Karfe a Wuta Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   5 / 67

12K to 15K   out of 199.8K words

zuwar mata, sayen kayan beads da stone work."

"Ta dafa abinci ta bashi, duk da yaron mijinta ne, kuma tana aikensa, hakan bai hanata girmama shi"

"ba, da yi masa nasiha wasu lokutan."

"Ganin shi ne sila, a oarin hana shi illata lafiyar sa da Al'amin yayi tsautsayi ya faWa kanta, ya"

"sanya ya koma gefe yana kuka, saboda ya firgita da yanayin da ya ganta kamar gawa."

Al'amin cikin tsawa ya ce masa ya fita ya bashi wuri.

Nura ya fita wajen Wakin ya tsaya cikin damuwa.

"Al'amin ya je gida, ya bar jauhar da wasila, ya je ya yi wanka, ya Waukko mata kayan da za a"

canza mata.

"Sai bayan sallar magariba ya dawo, ya tarar da Baba tare da mama Anty zakiyya da kuma saifu a"

"Wakin, wasi ta goge mata jikinta, da taimakon Nurses ta saka mata kaya."

"Tsayawa yayi yana kallonsu, yana tunanin ma a ina ya san su."

"Sai daga baya, ya tuna Baba, ya durusa ya gaishe shi, ya amsa masa tare da faWin ya mai jiki."

"Ya amsa da ""Da saui"" yana tunanin me Walid ya je ya gaya musu."

"Baba ya ce ""Meyafaru ne? Wani ya je ya ce mana abokinka ne shi, wai ka turo shi an kwantar da"

"jauhar a asibiti, hankalinmu duk ya tashi"""

"Al'amin ya ce ""ari ta yi"""

"Anty ta ce ""Amma shi ne aka je aka Waga mana hankali, ni wallahi na zata wani abun ne ya same"

"ta ma""."

"Mama ta ce ""Duk da haka, tun da aka kai ga arin jini tana jin jiki, Allah ya sa ba wani abun ne ya"

"faru ba tayi Sarin"""

"Al'amin bai ce komai ba, ya ajiye kayan hannun sa, dai-dai lokacin Jauhar tayi wani yinuri zata"

"faWo daga kan gadon tana kiran ""Master kana ina?"""

"Cikin hanzari ya arasa gaban gadon, suna rige-rige da shi da Saifu."

"Yayi hanzarin rie ta ya ce ""Zahra"""

"""Master"""

"""Na'am sannu"""

"""Meyasame ni ne? Kaina fa zai tarwatse ciwo master"""

"Babu kunya ya rungumeta ya ce ""Zai daina, ki daina Waga muryarki"""

"Cikin kuka ta ce ""Master bana gani, duhu nake gani bana ganinka"" tayi maganar tana tittirza "

afarta a kan gadon.

"Ya ce ""Zaki ganni in sha Allah, ki daina magana"""

"Al'amin ko a jikinsa, ya ttatara hankalinsa a kanta, Baba ya ce ""Waliyiyya, sannu kin ji"""

"Ta ce ""Baba"""

"""Na'am jauhar"""

"""Baba kai ne ka zo bana ganinku, duhu nake gani, makancewa na yi?"""

"Saifu ya ce ""Baki makance ba, bacci ki ke ji, ki yi shiru"""

"""Yaya saifu, bana gani fa"""

"Saifu ya ce ""Bacci ki ke ji ne"""

"Cikin fita hayyaci ta aname Al'amin ta sake cewa ""Master"""

"""Na'am madarata"""

"""Kaina zai fashe, ka rie mini shi da arfi, marata ma ciwo take yi mini sosai"" tayi maganar"

numfashinta yana fita sama-sama.

"Yayi asa da muryarsa yana yi mata raWa ya ce ""Kina jina"" ta Waga masa kai."

"""Ki daina magana, ki yi shiru baki da lafiya"""

"""To meyasame ni?"""

"""ZazzaSi ki ke yi"""

"Ta ce ""To, ka je sallar asubar ne?"""

"""Na je mana, har na yi mana addu'a"""

"""To ka rie kaina da arfi ka yi mini addu'a, jikina ma kamar an jona mini shocking nake ji"""

"Nurse Win da ta shigo ta ce ""Malam ya ka Wagata ana ara mata jini, so ake ta kwanta"""

"Mama ta ce ""FaWowa zata yi daga kan gadon, fizge-fizge take yi"""

"Nurse Win ta ce ""Kwantar da ita, sai ayi mata allurar bacci"""

"Ta rirrie Al'amin ta ce ""Kar ka ajiyeni, idan na kwanta bana iya numfashi""."

