Karfe a Wuta Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   25 / 67

72K to 75K   out of 199.8K words

kuka."

"Ta Wauki wayar, tun da ya tafi, take gwada kiran lambobi daban-daban, amma ba ta tafiya sai ta sa"

"kawai. Ta dudduba ko ina, ko da hanyar da za ta iya guduwa, amma babu ga wata irin kewar mama da sani ™aninta da take yi."

"Su liti tamkar za su yi hauka, gaba Waya suka rikice, da Viper bai kwana a gida ba, duk in da suke tunanin za su ganshi ba su same shi ba. Har gidansa Walid ya je, ya haura ta katanga, ya shiga amma ba su same shi ba, gashi madakin da aka ce ya zo yana unguwar, shi ma yayi Satan dabo,"

an neme shi an rasa.

"Gaba Waya hankalinsu ya tashi, mussaman liti, amma saboda tsananin ™i faWi, ya™i yarda ya karSi"

"laifin, Walid ya din ga yi musu luguden ashariya daga shi har Wan mama, suka yi masa shiru suka"

™i kula shi.

"A sukwane Nabila ta tashi daga wurin aiki, bayan cin karo da batun faWan daba a tsakanin yaran"

"madaki da na Viper, sai dai babu Waya daga cikin su da ya zo hannu, tsakanin Viper da madaki, al'ummar unguwar na cigaba da zaman War-War, sakamon rashin tsaro."

"Ofishin Nasir ta tafi, babu sanarwa sai ganinta yayi, sai da hankalinsa ya tashi ya ce ""Arfa lafiya"

"kuwa?"""

Ta ciro wayarta ta nuna masa posting Win.

"Ya ce ""To wannan ne ya saka ki ka taho har nan?"""

"Ta ce ""Eh, na yi zaton baka sani bane"""

"Ya girgiza kai ya ce 'No, na sani"""

"""To yaya ake ciki?"" Ya Wan tsareta da idanunsa sannan ya ce ""Ni duk kin ruWa ni, ko kece ke"

"binciken nan, sai haka Arfa. Na je, sun yi faWan daba, amma babu tabbacin yazo""."

"""Baka kama shi ba kenan?"" Ya jinjina mata kai alamar eh."

"""To ko yaran nasa ba ka kama ba?"""

"""Lokacin da muka je, sun yi sun watse"" wata irin Soyayyiyar ajiyar zuciya ta yi, sannan ta ce ""To"

"shikenan, ai ban zaci ka gani ba, shiyasa na zo da kaina, bari na tafi"""

"Nasir ya ce ""Yanzu mussman ki ka baro aikinki ki ka zo kawo mini rahoto, arfa mai abun mamaki,"

"zauna na gama abun da nake yi, na rage miki hanya"""

"Ta ce ""A'a yi aikinka, ina da wurin zuwa"" ta lallaSa shi ta fice."

"Sai dai hankalinta ya rarrabu kashi-kashi, voice Win nan da aka turo mata, babbar shaida ce da zata"

shiga kotu da ita da ™warin gwiwar ta.

"Abdul ya kira saif a waya, ya tambaye shi yaya ake ciki ya ce masa ""Wallahi Abdul babu labarin"

"matar nan, duk wani bincike da yakamata na yi na yi, amma shiru babu labari""."

"""Lahaula wala ™uwwata illa billa, Saif akwai matsala me zan ce wa yarinyar nan idan ta gano"

"mahaifiyarta tayi Satan dabo, bayan babu irin magiyar da ba ta yi mini ba, a kan na mayar da ita"""

"""To wannan kuma kai ta matsewa, tuntuni da ka san abun yi a kanta da duk ba a kawo nan ba"""

"Abdul ya ce ""Dole na gano in da mahaifiyar rayya take, idan ba haka ban san kalar tsinuwar da za"

"ta yi mini ba"""

"Saif ya ce ""Ban gane tsinuwa ba, tsine maka take yi?"""

"""Manta kawai"" ya kashe wayar, ya din ga kiran wayar ramma, saboda tun jiya da safe da tayi kukan nan, ba ta sake Waga wayarsa ba, hankalinsa yayi mummunan tashi, ya fara tunanin ko wani abun ne ya sameta, kar ya je ta yi wa kanta illa, dan da wu™a™e a kitchen, kuma tana yawan i™"

irarin cewa zata kashe kanta.

