Chapter 14 Reading SAFARA A TAƁO Kunya Ba Tausayi By FATIMA MUHAMMAD | Hausa Novel READ HAUSA Novels

SAFARA A TAƁO Kunya Ba Tausayi By FATIMA MUHAMMAD | Hausa Novel

Author :  FATIMA MUHAMMAD Category :  African Stories & Novels

Chapter   14 / 62

39K to 42K   out of 184.1K words

saboda lafiyarka kar ka manta sai da lafiya ake komai"""

"Numfashi ya sauke a hankali kan ya kalleta da idanunshi da suke a rine ""Fatima Ya Hibbah?"""

Itama dai cikin 'yar damuwa tace

"""Idan na ce maka lafiyarta ™alau na yi ™arya, Hibbah banda kuka da damuwa babu abin da take yi tsawon sati biyu kenan ko magana sai ya kama dole take yi shima sai da ni amma ™annenta kam ko kallonsu bata yi, dole ta shiga wannan hali dama duba da yanayin yadda kaddararta ya faro amma komai zai wuce with time za ta manta"""

"""Ina tsoro Fatima, ina tsananin tsoron alhakin Aisha ne ke bibiyar yarinyata ina tsananin son neman yafiyarta amma ban san ta yaya ba, dole mijinta sai yayi min umurnin zuwa gidanshi duk kuma sadda zan ™ira kina ji yana cewa Aisha bata shirya ganina ba in yi ha™uri, office na Najeeb kuwa sun ce ma ya cika wani course wani sati zai bar ™asar nan kuma na san duk saboda su kaurace mini ne, a nan Hibbah ta kasa lafiya da sukuni duk na rasa Makama ba dole"

"na shiga halin damuwa da tunani ba Fatima."""

Ta ri™o hannunshi Waya

"""Komai zai daidaita ni na gayamaka hakan amma sai ka kara hakuri da juriya, Allah da zuciya yake amfani kuma yana sane da cewa tun ba yau ba ka yi nadamar duk abin da ya faru a baya bisa kaddara da sharrin shaidan su ma in shaa Allahu za su sau™o ne ai kai uba ne a gareshi kuma har abada hakan ba zai chanza ba"""

"""hmmm"""

"Shine kawai abin da ya iya cewa, saboda ya kwantar mata da hankali ya sake kaWan don duk cikin matanshi ita ce take a tare da shi take kuma kwantar masa da hankali bisa damuwar da ya jima ciki, Hajiya kamila kam ma banda kananun habaice habaice babu abin da take, kuma yana sane da duk takaicinsu me yasa Najeeb babban danshi ya zama namiji, idan ya tuna yadda ya ga Najeeb cikakke, kamilallen namiji mai kwazo akan aikinshi sai ya ji tamkar ya lalabo shi duk inda ya shiga ta karfin tsiya ya dawo dashi kusa dashi amma bashi da wannan dama don ya riga yayi wasa da ita tun a baya, a Sangaren Hibbah ma da yake jinta tamkar rai yana iya taya"

ta jin raWaWi da zafin rasa namiji irin Najeeb da ta sanyawa rai...

"Tana zaune daga bakin gado da karamin hijabi a kanta hannunta alqur'ani ne take karantawa, Dukda ba kuka take ba sai dai fuskarta yana nuna halin da take ciki na rashin walwala, ta rame sossai ta kuma kara haske, turo kofar Wakin aka yi bata Wago ba sai da ta kai aya ta Waga ido ta"

kalli Aina'u dake tsaye bisa kanta

"""Ya Nasir ne ya zo yana son ganin ki"""

"Tsaki tayi a fili Aina'u ta juya ta fita, idan tace bata fara jin haushin Nasir ba tayi ™arya Dukda ba wani abu yake zuwa mata ba bayan duba lafiyarta da kuma ™o™arin kwantar mata da hankali tunda abin nan ya faru sai dai tuni ta tattare maza ta yi musu kuWin goro. Ta san Najeeb ba yaudararta yayi ba sai dai cin amanar da Daddynta yayi ne Allah ya rama wa Umma a kanta hakan in ta tuna sai ta ji kunci da damuwa sun sake mamaye ruhinta, qur'anin ta rufe ta mi™e ta"

fito babban parlorn ta same shi zaune yana hira da su Fadeel.

