Karfe a Wuta Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   63 / 67

186K to 189K   out of 199.8K words

su a gaSar tekun italy. Kamar yadda nayi maka aike na farko, ina tare da Simon kuma shi ya bani wannan sa™on naka""."

"Jiki na rawa ya buWe videon, shi ne a cikin videon, yana ta kokowa da Nura guduma, wasu irin ™"

"arti majiya ™arfin gaske, suka ri™e Nura, yana kururuwa yana ™o™arin ™watar kansa, amma abu ya gagara, kuma ba iya fuskar Indabo ba ce a videon, har da wasu daga cikin manya a ™asa."

"Da ™yar Indabo ya iya Waga ido, ya kalli Abdul, ya haWiye wani irin abu mai yaji da Waci, ya kasa"

"magana. Abdul kuma ya ™ure shi da ido, yana jiran ya ji mai indabon zai ce."

"Mahaifiyar Abdul tayi shiru, suka yi tsuru-tsuru."

"""Na tabattar ba sharri aka yi maka ba, kai ne a jikin videon nan, naga baka buWe sauran audios Win ba, amma ya tabattar da cewa, mutum goma ne suke da videon, muddin ka cigaba da takura musu, sai sun sake shi a duniya, kuma sai an Wauki mummunan mataki a kanka, babban takaicina me zan cewa rahama, yarinyar da nake nema ta yafe mini, ashe akwai babban aiki a gabana jawur, kai kayi silar mutuwar Wan uwanta, tayaya mahaifiyarta zata yafe mini ta bari na cigaba da rayuwa da"

"ita?"""

"""Abdul ka cigaba da rayuwa da wa? Tona wa mahaifinka asiri zaka yi? Satin bikinka ya kama"

"kana nufin zaka yi aure kuma ka ajiye karuwa?"""

"""Rahama ba karuwa ba ce, aurenta nake yi, kuma yau zan tattara na bar garin nan da ita, da"

"wannan abun kunyar da ka aikata"""

"Indabo ya ce ""Aurenta ka ke yi kamar yaya?"""

SOME MONTHS BACK.

"Abdul ne ya shigo, ya tarar da rahama a rakuSe, a jikin gado, idanu duk sun kumbura saboda kuka."

"""Wai ba zaki raba kanki da wannan kukan ba? Aikuwa kina tare da wahala, dan kuwa yanzu ki ka"

"fara, tashi ga abinci"""

"Ta Wago ta kalleshi ta ce ""Ba na ci, ka ™yale ni na mutu, ai tun farko cewa kayi zaka kashe ni, menene na ajiye ni kana tozarta rayuwata, saboda kawai ina 'yar talaka? Talauci ne ya saka na fita aikatau, da burin yin karatu, mahaifiyata ba zata iya Waukar Wawainiyata ba, ban da haka killace ni zata yi a tare da ita, ba zata bari ma ka ganni ba balle ka keta mini haddi"" ta yi kneel down ta ce"

"""Dan girman Allah ka kasheni na huta"""

"""Ke naji, kin cika mini kunne da koke-koke, zan mayar da ke"""

"Ta girgiza kai ta ce ""Ko ka mayar da ni, ba zan yi daraja ba, abar ™yama zan zama, kawai ka"

"kashe ni, ka kaiwa mama gawata dan Allah"""

"Abdul ya zauna a kusa da ita ya ce ""Ya isa haka kukan, ki ci abinci zan san abun yi"" kwanaki biyu, tana jiran ya kashe ta, ko ya mayar da ita amma shiru, gashi tun da tayi Sarin nan, da ya zo mata"

"zata fara kuka kamar ranta zai fita, tana yi masa magiyar ya daina wula™anta mata rayuwa."

"Cikin marairaicewa ta same shi, ta dur™usa a ™asa ta ce ""Ka ce zaka mayar da ni gida, kuma baka"

"mayar da ni ba"""

"""Rahama ba zan iya mayar da ke ba, zan ta tunaninki ne, kawai na ji ina damuwa da ke, ki ha™ura"

"kawai"" cikin kuka ta ™are masa zagi, amma ko a jikinsa."

"Washegari ya Wauki Salim, ko saifu bai gaya wa ba, suka tafi gidan su ramma."

