Karfe a Wuta Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   18 / 67

51K to 54K   out of 199.8K words

rantsewa sai na aiwatar"""

"""Da kuwa ka ci amanar 'yar madara"""

Ayshercool 08081012143

¦ 500 ne via 0009450228

Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne.

90009343

'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724

"Cikin hanzari ya kalli Nabila, yana mamakin a ina ta san wannan sunan, dan sam bai san Walid ya"

gaya mata labarin sa ba.

"Ya ™ureta da ido, ta kawar da kanta gefe, ta ce ""Eh, idan ka kashe ni, ka ci amanarta, ta barka ka kusa dawowa hanya, amma ka koma ruwa fiye da baya. Zan so na ji ™arshen labarinta, amma kafin nan bari na tafi yanzu, ga kayan dubiya nan na kawo maka, Allah ya ™ara sau™i"" sai da ta"

"gama maganar sannan ta Wago ta kalleshi, still ita yake kallo."

"Ta sake cewa ""Ina fatan zaka yafe mini laifin da nayi, rashin sani ne"" ta tashi a hankali ta Wauki jakarta ta fita, tana yi wa Allah godiya da wannan karon, ba ta sha sha™a ba, hakan ya sa ta ™ara"

kin ™warin gwiwar cigaba da gwagwarmayar da ™uduri aniya.

"Bayan fitar Nabila, Viper ya Waga kai yana kallonsu Waya bayan Waya, Walid ya ce ""Ko ba ka yi"

"magana ba, na san menene a ranka, ba kowa bane ba, ni ne nan na gaya mata labarinka""."

"Ya tsayar da idonsa a kan Walid ya ce ""Saboda me?"""

"""Saboda dalili mai ™arfi, cigaba da cusa kanta a lamuranka cikin duhun kai, tamkar ™ara yawan matsalolinka ne, zuciyar mace ta na da rauni, fiye da dukkaninmu, ina ganin hakan zai iya yi mana am..... Bai ™arasa ba, viper ya katse shi ya ce ""Ta yaya? Na ce ta yaya? Meye amfanin gaya matan, na gaya maka bana bu™atar cigaba da ganin yarinyar nan, sai an haWa baki da ita an ™ara rusa ni"

"kenan? Da raunin na su ake amfani a sarafasu a cuci mutum, halittu ne su marasa imani...."

"""Raunin 'ya mace, da tausayinta irin na halitta, kar ka manta shi ya jefa ka a cikin halin da ka ke ciki, idan mace Waya zuwa goma sun cutar da kai, Waya zuwa biyu sun yi maka abun da ba zaka taSa iya biyansu ba, wanda tausayi da soyayyar da mace ta nuna maka, giSin da ta bar maka ne, ya ™ara assasa tunzura zuciyarka ka ke fama da jinyar da muka rasa bakin zaren yi maka maganinta. Idan zaka yi adalci, ka yi musu hukunci da halin ™anwata, Jauhar ko ba dukkansu ba. Yarinyar nan gaskiya ta gaya maka, idan ka yi kisan kai ka ci amanarta, wannan miyagun ™wayoyin da ka"

"ke ™ara Wurawa kanka, su ma ba ka yi mata adalci ba""."

"Al'amin da ya ji maganganun Walid sun ishe shi, sai ya mi™e tsam ya sake ficewa."

Walid ya yi wa Šan mama inkiya ya bi bayan sa ya ga ina zai yi.

***

"Ramma ce take dukan gefen fion da Abdul yake ""Abdulyasar Abdul yasar"" ya buWe idonsa da kyar ya kalleta."

"""Ka tashi ka yi sallar asuba, gari yayi haske, sallar ma baka yi"" ya ja tsaki ya sake juyawa."

"Ta sake cewa ""Ka tashi gari fa yayi haske"""

"""Kin san jiya da daddare fa ban yi bacci ba, ki ™yaleni"""

"Ramma ta ce ""Haka ne kam, dama ba ka da lafiya, wata™ila a cikin baccin za a zare maka rai, ban sani ba ko kana da abun da zaka gaya wa Allah a kan rashin salla"" kan ta rufe baki ya tashi zaune"

yana ™ifta ido.