"""Gashi oya a je a yi wasa"""

KarSar choculates da yake basu suka yi suka fice da gudu.

"Ya kalleta jin ta yi shiru ""˜anwata ba gaisuwa?"" Numfashi ta sau™e a hankali tace ""Ina yini Yaya Nasir"""

Girgiza kai yayi ha™i™a yana tausayinta don dole duk wanda ya ganta ko ya ji labarinta ta bashi

tausayi.

"""Lafiya ™alau. Yau da albishir na zo miki mai daaWi"" Kallonshi kawai tayi da idanunta ba tare da ta yi magana ba."

"""Na san burinki na karatun Engineering babu yadda kika iya ne kike yin Biotech a Skyline to kuma kaddara ta yanke karatun don idan na tuna kin ce min kina jin kin bar makarantar kenan har abada shine da na ga an fara ba da Admission Unilag na nema miki kuma Alhamdulillah kin"

"samu field da kike so..."""

Ya ™arasa maganan yana zaro farin paper daga cikin Brown envelope dake kusa da shi ya mi™a

mata.

"Ha™i™a cikin sati biyun nan wannan ne abu na farko da ya sa zuciyarta ya washe, wani farin ciki ya ratsa ciki, a hankali murmushi marar nauyi ya ziyarci fuskarta ta Wago tana kallonshi ya sakar mata murmushi"

"""KarSa mana kanwata naki ne! Na san za ki bu™aci karatun kwarai saboda debe kewa"""

Mi™ewa tayi ta je ta sa hannu ta karSa aiko ga sunanta nan raWau kan takardar da ke nuna samun gurbin karatun ta.

"""Na gode sossai Yaya Nasir"""

"Tayi maganan tana kallonshi ya mata murmushi yana jin daaWin ganin walwala a fuskarta ""Yauwa kanwata ki cigaba da wannan farin cikin komai zai wuce kin ji?"""

"Kai ta gyaWa dole ne ta bar komai ya wuce Win tunda damuwa ko kuka bai isa sauya cewa Ubansu Waya da namijin da ta gama mafarkin rayuwar aure da shi ba, kuma ta ji za ta iya yin karatun don yanzu gidan da ma garin Kano ya sire mata daga zuciya babu abin da ke bata farin ciki daga rayuwar bayan alqur'ani da ta saka a gaba. Bai matsa mata ba ya yi mata sallama ya tafi yana cewa ta shirya komai don an fara lectures idan su Momma sun amince zai musu"

booking flight tare don shima next week zai koma..

"Šaki ta wuce hannunta rike da Admission Win, ba ita ta sau™o ba sai bayan Magrib ta samu Momma a Wakinta zaune kan sallaya Dukda ta idar da sallah tana zaune ne zaman jiran isha hannunta da chasbi tana hailala, admission Win ta mi™a mata a hankali kuma karon farko da ta"

yi magana mai tsawo da momman tun bayan abin da ya faru ta zama kurma karfi da yaji.

"""Momma Yaya Nasir ne ya nemar min admission a Lagos, course kuma da nake so Engineering ina fata a wannan karo ba za ku hanani cika burina ba kila aure ba ya daga cikin kaddarata na"

"nan kusa."""

Cike da wani yanayi Momma take kallonta kan ta karSi admission Win ta gani ta sake mayar mata

"""Allah ya sanya mishi albarka, kuma bani da wani matsala da hakan don na tabbatar kika je ma gidan Adda Kubra ne masaukinki za kuma ta baki duk wani kulawa da tarbiya fiye ma da yadda ni zan baki tunda dukkanmu itace ta Wora mu bisa turbar da muke kai. Sai dai Mahaifinki nake ji, kaman yadda kika sani bashi da ra'ayin nesantar mace da gabanshi da sunan karatu wanda tun farko dalilin da ya hana ki tafiya Lagos Win kenan karatu amma ba zan hanaki ba ki kai mishi da"

"kanki ki mishi bayani idan ya amince falillahil hamd"""

"Daga yanayinta Momma ta san bata ji daaWin batun kaiwa mahaifinta admission Win ba. ""Hibbah!"""