"Mahaifiyar ramma na ganin Abdul, ta tashi cikin ™arfin hali ta ce ""Ina ka kai mini 'ya ta? Ka dawo"

"mini da 'ya ta"""

"Abdul ya ce ""Mama masalaha na zo muyi, Sarna an riga an yi ta, dan Allah ki yi ha™uri ki bar"

"mini ramma, ki bani aurenta"" Sai da Salim ya kalle shi, dan bai san abun da zai ce kenan ba."

"""Allah ya tsare, cuta ka riga ka gama cutar da mu, kai da Allah, amma ka dawo mini da 'ya ta"""

"Ya girgiza kai ya ce ""Kar mu yi haka, a rufa wa juna asiri, kun Wauki aure da muhimmanci sosai,"

"ta ce babu lallai tayi daraja, ™yamarta za a din ga yi, dan haka ki yi ha™uri dan Allah, ki aura mini ita"""

"""Wallahi ba zan taSa aura maka ita ba, gara ayi ta tsangwamarmu, zan ri™a a bata na kula da ita,"

"kuma zan cigaba da nema mata hakkinta, har zuwa ™arshen numfashina"""

"Ya mi™e ya ce ""Shikenan, tana gaishe ki, ki kwantar da hankalinki, tana cikin ™oshin lafiya"" ya"

"ajiye mata kuWi suka fice, ta bishi tana ya zo ya karSi kuWinsa amma yayi mata banza suka tafi."

"Salim ya din ga yi masa masifa a mota ""Amma dai baka da hankali ko? Ka yi wa yarinyar fyaWe, mu zo gaban babarta mu yi rashin mutunci, kuma mu dawo ka ce zaka aureta, wai ma ka gaya wa"

"su daddy ne?"""

"Abdul ya girgiza kai ya ce ""A'a, yarinyar ce take bani tausayi irin sosai Win nan, virginity is very"

"important to woman's, i took it away just like that, she's very young and innocent, ina jin babu daW i, na san yadda zan Sullowa lamarin"""

"Tare da Salim suka cigaba da shige da fice, suka samo wani wan baban ramma, Abdul ya dan™ara masa kuWi, babar ramma bata sani ba, aka Waura musu aure, sai bayan an Waura ya je ya din ga yi wa babar ramma masifa, wai Allah zai rufa wa ramma asiri, amma tana ™o™arin tonewa, da ta samu ma mai kuWi da kyau kamar wannan ya saurari yar ta ta, a wurin Wan birni kamar Abdul ai"

ramma a bar ™yama ce.

"Cikin kuka ta ce ""Wallahi balarabe ba zai yiwu ba, ban san wani zancen aurar da ramma ba,"

"lokacin da nake wahala ta da ya ta da me ka taimake ni, ina har gonar su ta gado ka cinye""."

"""Oho miki, koma menene rashin iya takaucinki, da son abun duniya ya sanya ki ka kaita aikatau"" da kansa ya shiga ya kwaso wa Abdul kayan ramma, ya sake ba wa babar ramma kuWi, ya Wauki"

kaya suka tafi.

"Suna tafe Salim ya ce ""Ranar da asirinka ya tonu ban sanka ba wallahi, ko kuma ka gama abun da"

"zaka yi, salin alin ka sakar musu 'ya"""

"Abdul ya ce ""Ban aureta dan na saketa ba, sai dai ayi wadda za ayi"""

"Ya je ya samu ramma, ya kai mata kayanta, da goro da alawa ya ce ""Gashi nan, hankalinki ya"

"kwanta an Waura mana aure yau"" cikin mamaki ta kalleshi ta ce ""Aure kuma kamar yaya?"""

"""Ba damuwarki kenan ba? Ke ba zaki auru ba? To an Waura yau, yayan babanki wai malam bala,"

"shi ne ya Waura mana aure"""

"""Wane irin aure ne babu istibura'i? Cewa nayi ina sonka ne ma?"""

"Ya ce ""Meye istibura'i?"""

"""Sai nayi jini uku a addinance, dan tsaftace mahaifata kan ka aureni, tun da zina kayi da ni, kuma"

"ni bana sonka""."

"Abdul ya kalleta ya ce ""Allah ya nuna mana wata ukun, kuma ni ina sonki ai, Shikenan an wuce"

"wurin""."