"Ta girgiza kai ta ce ""Kai yanzu baka shirya wa mutuwa ba, ka ke rashin mutunci? Allah sarki Wan"

"Adam abun tausayi"" ji yayi jikinsa yayi mugun sanyi, kamar mutuwar ce ke tunkaro shi, ya je ya yi alwala, ya fito ya tarar tana gyara gadon da ya tashi."

"Wayarsa ce ta fara ringing, ya tashi da sauri, ya Wauka, ya saka a kunnensa ""Hello mummy"""

"""Kana ina ne?"""

"Ya ce ""Ina gidana"""

"""To zuwa anjima ka zo gida, zaka yi magana da babanka, shugaban jam'iyya ya ce ka je ka ga 'yar"

"sa, ku daidaita kanku, ayi magana dan ba za su yadda a baka takara ba, baka da aure""."

"""Haba mummy, aure kuma? Ni wai dole ne auren nan, a ha™ura mana"""

"""Ban gane a ha™ura ba, waye zai yadda ka yi deputy governor ba ka da aure, lallai ka zo anjima ku"

"yi magana dama yana cewa ni nake hure maka kunne"""

"Abdul ya ce ""Ba ni da lafiya fa"""

"""Ka sha magani ka zo, ulcer ce?"""

"Ya ce ""Eh, kuma wallahi ina jin jiki, dan Allah ki bashi ha™uri zan zo ne"""

"Cikin damuwa ta ce ""Ko na turo a Waukko mini kai, ba na son ciwon cikin nan naka fa"""

"Ya kashingiWa ya ce ""A'a, zan warware, idan na ji sau™i zan zo, sai anjima zan Wan kwanta"" ya"

"ajiye wayar. Tun da ya fara wayar, ramma ta ™ura masa ido har ya gama."

"Ta ce ""Ka ga banbancin rayuwar mace da ta namiji ko? Kaga duk abun nan da ka ke yi, kai an"

"samo maka mata ni mecece makomata?"""

"Ya kalleta ya ce ""Kishi ki ke yi ne?"""

"""Allah ya rufa mini asiri, na rasa a kan wa zan yi kishi sai kai, ka wula™anta mini rayuwa ka cuce ni, kai ka yi aure ka tara iyali, ni kuma babu wanda zai kalleni, ka yi mini fyaWe ka mayar da ni ™"

"aramar karuwa, har ciki na Wauka duk ta ™azamar hanya ka wula™anta rayuwata"""

"Abdul ya zauna sosai ya ce ""Ke ki ka fara wula™anta rayuwarki, da ku ka yi yin™urin cewa zaku"

"nemi hakkinku a kotu, alhalin ba zaku iya ja da ni ba"""

"""Sannu tsohon azzalumi, dama mai kuWi shikaWai Allah ya ce ya ji daWi a duniya? Yanzu duk wannan abun ta™amarka kana da kuWi ni 'yar talakawa ce? In sha Allah sai Allah ya ™as™antaka da kai da masu goya maka baya, suka tsaya maka kake rashin mutunci. Na san akwai ire-irena da yawa yaran talakawa da kuka zalunta, Allah ya na kallonku. In sha Allah sai Allah ya nuna maka"

"iyakarka tun a duniya Abdul yasar"""

"Duk da ya ji zafin maganganunta amma sai cewa yayi ""Ko wanda ya raWa mini sunan nan, bai kai"

"ki iya faWar sunan ba Rahama, Abdul yassar"""

"Kallonsa tayi tana kuka, haushin kanta yakamata da lokacin da yake waya, ba ta yi ihu a wayar ta ce a taimaka mata ba sace ta yayi. Yanzu ko wayarsa ta Wauka ba zata iya operating Win ta ba,"

kuma ba ta da lambar wanda ta haddace balle ta kira.

***

"Abba yana zaune yana kallon labarai a Aljazeera, Nabila ta shiga da sallama, yana kashingiWe, ya tashi zaune yana murmushi ya ce ""Barrister, kin yi mini wuyar gani da yawa fa, kullum na dawo kina aiki, baki dawo ba aiki ya hana mini arfana sukuni"""

"Tayi murmushi ta ce ""Abba ni kaina ina kewarka, bana samun zama, yanzu na shiryu ai, ina aiki"

"sosai da sosai, na san addu'a ka ke yi mini"""

"Ya ce ""Kullum Addu'ata a kanku take, mussaman ke arfana, Allah ya yi miki jagora a dukkan"

"lamuranki""."