"Kusan awanni ashirin da huWu suka shuWe, Nabila ba ta samu Viper a waya ba, can Sangaren su"

"Walid ma, hankalinsu ya kasa kwanciya, saboda yawon neman Viper."

"Har ta je wurin aiki, ta kasa sukuni, kawai ta yanke shawarar zuwa gidan da yake."

"Tana sauka daga abun hawa, wata mota ™irar helux ba™a, ta fito daga hanyar, duk da wurin mota ba ta iya bi, tayi ta tunanin yaya aka yi mota ta bi ta wurin, ta ™arasa gidan, tun a tsakar gida take sallama, amma shiru babu wanda ya amsa, ta nufi Wakinsa, ta ganshi a kwance a kan katifa, gefensa ga wu™arsa da wayarsa da ledar magunguna, yana sanye da riga ba™a armless, da dogon"

"wando shi ma ba™i, ga damtsensa an yi masa Winkin rauni, da sauran wurare a jikinsa."

"Cikin hanzari ta ™arasa tana faWin ""Subhanallah"""

"""Viper meyasameka?"" Sai dai kamar gawa, ta ™are masa kallo, an yi masa askin uwar sumar da take kansa, an yi masa gyaran fuska tare da rage masa gashin da ya taru a fuskar sa. Yayi wani irin ™ayataccen kyau, hatta kayan jikinsa ba ™aramin kyau suka yi masa ba. Wayarta ta ciro ta din ga"

Waukarsa a hoto.

"Ta daddaki gefen katifarsa ta ce ""Viper, bacci kake yi ne? Garin yaya ka ji raunuka haka?"" Sai dai"

shiru ko motsi baya yi.

"""Me ka sha har haka ne? Ko sai na ce Master zaka tashi?"" Babu tsammani ta ga yana motsawa a"

hankali.

"""Madarata"" Nabila ta ce ""Too yau kuma?"""

"Yayi murmushi idanunsa a lumshe ya ce ""Ai a duniya babu wanda ya raina ni, daga ke sai Walid, kin daina jin tsorona gaba Waya zan kama ki ne"" murmushi yake yi sosai, wanda hakan ya"

bayyanar da tsantsar shau™i da soyayyar da yake yi mata.

"Surutansa ya cigaba da yi ya ce ""Yakamata na gaya miki wani abu, da yakamata ace kin sani,"

"amma sai kin haihu tukuna, saura kuma ki isheni da tambaya na san halinki"" ya buWe idonsa a"

"hankali, ya kalli Nabila da ta zuba masa ido, ya mi™a hannunsa ya ri™o nata ya ce ""Zan gaya miki"

"me na je yi Lagos ne"" sai kuma ya saki hannunta yana girgiza kai."

"""Laaa, ke ya aka yi ki ka dawo da shi, Walid ™araso ka ga"" liti yayi maganar yana shigowa Wakin."

"Gaba Waya su ukun suka shigo, suka kewaye ta."

"""Da gidan uban wa ki ka kai shi?"""

"Ta kalli Liti ta ce ""Kamar yaya?"""

"""Gidan uban wa ki ka kai shi?"""

"A ™ule ta ce ""Gidan ubana, tayaya zan iya Waga wannan shirgegen ™aton"""

"""˜arya ki ke yi haWa baki aka yi da ke aka Wauke shi, wannan kayan na jikinsa ma ba nasa bane ba"

"macuciya"""

"Walid ya ce ""Ya isa dan Allah, Barrister nemansa muke ko sama ko ™asa bamu ganshi ba, a ina ki"

"ka gano shi?"""

"Ta ce ""Wallahi yanzu na zo, bana samunsa a waya, yanzu na zo kawai na tarar da shi a kwance, wallahi ban san ma neman sa ku ke yi ba, duba wayarsa zaka missed calls Wina da yawa. Amma dai naga wata ba™ar helux ta fita daga hanyar nan, ban san ta ina suka biyo ba, na ri™e lambar"

"motar a kaina"""

"Walid ya ce ""Karki damu, na yadda da ke"""

"""Wallahi mai laya, ka cigaba da sakankancewa da yarinyar nan, sai tayi dalilin an kashe ku"

"tukuna"""

"Liti ya ™arasa gaban Viper ya dur™usa a kansa, cikin zafin nama, viper ya dan™i wu™arsa ya saita"

ta a cikin liti yana wani irin huci.

