sai da ta ro™i na kawo ™arshenta, idan ban manta ba, har Abbu ta sako a al'amrin."

"Kukanta ne ya tsaye mini a rai, tare da magiyarta, har na ji a raina na yadda, na ha™ura zan kawo"

"™arshen gabata da shi, domin in faranta mata amma. Sai kuma yayi shiru, ya fara huci, jijiyoyin sa suka fara kumbura, gumi yana tsatstsafo masa a goshinsa."

"Walid cikin damuwa, ya daddaki kafaWar Viper ya ce ""Am sorry mai zamani, ka yi ha™uri, kayi ha"

"™uri"""

***

"Nabila na ta rubuce-rubuce a cikin system, ta jiyo muryar Abba yana ""Ina Arfan Abban ne, ko ba ta dawo ba ne?"""

"Daga Wakin ta amsa ta ce ""Ina nan Abba, gani nan"" ta fito tana murmushi."

"Ya Wago mata key, ya ce ""To, ga 206 Win ki can an kawo, duk da na san ba kya son kalar motar"""

"Wani irin tsalle tayi, ta rungume Abba, ta na ""Subhanallah, wayyo daWi ina zan saka kaina, Abba dama zaka sai mini motar? Na zata da wasa fa ka ke yi mini"" murmushi ya yi, ya kama hannun ta, suka fita harabar gidan, wanda suka kawo motar ma ba su tafi ba, Vibe ce blue black sai she™i take"

yi.

"Kawai ta fashe da kuka, Abba ya ce ""Ya kuka kuma?"""

"""Abba na gode, na ma rasa me zan ce ne"" 'yan gidan duk suka fito suna kallon motar, masu tayata"

"murna nayi, masu tsaki suna yi."

"Ana haka Nasir ya shigo, ta nufe shi da sauri, tana nuna masa key Win motarta."

"""Congratulations, amma tawa zaki Wauka ni bani sabuwar"""

"Tayi dariya ta ce ""Ai ba aro ba Wani, balle kyauta"" dama a karambani, Nabila ta iya mota, a kan ta Nasir, ya karSi mukullin, walida ta ce bari ta zo a Wana su, amma Nasir ya ce mata a'a, su biyu"

kawai za su fita.

"Suna tafe yana driving, bakinta ya™i rufuwa."

"""Wow na zama big girl, idan zan je trial, sai dai a ganni a motata, a din ga cewa hajiya, shikenan na huta da hawa Wan sahu, da masu warin hammata da zarnin fitsari"" ya ™are mata kallo, sai nisha"

Wi take yi tana murmushi.

"""Arfa"""

"""Yes sir"""

"""Ina son mu yi magana ne"""

"Ta kalleshi ta ce ""To yaya"""

"""Shari'ar da ki ke yi, da kuma adawa da Naja'atu Bunkure"""

"""Ok ina jinka"""

"""You have to withdraw the trial"""

"""What?"""

"Nasir ya ce ""For your own good and safety, mace ce mai hatsarin gaske, kar wani abu ya same ki,"

"Abba ba zai iya jurewa ba, nima kuma haka ki rabu da matar nan"""

"Nabila ta ce ""Yaya, ni fa dama masu ™aunata ba su da yawa a duniya, dan haka ka ™yaleni, why"

"would that innocent old man suffer just to cover someone's evil did, ita kuma ta din ga zaluntar mutane, kuma ayi mata shiri, i can't nima Allah ya tsaya mini""."

"""Shut up, ina magana kina mayar mini, babu wanda ya shiga cikin maganar sai ke, tun da ki ga kowa baya tsoma baki a lamarinta, dan me ke zaki yi? Ki janye shri'ar nan tun ban saSa miki ba, tun da baki san ciwon kanki ba. Ya zama dole ki janye, idan ba ™afar wando Waya ki ke so mu saka da ke ba"" ya ha™i™ance yana yi mata masifa. Tayi masa shiru, gaba Waya ta nemi farincikin"

"da take ciki ta rasa, saboda maganar da Nasir yayi, ya gama zagayawa suka koma gida."

"Matan Abba kuwa mussaman mama, ta din ga mita a kan saya wa Nabila mota, itakaWai a gidan, amma ya ce gidansa ne, abun da ya tsara shi za ayi, ba wanda aka tsara masa ba. Lokaci ne yayi da"

zasu girbi abun da suka shuka masa a kanta.

"Gaba Waya sai ta rasa karsashi, ta na ta zumuWin kiran sumayya, amma yanzu ta kasa, saboda"

haushi da mamakin abun da Nasir yayi mata yanzu.

"Kawai sai ta kira Viper, ya Waga ya saka a kunnensa."

"""Ina wuni, ya jikinka kuwa?"""

"""Alhamdilillah"" sai da ta tashi tsaye jin ya amsa ta ce ""Kai, yau ka amsa mini, masha Allah, Allah ya ™ara maka lafiya da nisan kwana, ya kare mana kai. Dama na kira ne in ji ya jikinka, kuma"" sai"

"tayi shiru, shima shirun yayi bai yi magana ba."

"""To ka tambayeni menene mana? Shikenan ma na san ba kulani zaka yi ba, sai anjima"" ta kashe"

"wayar ta ajiye, ta kwanta tayi shiru, zuciyarta a cunkushe babu daWi, ga abun farinciki, amma Nasir ya Sata mata. Kawai ta fashe da kuka, ta yi ta gama, ta kwanta ta hau bacci."

***

"Yau a kotu, hujjojin da Nabila ta bayar masu kyau ne sosai da sosai, sai dai lauyan gwamantin da yake kare Sangaren ramma, sun fita gogewa suka din ga dankwafar da ita, kuma al™alin ya din ga Waukar side, tare da soke wasu daga cikin hujjojin Nabila. Ya sake Waga shari'ar zuwa wata guda."

"Ta kalli dattijon, gaba Waya sai ta ji ta fara karaya."

"Jiki a sanyaye ta fito, tana fitowa murtala yana tsaye a harabar kotun yana jiranta."

"Kamar ta fashe da kuka ta ce ""Yaya murtala kaga yadda shari'ar nan ke tafiya ko?"""

"Murtala ya ce ""Kar ki damu, ai idan sun san wata, ba su san wata ba, kamar yadda muka tsara zan"

"tattauna da ke a kan shari'ar yanzu, ki faWi hints mai muhimmanci, zamu saka a live program yau"

"da ni da Sumayya, sai dai duk mai faruwa ta faru."

"Cikin damuwa ta ce ""Kar fa ku samu matsala a wurin aiki"""

"""Manta da su, duk da su ake haWa baki ai, dattijon ne ma abun tausayi"""

"Nabila ta ce ""Wallahi ko kallonsa nayi, sai tausayinsa ya kama ni, bana son na kasa sakawa a"

"wanke shi"""

"Murtala ya ciro recorder Win sa, ya tattauna da Nabila, na mintuna biyar, a kan shari'ar sannan ya"

tafi.

***

"Indabo tamkar zai kwaWawa Abdul mari, saboda takaici ""Abdul wai me kake nufi da ni ne? Sai ka yi mini

26 / 67