Ta kirata a sadda ta mi™e za ta fice

"""Na'am"""

Ta amsa tana dawowa ta zauna.

"""Ba zan miki dole ki daina fushi da mahaifinki ba kuma ba zan wanke shi nace ya aikata daidai ba amma ki sani matsayin uba yake a gareki, jigo kuma majingina da ya haifeka, ya ciyar dake ya shayar dake bisa sahalacewar ubangiji ya kula da duk wani hakki da tarbiyarki tun daga yaranta har kawo yanzu. Ubangiji da kanshi ya ambaci iyaye da irin girmansu wuraren dayawa. Ko kin san me kalmar Uffin take nufi da Allah ya ambata a suratu Isra'i? Yana cewa ""ubangijinka ya hukunta cewa kada ku bautawa kowa sai shi, kuma ku kyautawa iyayenku. muddin dayansu ko biyunsu suna da rai, kada ku taba ce masu ""tir"" (na nuna dan alamar fushi da su), kuma kada ku yi masu kuwa; ku yi masu magana mai karimci"""

Ina miki nasiha da tuni cewa ki daina wannan fushi da mahaifinki ki kuma je gareshi da kalamai

"ma tausasawa don neman yardar ubangiji kina ji na?"""

Hawayen da suke zuba mata ta share kan ta yi godiya ta mi™e ta fice Momma ta bi bayanta da

"kallo, kai tsaye Waki ta koma tayi Sallar isha tayi kuka sossai bayan ta idar ta mi™e ta fito har"

lokacin da hijabinta mai girma ta nufi Sangaren mahaifinta.

"Yana zaune da Hajiya Zakiya bai jima da shigowa daga sallah ba, idanunshi na zube a kan Tv yayinda take zaune ta kame gefenshi cikin kwalliyarta kaman yadda suke gasa da Momma a Kwalliyar ganin yadda koyaushe tana cikin kwalliya da kamshi kusa dashi, tunda ya dawo ta mishi sannu bai sake magana ba takaici ne fal cikin ranta amma bata tanka ba, sallamar Hibbah"

"ciki ciki da Shigowarta ya sa duk suka mayar da hankali kanta, chan nesa da su ta tsuguna"

"""Mama barka da dare, Daddy barka da dare"""

Hajiya Zakiya tana murmushin keta tace

"""A'a Hibba ce? Barka dai ya jikin? Sai fa ha™uri rayuwar kenan"""

"Murmushi tayi wanda bai mamaye fuskarta ba bata ce komai ba, Daddy ya ce ""Ya dai Mamana kina so mu yi magana ne?"""

"Kai ta gyaWa har lokacin idanunta na a ™asa, jin shiru na seconds yasa ya fahimci bata son yin"

"maganan ne a gaban Hajiya Zakiya don haka ya ce ""Zakiya ki Wan je daga ciki bari mu tattauna da Hibbah"""

"""Haba Alhj! Yanzu Hibbah nawa take da har don za ka yi magana da ita sai na baku wuri? Na ga dai 'yata ce ko kuwa?"""

"""Yarki ce tabbas amma tunda kika ga bata turo mahaifiyarta ba kenan da ni take son Magana"

"kai tsaye don haka ki yi respecting dicision Winta ki ba mu wuri duk cikinsu ko waye ne ya zo yana son Magana da ni personally kema kin san ni mai bashi dama ne"""

"""Ba girin-girin ba dai ta yi mai... In bata yi hankali ba haka za ta tsofe gida ana nan ana baza"

"ba™in hali"""

Tana kunkunin hakan ta fice fuuu shi Daady kam ma ko jinta bai yi ba Hibbah da ta ji ta ta bita

da kallo har ta fita kan ta mayar da kanta ™asa

"""Ehen Hibbah ya dai?"""