"Liti ya buWe baki ya ce ""Ni zaka sa wa russia Viper?"""

"A hankali ya ™ara buWe idonsa, ya hankaWe liti gefe ya ce ""Na zata madaki ne"" sai kuma ya kalli"

"jikinsa, ya kalli kayansa, ya kalli damtsensa ya ga Winki, ya kalli Nabila ya kalli Wakin ya ce ""Ke a ina muka rabu da ke?"""

"Ta ce ""A titi, bayan ka dire daga adaidaita sahu""."

"""Me ki ka yi mini?"""

"Nabila ta ce ""Au kaima ni ka ke zargin na sace ka kenan?"""

"Walid ne ya yi masa bayanin abun da ya faru, ya lalubi wayarsa da sauri yana duddubawa."

"""Don't endanger your life again, madaki is still not your mate, da sauran lokaci"" ya ajiye wayar ya"

"sunkuyar da kansa, da yayi masa nauyi yana tuno abun da ya faru a ranar."

"Nabila ta kalli Walid ta ce ""Yay walid, yayana yana zuwa wurin sayar da shayinku, kuma akwai jami'ansa a farin kaya suna zuwa, kayi taka tsantsan, yanzu aikinsa a kanka yake. Kuma ka kula da"

"wanda suke zuwa wurin sosai, kar wani information yayi leaking a wurin"""

"Liti ya ce ""Munafuka, wadda take kwarewa Wan uwanta baya ne, ku ke tunanin kuma ba zata bar"

"ku ba wataran. Shegen yayan naki azzalumi, ™ugu kamar gatari"""

"Nabila ta ce ""Allah ya isan sa, kuma ni ba munafuka ba ce, kuma wallahi idan baka kiyayeni ba,"

"zan kuma sakawa a kama mini kai, sai igiya tayi saura"" tayi maganar tana hararsa ta Wauki jakarta."

"Ta dur™usa a gefen Viper ta kai bakinta, kunnensa ta ce ""Viper, zan tafi zan je wani wuri, zamu yi waya, ka samu ka ci abinci, kar ka takurawa kanka da tunani da yawa, kar ka sha ™wayoyin da za su yi maka illa. Saboda muna son ganinka cikin ™oshin lafiya da ni da 'yar madara, na ji ka ce zaka gaya mata wani abu, to nima sai ka gaya mini, tun da nice amarya. Kayan nan sun yi maka kyau sosai da sosai, ka ci abinci kayi salla ka huta, ka bar wayarka a buWe zamu yi magana dan Allah, ka yi mini addu'a zan cigaba da shari'a da su bunkure, take care dear"" ya Waga kai ya"

"kalleta, ta™i kallonsa tayi waje."

"Liti ya ce ""Makira, duk makircinki sai ya koma kanki"". Ta galla masa harara ta tafi."

***

"Abdul yana ta kiran ramma, har ya fitar da ran zata Waga, yaji ta Waga muryarta ™asa-™asa."

"""Bacci ki ke yi ne?"""

"Ta ce ""Eh"""

"""Eyya sorry na tashe ki, nake ta kiranki a waya amma ba kya Wagawa, lafiya dai ko?"""

"""Haushinka nake ji ne, zan iya WuWWura maka ashar, shiyasa bana Wagawa"""

"Yayi dariya ya ce ""Yanzu kin huce?"""

"""Eh"""

"""To masha Allah, kin tashi lafiya?"""

"""Eh"""

"""Duk muryarki wani iri, anya lafiya kuwa?"""

"Ramma ta ce ""Ba wani lafiya, ni na gaji da zaman gidan, nikaWai kamar mayya sai tv da haushin"

"karnuka, ni ba prisoner ba""."

"Abdul ya ce ""To yanzu ya ki ke so ayi?"""

"""Ni koma yane ayi"""

"Ya ce ""To shikenan, zan dawo gobe in Allah ya kaimu"""

"""Ba sati ka ce zaka yi ba?"""

