Karfe a Wuta Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   59 / 67

174K to 177K   out of 199.8K words

shi ma ki ke yi""."

"""Laifi ne dan ka tsayawa wanda aka zalunta?"""

"""Aka zalunce shi a gidan uban wa, mutumin da ya yi kisan kai? Kisan kai fa yayi. Kuma babban tashin hankalin son sa da ki ka fara yi. Ba zaki taSa ganin laifinsa ba, mutuncinki ya zube a banza, a din ga yi miki kallon mutuniyar banza, wallahi hukuncin da Abba ya Wauka a kan ki, yayi dai-dai duk wani abu na shaida ko hujja, ki tattara ki ba wa Yaya Nasir, a kama shi kowa ya wuce wurin, kan ki janyo wa mutane magana, ni ba a kyauta mini ba, da bai haWa woyoyinki ya ™wace ba, ya bar ki da su"" Ta ™ura wa Sumayya ido, yadda ta Wauki zafin nan, babu alamar za ta tsaya ta"

"fahimce ta, kawai ta yi mata shiru, ta gama masifarta, ta tashi ta fita."

"Tayi shiru, gaba Waya ta rasa abun da yake yi mata daWi, ta ji gaba Waya duniya tayi mata zafi,"

"rana zafi inuwa ™una, ta rasa ina zata kama, wurin wa za ta je taji sau™i."

"Gari ya waye, Nabila ta shirya tayi ficewarta wurin aiki, ba wanda ta kula, ta yi ficewarta ta tafi."

"Ofishin barrister Habib taje, ta jira shi, ta samu wuri ta zauna, tana jiransa."

"Kallo Waya yayi mata, ya buWe ofishin sa, ya ce mata ""Taso"""

"Ta tashi ta shiga, suka zauna, ya kalleta ya ce ""Ina jinki yau kuma menene?"""

Nan ta kwashe komai ta zauna gaya masa.

"Ya ce ""Ai dama na gaya miki, dole ki fuskanci ™alubale, ki yi ha™uri, komai zai wuce, gobe in Allah ya kaimu kotu zata zauna a kan case Win su rahama, sannan zan cigaba da duk wani ™o™ari"

"na baki dukkanin goyon bayan da ki ke bu™ata, amma mu cigaba da addu'a"""

"""To yaya Habib, kai kaWai ne ka fahimce ni, kotu na yanke hukunci zamu shigar da ™arar kotu ta"

"tilasta wa bunkure foundation fito da ramma, tare da gurfanar da ainihin wanda ya aikata laifin""."

"""Ki yi ha™uri ™anwata, nasara na tare da ™alubale, ina yi miki fatan alkhairi da fatan nasara""."

"A sanyaye ta ce ""Na gode"""

"""Amma Nabila, a ina zaki yi generating shaidun da zaki shiga kotu da su, a kan case Win Viper? A"

"ina zaki ganshi?"""

"""Na ma ganshi, na riga na tanadi duk abun da nake bu™ata, domin fuskantar shari'a"""

"""You can do it my dear, kuma in sha Allah za ki yi nasara, akwai yiwuwar zan je na samu major da"

"kaina, nayi masa bayani"""

"Ta girgiza kai ta ce ""No need, kar ka je, hakan ba zai sauya komai ba"""

"Ta mi™e ta nufi hanyar fita, tana duba message Win da ya shigo wayarta."

"""Mu haWu a garden, idan baki da aiki"""

"Tayi masa reply da ""On my way""."

"Yanayin yadda take tafe, tana jefa ™afa, ya tabattar masa da a cikin damuwa take."

"Tana zuwa gabansa kawai ta nemi wuri ta zauna, ba tare da ta ce masa uffan ba."

"Ya samu wuri ya zauna a gefenta ya ce ""Ya aka yi ne?"" Ta girgiza masa kai alamar babu komai."

"""Akwai mana, fuskar ki ta nuna"""

"""Kowa ya™i fahimta ta, Abba yayi zazzafan fushi da ni, wai sai na bawa yaya Nasir haWin kai ya kama ka, ya je ya gaya wa Abba ™arya da gaskiya, sam Abba ya™i saurarara ta, sumayya ta™i fahimta ita ma, barrister Habib ne kawai ya fahimce ni, Vi na rasa ya zan yi, zuciyata zafi take yi"

"mini, Nasir ya cuce ni, ya haWa ni da Abba"""

"""Yanzu zaki ba shi haWin kai ya kama ni kenan?"""

