Karfe a Wuta Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   61 / 67

180K to 183K   out of 199.8K words

matar Viper, shekaru shida da suka gabata."

"Yau tana da program a gidan radio, kuma yanayinta ya nuna wa Sumayya tana cikin"

"matsananciyar damuwa, sai dai ta shigo a ™urarren lokaci, zasu fara gabatar da shirin, dan haka ba ta samu damar yi mata tambayar meyake damunta ba."

"Nabila tayi iya ™o™arin ta, wurin ajiye damuwa a gefe, suka fara gabatar da program."

"Sumayya ta kalli takardar hannunta sannan ta ce ""Jita-jita ta cika gari, cewa kin shigar da koke gaban kotu, a kan lallai kotu ta hana hukumar'yan sanda kamar shahararren Wan ta'addan, da addabi wani yanki na garin nan, kuma akw zargi da kisan matarsa, duk da yadda hukumar ta 'yan"

"sanda, take nemansa ruwa a jallo?"""

"Nabila ta kalli sumayya da rinannun idanunta, tayi mamakin yadda sumayya tayi mata wannan tambayar, a tsakiyar program Win su haka, saboda ba magana ce da ta fita ba, balle ta ce an yi"

"Jita-jita a kai. Sumayya ma ta tsare ta da ido, alamar tana jiran amsa."

"Tayi wani irin murmushi ta ce ""Ba Wan ta'adda bane ba, mutum ne kamar kowa, kuma Wan ™asa da ya dace ya samu duk wani 'yanci da kowane Wan ™asa ya dace ya samu. 'yan ta'adda na yawonsu a gari, an san in da suke, an san in da za a same su, hakkinsa muke nema a kotu, ba shi ya kashe matarsa ba. Na san mutane za su yi mamakin yaya aka yi mai dokar bacci ya Suge da"

"gyangyaWi, amma a bibiye ni a cikin shari'ar da zamu gudanar""."

"""Amma ba kya ganin hakan kamar taka doka ne, zaki yi amfani da damarki ta lauya ki taka doka,"

"ki kare mai laifi?"""

"""Sam, dokar da aka wula™anta, da ita nake son yin amfani wurin gyara kuskuren da aka yi. Tayaya mutum zai shafe shekaru babu Shari'a, daga baya al™ali da saka hannunsa da umarninsa da komai, a sake shi bisa doron doka da ™a'ida, kuma daga baya a zo ana nemansa. Shin wanke shi aka yi daga laifin? Ko kuma akwai wani Waurin Soye da yakamata a warware? "" Tayi maganar tana ™"

ure sumayya da ido.

"Sumayya ta kalli agogo, lokaci ya cika, ta na tsaka da sallama da masu saurare, Nabila ta tashi ta"

"fice, tana kammalawa, ta tashi ta bi Nabila, amma tuni ta ja motarta ta bar wurin."

"Ta koma tana sauke numfashi, kiran kankarofi ta gani, ta Waga wayar suka gaisa, ya ce ""T ladan,"

"meyasa ki ka yi wa Nabila wannan tambayar a tsakiyar program?"""

"""Sir nayi ne, dan tun yanzu ta kare kanta a wurin mutane, kafin abu ya bayyana su yi mata kallon,"

"maciya amana mai fuska biyu """

"""Sumayya waye ya gaya miki ana iya wa Wan adam ne? Ba a taSa iya wa mutum, dan haka ki kiyaye gaba, yayi wuri ki fallasa abun haka gaba Waya, amma babu laifi, baki yi kaifi ba, hakan"

"zai ™ara mata ™aimi"""

"Sumayya ta ce ""Ok sir, na gode"" ta ajiye wayar ta yi shiru, ita a zahiri tayi hakan ne, ko Allah zai sanya Nabila ta ji nauyin dubban al'ummar da suke goyon bayanta, ta sassauta koma ta ha™ura da"

"batun Vipern nan, amma ba ta ga alamar hakan a tattare da ita ba."

"Abbu kuwa a zabure ya mi™e tsaye, jin program Win da yayi, shi ba wani ma'abocin jin radio bane ba, yau kawai ya kunna yana saurare, ya ji shirin ya ™ayatar da shi, haka zalika muryar barrister, kamar sananniya ce a gare shi."