"Al'amin ya ce ""To shikenan, ba zan kwantar da ke ba"""

"Anty Zakiyya ta ce ""Wannan wane irin Sari ne, zai saka mutum yayi ta surutai kamar"

"mahaukaci?""."

"Nurse Win ta kalleta ta ce ""Jini ta zubar sosai da sosai, dan haka jikinta yayi weak, alluran da"

"muke yi mata kuma, sune suke burkita ta, dan haka ba abun mamaki bane ba""."

"Al'amin yayi ajiyar zuciya, jin yadda Nurse Win ta rufe musu ainihin abun da ya faru."

"Ita kuwa tayi hakan ne, dan tausayin yadda tun da ya kawo jauhar yake Wawainiya, ko da"

ganganci a lamarin yayi nadama.

"Sai wurin sha daya suka tashi za su tafi, dan bayan allaurai arancin jini ya saka ta fara haki,"

"athma kuma ta tashi, sai da aka sakata a kan oxygen."

"Sai dai daga baya ta zama stable, baba ya din ga yi mata addu'a kan su tafi ya ce tsakanin mama"

ko Anty Zakiyya wani ya kwana da ita Al'amin ya je gida.

"Al'amin ya ce ""A'a baba, zan kwana da ita ba wani abu"" dama yanayin fuskarsu ya nuna ba su yi"

niyya ba.

"Baba ya din ga yi masa addu'a, sannan suka tafi."

"Har suka je gida, suna mamakin kulawa da tashin hankalin da suka gani a tatatare da Al'amin."

"Su Walid ma a reception suka kwana, da an ce a nemo abu, za su fita su sayo, shi kuma yana tare"

da ita yadda ya ga rana haka ya ga dare.

"Lokaci -lokaci tayi ta surutu, duk a dalilin mugun arfin da wayoyin suka yi mata."

"Daf da asuba ta sake farkawa, sai dai ba ta zaburar, wannan karon tana gani, sai dai daga kwance"

ma jiri take yi.

"""Master"" ya Wago daga kifa kan da yayi, ya ce ""Sannu zahra ya jikin?"""

"""Alhamdilillah, jiri nake ji""."

"""Ki yi hauri, kin ga jini ake ara miki. Zaki daina ji in sha Allah, sannu"" yayi maganar yana"

"shafa kanta, yana yi wa Allah godiya da ta farfaWo."

"Da sassafe Nura ya sake dawowa, har da guzirin bredi da madara da suga, ya dawo sake duba"

"Jauhar, amma al'amin ya kore shi."

"Liti ne ya dawo da shi ya ce ""Haba maza, Nuranka ne fa, waye ba ya kuskure? Kar ka yi masa haka dan Allah, kuma sakacin naka ne ba na sa ba, daka karSa kamata yayi ka zubar ai, dan Allah"

"ka yi hauri"""

"Nura har da kuka ya ce ""Dan Allah yaya Aminu ka yi hauri, dan Allah wallahi ban ji dadin abun"

"da ya faru ba"""

"Daga kwance ta ce ""Master, laifin me ya yi ka ke korar aninka, ayi hauri dan Allah, kalli ka"

"saka yana kuka"""

"Al'amin ya ce ""Ki daina magana kar hakin ya dawo"""

"""To ka ce masa ka haura, ka ga kuka yake yi"""

"A hankali ya furta""Ya wuce"""

"""Yauwwa mai zamani, Allah ya ja zamanin maza"" tayi maganar tana Waga hannunta da yar ta ta"

Sa fuskarsa.

"Cikin jin daWi yadda take arfin hali, yayi murmushi ya ce ""Ban hana ba?"""

Murmushi ta yi masa ba ta ce komai ba.

