Chapter 8 Reading SAFARA A TAƁO Kunya Ba Tausayi By FATIMA MUHAMMAD | Hausa Novel READ HAUSA Novels

SAFARA A TAƁO Kunya Ba Tausayi By FATIMA MUHAMMAD | Hausa Novel

Author :  FATIMA MUHAMMAD Category :  African Stories & Novels

Chapter   8 / 62

21K to 24K   out of 184.1K words

kallo tare da mahaifiyarsu suka haWa baki ""Ciki??? Tabbbbb"""

Nusaiba da ita ce ta Wora da

"""Aiko wallahi in haka ne ba'a gidan nan ba don ba za'a hana mu auruwa ba saboda waenda su sun riga sun saba sai dai Daddy ya zaSa wallahi don dai da irin Hibbah a zuri'a gwara babu.."""

Hajiya Zakiya tace

"""Ai tunda ya Wauko uwarsu ya san me ya kwaso yana murna da ta zuba mishi maza ba bai sani ba duk gayyar 'ya'yan Kuka ne..."""

"""YA ISHEKU DUKA!!!"""

Daddy ya daka musu tsawa.

"""Ku Sace min da gani tun kan in sassaSa muku kamanni"""

"Yaran duk suka watse, ya dubi Hajiya kamila yace ""Duk ku uku ku zo nan"""

"Yana kai nan ya juya ya koma parlornshi, sai mita Hajiya kamila ke yi har suka isa suka"

"zazzauna, Momma dai shiru bata ce uffan ba."

"""Abin naki ya kai a gaban idona kike jefar Wiyar cikina da ciki out of wedluck? Kamila ko kunyar ubangiji ba zaki ji ba? Wallahi ko da wasa na sake jin wannan kalma a gidana zan Wauki mummunan mataki a kanki, duka yaranmu basu fi karfin kowace iriyar kaddara ba, kuma idan baki kiyaye bakinki ba sai Allah ya hukuntaki bisa dariyar ™addarar Hibbah da kike har kika mayar dashi abin zagi da habaici. Na gayamiki wannan ne karo na karshe da zan ja kunnen ki"

"akan aibatamin yara da mata ta mummunar hanya"""

"""Amma Alhj a fa gaban idonka yarinyar nan ta yi min rashin kunya har ta nemi ta kai min hannu duk baka gani ba sai don na ce tana da ciki, idan ba Wakin saurayi taje ba wani saurayin ne zai samu hotunanta har ya yaWa duniya tana sanye da panti da breziya?"""

"Runtse ido Mommah tayi don maganan ya daketa da har take sake ganin hotunan da ta gani ranar da aka fasa auren Hibbah Win da sauri ta mi™e ta fice daga parlorn hatta kalar pant da bz din dawo mata yake a kai yana sakata ganin jiri, Daddy yayi shiru kawai idanunshi da suka sauya sossai akan Hajiya kamilar, ta ja kwafa ta tashi ta fice ko a haka bukatarta ya biya ta ba™anta ran matar son, don wulakanci zai wani ce kar ta sake aibata mishi mata ta ga ita Win ma igiyoyi ukun ne kanta, sai da ma ta fara samu kan ita wacce yake fifitawar yana ganinta uwar"

Maza ta samu.

Hajiya Zakiya da take kallonshi tayi murmushi kaWan kan tace

"""Ka yi ha™uri gaskiya kalaman sun yi tsauri in shaa Allahu ba zaka sake jin su ba, bari na je na ba ita Fatimar ma ha™uri ai duk ba zamu yi wannan fata ba ko don 'ya'ya mata da muke dasu mu ma"""

Numfashi ya Wan sau™e kan ya gyaWa kai a sanyaye ya ce

"""Don Allah ku dinga tausayin yarinyar nan Fatima, ko don saboda ha™uri da take dashi da"

"kawaici ga girma da take ba kowaccenku"""

Ta Wan taSe baki kan ta mi™e

"""In shaa Allahu. Na barka lafiya"""

Tana kai nan ta fice tana kwashewa yarinya da ya kira Momma dashi albarka.

"Ita kam Hibbah tana shiga parlor ta ci karo da Aina'u da Mumtaz bata ko tsaya yi musu magana ba ta haura abin ta, dawowar Momma duk ya sake saka jikinsu sanyi ganin yanayinta Aina'u tace"

"""Ni kam Ya Mumtaz anya Adda Hibbahn nan!"""