"Sai dai jin sun yi maganar Viper, ya sanya ya tashi a kiWime, tare da Waukar radion ya fito tsakar"

gida.

"Rahila ta ce ""Ya dai na ganka a firgice haka?"""

"""Wani shiri na gama saurara, wata lauya ta shigar da koken kotu ta hana kama Aminu, ko gidan"

"radiyon zan je, wata™ila su sun san in da yake"""

"Ta kwaSe baki ta ce ""Ina rabaka da sabgar yaron nan, idan sun san in da yake me zaka yi masa? Salon ka sanya kanka a masifa, wanda ake nema ruwa a jallo da laifin kisan kai? Ka ganshi ka yi"

"masa me? Guduwa fa yayi daga gidan yari"""

"Ya ™ura mata ido, kawai ya girgiza kai, ya kashe radion ya fice."

****

"Nabila tana driving, wani abu ya tsaye mata a ma™ogwaronta, kukan ma gaba Waya ta kasa saboda"

ba™in ciki da Sacin rai.

"Katafaren gate Win aka buWe mata, ta shiga da motarta, tayi parking, ta sauka ta nufi cikin gidan."

"A falo ta tarar da mahaifiyar ramma, tana ganin Nabila, ta tashi da fara'arta, tana yi mata sannu da"

zuwa.

"Nabila ta zauna cikin ya™e, suka gaisa, kamar kullum yau ma mahaifiyar ramma, kallon Nabila take yi, kamar ta haWiyeta, ita dai ban da an yi mata gargaWi, da tuni ta faWi abun da yake ranta, dan ta tantance abun da take tunani, sai dai an gargaWeta a kan aikata hakan, dan haka ta ja bakinta ta"

tsuke.

"""Mama ina fatan dai babu wata matsala ko? Ki cigaba da ha™uri, in sha Allah an kusa dawo miki da ramma, kuma hujjoji nake son kammala tattarawa, na gano ainihin mai laifin, za a gabatar da"

"shi a gaban kotu, idan da wani abu ki gaya mini"""

"Ta girgiza kai ta ce ""Ba wani abu, ina ta godiya Ubangiji Allah ya baki nasara, na gode sosai da sosai da ke da Alhajin da ya taimake ni, ina godiya Allah ya biya ku, ya ™ara miki zaman lafiya da"

"mijinki"""

"Nabila ta ce ""Ai ba mijina bane mama"""

"""A'a ba Alhajin ba, Aminu"""

"Cikin mamaki Nabila ta ce ""Aminu kuma? Nifa ban taSa aure ba, ba ni da aure"" tayi maganar tana"

murmushi.

"Babar ramma ta Soye mamakinta, kar kwaSarta tayi ruwa ta ce ""Au, ai na zata kina da aure ne, Allah ya kawo miki nagari, ya baki mai sonki da gaskiya, Allah ya tsaya miki, kamar yadda ki ke"

"ta ™o™ari a kanmu"""

"Nabila ta ce ""Amin mama, dan Allah a cigaba da yi mana addu'a, addu'aeku, ita ce ke tasiri a"

"rayuwarmu"""

"Maman ramma ta ce ""In sha Allah, addu'a yanzu aka fara"""

"Nabila ta ce ""Na gode sosai"" ta tashi ta nufi hanyar fita, babar ramma ta bi ta da ido, dan ranar"

"farko da ta fara ganin Nabila, ban da an gaya mata kafin ta zo, an yi mata bayani, da babu abun da zai hanata kurma ihu, ta ce taga gawa."

"Tana driving sannu a hankali, ta tsaya ta sai abun da zata ci a gida, dan ba sabgar su take shiga ba."

"A harabar gidan, ta wuce Nasir, ya zuba mata ido, duk ta bi ta rame, saboda ta saka jaraba a ranta,"

"ko kallonsa ba ta yi ba ta wuce. Duk sai ya damu da ramar da ya ga tayi, amma yana nan a kan bakansa sai ya kama Viper, ko zata mutu dan haushi."