"Da nurse ta shigo ta tarar da ita, tana magana, ga su liti a gefe ta ce ""Zahra gawa tai rami, sannu"

"kin ji"""

"""Yauwwa Anty na gode """

"Ta kalli Al'amin ta ce ""Congratulations, na tayaka muranr farfaWowarta, dan wallahi mun sare"

"bamu zaci zaki tashi ba"""

"Walid ya ce ""Sannunku da oari, Allah ya biya ku"""

"""Amin, bari mu gyara mata jikinta, a bata abinci "" su liti suka fita, ya taimakawa nurse Win, ta"

"gyara jauhar, ta zaunar da ita, duk da tana ta kuka da jiri da ciwon kai da na mara."

"Ya haWa mata shayi, da buredi, sai dai ta kasa ci, sai lallaSata yake yi."

"Wasila tayi sallama, suka amsa."

"Ta ce ""Alhamdilillah anty jauhar jiki yayi kyau, ikon Allah"""

"Nan suka ara gaisawa, ta ajiye abincin da ta zo da shi, jauhar ta ce za ta sha kunun gyaWar da ta"

kawo.

"Ana haka su Baba suka zo, suka tarar da Al'amin yana ba ta abinci an zaunar da ita."

"Gab Waya zamansu a wurin, bai hana shi tattalin matarsa ba, dan gani yake yafi kowa sa'a farfaW"

owar da ta yi.

"Babban abun da ya yi wa jauhar daWi, bai wuce ganin 'yan gidan su, sun zo dubata ba, ko ba komai"

sun nuna damuwar su da ita.

"Duk saifu na ta zuga Baba ya bi diddigin yadda aka yi tayi Sarin, ko dukanta Al'amin yake yi, amma yanayin yadda suke mu'amala ita da Al'amin ya sanya kowa yin wani tunanin daban, dan sa"

Sanin abun da ake tunani ake gani.

"Har Abbu sai da ya zo duba jauhar, su shahida ma duk sun zo, Baba sai da ya yi ta yi wa wasila"

"godiya da Addu'a, tana ta oari da jauhar, mawabtan su ma na ta zuwa dubata."

"A kwana na uku, da daddare take tambayar Al'amin ""Master wai dan Allah meya same ni ne? Na san kawai na ga lemo a Wakinka na sha, daga nan ban san meyafaru ba, kuma na ji ana cewa nayi Sari, ya aka yi na yi Sari ai bani da ciki, ko kuma ina da shi ban sani bane? To yaya aka yi ya"

"zube?"""

"""Ki yi hauri, likita zai yi miki bayani in sha Allah"""

"""To kai ka yi mini mana, wai shikenan babyn yanzu babu a cikina"" tayi maganar tana shafa cikin"

Wauke da damuwa.

"""Ni likita ne?"""

"""A'a amma ka gaya mini, haryanzu ina da cikin?"""

"Al'amin ya ce ""Wai abun da baki san da shi ba ma, zaki bi ki damu, ki yi hauri za su yi miki"

"bayani"""

"Ta ce ""To shikenan, yi mini addu'a na yi baccin""."

"Ya ce ""To"""

"Gari ya waye, su surayya ma suka zo dubata, saifu ya kawo su, take tambayar ina yaya hafsa, aka"

ce mata ta tafi umara.

"Jauhar ta ce ""Dan Allah ku ce ta yi mini addu'a sosai da ni da master"""

"Suryaya ta ce ""Wai ke kowa na gaya wa miji sunan 'yan gayu ke kina master"""

"Tayi murmushi ta ce ""Baki ga mastern ne ba? Kuma ai mu ba 'yan gayu bane"""

"Kasancewar Al'amin ba ya Wakin ya sanya saifu cewa ""Ke, ki faWa mini gaskiya, wani abun yayi"

"miki ko?"""

"Ta ce ""A'a me ka gani?"""

"""Wallahi ki ka rufa masa asiri sai kin daku, har likita na saka baba ya tambaya, ko dukanki yayi ya"

"ce babu alamar duka a jikinki da aka kawo ki"""

"Jauhar ta ce ""Master ba ya duka, bai taSa dukana ba""."

"""Na san halinki da shegiyar gwaninta ne, da kare mai laifi ki gaya mini gaskiya"""

"""Wallahi babu abun da ya yi mini"""

"Dawowar Al'amin ya sanya su yin shiru, ya arasa gaban gadonta ya ce ""Me zaki ci?"""

"""Bakomai, kawai a sallame ni"""

"Ya zauna a gefen gadon ya ce ""Ba na son rigima, wace irin sallama kuma?"""