"Ta girgiza kai ta ce ""Ba zan iya ba, ba zan iya bari a kama ka ba""."

"""Meyasa?"" Ta Waga kai ta kalleshi ta ce ""Ka sani ai"""

"""Ban san komai ba"""

"Cikin basarwa ta ce""Kawai ina so ayi wa matarka adalci ne, kuma a hukunta wanda suka yi maka"

"laifin"""

"Ya ce ""Gwargwadon yaya ki ke son yar madara?"""

"""Gwargwadon yadda nake son ka"""

"""Ki ke son wa?"" Yayi maganar ™asa-™asa."

"Kasa jurewa tayi, duk jikinta yayi sanyi, ta kasa kallonsa, gashi ya matso daf da ita sosai."

"""To ungo share hawayen"" yayi maganar yana bata handkerchief Win sa."

"Ta karSa, amma ta kasa gogewar, ta cigaba da kuka."

"""Dan Allah kar ki karaya, ina ™ara jaddada miki, da Allah na dogara da ke na dogara, amma idan"

"kin ga matsin yayi yawa, ki bayar da kai bori ya hau, ki bashi dama ya kama ni"" ta girgiza kai ta ce ""A'a, ba zan iya bari a kama ka ba"" tayi maganar tana sheshshe™ar kuka."

"""To ya isa haka kukan, ga wata 'yar ™aramar kyauta zan baki"" yayi maganar yana sake bata"

envelope Win da ya bata wancan karon.

"Ta saka hannu ta karSa, tana goge hawayen, tana buWewa ™ananan hotuna ta ciro guda biyu,"

"wadda ta yi tozali da ita a jikin hoton ce, ta sakata razana, ta kalli hoton, ta kalli Viper ta shafa fuskarta ta ce ""Wace wannan?"""

"""Ni ma ban sani ba"""

"""Yaya zaka bani abu ka ce mini ka ce baka san wace ba? Wannan....wann... Kai wannan ba ni ba ce ba, bani ce a jiki ba, yaushe aka yi wannan hoton ban sani ba? Kai wallahi bani ba ce ba, wacece wannan meyasa take kama da ni"" ta yi maganar tana kallonsa, idanunta yake kalla, amma"

bai yi magana ba.

"""Kayi mini bayani, ka yi magana wacece wannan"" tayi maganar kamar zata zare, tana ri™e rigarsa"

tana zazzaro masa ido.

Ayshercool 08081012143

¦ 500 ne via 0009450228

Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne.

90009343

'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724

*BRIGHT PENS SECOND BATCH*

"KU KASANCE DA LITATTAFAN BRIGHT PENS A SECOND BATCH, NA ˜ARFE A WUTA (AYSHERCOOL)."

MUTALLAB (NIMCYLUV)

ZAYTOON (ZEE KUMURYA) DA HADARIN GABAS (NAZEEFA SABO NASHE)

"Idanunta yake kallo, jikinsa a sanyaye amma yayi shiru bai yi magana ba."

"""Kayi magana, ka gaya mini wacece wannan? Bani ba ce a jiki, amma meyasa take kama da ni? A"

"ina take?"""

"Still bai yi magana ba, ™ara tsananta ri™on da tayi masa ta ™ara yi, cikin matsanancin kuka tashin hankali da ™araji, take jijjiga shi ta ce ""Ka yi magana, ka gaya mini wacece meyasa take kama da"

"ni? Kuma a ina take?"""

"Viper ya ce ""Ban santa ba, tsintar su nayi, naga ya dace kema ki gani, ban taSa jin kin ce kina da"

"yar uwa da ku ke ciki Waya ba, amma kamarku ta Saci da ita, shiyasa na ga ya dace na baki ki gani"""

"""Ka san wacece, ka saba yi mini wasa da hankali wasu lokutan, Please na ro™e ka, don't play with"

"my emotions, ka gaya mini dan Allah"" tayi maganar tana kallon ™wayar idonsa."