"""Eh mu ma Allah ba zai tagayyara namu ba"" Umma tayi maganar tana harar Nabila."

"Nabila ko a jikinta ta ce ""Abba dan Allah abu na zo ro™onka"""

"Ya ce ""Ina jinki ´ar albarka"""

"""Abba dan Allah mota nake so, wallahi wahala nake sha samun napep, ayi ta haWani da maza, ga zirga-zirga na yi ta kashe kuWin mota, kuma haryanzu ni ba na yi wa client Wina charges mai"

"yawa"""

"Yayi dariya ya ce ""Nawa ki ka tara?"""

"Tayi shiru sannan ta ce ""Ina da 400k"""

"Ya kwashe da dariya ya ce ""400k, sai dai a gyara miki tsohuwar honda ta"""

"Cikin shagwaSa ta ce ""Haba Abba, big girl kamar ni, da tsohuwar mota, ka taimaka Please"""

"""Babu komai, za a sai mota in sha Allah, amma da sharaWi ba na son yawon babu gaira babu dalili,"

"kuma ke zaki din ga zuba manki, ba zan sai mota na din ga cacar mai ba"""

"Cikin takaici Umma ta ce ""Major mu fa? Muna zaune zaka saya wa Arfa mota, wannan wane irin"

"rashin adalci ne?"""

"Ya kalleta ya ce ""Da walida zan saya wa mota, ba zaki faWi haka ba, ku fa da me? Ga mota nan ana kai ku unguwa a ciki, meye na kishi da 'yar cikinku? Ku daina haWa kanku da ita, kun san abun da"

"nake nufi""."

"Arfa ta tashi ta ce ""Abba sai da safe"" ta juya zata fita, ta yi wa Umma gwalo, a ranta ta ce ""Saura"

"ma babar su DSP idan ta ji, sai dai ku mutu""."

"Ta koma bedroom Win ta tana murna, ta Wauki wayarta, Viper ya faWo mata a rai."

"Lambarsa da ta saka a wayarta, ta lalubo, ta zubawa ido, murmushi ta yi, ta kira lambar ta saka a"

kunnenta.

"Yana zaune a kan katifa, yana ta shan sigari, zubawa lambar ido yayi, ya gaji ya ajiye wayar, ya"

"cigaba da abun da yake gabansa. Ba ta gaji ba ta din ga kiransa babu ™a™™autawa, har sai da ya hasala, ya Waga wayar, amma bai yi magana ba."

"""Har na kusa fushi sannan ka Waga, na san da 'yar madara ce, ko ba ta san mai lambar ba, zata W aga kuma za ta saurareni, haka zalika zata yafe mini laifin da na yi mata. Akwai abubuwan koyi sosai da sosai a rayuwar ta, da ya ci ace ko ba duka ba, ka yi koyi da wasu, ba ta wula™anta Wan Adam da tana yi, da ba ta ri™e ka da amana da tausayawa ba. Ina sake ro™onka yafiya, da kuma fatan samun haWin kanka, ka ™arasa mini labarinka da kanka, ina sha'awar kasancewa wani S angare na labarin nan, mai ban tausayi da ratsa zuciya Viper, sai da safe"" tun da ta fara maganar, ya sunkuyar da kai, ya saki sigarin da take hannunsa, ya sunkuyar da kai hannunsa yana rawa. Ta"

"gama maganar ta katse wayar, amma ya kasa ajiye wayar."

"Sai da liti ya dafa shi ya ce ""Maza yane?"" Ya Wago idanunsa ya kalli liti."

"""Kamar Muryar wannan shegiyar yarinyar na jiyo a wayar, duk Walid ne da wannan sheWancin"""

"Ya cigaba da ™urawa Liti ido, babu abun da yake fata, banda ya zubar da hawaye ko na mintuna"

"biyar ne, amma ko na sakan Waya ya kasa tsawon shekarun nan."

"Murya a sanyaye ya ce ""Liti"""

"""Na'am mai zamani""."

"""Ina kewar jauhar sosai"""

"Walid da da yayi musu shiru, dan ya lura daga Viper har liti haushin sa suke ji, amma maganar da"

"Viper yayi yanzu ta sanya jikinsa ya yi sanyi, tausayin Viper ya ™ara kama shi."