"Ya ce ""A'a hankalina ya™i kwanciya ne, zan dawo gobe in Allah ya kaimu """

"Ramma ta ce ""To Allah ya tsare"""

"""Kin fasa in faWi a jirgin, kar in dawo?"""

"""A'a jirgin ya faWi kai kaWai ka mutu"""

"""Muguwa ba Amin ba"""

"""Ban kai ka mugunta ba ai"""

"Yayi dariya ya ce ""Sai anjima""."

***

"Washegari ya kama ranar da Nabila zasu cigaba da shari'ar mai gadi, ta shiga office Win ta, ta tarar da wani file a ajiye a kan teburinta, har ta fara masifar na meye wannan aka ajiye mata a kan tebur. Ta nemi wuri ta zauna, ta Wauki wayarta, ta shiga social media ta rubuta, kuraye masu fatar akuya, an kusa wal™iyya mu ga kowa"" ta yi tagging Win Naja bunkure.Washegari ya kama ranar da Nabila zasu cigaba da shari'ar mai gadi, ta shiga office Win ta, ta tarar da wani file a ajiye a kan"

"teburinta, har ta fara masifar na meye wannan aka ajiye mata a kan tebur."

"Ta nemi wuri ta zauna, ta Wauki wayarta, ta shiga social media ta rubuta, kuraye masu fatar akuya,"

"an kusa wal™iyya mu ga kowa"" ta yi tagging Win Naja bunkure."

"M karofi ya kirata, ya din ga yi mata surutu, da neman ta bashi damar zuwa gidansu, ta ce masa"

"yanzu aiki take yi, bayan sun yi sallama, ta ja file Win tana dubawa."

"Sunan Naja'atu Bunkure ne a sama, sannan aka fara bayanin tarihin rayuwarta tiryan-tiryan, har zuwa fara aikinta, yadda ta taso cikin rayuwar ™unci da wahala, yadda ta zama lawyer, bayan fyaW e da aka yi mata da ™anan shekaru, gaSar da Nabila ke son ganin meyafaru, a nan aka tsaya. Ta daki tebur, ta din ga jujjuya file Win tana tunanin waye wannan ya kawo mata file Win nan, da kyar"

idan ba shi da ala™a da wanda ya tura mata voice message Win nan.

***

"DSP Nasir yana zaune yana rarraba ido a ™aton falon, da ko ina sanyin A.C ne ke ratsa shi."

"Babu tsammani mutumin ya fito, ya samu wuri ya zauna, cikin girmamawa Nasir ya ce ""Barka da"

"wannan lokaci sir"""

"""Yauwwa barka, DSP Nasir Yusuf maitama, Wan uwan barrister Nabila Yusuf maitama"" ya Wago"

ya kalle shi.

"""Na san zaka yi mamakin kiran da nayi maka ko?"""

"Nasir ""˜warai sir, na san ni dai babu wani abu da ya taSa haWa ni da kai, amma ka saka a nemo ni,"

"kuma ga sunana ka kama, da na ™anwata"""

"Indabo ya gyara zamansa ya kalli Nasir ya ce ""Nabila!"""

"Cikin rashin fahimta ya ce ""Me tayi?"""

Ayshercool

0808101243

¦ 500 ne via 0009450228

Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne.

90009343

'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724

"Cikin rashin fahimta, Nasir ya ce ""Amma YallaSai me tayi ne?"""

"Indabo yayi murmushi ya ce ""Bari mu Wan ajiye batun ta a gefe. Aminu Viper, wanda aka fi sani"

"da mai zamani a baya, kai ne incharge of bincike da ™o™arin kama shi haka ne?"""

"Ya jinjina kai ya ce ""Eh sir"""

"""Na san kana fuskantar matsin lamba, daga wurin na sama da kai, a kan lallai ka kama Viper. Duk da abun mamaki ne, a baya yana tsare a prison lokaci guda yayi Satan dabo sama da shekara guda"

"ana nemansa""."