"Ya Wan jima yana kallonta, kan ya saka hannu ya cire hannunta daga ri™on da tayi masa, yana ri™e"

"da hannunta ya ce ""'yan gidanku yakamata ki tambaya bani ba"""

"""Tayaya zan tambaya? Alhalin a duniya babu abun da Abba ya tsana sama da nayi masa zancen mahaifina, ban san dalilin wannan mummunar ™iyayyar ba, sun yi abun su ya riga ya wuce, amma ya nesan ta duniyata da mahaifina, duk wata hanya da zata saka na san in da yake, Abba ya tosheta wai ba wani abu da zai tsinana mini. Wani abu ne mai ciwon gaske da yake addabar zuciyata, ka fama mini ciwon da yake zuciyata, kuma ka bar ni a duhu, ka taimaki rayuwata wallahi ko Wacece"

"wannan tana da ala™a ta kusa da ni"""

"Viper ya ce ""How, an ce kowane mutum akwai irinsa guda uku a duniya..."

"""Ba wani guda uku, wannan kamar nice a jikin hoton, kamannin nan sun yi yawa, ka wayar mini"

"da kai dan Allah"""

"""Me ki ke so na ce, duk abun da zan faWa miki ™arya zan yi miki, ki je gidan abun da suka ce miki"

"shikenan"""

"Ta fizge hannunta, ta yin™ura zata tashi, jiri ya kwasota ta hau tangaWi, ya ri™e ta, ta Wan yi shiru"

"ta samu nutsuwa, ta juya ta bar wurin."

***

"Ramma kuwa kwana suka yi, Abdul yana juye-juye, ciwon cikinsa ya tashi, ko baccin kirki ba su yi ba, sai bayan sallar asuba ya Wan lafa masa, ya din ga tofa fatiha da bisimillah tana bashi yana sha."

"Yana kwance a kan cinyarsa, tana ta shafa masa ruwan tofin a kan cikin, tana shafa masa, ya ri™e"

hannunta yana mayar numfashi.

"""Sannu Abdul"" ya jinjina mata kai alamar yauwwa."

"""Wai wannan ciwon cikin, ka dudduba kanka sosai mana, kana likita amma ka din ga wasa da"

"lafiyarka, kalli yadda ka ke shan wahala dan Allah"""

"""Tausaya mini ki ke yi?"""

"Ramma ta ce ""Duk rashin imanina, idan ban tausaya maka wannan wahalar ba, ya zan yi, idonka"

"har ja yayi saboda wahala""."

"""Rahama ina ga ciwon cikin nan ne zai yi ajalina, har ™asashen waje na je, an kasa gano menene"""

"Dummm ta ji ™irjinta ya buga, jin abin da ya ce, amma ta ce ""Dan Allah ka daina wannan"

"maganar, ka din ga addu'a ka cigaba da shan magani"""

"""Rahama baki san me nake ji ba ne, ina shan wahala fa"" yayi maganar yana mi™a, tare da lan™"

"washe yatsun ™afarsa, hawaye na bin gefen idonsa, saboda azabar ciwo"""

"""Dan Allah ni ka daina wannan maganar"" ya juya yayi ruf da ciki."

"""Idan na mutu zaki yafe mini?"""

"Ta ce ""Wata™ila, ai ni dama bana fatan na je gaban Allah ina neman hakkina a wurin wani, ko wani yana nema a wurina, a duniya nake fatan Allah ya saka mini abun da ka yi mini, da kai da wannan jakar matar""ya yi murmushi ya ce ""Hakan ma na gode, alfarma Waya da zan nema, dan"

"Allah rahama kar ki zubar mini da cikin nan, ina matu™ar son abun da yake cikinki"""

"""Wallahi sai na zubar tas, sai ya bi rariya, ni ka daina yi mini magana kamar wasiyya wasiyya, dan"

"na tausaya maka"""

"Sai da yayi dariya ya ce ""Abubuwa ne suke ta hargistewa Rahama, komai ya cukurkuWe, ban san ya abubuwan za su kaya ba, ina ta ™o™arin baki kariya ne iya yi na, duk da ni mai laifi ne"" yayi"

"hamma ya ce ""Idan ya lafa sai na ji daWi, gashi bacci nake ji, ke ma na hana ki bacci"""

"Yayi maganar yana shafo fuskarta, ta saka hannu ta sauke hannunsa, ta shafa kansa ta ce ""Kayi baccin, ko ka samu relief"" ya juyo yana fuskantar cikinta, da yake shafe a jikinta ya ce ""Bari na yi"

"magana da yarona"" maganar ta sa tayi daidai da jin motsi a ™asan mararta."