"""Da yanzu yarona ya isa shiga makaranta, wata™ila ma ta kuma haifa mini wasu"""

"Walid ya taso, ya dawo gaban Al'amin, ya ri™e hannunsa ya ce ""Ka ™ara ha™uri mai zamani""."

"""Zuwa yaushe? Ko na Wauki fansa kamar yadda nake buri da fata, kashe kaina zan yi saboda ba ni"

"da wata makoma, idan kuwa hakan ba zai samu ba, zan koma in da na fito na ™arasa rayuwata""."

"""Dan Allah maza ka daina irin wannan maganganun, kana karya mana zuciya wallahi "" liti yayi"

maganar cikin damuwa.

"Viper ya girgiza kai ya ce ""Ba zaka gane ba"""

"Kawai ya gyara ya kwanta, gaba Waya suka kewaye shi suna kallonsa."

"Nabila kuwa kallon wayar ta cigaba da yi, ta ce ""Allah ya bani nasara a kanka, ya bani ikon"

"taimaka maka""."

"Kira ne ya shigo wayarta, ta Waga ta saka a kunnenta, ta yi sallama."

"""Wa'alaikum Salam da 'yar ™walisa""."

"""Wa ke magana?"""

"Yayi murmushi ya ce ""Bawan Allah ne"""

"""To, ai kowa ma bawan Allah ne, wanne daga ciki?"""

"Yayi gyaran murya ya ce ""Wani case ne da ni, nake so a taimaka mini"""

"Nabila ta yi hamma ta ce ""Office zaka zo, ba ta waya ba"" ta katse kiran, dan a zatonta irin samarin"

"nan, ne masu kiran wayar mata anyhow, duk da Muryar wannan ba ta yaro ba ce."

"Wani nannauyan bacci, yayi awon gaba da ita wanda babu abun da take yi ban da mafarkin Viper,"

dan sai da ta kusa makara yau.

"Kwanaki uku da zuwanta wurin su Viper, ba ta sake zuwa ba, she's very busy, tana ta off and down"

"na tattara hujjoji, duk da ana ta taWiyeta, duk in da za ta bi ta samo shaida, sai a rufe, sai da aka aike da dattijon nan gidan kaso."

Gashi sai tayi ta sintiri a hanata ganinsa.

"Kamar uba da Wa haka Walid yake ta lallaSa Viper ya ci abinci, sai dai ya cakala ya bari, ba ya cin"

abinci.

"Private numbrn nan da ake kiransa da ita ce, ta kira shi, wayar tana ta ringing liti ya ce ""Maza ka"

"Waga mana"""

"""Me zan ce?"""

"Walid ya ce ""Ko ba ka da abun cewa, ka Waga kawai"""

"Ganin ba shi da niyyar Wagawar, ya sanya Walid ya Waga ya sakata a hansfree."

"""Aminu Viper, kwana biyu. Ashe ta dawo maka da wayar. Alamu sun nuna kwana biyu ka yi sanyi,"

"Kodayake kai sai an sakankance ka ke Sarna. GargaWi nake sake yi maka, ka nesanta yarinyar nan da ga gareka, za a iya cutar da kai ta hanyarta""."

"""Ni nake da ikon yanke hukuncin abun da yake daidai da rayuwata, babu wanda ya isa ya juya mini rayuwa yadda nake so, ka cigaba da Suya ko ka bayyana kanka, zan yi abun da nake ganin"

shi ne dai-dai da rayuwata.

"Mutumin yayi murmushi ya ce ""Aminu Viper, shikenan idan ka ™i ji, ba zaka ™i gani ba ai"""

"""Babu abun da ban gani ba, dan haka na shirya ganin koma menene"" ya katse wayar."

"Liti ya ce ""Duk walid ne ya janyo komai, ni na san a rina, wannan yarinyar idonta kawai zaka"

"kalla ka gane munafuka ce"""

"Kallon da Viper yayi masa ne, ya sanya shi yin shiru, Walid yayi dariya ya ce ""Ayi dai mu gani, za"

"a gane waye mai gaskiya tsakanina da ku""."

"Liti ya ce ""Ba wata gaskiya da ka ke da ita, ka dakatar da mu daga making moves, wallahi mun"

"kusa fita operation kwanan nan"""

"""Ku fita ya™i ma ba operation ba"""

Haka liti da Walid suka kusa yin faWa.