"""Kul! Kul nake gaya miki kallonki kawai nake yi dama na fahimci gani gani da kike yi mata, bari kiji su Hajiya kamila ko da Hibbah ko babu ita za su ja Momma a ™asa, ki daina ganin kaman saboda Adda Hibbah ne tun kafin ma a haife ta a haka suke kawai Hibbah ba zata iya shiru bane mu kuma mun zabi mu yi shirun a lokuta da dama amma sau dayawa Adda Hibbah na burgeni ta yadda take kare mahaifiyarta with all her might. Sannan kaddara ce ta faWa mata har ke baki fi ™arfi ba kar ki ga don kin yi tsawo kin kamota ko kin fara kula samari shi zai sa ki raina ta don abin da ya faru da ita, tana bukatarmu duka a gangarta don haka don Allah Aina'u ki"

"natsu ki fahimci yadda ya kamata ki tafiyar da alakarku da yayarki da ta fi kowa shan wahalarki"""

"Yana kai nan ya tashi ya fice ya barta da tunani, hakika bata kyauta ba a duk abubuwan da suke faruwa ta bari shaidan ya saka mata jin haushin 'yar uwarta tana tunanin kawai zata kashe musu uwa ne alhali ita ma ta san zafin uwar tunda tata ce itama, sannan da gaskiyar Mumtaz idan su ba zasu iya karbarwa uwarsu faWa ba ita ta zaSi hakan don babu wanda zai ga ana taka"

uwarshi ya kyale musamman idan irin Momma ce da bata ™aunar hayaniya.

"Mi™ewa tayi ta nufi sama wurin Hibbahn, sai ta samu ta watsa ruwa kenan ta fito ganin"

Shigowar Aina'un bai sa ta tsayar da abin da take yi ba har ta iso gangarta ta zauna

"""Addah Hibbah don Allah ki yi ha™uri da abubuwan da suka ta faruwa, na san ban kyauta ba"""

Murmushi ta yi

"""Ba komai Aina'u, ke kalar naki nuna jin haushin kenan ga shirmena na fahimceki"""

Numfashi ta sau™e ta cigaba da zama gangar yayartata dama Waki daya suke kwana daga lokacin kuma suka cigaba da shirin su kaman baya Dukda dama kusancinsu ba kaman ita da Hudah ba da suke komai tare.

"Fara raka Hibbah asibiti da Aina'u ta yi shine sanadiyar fara wayar Dr. Najeeb da Hibbah sossai suka samu kusanci sanadiyar wayan don idan ya kira Aina'u za ta bata su sha hirarsu, maganar makaranta kam tace ba yanzu ba so Daddy ya saka an yi mata deffering semester Win kila"

bayan watanni uku ko huWu ta ji zata iya komawa.

"A yanzu watanni biyar kenan churr da watse zancen aurenta, har yau mijin Amal dai bai dawo ba tana gida tun ma Daddy na fahimtar zantukar mahaifin nashi har ya daina fahimta a gida kuma sun matsa mishi lamba akan yayi wani abu ai asiri ne aka yi don a rabata da shi da kuma"

gidan aurenta.

"Ta Sangaren Hudah zamanta dai ba zata ce ga wani tarin farin ciki da ta tsinta ba saboda matsawar hajiyar Mu'azzam da Falmata, a hankali ta fahimci falmata ce ke zuwa Wakinta ta Waukarta mata kaya ta saka, ranar da ta fara fahimta bata ce komai ba da zata tafi makaranta ta cewa Mu'azzam idan zai fita ya tabbatar ya rufe mata sashe kuma ya tafi da key yace"

"""Akan me? Bayan ga su Hajiya a gida? Bamu yarda da su ba kenan ma idan za mu kama rufe"

"sashe kan mu fita"""

"""Ba maganan yarda bane, kowa na da nashi privacy Win Wakin baccina ko naka ba abin da zan iya sakaka dashi bane bare bana son abin da zai janyo min magana har a ga laifina don haka don Allah kawai ka rufe Win"""

Bai ja ba ya rufe suka fita Haba ko da suka dawo hajiyar shi duka ne kawai bata kai musu ba.