"Ramma tayi kuka a kan wannan wula™anci da Abdul yayi mata, da nuna mata tsantsar isa da gadara, ta fara yi masa misbehaving ta daina tsoronsa, amma ko a jikinsa, sai dai zamansu tare ta gane yana da wasu Wabi'u na tausayi da sau™in kai, rashin tarbiyya da ilimin addini ne kawai yake"

"Wawainiya da shi, bai sake nemanta ba, sai da ta cika watanni uku, kamar yadda ta bu™ata."

"Idan tana yi masa masifar ba dan Allah ya aure ta ba, ya kan ce mata ""Ba dan ina sonki ba, babu dalilin da zai sanya na zauna da ke watanni uku ina kallonki, kina gindaya mini sharuWa ina ™yale"

"ki""."

****

"Mahaifiyar Abdul ta ce ""Aure ka yi bamu sani ba Abdul, rashin muhimmancin namu har ya kai haka?"""

"Ya kalleta ya ce ""Ko zan mutu ba zaku yadda ku aura mini rahama ba, zaku yi i™irarin yar talakawa ce, ba tare da la'akari da Sarnar da na akata mata ba. Kuma sakawa zaka yi a kasheta, sannan mutumin nan da ka saka aka kashe, ba ruwana babu saka hannuna a ciki. Zan Wauki matata mu bar garin nan, dan Allah kar ka neme ni, takara kuma ka bawa wani, ba zan iya ba"" ya Wauke"

"wayarsa, mahaifiyarsa ta bishi tana ™wala masa kira, amma yayi waje."

***

"Viper ne ya shigo Wakin da Nabila take, tana zaune ya shigo da waya a kunnensa ya ce ""Eh na je wani wuri ne, Wan mama ya dawo gidan nan ne, ya gudu na neme shi na rasa, ya kuma kashe wayarsa"""

"Walid ya ce ""A'a bai dawo ba, ko laifi yayi maka ka ce zaka hukunta shi?"""

"Yayi murmushi ya ce ""Laifi yayi, kuma duk in da ya shiga zan nemo shi, zamu gauraya da ni da"

"shi""ya katse wayar ya ™arasa gefen Nabilaya zauna."

"""Vi"""

"""Mmm"""

"""Wai dan Allah ina ne nan? Ina son na tafi gida ne"""

"""Ai ba zaki koma gida ba, kin zo kenan"""

"Dariya tayi, dan ta zata da wasa yake yi."

"""Daga fitarka ka sha sigari ko?"""

"""Eh"""

"Nabila ta ce ""Au eh, baka jin kunya wai ka amsa ka tsaye, sai ™auri ka ke yi, ba na son ™aurin"

"abar nan ko kaWan wallahi"""

"Ya tsura mata ido, ya girgiza kai ya ce ""You can't be her"""

"""Who?"""

"Ya lan™wasa ™afarsa Waya a kan gadon ya ce ""Jauhar, ba ta taSa nuna warin sigarina da wiwi yana damunta ba, sai dai ta ce ; Master kar a sha da yawa, dan Allah a sha kaWan, idan nayi shaye-shaye na dawo, ta bani ruwan wanka, ta bani wankakkun kaya, ta fesa mini turare, sai daga baya na fahimci, warin wiwi ne ba ta so, amma bata taSa yi mini complain ba. Yanzu bana iya shan komai, na yadda ™wa™walwata da lafiyata suna da amfani, ko dan ganin bayan wanda suka cutar da mu."

"Ke kuwa masifaffiya ce, always angry, ki ka gaya mini ina ™aurin taba"""

"""Sai na zama irin ta zaka so ni? Gaskiya ba zan iya shiru ba, ni kawai ka daina gaba Waya"""

"Viper ya ce ""Ai babu wannan maganar tsakanina da ke, na gaya miki ki daina wahalar da kanki"""

ya yi maganar yana mi™a mata wayarta.

"KarSa ta yi tana hararsa ta ga sunan sumayya ta ce ""Ba zan Waga ba"""

"""No, ki Waga baki san me za ta ce miki ba"""

"Ta Waga ta saka a kunnenta ta ce ""Ina jinki"""

"""Nabila kina ina ne?"""

"""Menene?"""

"""Kawai malama kina ina?"""