"Tun ana gobe Nabila zata je wurin Naja'atu Bunkure, suke waya da sumayya, take bata ™warin"

"gwiwa, a kan za ta iya, kar ta ji tsoro."

"Da safe sai da ta fara zuwa wurin aikinsu, ta samu barrister Habib, shi ma ya ™ara mata ™warin"

"gwiwa, da yi mata fatan alkhairi."

"Cikin ™asaita take fiya a farfajiyar office Win, har ta ™arasa, mutane ta tarar jingim. Wanda"

"galibin su mata ne, suna jiran shiga wurin Barrister Naja'atu Bunkure."

"Kai tsaye Nabila ta shiga wurin sakatariyarta, ta nuna mata ID card Win ta, nan da nan ta bawa"

"Nabila wurin zama, na ciki na fitowa ta yi mata iso zuwa wurin Barrister Naja'atu."

"Tun a hanya take maimaita ""la hula wala ™uwwata illa billa"". Har ta shiga wurin Bunkure."

"Tayi sallama, ba tare da ta Wago ta kalli Nabila ba ta amsa mata, ta ™arasa ta zauna ba tare da an"

yi mata umarnin hakan ba.

"Kayan jikin Nabila kawai ta kalla, ta fuskanci ba kalar gajiyayyun da suke zuwa wurinta bane ba."

Ta gyara zaman gilashin fuskarta ta na kallon Nabila.

"""Sannu da aiki ma"" Nabila tayi maganar tana murmushi."

"""Yauwwa sannu"""

"Nabila ta Waga mata id card Win ta ta ce ""I am barrister Nabila Yusuf maitama"""

"Bunkure ta jinjina kai ta ce ""You look familiar to me"""

"Nabila ta jinjina kai ta ce ""Na yi mamaki ma, da ki ka iya tuna kamar kin sanni, saboda na san"

"jama'ar ne da yawa. Ni abun da ki ka yi mini ba zan taSa mantawa ba har abada"""

"Bunkure ta ce ""Ohh really"""

"""Yeah and i have a promise to fulfil, a dalilin abun da ki ka yi mini"""

"Ta kashingiWa da jikin kujerarta ta ce ""That's very good, ina son mutane masu yarda da kansu, ba"

"na bu™atar sanin me nayi miki, ko kuma wani alwashi ki ka yi ba, ga ki ga bunkure Allah ya ida nufi """

"Nabila ta ce ""Na ji daWi da ki ka ce Allah, dan kuwa shi ne gaba da komai, na gode sosai barrister"""

"""Mentioned not"""

"Nabila ta gyara zamanta ta ce ""Yauwwa, ba komai ne ya kawo ni ba, na zo ne a kan wani case, duk"

"da ba mu haWu a court ba, an kai wanda nake depending prison, amma ban ganki a court ba sai wakilanki"""

"Bunkure ta ™arewa Nabila kallo, sannan ta ce ""Wane case ki ke magana a kai?"""

"""Yarinya da aka yi wa fyaWe, ki ka ce kin tsaya mata, ni ce lawyer wanda ake ™ara, na je wurin"

"'yan sanda ana ta yi mini yawo da hankali, ina son doctors report, kuma ina son zan ga yarinyar zan yi magana da ita""."

"Naja ta yi wa Nabila kallon baki da hankali sannan ta ce ""Kin san a gaban wa ki ke?"""

"""I am barrister Nabila, ba ruwana da a gaban wa nake, ina neman hujja ne da zan kare client Wina"""

"""Nawa suka baki, ki ka samu ™warin gwiwar yin wannan kasadar? Zan ninka miki, ki ajiye case"

"Win, kafin ki kunyata a idon duniya """

"""Watch your words, it can be use against you a kotu, kin san me nake nufi, you are also a lawyer"""

"""Who the hell are you?"" Bunkure ta yi maganar tana tashi tsaye, Nabila ma ta tashi tana sake Waga mata id card Win ta ""Sai da na fara gabatar miki da kaina, sannan na gaya miki meya kawo ni."

"Ko dai ki bani abun da nake bu™ata kawai, ko kuma na fasawa duniya wacece ke?"""

"""Ni Win? Yaushe ki ka yi grduating, da me ki ke ta™ama ki ke jin

18 / 67