Chapter 62 Reading SAFARA A TAƁO Kunya Ba Tausayi By FATIMA MUHAMMAD | Hausa Novel READ HAUSA Novels

SAFARA A TAƁO Kunya Ba Tausayi By FATIMA MUHAMMAD | Hausa Novel

Author :  FATIMA MUHAMMAD Category :  African Stories & Novels

Chapter   62 / 62

183K to 184.1K   out of 184.1K words

ganin na zama mutumin kirkin, kila ba don kai Win ba da a yanzu ban san wani hali nake ciki ba da rayuwata"""

Hibbah da ta matso ne tace

"""Ina tayaka murnan fitowa Mahir"""

"Ya kalleta ta kara girma, ta sauya sossai ta yi wani irin kyau, alamunta suna nuna kula da dukiya sun zauna mata kwarai da gaske."

"Ya kalli MB, MB yayi murmushi ""Ga Matata uwar 'ya'yana Mahir"""

Mahir yayi murmushi

"""Kun dace da juna Yaya, ina Abbana?"" ""Yana gida yana jiranka"""

"Nan suka dunguma zuwa mota, driver ke ja Mahir na daga gefenshi Hibbah da MB na baya har lokacin ransu kal na ganin sauyawar Mahir Win har suka isa gidan Abban da ya sauya sossai"

saboda gyara da kula da yake samu.

"Ciki suka nufa parlorn hayaniya ne fal cikinsa har waje suke jiyowa, suna kutsa kai Jasrah ta biyo Manar za ta daka MB yayi saurin dageta sama yana cewa"

"""Ya ilahi Me Ummanmu ta miki za ki daketa Adda manga?"""

Ta tura baki

"""Daddy Manar bata ji, tun Wazu fa sai tsokanan Inaaya take yi don ta samu yarinya mai ha™uri,"

"nayi ta magana sai tayi kaman ta bari ina juyawa za ta cigaba"""

"Hibbah tayi murmushi don Manar wane Hibbah tana karama duk wani halin Hibba na tsokana, faWa da rashin barin ko ta kwana duk ta kwashe."

Inaaya 'yan biyunta ce ba karamin wahala take sha da ita ba sai ta tuna su da Hudah.

Mahir yace

"""Masha Allah, yanzu duk nan zuri'arka ne Yaya?"""

Jasrah ta kura mishi idanu tana tuna inda ta sanshi amma ta kasa tunawa shima yana kallonta yace

"""Jasrah?"""

Sai tayi murmushi ta gaishe shi hawaye ne ya shiga zubo mishi.

Hibbah tace

"""Duk ku zo ku gaida Uncle Winki Uncle Mahir"""

MB ya ce

"""Ga Chan Jawad shi ke bin Jasrah, sai wanchan dake ta aikin zanen shi ne Abba kenan Bashir muna kiranshi Aryan sai twins Inaaya me sunan Momma(Fatima) da Manar me sunan Umma(Aisha)""."

"""Masha Allah, Allah ubangiji ya raya mana su cikin tafarki madaidaici"""

suka amsa da Ameen suna zama.

"""Jasrah kira Abba"""

Ta haura sama da sauri tana amsawa baban nata.

"Yaran da ba'a mishi bayani ba ya nuna su biyu da suke ta wasansu suma ""Waennan fah?"""

Hibbah ce ta amsa

"""jikokin Mama ne, Amaryar Abba wanchan Wiyar Zainab Sa'idah sai karamin Shuraim yaron Amirah"""

Allah sarki kan yayi wani magana Abba ya sauko.

"Sai yaje ya rungumeshi suka shiga kuka a tare yana neman Yafiyar Abba Abban ma na neman yafiyarshi, da kyar suka yi shiru Hibbah ta sa Jasrah ta haWe yaran suka yi baya suna wasa anan Mahir ya sake neman yafiyar kowa a wurin da ya cutar ciki har da Hibbah suka ce sun"

yafe.

"Ya san labarin mamanshi don haka bai tambaya ba, sai da ya natsu kwarai ya fi watanni uku da fitowa kan ya karbi kudi wurin Abba ya tafi Nassarawa neman Mum, ko ba komai tana da hakki"

"a kanshi da dole ya saukar, gidan Yayanta ya sameta sun yi mata Waki daga chan gefen kofa"

"gado na karfe me spring Win nan ne Wakin sai katifa da ya tsotse kwarai, kafarta daya daure da sarka da iyakacinshi zai barta ta zagaye Wakin a Wakin take kashi da fitsari, daga bakin kofan Wakin suke ajiye mata abin da suka samu don suma ba arziki bane da su kuma da tana da shi"

ba taimakonsu tayi ba.