"""Ga agolancin ga yawon ta zubar, ga ta'addanci, gashi an gandame an ri™a a gida babu aure, abun"

"bai yi miki yawa ba kuwa Nabila"" Sauda tayi maganar tana dariya."

"Ta sake cewa """

"An baki damar ki gusa ki bamu wuri, saboda ba™in naci, kin li™e mana a gida, tun da ba zaki tafi ba, ki iya kanki, muna son ubanmu, ba zaki kashe mana da ba™in cikin ki a banza ba"""

"Nabila ta tsaya cak, tare da murnar Sauda ta takale ta, ko banza ta rage zafi idan ta yaSa mata"

magana.

"""Ke da ki ke son uban naki, sai gashi kin gagara zaman aure, kin ™i karatu balle hankalinsa ya kwanta. Ai sauda zaki yi mini gorin aure ne, a lokacin da ke ki ka iya zama a gidan naki mijin. Kuma karki manta da ni agola ce mai 'yanci, a dalilina igiya biyu aka sauke wa babarki ta aure, idan ku ka cigaba da matsa mini, ragowar Wayan ma sai na tsinketa, sai ku ji daWin zawarci tare ga uwa ga 'ya. Yawon ta zubar kuma, ina da abun bayar wa yayi mini rana, kema idan ki na so ki"

"bayar nonsense"""

"Sauda ta tashi a ™ufule, Nabila ta ce ""Kin san dai ba dakuwa zan yi ba, dama koma wa ki ka yi ki"

"ka zauna"""

"Sauran wanda suke wurin, suka tuntsure da dariya, dan yadda Sauda ke zuba mulki da rashin"

"mutunci a gidan nan, Nabila ce kawai maganinta."

****

"Cikin mamaki Abdul ya Wago ya kalli indabo, saboda marin da ya kwaWa masa."

"""Ina na kai mini kuWi Abdul?"""

Abdul ya yi shiru ya™i magana.

"""Ka gaya mini in da ka kai mini kuWi, kafin na tattaka ka a wurin nan? Yarinya da ka fito da ita, da kar ka fito da ita, matsalarka ce, ba zaka kashe ni da Sacin rai ba, sai na samo wani wanda ba zai"

"watsa mini ™asa a ido ba, ina ka kai mini kuWi?"""

"Mahaifiyar Abdul ta ce ""Abdul wai ba magana ake yi maka ba? Ina kuWin da ya zuba a account W"

"in ka, da sunan campaign kuma ya muka yi da kai a kan yarinyar nan?"""

"Abdul ya numfasa ya ce ""Na yi wa 'yan garin su rahama gyaran makarantu da hanyoyi, na yi musu"

"boreholes, sai kuma registration da nayi mata na karatu bar zuwa jami'a"" ya faWa kai tsaye."

"Salallami suka hau yi, da tafa hannu."

"Indabo ya ce ""Abdul, kuWin ka kwasa ka ™arar a kan garin yar matsiyata da karuwa?"""

"Ya girgiza kai ya ce ""Daddy ba karuwa ba ce ba, koma menene ni ne mai laifi, fyaWe nayi mata,"

"nayi hakan ne, dan na goge laifina"""

"A fusace Indabo ya rufe shi da duka, ga ™iba ga hawan jini yana fama, a take ya hau haki, da kyar"

P.A ya janye shi daga jikinsa.

"""˜arya ma kake yi, ka fito mini da kuWina, sai na yi seazing Win asibitocinka, da duk wata kadara daka mallaka, da wadda na mallaka maka, ni zaka tonawa asiri, wallahi baka isa ba, kuma zan"

"saka a nemo mini yarinyar ko ina ka kai ta, zan yi maganinka daga kai har ita""."

"""Dan Allah daddy kar ka cutar mini da ita, ba tayi laifin komai ba, ni zaka hukunta"""

"Ashariya ya din ga zabgawa Abdul, yama rasa me zai yi, kuWin da suka yi sama da faWi da su, domin campaign bisa ga yarjejeniyar idan an yi nasara zasu mayar da kuWin da uwar riba, ga balli na neman tashi, dama kuWin mutane ne na wasu hukumomi a ™asa, ga balli na neman tashi, kuma"

Abdul ya yi masa hauka.