"Irin maganganu da tayi ta yada wa ya sa dole ya ba Hudah ha™uri akan za su bar mata key Win ko da sun rufe, sam bai fahimci abin da take so ya fahimta ba har saida ta sake ganin falmata da kayanta a ranar Hibbah ta je gidan da Aina'u don a yanzu ta kan fita sa'i da lokaci kuma Daddy ya bata wayoyinta da car key Winta don duk gidan ita kaWai ce take tuka mota saboda masifar son injuna da Allah ya yi ta dashi tun tana karama ita ko wasan baby doll bata yi sai na"

motoci da parts Winsu.

Irin kallon da Hudahn tayi ta bin Falmata da shi ne ranta na nuna a fili ya Saci ya sa Hibbah ta yi magana

"""Twinee! Lafiya ko? Tana miki wani abu ne?"""

Numfashi ta sau™e

"""Ban san ta ina zan Sullowa wannan al'amari ba twinee, yarinyar nan idan ta tashi kawai sai dai ta shiga Wakina ta daukar min kaya ba tambaya ba komai sai dai in gani jikinta"""

"""Kan bala'i! Kuma ta dawo da shi ki dauka ki sa??"""

Girgiza kai ta yi

"""Ko ta dawo dashi dauka nake in mayar mata har gaban mahaifiyarta amma abin na yawa, na rasa ta ina zan fara daukar mataki in yi magana Hajiyarshi tace ina musu gani gani don mahaifina ya fi su arziki alhali wallahi ban taSa kawo ko da hirar abin da ya shafi iyayena bane a gabansu"""

Ta ™arasa tsiririn hawaye na gangaro mata

"""Ni ban san me na tsare musu ba, aikin duk da nake musu na abinci safe, rana dare duk gajiya ko jiggatar school bai dame ni ba amma kin ga kananun maganganu da yawan kaiwa Mu'azzam"

"™arata da har yake ganin ina yiwa mahaifiyarshi rashin kunya abin na damuna"""

"""Ina zuwa!"""

Ta faWa tana ™o™arin Mi™ewa da hanzari Hudah ta mayar da ita zaune.

"""Ina za ki je? Ki rufa min asiri Hibbah don Allah"""

Da kyar Hudah ta hana Hibbah fita don ta san wallahi tsaf zata je ne ta samu falmata ta tsefe ta don yanzu hibban da ce ba wacce kaddara ya so ruguzawa ba.

"Aunty Kubra Hibbah ta ™ira a labari take ce mata ai aiki ya yi wa Hudah yawa ga girki ga kula da gida ga makaranta tana jiggata don Allah ta sa Momma ta dinga tura mata mai tayata ayyukan ko da yini ne take yi, ta kuwa yarda da shawarar Hibbahn suka sake hira kadan suka yi sallama suka fito, ko hajiyar bata je ta gaisar ba don haushinsu take ji suka bar gidan wanda hakan sai da ya zama abin magana a wurinta ai Hibbah marar kunya ce, dama fitsarar da ake cewa ta yi ashe kaWan ne tunda gashi ta zo ta musu a gida, sossai Mu'azzam din ya chanzawa Hudah"

amma haka ta ba su ha™uri.

"Bayan kwana biyu Momma ta yi wa Daddy bayanin batun mai taya Huda aiki ya kuwa amince aka tura ta, ranar da ta je hajiyar ta sa Mu'azzam ya sallame ta akan basa bu™ata wato sun raina shi ne ma da arzikinsa da har za su Wauki mai aiki su ce babanta ne zai dinga biya, idan yana bukata zai Wauka da kuWin shi wannan abu ya matu™ar cika Hibbah, aiko ranar da ta tabbatar Hudah na school ta san ba zata samu Mu'azzam a gida ba ta shirya tsaff ta nufi Gidan"

Hudar bayan ta cewa Momma asibiti zata.

"*Littafin nan na kuWi ne ki biya Naira Šari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faWakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun"

0545475847

Gt bank

Fatima Muhammad Gurin

Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763

Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi.

Sai na ji ku*

Note: Da dare ne zan dinga posting da rana zan bi in dinga karanta comments naku so please a

ba ni haWin kai mu tafi lafiya kaman yadda muka fara lafiya. Na gode sossai.