"""Daddy da ma Admission ne na samu a Unilag shine nake so idan ka amince min in tafi chan in yi karatun"""

Idanu ya Wan zuba mata zuciyarshi babu daaWi ya tabbatar ya hanata ya shiga hakkinta dayawa bayan abubuwa da suka ta faruwa don ta nemi chanjin environment da kuma natsuwa ta hanyar karatu bai kyautu a ce ya hanata ba amma kuma shi ba wannan ne ra'ayinshi kan 'ya'yanshi

ba...

"""Online ne kika nemi admission Win?"""

Girgiza kai ta yi

"""Yaya Nasir ne ya nema mini, ya san yadda nake son karatun Engineering Win and he thought hakan zai saka ni farin ciki shiyasa"""

Shiru ya sake yi kan ya sau™e ajiyar zuciya chan dai ya muskuta ya kira sunanta

"""Hibbah!"""

"*Littafin nan na kuWi ne ki biya Naira Šari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faWakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun"

0545475847

Gt bank

Fatima Muhammad Gurin

Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763

Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi.

Sai na ji ku*

Gureenjoh

18

"""Hibbah karatun zai saka ki farin ciki?"""

Kai ta gyaWa

"""Zan cika wani buri nawa ne ta hanyar karatun Daddy"""

Murmushi yayi

"""Lallai kin zama ta daban Mamana duk kin karye min record kina sa ana ta ganin laifina"""

Ta kalleshi karon farko yana murmushi yace

"""Eh mana, kin manta ke kika fara mallakar mota a gidan nan saboda kaunarki da harkar motoci da ma iya sarrafasu? Yanzu kuma gashi za ki tafi har Legos karatu hala kina so baki ya kasheni kenan"""

A hankali tace

"""Daddy ka amince kenan?"""

Kai ya gyaWa

"""Ya na iya tunda uwata tana so! Zan saka miki kudi account naki sannan zan aika miki sabuwar mota gidan Adda Kubrah don Allah ki mayar da hankali akan abinda ya kai ki kin ji?"""

Sanyi sanyi ne taji ya mamaye mata zuciya saSanin raWaWin da yake ciki na tsawon kwanaki fuskarta bai Soye ba cikin murmushi tace

"""Na gode Daddy Allah ya kara buWi da arziki mai amfani"""

"Ya amsa ""Allahumma Ameen"""

"Ta sanar da shi ranar tafiyar da Nasir yace zai musu booking tare Daddyn yace ta ce mishi ya bari zai saya mata ticket da kanshi ta san yana so tayi farin ciki ne kuma ta sake Alhamdulillah kuma ya ci nasara don da walwala ta fito, ko da ta dawo sashensu sai da ta sanar wa momma"

amincewar Daddyn kan ta nufi Wakinta ta shiga neman Hudah.

"""Twinee sai yau kika tuna da ni?"""

"""Afuwan maman twins. Yanzu dai Albishir na kira na miki"" Hudah cike da farin cikin jin samun natsuwar twineen nata tace ""Goro fari kal"""

"""Next week zan tafi Lagos karatu"""

"Wani irin ihun murna Huda tayi kaman ta tashi ta tiki rawa ""Da gaske twinee? Kuma Engineering Win?"""

"""Kwarai da gaske mechanical Engineering"""

"""Alhamdulillah! Alhamdulillah kaii na miki murna twinee sai dai kam zan yi kewarki kusa da ni"""

"Hira suka cigaba da yi cikin kaunar juna, Hibbah na ta bata labarin abubuwan da za ta yi don ba karamin daaWi tashin tafiyartan yayi mata ba bayan sun gama magana ta ajiye wayar tana tuna Najeeb cikin ranta ko wani hali yake ciki? Ko ya yake jin tsanar wanda ya kawo shi duniya? Ta san dai ba zai yafe wa Daddy ba don ko ita ce bata jin zata iya manta komai ta cigaba da karbar Daddy matsayin uba don bai ba wa kanshi matsayin ba, hakika ta ji wa Umma raWaWin yaudara, ta ji mata Wacin don ta san menene heartbreak, wanne ne za ta ce ya fi mata sau™i? Rabuwa da Sagir ko tonon asirinshi? Ko kuwa fasa aurenta bayan gangami? Ko kuma Rabuwa da Najeeb?"