"P. A ya ce ""Kayi ha™uri, kar ka je wani abun ya sameka, ka rabu da shi, zamu san abun yi, mu fara"

"kashe case Win can na gaban kotu tukuna""."

"""Na fara tunanin anya Abdul Wa na ne? ˜iri™iri ya zaSi mace a kaina, ni zai tozarta?"""

"P.A ya ce ""Jarabta ce da kuma ™uruciya ke damunsa"""

"""A shekara talatin da shidan ne ™uruciya?"" P.A ya din ga bashi ha™uri yana lalaSa shi, Abdul kuwa"

tunu yayi ficewarsa.

*****

"Madaki na zaune a cikin Waki, ya din ga jin hayaniya, da iface-iface ana sara suka a ™ofar gidan"

da yake.

"Wani daga yaran sa ya shigo da kyar, ya ce ""Madaki, yan ™ofa ne fa suka zo gidan nan, muna ta"

"fama da su, sai ™o™ari suke lallai sai sun shigo gidan nan, su sareka"""

"Madaki ya tashi ya ™walalo ido, sai dai kan yayi magana, sun faWo gidan, sun kai su bakwai, suka"

"zo ka hau shi da sara da suka, wasu na waje na faWa da yaran madaki."

"Duk da akwai ™arfin zuciya, yana ta ™o™arin kare kansa, amma sai yaji jikinsa kamar an canza masa wani, duk yayi wani iri babu ™wari, suka din ga saransa, ™arshe suka janyo shi daga cikin gidan, suka din ga jan sa a ™asa tamkar abun banza, duk da iya ™o™arin da yaransa suka yi, su ™ wace shi, amma abu ya ci tura, tsofaffin yaran Viper, da yan unguwar su, da ya din ga shiga yana addabawa ya hana su sukuni, su suka yi gangankon Waukko shi, suka yi masa laga-laga, suka din ga yawo da shi, lungu da sa™o, daga ™arshe da ™yar jami'an tsaro suka kawo masa Wauki, suka"

"tarwatsa matasan, suka Wauke shi a galabaice, dan ba su zaci yana raye ba, suka kai shi Asibiti."

*****

"""My Abdul"" ta yi maganar tana murmushi, cikin hanzari ya Wago, dan bai zaci daga bakin ramma maganar ta fito ba."

"""Meyafaru ne? Gaba Waya na ganka a cikin tashin hankali?"""

"""Rahama abubuwa sun ™ara cakuWe mini, barin ™asar nan zamu yi"""

"Cikin mamaki ta ce ""Mu bar ™asar nan, mu je ina?"""

"""Rahama abubuwa ba zasu tafi yadda na tsara ba, zamu bar Nigeria"""

"""Ban gane ba, uwata fa?"""

"Abdul ya ce ""Zan saka a kawo miki ita, yanzu visa za ayi miki, amma sai na fara barin garin nan"

"da ke"""

"""Abdul, ni fa gani nake wannan guje-gujen, duk ba zasu kaimu ba, kayi ha™uri ka yi abun da"

"mahaifinka ya bu™ata mana"""

"Ya kalleta ya ce ""Na kai ki kotu ki gaya wa duniya, ni ne nayi miki fyaWe? Ba wannan ne ya dame"

"ni ba, abun da zai biyo bayan shaidar da zaki bayar shi ne abun jin, dan haka ki nutsu kiyi abun da na ce kawai"""

"Murmushi ta yi masa da ita kaWai ta san ma'anarsa, ta wuce shi ta tafi kitchen."

****

"Daga Naja'atu har Indabo fuskokinsu Wauke da damuwa, Bunkure tayi ™wafa ta ce ""Gaba Waya hankalina a tashe yake, lallai gaskiyar hausawa, Wan hakin da ka raina, shi ne yake tsole maka ido, yarinyar nan dai ta dage sai ta ga bayana, idan asirina ya tonu, ban san wane irin kallo zan yi wa al'umma ba. Abdul duk shi ya janyo wannan abun."