Gureenjoh

SAFARA A TAO

FATIMA MUHAMMAD GURIN

*GUREENJOH*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*PAID BOOK*

*010*

"Ta isa gidan kai tsaye sashensu hajiyar ta yi, ta kuwa sameta tana zaune tana hutawa. ""Barka da hutawa Hajiya"""

Ta faWa tana zama.

"""Yauwa, ya aka yi kika tashi da wuri yau? Ko tun dama chan kina tashin yawonki kawai kike tafiya?"""

Ido ta Wan tsayar a kanta

"""Ai Hajiya ban isa yin wannan hali ba don gidan da na fito ya fi gaban nan"""

"Da Wan sauri ta kalleta don bata zaci samun amsa ba kaman yadda ta saba da Hudah, kuma sam bata fahimci cewa ba Hudar ba ce."

"""A ina kenan aka saba da yawon?"""

"""Uhmm ai ba za'a ji mutuwar sarki a bakina ba, dama makulli na zo amsa wanda Mu'azzam ya baki"""

"Ido ta zaro cike da mamaki kala biyu, a gabanta take kiran sunan Mu'azzam gatsal? Sannan ita zata faWawa magana a fakaice?"

"""Ko ba'a ji a bakinki ba ai an sani ne don an ce kura ma ta san gidan mai babban sanda, don"

"nan kam baki ga tambarin hakan ba. Sannan batun makulli ina ga ai shi Mu'azzam din kika ce ya ba ni saboda haka ki jira ya zo sai ya karSar miki."""

"""Meyasa? Na ga gidana ne kuma sashena ne, kayan dake ciki kuma nawa ne ko kina tsoron ba"

"ni in ™i dawowar ne a rasa na zuwa saane?"""

"Da sauri hajiyar ta mi™e tsaye, itama Hibbah ta mi™e tana kallonta a ido ""Ni kike ™ira Sarauniya? Da ni kike sa'insa?"""

Ta Wan yi farr

"""Ni??? ai ban isa ba, ina son albarkarki ba zan taSa kiranki Sarauniya ko yin sa'insa da ke ba na ga dai hira ce tsakanin uwa da Wiya muke y. """

"""Allah ya sawaake in haifi irinki, dama tun farko ba son wannan aure na Mu'azzam nake ba gashi nan ba'a je ko ina ba kina nema ki min rashin kunya ki kalli cikin idona don tsageranci ki zage ni! Toh wallahi zai dawo ya sameni aure zan masa"""

"TaSe baki Hibbah ta yi tana jin haushin Mu'azzam din na kamata fiye da Hajiyar don duk laifin shi ne, shi ya kamata ya taka ma mahaifiyarshi da ™anwarshi birki idan dai tabbas yana kaunar matar shi, wani irin auren soyayya ne wannan? Ana ganin kaman Hudah ta yi aure tana hutawa"

ai da zama da irin hajiyar Mu'azzam wallahi gwara mata ta tabbata bata da aure.

"""Ina bukatar key a yanzu dai sashena ne kafin ki kawo wacce zaki kawon"""

Har lokacin mamaki da kaWuwa bai bar hajiyar ba ta zaci Hudah shiru shiru ce kuma natsatsiya ta yadda bata ko Waga ido ta kalleta yau ita ce take kallonta cikin ido?

"""Hajiya!"""

"Ta sake kiranta tana kallonta sai kawai hajiyar ta Wauki keyn ta jefa mata, ta tsuguna ta Wauka ta"

Wago ta kalleta a ranta tana cewa za ki gani.

"Ta fice daga sashen ta nufi na Hudah ta buWe ta shiga, kai tsaye kitchen ta je ta shiga girki wata iriyar shinkafa ta dafa kofi uku ita ba danya ba ita ba nunanna ba ta zabga yaji don atturugu goma sha wani abu ta zuba ta yadda sai ka WanWana za ka gane, ta juye a warmer ta ajiye."

Cikin natsuwa ta girka wani farin macroni da sauce ta zuba kuloli daban ta kai parlor ta dibo

kaWan ta zo ta zauna tana ci kenan sai ga Falmata ta shigo ita da wata yarinya da daga gani rashin kunya ne fal cikinta.

Basu yi sallama ba don haka bata ko Wago ta kallesu ba.

"""Hudah! Hajiyar kika je kika yi ta yi wa rashin kunya? Ashe baki da mutunci? Nan Win fa gidan yayana ne, guminshi ne ba na uba..."""