"Nasir ya ce ""Haka ne sir"""

"Indabo ya sassauta muryarsa ya ce ""Akwai ji™a™™iya tsakanina da Viper, wanda barazana ne ga siyasata da mutuncina. Saboda haka na yanke shawarar yin gaba da gaba da kai mu tattauna wata™ ila kafi bawa aikin muhimmanci, tun da na samanka kawai nake gani, kai bamu taSa haWuwa ba,"

"kuma Alhamdilillah sai na yi sara a kan gaSa"""

"ya ajiye masa wata jaka ya ce ""Ga wannan ka sha mai, sannan akwai fuloti mai rai da lafiya a unguwar tudun yola da takardunsa a ciki, wannan zai zama wani Wan hasafi, ko in ce ihsani domin ™ara maka ™warin gwiwa, idan aiki ya kammala, ina da kyakykyawan Albishir gareka, muddin Viper ya zo hannu, ko ma ya bar duniyar baki Waya ina da ™arin Albishir gareka. Šana na shirin zama deputy governor a garin nan, zaSe mai zuwa. Kuma ka san kujerar da nake kai, ka san ma'anarta. Zan iya yi maka al™awarin zama CP na jihar nan, kai koma na yi maka babban mu™ami a ™asa. Akwai kyautar mota irin ta sanatoci, da gwamanti kan yi gwanjon su, gida ko fili sai wanda ka zaSa. Kar ka yi dogon tunani, ba wai cin amanar ™asa zaka yi ba, taimakon kai da kai ne, kai ma ka taimaki gobenka, idan ba haka ba, a haka zaka ™are kana yi wa ™asar da ba ta san muhimmancin ka ba bauta, ka gama babu wani allowance Win kirki ka ™are rayuwarka a"

"tagayyare"" Nasir yayi shiru yana ajiyar zuciya."

"""Sai magana ta biyu, Nabila ™anwarka, akwai wasu abubuwa muhummai a tattare da ita. Abu na farko na sanya rayuwarta a matsayin tarkon da zan kama Viper ba tare da ta sani ba, duk da hanyar tana tangarWa, amma tabbas ina ™o™arin kama Viper ta hanyar ta, ko da kuwa hakan yana nufin"

"salwantar da rayuwarta ne"""

"Cikin mamaki da rashin fahimta ya ce ""Kamar yaya?"""

"""Kamar yadda nake gaya maka, ai ba ta hannunku kawai nake nemansa ba, dan ha™a ™wazonka, da nemo Viper shi ne zai kuSutar da rayuwarta, haka zalika ka taka mata burki a kan shari'ar da take yi, na son yin gaba da gaba da Naja'atu Bunkure, saboda yin hakan tamkar yin fito na fito da ni ne, idan ba haka ba, wallahi rayuwarta zata salwanta a banza, ba zan taSa bari sunana ya Saci a"

"banza ko asirina ya tonu ba"""

"Nasir ya ce ""Amma sir, dole sai an shigar da Nabila cikin wannan lamarin?"""

"""Dole ne, muddin kana son rayuwarta, make her withdraw the case, ta fita daga shari'ar nan"""

"Nasir yayi sassanyar ajiyar zuciya ya ce ""Zan duba naga menene abun yi"""

"Indabo ya ce ""Yauwwa, a ™o™arta, zaku tafi da P.A Wina, za ayi wa motarka full tank, ka sanya"

"ido sosai a kan yarinyar nan"""

"Nasir ya tashi ya ce ""Thank you sir"""

"Indabo yayi murmushi ya ce ""In dai muna tare, ka din ga samun damrmaki kenan, ai ba a zama"

"haka DSP"" ya jinjina kai ya juya ya fita, kansa yana wani irin nauyi."

***

"Cikin hanzari Nabila ta fito daga office Win ta, ta kalli mai goge-goge ta ce ""Baba, akwai wanda"

"ya shiga office Wina kafin na zo ne?"""

"Ya ce ""A'a, shara kawai na yi na goge miki, na fito"""

"""Kai ka ajiye mini wani file a kan tebur?"""

"Ya girgiza kai ya ce ""A'a, ban tarar da komai ba da na goge teburin"" ta jinjina masa kai ta koma,"

tana cigaba da mamakin waye haka?.

"Ta window ta le™a taga zuwan barrister Habib, tayi sauri ta fita, a ™ofar office Win sa ya tarar da"

"ita ya ce ""Ya

25 / 67