"""Ki gaya mini meyafaru? Nayi nisa ne"""

"Sumayya ta ce ""Mahaifin Viper, ya zo gidan radionmu, ya ce yana son zai yi magana da ke, na ce"

"masa zan haWaku, zan yi miki magana"""

"Nabila ta ce ""Are you serious dan Allah da gaske?"""

"""Wallahi da gaske nake yi miki"""

"""Shikenan, in sha Allah zuwa gobe in Allah ya kaimu, zan zo zamu haWu, kin karSi lambarsa?"""

"""Eh na karSa"""

"""Shikenan in sha Allah zan zo"" ta katse wayar, ta ga wani irin kallo da yake yi mata."

"""Vi snake, menene? Abunka ne ya zo yana nemana, wata™ila....."

"""Silent. Kar ki kuskura ki fara, ke gaba Waya baki da lissafi, idan wani trap Win ne fa?"" Yayi"

maganar cikin hargowa.

"""Bari na zama kamar jauhar, ba zan biye maka ba ai yanzu, hukuma sai da rarrashi, hadari malafar duniya. Tsakanin Wa da mahaifi sai Allah. Nifa duk da ina da labarin abun da babanna yayi wa mahaifiyata, fata nake yi na ganshi, haka zaka cigaba da rayuwa ba dangi, kaikaWai sai su oga"

"Walid, sai kuma Ni"" ta yi maganar tana murmushi."

"""Ka bari mu haWu da Abbu dan Allah, na san maybe nemanka yake yi, so yake ya ganka, haba sweetheart, namijin duniya, kar ka saka muyi babu, kai ba uba nima haka, kayi ha™uri dan Allah, ka manta da komai My Vi. Magana fa nake yi an yi mini shiru, talk mana, ko sarautar ce ta motsa?"

"Master magana nake"" tsigar jikinsa ta mimmi™e ya juya yana kallonta."

"""Ban taSa kallon wani abu na ji ina son shi ba, sai kai Vi, duk a dalilinka na rasa ajina da jin kai na 'ya mace. Gashi ka yi ta hantarata, baka tausayina ko kaWan."

"Šan nuna mini hoton 'yar madara mana, ko sau Waya ne"""

"""Hotonta mai tsada ne, yarinya mai ha™uri da aji"""

"""Ni kuma masifaffiya mara aji, daga nan kuma sai me?"" Ya fuskanci kawai kunna shi take yi."

"Ya ajiye mata wata leda, ya ce ""Gashi nan, abinci ne, za a kawo miki kaya"""

"""A'a nifa ban gane ba, gida fa?"""

"Ya mi™e tsaye ya ce ""Ba sa bu™atar ki, na fi su bu™atar ki a yanzu, muddin wani abu ya sameki, ni"

"aka ji™awa aiki"""

"Nabila ta ce ""Ban gane ba, garkuwa zaka yi da ni?"""

"""Na ma yi"" yayi maganar tare da ficewa."

****

"Hanklin can gidan su Nabila ya tashi, bayan an shafe kwana na biyu, ba a san in da take ba, Abba ya maze kamar ko a jikinsa, amma hankalinsa a matu™ar tashe yake. Nasir ma ya din ga up and down, haka ma sumayya dan sai da ta gaya wa Kankarofi an nemi Nabila an rasa."

"Ta gaya wa Nasir cewa, ranar da ta Sata sun yi waya, bayan la'asar kuma da alama tana cikin ™"

oshin lafiya.

"Nasir ya ce ""Abu ne mawuyaci ace barin gidan nan tayi, wata™ila mutanen da take addabawa ne"

"suka sace ta"""

"Aka din ga kiran wayarta, amma a kashe."

"Kwana na uku, Nasir ya kira wayarta, ta shiga, amma ba a Wagawa."

"Dan haka ya saka layin a tracker, ya fara tracking in da wayar take, sai dai ga mamakinsa, wayar"

tana cikin garin kano.

****

"Abdul tamkar zai haukace, duk wani lungu da sa™o na gidan ya duba, amma bai ga ramma ba, ya dudduba ko ina da ina, amma bai ganta ba. Ya kira wayarta amma a kashe."