"A haka bacci ya kwashe shi, ta zuba masa ido, tana jin tausayin sa, gaba Waya ya rikice saboda ita,"

ta ™ara lura da shaye-shaye da rashin tarbiyya ne kawai yake ingiza shi yake rashin mutunci.

"""Kayi ha™uri Abdul, amma komai ya kusa zuwa ™arshe da yardar Allah"""

*****

"Walid ne ya magantu, dan tun shigowar Viper ya lura kamar yana cikin damuwa, ya ce ""Mai"

"zamani, ya ake ciki ne? Jikin ne ko wani abun ne ya faru?"""

"Ya numfasa ya ce ""Na yi abun da ka ce, Nabila"""

"Walid ya ce ""Masha Allah, ya ake ciki?"""

"""Ba ta da masaniya a kan hakan, things are complicated, ta shiga matsala daban daban, ta samu"

"matsala da gidansu, an ce lallai ta bawa Wan uwanta dama ya kama ni, she's almost alone, kamar ban kyauta ba, na Wora mata abun da ya fi ™arfinta"""

"Walid ya girgiza kai ya ce ""˜addara ce ta haWa ku, kuma she's not alone, tana tare da kai, muna"

"cigaba da addu'a in sha Allah, komai zai dai-dai ta, ba ta gaya maka komai game da labarinta ba?"""

Viper ya girgiza masa kai.

"""Bata bani ba, amma na bata hoton, na ce taje ta tambayi yan gidansu"""

"""Ina jin alamun nasara, in sha Allah ka kwantar da hankalinka"""

Viper ya amsa da Allah ya sa.

****

"Nabila kamar mara laka, ta fito daga wanka, jikinta Waure da towel, ta ji™o kanta da ruwa,"

"idanunta sun yi jawur, saboda ta yi kuka sosai da sosai."

"Kawai ta Waga kai ta ga Nasir a tsaye a ™ofar Wakin, ta ™ara haWe rai, ta ™arasa tsane jikinta."

"""Nabila, lokaci yana cigaba da ja, kuma ke nake jira, haryanzu baki ce mini komai ba, ki gaya mini in da zan samu mutumin nan, ina Waga miki ™afa ne saboda Abba, kuma nima ina jin nauyin"

"aikata miki hakan"""

"BuWe wardrobe tayi, ta Waukko phant da breziar ta jefo kan gado."

"""Magana fa nake yi miki"""

"Tayi masa banza, ta Waga breziar tana ™o™arin fara sakawa."

"""Nabila wai baki da hankali ne? A gaban nawa zaki saka kaya?"""

"""Ni na kawo ka? Ko ka manta bin maza nake yi? Ba abun da zai hanani saka kayana, ai yanzu ba"

"kunyar wani nake ji ba"""

"Galala ya bi ta da kallo, jakar da ta fita da ita, ta janyo, ta ciro ™aramar wayarta da take vibrating"

"ta ciro ta Waga ta ce ""Hello V"""

"""Are you safe?"""

"""Yes Alhamdilillah"""

"""It seems you are bit disturbed"""

"""No at all"""

"Yayi ajiyar zuciya ya ce ""Kin tambaya Win?"""

"""A'a, ai bai dawo ba, yayi tafiya ne, ni yanzu ina jiran abun da zai kasance a kotu ne gobe in Allah"

"ya kaimu, and su oga Walid su shirya, zasu kasance cikin shaidun da zamu gabatar a kotu fa"""

"""Shikenan, zan gaya musu"""

"""Yauwwa, gobe in Allah ya kaimu daga kotu zan wuce wurin 'yan sanda, a kan case Win ka, Allah"

ya sa......