"""Kai ka koya mini ai, kai fa har guduwa ka ke daga asibiti"""

"Yayi murmushi ya ce ""Zaki gudun kenan?"""

"Ita ma murmushin ta yi ta ce ""Kashe kuWin yayi yawa, ina iya tashi ai"""

"Rarrashin ta ya din ga yi, dan shi kansa ya san zaman asibiti da gundura."

"Sai da ta kwana shida, an saka mata jini ya kai leda biyar, sannn aka fara zancen sallamar ta ranar."

"Daga likitan sai ita da Al'amin a Wakin, yayi mata bayanin abun da ya faru, tare da gaya mata"

akwai buatar ta huta kan ta sake Waukar ciki.

"Ya yi wa Al'amin faWa a kan ya kiyaye sosai da sosai, wannan karon sun rufa masa asiri idan ya "

ara faruwa.

"Jauhar ta sunkuyar da kai, sai kuka."

"Likitan ya ce ""Menene? Meyafaru? Kuma?"""

"Al'amin ya ce ""Bakomai, zamu yi magana da ita"""

Likitan ya rubuta musu sallama ya fita.

"Yana fita ya ce "" 'yar madara menene kuma?"" Shiru ta yi masa ta cigaba da kuka."

"Duk yadda ya rarrasheta, tayi hauri ta i yin magana."

"Baba ya zo da mota, ya Wauke su ya kai su gida, ya yi ta yi wa Al'amin godiyar Wawainiyar da ya"

"yi ta yi da jauhar a asibiti, yayi musu sallama ya tafi."

"Al'amin ya zauna kusa da jauhar ya ce ""Dan Allah ki gaya mini menene?"""

"""Komai ma, kawai ka janyo na rasa babyna, kuma wai ba zan haihu yanzu ba, wataila ma ba zan"

"sake haihuwa ba""."

"""Subhanallah kar ki yi mana wannan fatan, zaki kuma haihuwa cewa suka yi kawai ki bayar da"

"tazara saboda yanayin jikinki""."

"Cikin kuka ta ce ""Ai da ka daina shan Wannan abubuwan, duk da ba haka ba. Kawai ka ja na yi"

"asara ga jinina ya are, kuma wai ba zan haihu yanzu ba"""

"Cikin tsananin nadama yake rarrashinta, sallamar mutane ya sanya ya tashi, 'yan dubiya suka din"

ga zuwa duba jauhar.

"Al'amin na ta hidima da ita, da sassafe yake tashi ya yi aikace-aikace, girki ne kawai sai mawabta"

sun shigo suke yi mata.

"Shahida ma ta yi oari sosai, dan tana zuwa ta taya jauhar aiki, a haka suka saba."

"Guduma ya sake zuwa har gida ya duba jauhar, tare da gaya mata abun da ya faru."

Jauhar tayi masa nasiha sosai a kan shaye-shaye.

"Al'amin ya fara bata tausayi, har rama yayi sosai, mussaman daina kula shi da tayi, sai yayi ta"

kame-kame.

"Yau da ya dawo, normal ta karSi abun ta."

"Har ya tafi ya kwanta, ta bishi Wakinsa."

"Ta hau gadon ta kwanta ta ce ""Master"""

"""Mmm"""

"""Ka yi hauri dan Allah, komai ya wuce na ji babu daWi ne kawai shiyasa kawai"""

"Ya ce ""To"""

"""Kayi magana mana, ba to ba"""

"""Ina jin babu daWi, missing babynki da ki ka yi, ki yi hauri laifina ne"""

"""Ba fushi na yi dan cikina ya zube ba, fushi na yi saboda bani ba har kai kana yi mini ganganci da"

"rayuwarka, ka daina dan Allah for our own good and safety"""

"Ya ce ""To in sha Allah"""

"""Yaya za a sha fankar ne?"""

"Ya girgiza kai ya ce ""Likita ya ce ki huta tukuna kar ki sake Waukar ciki""."

"""Sun yi mini allura ai, ko haryanzu ba ka jin komai"""

"Ya ce ""Da Win ma ina ji, mazewa nake yi, a madadin hakan sai in sha in bugu in manta da ke"""

"""Master nawa nikaWai, daga ni ba ari"""

"""A'a saura uku"""

"Ta ce ""To ga fili ga mai doki nan ai"""

"Ya ce ""Filin da dokin naki ne ai, ki yi yadda ki ke so madarata"""

***

"Jauhar ba ta samu damar yin jamb ba, saboda rashin lafiya, dan haka Al'amin ya samu indabo ya ce A alawarurrukan da ya yi masa, yana son ya samawa jauhar admission, tare da samawa Nura"

"guduma aiki ko na direba ne, a manyan ma'aikatu."