"Ita da skeleton ba maraba, ta jeme ta kare ga rashin bacci da ya haifar mata da hauka yau tana lafiya gobe tuburan idan ta rufe da niyyar bacci babu wanda take gani sai Rabi'ah da Anam gashi bata magana ta azabtu kwarai, da kyar ta iya gane Mahir sun yi kuka sossai a tare tana mishi maganan kurame tana ro™on shi ya yafe mata kuma ya nema mata yafiya wurin su Almustapha da Abba, a hannunshi ta cika cikin mummunan yanayi yayi kuka yayi kuka kaman ba gobe haka yayi mata wanka ya suturtata ya kira su suka zo aka yi mata sallah aka kaita kan ya juyo ya dawo legos da labarin rasuwarta Abba da MB suka ce Allah ya yafe mata kawai daga"

nan babu wanda ya sake batun ta.

****

"Cikin wasu kyawawan Pajamas Wine colour Hibbah ta shirya tayi barin turare musamman inda ta san MB na son shaka a jikinta wuyanta da bayan kunnenta, don tsokana har da Red lip stick ta zizara tayi wani irin kyau kaman ka saceta don ba za ka ce ta yi haihuwa uku ba yara huWu,"

gidan shiru alamun kowa yayi bacci ta nufi Wakinshi..

"Yana tsaye jikin madubi shima wanka ya fito yana fesa turarukanshi ta buWe kofan ta shigo, sassanyar kamshinta shi ya sanar da shi tana kusa sossai ya Waga idanu ya zuba mata ta cikin madubi sai ta sauya tafiya tana mishi wani irin yanga, kasa jure kallon madubin yayi ya juyo gabaWaya yana dafe zuciyarshi"

"""Wayyoo Allahna Sugar za ki yi kisa"""

Tayi mishi wani murmushin tare da blowing mishi Kiss a iska ya cafe yana sake mannawa

"kirjinshi, ba zai iya jure yangarta ba ya nufeta ya rungume tsamtsam yana sauke numfashi."

"""Watarana sai sonki yayi ajalina Sugar! Zuciyata bugawa take da Sunanki, siffarki da tsantsar"

"™aunarki"""

Ta lumshe ido tana shakar kamshinshi a hankali tace

"""Ina kaunarka kwarai nima Rouhy, kar ka manta kai ne fa ka tsamo ni daga doguwar SAFARA A TAO da na Wauko tun daga balagata bata ™are ba sai da na ci karo da kai a hanyar ™addarata ka zare ni ka wanke ni fesss da farin ruwa na fita kal kan ka Wora ni bisa jirgin sama wanda ba zan sake tuntube da taSo ba bare ya Sata ni har ya bakanta zuciyata...My plan was to never fall inlove again sai kwatsam na ci karo da Wan kyakyawan saurayina, ya zama Mayen Hibbah, mai nagarta, mai kyakyawar murmushi da iya lafazi, mai kyakyawar nasaba, tall and charming, My 1"

"in a billion I can't resist him dole ya mayar da Hibbah ruwa a soyayyarsa..."""

Bata ™arasa ba ya haWe lips Winsu ya fara bata psssionate Kiss hannayenshi na yawo a jikinta yana birkitata a kaunarshi da kyar ya raba bakinsu ya ce

"""Sugar kin ja yau dai sai Rouhynki ya samarwa su Manar kanne twins maza in shaa Allah"""

Daga nan suka yi kan gado cikin tsantsar ™auna suka raya daren.

Ya ™an™ameta bayan lafawar komai

"""You always give me peace Sugar, kin bani abin da ko duniya aka hada babu mai bani irinshi,"

"thank you for being with me always... ina ™aunarki! I love you Forever and always Sugarplum!"""

TAMMAT BI HAMDILLAH

"ANAN NA KAWO KARSHEN WANNAN LITTAFIN ABINDA MUKA RUBUTA DAIDAI ALLAH UBANGIJI YA BAMU LADA, WANDA MUKA KUSKURE YA YAFE MANA. A WANNAN TAFIYA IN AKWAI WANI WANDA NA SAAWA DA SANINA KO BA DA SANINA BA INA RO˜ON YA YAFE MIN NIMA NA YAFEWA KOWA DUNIYA DA LAHIRA, ALLAH UBANGIJI YA HAŠA MU A WANI SABON LABARIN. NA GODE! NA GODE!! NA GODE KWARAI DA GASKE DA ˜AUNARKU GARENI ALLAH UBANGIJI YA BAR ZUMUNCI. I WILL MISS YOU GUYS LIKE"

CRAZY MY PEN FAMILY 

62 / 62