"Šago ido da tayi ta kalleta a zafafe shi ya katse mata maganar, ran Hibbah ya zo wuya Dukda ta so ne ta yi maganin abin da fatar baki amma tana ganin sai ta karya yarinyar nan dake tsaye"

hankalinta zai kwanta.

"""Dama a cushe muka karSeki ba don muna so ba, ga abin kunya da aka zabga lokacin biki da har yanzu kunyar ma a ce mun haWa zuri'a da gidanku nake... Kinga 'yar dangi kuma Wiyar mutunci ita ce zata shigo ta zama matar ™warai don na tabbatar ba zata taSa yi wa uwarmu fitsara irin naki ba..."""

Maganar farkon a gunguni ta yi na biyun ne tayi shi a fili kuma da kyau amma duk Hibbah ta ji.

"""Fita a parlorn nan"" Ta faWa cikin gargaWi."

"""Sai ki gayamin idan da shi kika zo a ™unshin gararki"" Remote ta Wauka ta chanza channel ta kalli Raliya ""Shiga ki duba gidanki ne ke a very soon.."""

Abincin Hibbah ta ajiye daga Raliyar har Falmata sai gwaruwar kansu suka ji wuri guda

™uuuummm.

"Kan su gama fahimtar bomb ne ya sau™a ko menene ta rufe su da duka, sun kasa kare kansu"

ta nemi wayar wuta ta shigesu ihu kawai suke na neman agaji da taimako don basu taSa tunanin za ta iya dukansu ba har su biyu.

"""Na rantse da girman zatin Allah ko kofar sashen nan kika kara takowa bare har cikin parlorn nan ko zuwa cikin Waki don min bincike ko Waukar min kaya sai na yi miki abin da ya fi wannan ai ba hauka bane. Baki da hankali? Ke ba mace ba ce? Baki san boundaries Winki ba baki san zuru ba?? To ki dawo ki cigaba da rashin kunyar ki ga idan na cigaba da kallonki..."""

Hauka sossai ta nuna musu ai a tsiyace suka tsira da kyar jiki duk ciwuka da tabbuna.

"Gyare parlorn ta yi tana haki ta nufi kitchen ta Wauki kular shinkafar ta bi bayansu, kuka ta samu suna risga ganinta ya sa har rige-rigen shige wa Waki suke don sun tsorata, hajiyar ta mi™e"

tsaye

"""Hudah! Hudah falmata kika kama da duka kaman kin haife ta? Uban me suka miki haka? Ko"

"ma me suka miki uban wa ya baki damar taSa min yarinya?"""

"""Idan da sun zauna iya matsayarsu da yanzu kila suna nan jiki bai ci na jaki ba, amma dayake marasa kunya ne sun gane kurensu."

"Hajiya bari na fito miki a mutum, wallahi ba duka ba sai in kakkarya falmata in watsar kuma babu abinda aka isa a yi min muddin ta sake taka kafarta sashena da rigima ko rashin kunya. Wallahi wannan kaWan ne muddin ta sake taSa abin da yake nawa ba tare da sanina ba, you guys should be on your length ku barni na sha iska a gidana habaa!"""

Hawaye ma take ji tsabar bakin cikin da take ji wa Hudah.

Hajiyar ma ta tsorata don idanunta sun kasa Soye wa

"""Toh fa dama mai aljannu Mu'azzam din ya Wauko mini ni Tani..."" ""Sai dai Mayu don aljannu ma kila sun yi kaWan"""

"Tana kai nan ta fice ta bar hajiyar baki sake, ai da gudu taje ta rarumo wayanta ta shiga kiran Mu'azzam yana Wauka ta hau ihun ya kawo musu ceto Hudah zata kashe su a gidan don dab"

"take da ™one su su mutu, hankalinshi ya tashi a fujajan ya baro wurin aikin nashi yayi gidan."

"A hanya ta gamu da Hudah zata je karSo key, ido ta zaro ganinta."

"""Hibbah! Me kike yi a gidan nan? Meyasa ban ga motarki ba? Daga fa sashen Hajiya na ganki..."""

"Janta Hibbah tayi suka yi parlornta suka zauna ""Hibbah me ya faru? Baki yi wani abin ba ko?"""

"""Falmata da wacce uwar mijinki ke son aura mishi na daka! Na yi musu jina-jina""

8 / 62