"Al'amin ya daina shigo da duk wani abu na shaye-shaye gidan, ko zai yi a iya waje yake tsayawa"

yayi abun sa.

"Jarin su duk ya are a asibiti, dan haka ya yanke wata shawara a ransa."

Ayshercool 08081012143

500 ne via 0009450228

Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343

'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724

"Jauhar ya fara samu da maganar, da daddare suna tare ya ce ""Na ce ba"""

"""Ka ce me ranka ya daWe?"""

"""Wani abu na yanke ne, ina son na samu Abbu, ya bani gadona na wurin ummi, in sayar da abun"

da zan sayar na karSi kuWi a wurin indabo na haWa na fara wata sana'ar ina son barin sayar da wiwi

"gaba Waya""."

"Tayi murmushi ta ce ""Alhamdilillah, tunani mai kyau, amma ba a yadda ka gaya mini haka zaka je"

"ka gaya wa Abbun ba ko?"""

"""A yaya zan gaya masa?"""

"""Cikin kwantar da murya, zaka yi masa bayani, ka san iyaye sai ana lallaSa su, ka sani ma ko ya"

"kai ka kasuwa?"""

"Ya ce ""Ko ya kai ni ba na so, ya je ya cigaba da rie 'ya'yan matar can. Dama alhkina ne ya sa"

"yanzu ba shi da kuWi kamar da"""

"Jauhar ta ce ""Haba master, Abbun ka ke gaya wa haka, kai zaka ji daWi ka haifi Wa yayi maka"

"haka?""."

"Cikin ko in kula Al'amin ya ce ""Duk tsanani, ba zan yi wa Wa na abun da yayi mini ba"""

"""Master ka san shiga tsakaninka aka yi da Abbu, dan Allah ka daina irin wannan maganar""."

"Yayi mata shiru, ta sake cewa ""Master yaushe zaka kai ni mu gaida su Hajiya?"""

"""Ba rana? Tun bayan kawo ki sun kuma zuwa?"""

"""Hmm master, Allah ya baka damarmaki, duk da ka rasa ummi da yaya sadik, da kuma uban gidanka. Ko yaya dole nan gaba yaranka su so ganin 'yan uwanka, dan da dangin uba ake ado. Ni fa duk wannan abun da ake yi, bani da wayo sanin mahaifiyata ta rasu, ba 'yar gari bace, yar jalingo ce, ba a taSa kai ni garinsu ba, ba a taSa nuna mini ko mutum Waya a danginta ba, kuma ban taSa ganin kowa ya zo daga garinsu ba. Da na fuskanci babu uwata a gidan, na nemi ba'asin in da take, baka ga dukan da mama tayi mini ba, ban haura ba na tambayi baba, amma ya ce idan na kuma yi masa zancen dangin mamana, sai ya zane ni. Yadda yake nunawa da yadda su mama ke fa Wa yana son mamana, amma nayi mamakin yadda yai yadda a kai ni garin su na ga ko 'yan uwanta, da naga ba ya so kawai na daina maganar. Kai kuwa da ka rasa uwa akwai makwafinta, yakamata mu je mu ga hajiya mu gaisheta, ni ba wanda zan kalla na ce daga wurin dangin"

"mahaifiyata yake""."

"Yayi ajiyar zuciya ya ce ""Kuma ba ki san a ina take a jalingon ba?"""

"Ta girgiza kai ta ce ""Ban sani ba, kawai iya abun da na sani kenan"""

"""Shikenan, zamu je mu gaida hajiya, amma sai na tambayi Abbu in da take a tofan ba zan iya"

"tunawa ba"""

"""Yauwwa maigidan Allah dai ya iya maka, ya goyi bayanka yayi maka jagora """

"Ya shafa fuskarta ya ce ""Amin madarata"""

"""Yauwwa milona"""

"Ya ce ""Ga madara ga milo, sai Shan shayi"" suka yi dariya tare."

"Washegari da

5 / 67