"P.A ya ce ""Duk ku kwantar da hankalinku, babu wani abu da zai faru, kamar yadda ka yi umarni, dattijon nan zai shiga silent, yanzu uwar yarinyar ta rage, ita muke binciken in da take, kuma ita"

"ma zamu ganota in sha Allah, Abdul ma muna daf da gano, wurin da ya Soye yarinyar nan"""

"Indabo ya girgiza kai ya ce ""Ban san in da Abdul ya koyi wannan ba™in taurin kan ba, magana ta fito fili, an ce a binciki ministocin da muka ™ulla har™allar kuWaWen nan da su, na san kuma dole sai sunana ya fito, wai ya kwashe kuWin nan, ya yi wa yan ™auye ayyukan raya ™asa, na rasa uban abun da ya samu a jikin yarinyar talaka mara galihu, ya nace mata take abun da ta ga dama har"

"haka"""

"Bunkure ta sauke numfashi ta ce ""P.A ya batun barrister Nabila?"""

"""Kamar yadda na gaya muku, sponsiring Win ta ake yi, na gwada sakawa a kamo mini ita, amma"

"hakan ya gagara akwai jami'an da suke bin ta, wanda ba san suwaye ba, kuma da alama ita kanta ba ta san suna bin ta ba"""

"Indabo ya ce ""Kar ku ja da nisa, kankarofi ne, babbar bu™atar sa ya ga ya kai ni ™asa, ya rama"

"abun da nayi masa, kuma yayi kaWan""."

*****

"Nabila na zaune a Wakinta, tunanin ma ta rasa wanne yakamata ta yi, kawai ta ga Nasir ya shigo W"

"akin, ba ta ko motsa ba, balle ya sanya ran za ta kula shi."

"""Nabila"""

"Ta Waga ido ta kalleshi. ""Da gaske ke ki ka nemi a hana kama Aminu Viper"""

"""Eh"" ta faWa a nutse."

"""Nawa aikin ki ke burin Satawa kenan, me nayi miki haka ne?"""

"Ta kalleshi ta ce ""Ba kai nake fatan Satawa aiki ba, duk wani mara gaskiya sai na Sata masa aiki. Gaba Waya ka canza i miss my old DSP, the only person that understand me"" tayi maganar tana"

tashi ta bar shi a Wakin.

"Tana office Win ta, tana son zuwa duba jikin malam garba, tana son zuwa wurin 'yan sanda, tana"

"son ganin Viper, ga kuma maganar Abba da ta tsaye mata, da ya ce taje ta nemi ubanta, ta bar"

masa gida.

"Kenan Abba ya goyi bayan Wan sa, shi ma a wannan karon ya nuna mata, gurbin ido ba ido bane ba."

"Turo ™ofar office Win aka yi, ta tashi zaune sosai daga kashingiWar da tayi, tana tunanin ina ta taSa"

ganin ba™on nata.

"Ya samu wuri ya zauna, suka gaisa, ya ce ""Baki gane ni ba ko?"""

"Ta jinjina kai ta ce ""Gaskiya dai"""

"""Haka ne, magana na zo mu yi da ke mai muhimmanci"""

"Nabila ta ce ""Ok, ina jinka"""

"""Sa™o ne daga wurin distinguish Ma'aruf Indabo, na zo mu yi magana mu fuskanci juna da ke"""

Nabila ta yamutsa fuska tana kallonsa.

"""Muna yi miki tayin ki fanshi kanki da kanki ne, kan abun da ba a so ya afku"""

"""Šan yi sauri, ina da wurin zuwa"""

"P.A ya ce ""Maganar da na zo da ita, ta fi abun da zaki je yi muhimmanci, muna son ki janye"

"shari'ar nan ta batun fyaWe nan, case ne tsakanin ki da Bunkure, kuma ko yanzu kin cika burinki a kanta, akwai ma™udan kuWaWe muddin ki ka aikata abun da na ce"""

"Nabila ta ce ""Malam na yi maka kama da shashasha ne? Da Bunkure nake case Wina, meye nasa a ciki? Bibiyar rayuwata da ya saka aka din ga yi, da ™o™arin kashe ni, duk bai ishe ku ba, shi ne zaka zo mini da maganar bunkure? Wallahi idan kaga na bar case Win nan, to an hukunta ainihin mai laifin ne, kuma muddin wani abu ya same

61 / 67