"Taka jikinsa ya hau tsuma, ya tabattar da cewa Indabo ne ya saka aka Wauke ta, jikinsa na rawa ya"

"Waukko mota ya fito, tare da sakawa a ransa komai zai faru sai dai ya faru, amma sai indabo ya fito masa da matarsa, ko kuma shi da kansa ya tona musu asiri kowa ya huta."

****

"Nasir yayi mamakin sur™u™in wurin da yake indicating in da wayar Nabila take, da shi da abokan aikinsa, ™arshe ajiye motar suka yi, suka din ga shiga wurin da ™afa, suna cigaba da dubawa."

"A tsaye suka tarar da shi ya juya baya, haya™i yana tashi."

"Nasir ya ce ""Malam waye kai?"""

"Sai da ya ja sakanni, sannan ya juyo a hankali, hannunsa Waya da wayar Nabila, Waya kuma ri™e"

"da sigarinsa, gaban rigarsa Wauke da sunansa Viper da hoton maciji a jiki."

"""Al'amin Viper, ko ka ce mai zamani"""

Ayshercool 08081012143

¦ 500 ne via 0009450228

Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne.

90009343

'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

https://whatsapp.com/channel/0029Va9QtrY4dTnBYG1hST2VHADARIN

*BRIGHT PENS SECOND BATCH*

"Ku kasance da littatafan bright pens, second batch."

*˜ARFE A WUTA (AYSHERCOOL)*

*MUTALLAB (NIMCYLUV)*

HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)*

*ZAYTOON (ZEE KUMURYA

"Cikin matsanancin mamaki, Nasir ya cigaba da takawa zuwa gaban Viper, ya Wan bayar da tazara"

tsakaninsa da shi.

"Nasir ya ce ""Dama kai ne Vipern?"""

"Ya Wan kaWa kai ya ce ""Ni ne Viper, abun mamaki ko? HaWuwar mu biyu, amma baka san ni ne ba, haryanzu ina mamakin wane irin aiki jami'an tsaron ™asarmu su ke yi, kodayeke ™ulafucin cin hanci ne yake rufewa galibinku idanu, ku danne masu gaskiyar cikinku, ko ku sauya musu ra'ayi"

"domin neman mafitarku kawai"""

"Nasir ya ™are masa kallo ya ce ""Ina 'yar uwata take? Ina Nabila?"""

"Viper ya jujjya wayar Nabila sannan ya Wagawa Nasir ita ya ce ""Baka bu™atar yi mini wannan"

"tambayar, tun da ka samu wayarta a hannuna"""

"""Tana ina?"""

"""Tana wurina ™ar™ashin kulawata, na fiku bu™atar ta, ina bu™atar ganinta a raye domin nayi"

"surviving, dan haka za ta cigaba da zama a ™ar™ashin kulawata, har zuwa lokacin da ya dace"""

"A fusace Nasir ya ce ""A matsayinka nawa, am arresting you, ba zan bar wurin nan ba, sai na kama"

"ka"""

"Viper ya kalle su gaba Waya 'yan sandan su biyar Win ya ce ""Bisa wace dokar? Ko bisa umarnin indabo da ka karSar wa kuWi, zaka kama ni?. Viper ya zaro takarda a aljihunsa ya ce ""Na sami wannan takardar yau da safe, kai ma kuma ka je ka bincika, kotu ta hana hukumar 'yan sanda da kowace hukuma kama ni, har sai an kammala bincike, dan haka ba ka da wannan ikon, hannunka bashi da ™warin Waukar ™arfen cikin wannan wutar, ba zaka jure ba, muddin ka taSa kuwa, zaka"

"yi ™unar da zata yi dalilin rabaka da hannun"""

"Nasir ya fizgi takardar hannun Viper, jikinsa na rawa, ya hau karantawa, tabbas Viper da gaske"

"yake, kotu ta bayar da umarnin hana kama shi."

"Nasir ya ri™e takardar, ya zaro bindiga a jikinsa, ya ce ""Idan kuma na kashe ka a wurin nan fa, waye ya sani?"""

"Viper ya nuna masa mutanen bayansa ya ce ""Ku 'yan sanda ai ba dukkanku ne masu amana ba, wane tabbaci ka ke da shi cewa mutane huWun nan na bayanka, ba zasu tona maka asiri cewa ka kashe ni ba? Beside kana sakin bullet Win bindigar ka, kaima

63 / 67