"""Nabila, wai me ki ka zama ne?"" Nasir yayi maganar yana tunkararta zai fizge mata waya, ta ja da baya ta ce ""Wallahi ka zo in da nake sai na saki towel Win nan, na saki ihu ai kai ka zo in da nake, get out from sight, wallahi Nasir ko me zaka yi ina kan bakana, ni, ko wani kaga zai yi mini ™ azafin da ka yi mini, yakamata ka tare mini, amma ka Sata ni a wurin mutumin da bani da tamkarsa, wallahi ka cigaba da matsa mini kai ma sai na Sata maka suna a gidan nan, ka fita daga rayuwata ba Wan daba ba, ko uban wa zan kare ni naga zan iya. Ka je ka yi aikinka nima na yi nawa, kai ma ai amfani ake yi da kai, ake son kama shi ba dan taimkon al'umma ka ke son kama shin ba, get out please"" yadda jikinta yake rawa take nema ta saki towel Win, muddin ta saki ba shi"

da kalaman da zai kare kansa da su.

****

"Indabo ya kalli Abdul da yake zane yana wasa da mukullin motarsa ya ce ""Wai meye ne, na ganka"

"kamar wani mara lafiya?"""

"Ya ce ""Bakomai, ka yi ha™uri na san maganar yarinyar....."

"""A'a, ai ba maganar yarinyar nan zan yi maka ba Abdul, ka yi abun da ka ga dama, yau saura sati biyu Waurin aure ko wurin yarinyar da zaka aura duk ka kyauta. Magana ce zan yi maka a kan kuW aWen da nake sanya wa a account Win ka, balli na nema ya tashi, an naWa kwamiti bincike a kan ku"

"WaWen nan, shi ne nake son ka dawo mini da shi, na mayar kan balli ya tashi asiri ya tonu"""

Abdul ya yi sororo yana kallon Indabo .

"""Kake kallona kamar shashasha, ka dawo mini da kuWi na ce, na mayar musu dama na Wan jinkirta ne, idan komai ya tafi daidai ayi ya™in neman zaSenka da su, amma zan tanade su a kusa, da na ji"

"™ishin-™ishin na mayar da su"""

"Abdul ya ce ""To, zan dawo da su"" ya tashi ya fita."

"Bayan fitar Indabo P.A ya shigo, ya samu wuri ya zauna, suka gaisa da Indabo."

"Indabo ya ce ""Yaya me ka gano?"""

"""Eh, ana bibiyarsa gidan sa na lay out, ba kowa a ciki, duk gidajen sha™atawarsa, baya nan"

"abokansa duk na neme su, na bibiye su, amma babu alamar sun san zancen yarinyar ma, amma na"

"in da yake kwana ne, haryanzu ba a gano ba, ka san wayo ne da shi, wasu lokutan a asibiti yake"

"kwana, amma sannu a hankali ana cigaba da bibiyarsa"""

"""Abdul ban san ya aka yi ya zama haka ba, yanzu idan na matsa tsaf zai yi wani rashin hankalin, yanzu ka duba ka gani, saura sati biyu fa auren sa, amma gaba Waya hankalinsa baya jikinsa, idan na matsa masa a kan yarinyar nan hauka zai yi mini, shiyasa nake bin sa a sannu, zai zo hannuna"

"sai ya ci ubansa"""

"P.A ya ce ""Distinguish akwai matsala fa"""

"""Wace irin matsa kuma? Kullum cikin kiran matsala ka ke kwanakin nan"""

"Ya gyara zamansa ya ce ""Distinguish, yarinyar nan sumayya T ladan, sai buWa maka aiki take yi, kuma duk yan siyasar nan a kanka ta fi cin kashinka, yanzu wasu matasa daga yankinmu, sun kafa wata ™ungiya suna wayar da kan jama'a, wai za su rubuta takarda kiranye za su yi maka, ka dawo"

"gida babu abun da kake tsinana musu sai kwashe musu kuWi"""

"Indabo ya kalleshi ya ce ""Kai ka taSa ganin wanda aka yi wa kiranye a Nigeria? Rabu da su, ™"

"aryar banza ce, yanzu muna da abubuwan da suka fi wannan muhimmanci""."

"P.A ya ce ""A'a honorable, kar a fara a kanmu, matasan nan fa da gaske suke yi, ka san yanzu muna"

"zamanin social media ne, har cikin ™auyuka suke bi, da gaske

59 / 67