A wurinta duk babu gwara amma ta tattaresu ta mayar gefe ta fara shirin makaranta.

****

"A chan Sangaren Amal bata san me ya shiga kanta ba, bata san ina hankalinta ba ta dai san bayan karamar waya da yake hannunta ta kan yi waya da Hajiya kamila shima da kyar kuma gaisuwa kawai take ta kashe, duk wani abu nata na kuWi ko accesories Qasimu ya karSe, Wakin da suke ciki bayan katifa shima yamusashe babu abin da ke kai, tun idan ta ci abincin gidan tayi ta amai da zawo har ta zo ta saba yana dan zama ruwan kuwa ya dafar da ita a sati biyu ta zama tamkar wacce ta sabawa rayuwar wurin kuma ta kasa kawo maganar wa Hajiya kamila bare ta yi yunkurin fita, tana yi wa Inna biyayya wanda take jinshi kaman tilas daga zuciyarta amma ta kasa dainawa haka Qasimu bata iya daga ido ta kalleshi tayi mishi musu karfi da yaji"

ta lalace ta ™are.

Ciwo kuwa idan ta fara amai kaman ba zai tsaya ba don malaria ya Buge ta sossai da cholera saboda rashin sabo amma haka ake mata jike-jike a bata ta sha ba zancen magani ko chemist.

Ta san ba daidai rayuwarta ke tafiya ba amma ba za ta iya yin komai a kai ba.

****

"""Ta amince za ka iya zuwa"""

Sune kalaman Mal. Abubakar bayan tsawon sati biyu da kwanaki da Daddy ke mishi magiya a kullum akan yayi ha™uri ya bashi lokacin ganin Umma don yana son ro™on yafiyarta kan Allah ya karSi ranshi don haka ya yi farin ciki sossai kuma ya nemi da ya bashi lokaci ya kuwa bashi

Win.

"Washegari da yamma ya Wauki Momma da Yaya Rabi'u suka tafi wurin Umma Win, tarba mai kyau Nihla ta musu zuwa masaukin ba™i, ta gaishe su cikin ladabi bayan sun gama gaisawa ta kawo musu ruwa da snacks kan ta fice shi dai Daddy duk ya zama wani iri guiltness yayi mishi"

yawa amma kuskure kam ya san ya aikata.

"Suna nan zaune sai ga Abba da Umma tana sanye da hijabi har ™asa fuskarta babu walwala, gaisawa suka shiga yi yayinda ita kam ko kallon Waya daga cikinsu bata yi ba sai da Momma tace"

"""Maman Najeeb barka da yammaci"""

Tace

"""Yauwa barka"""

Yaya Rabi'u ma yayi mata sannu kan ta gaishe shi a hankali

"""Ha™i™a Aisha sai an cuceka ne ake furta maka kalmar ha™uri, na tabbatar a cikin mu babu wanda ya isa ya ce ya dandani kwatankwacin abin da kika WanWana, a sadda na samu labarin barin ki rayuwar Mudassir gashi a zaune kuma Allah ne shaida har marinshi na yi, na gaya mishi magananu marar daaWi na kuma yi mishi izini da ya biki ya nemi yafiyarki amma ya nuna min shi ya gama da baabinki, na tabbatar mishi hakkinki ba zai taSa barinshi ba Dukda yana ganin yana da kuWi kuma yana da damar auro mata masu yawa, a hankali ya rasa kwanciyar hankali da matan nashi guda biyu duk inda ya zauna ya kan fadi irin biyayya da ladabinki"

"gareshi, ya kan yabi kunya da kawaici irin naki a hankali damuwa ya mishi rubdugu kuma ya"

"rasa haihuwar da Kamila har ma ya ™aro aure itama bata haihu ba sai ya koma nemanki, amma"

bai same ku ba an ce masu gidan sun rasu kun sayar da gidan kun raba gado. Wallahi ko da ya dawo bamu iya gane kanshi ba don a lokacin ya tabbatar da ya rasa ki har abada.

"Dukda daga baya ya samu haihuwan amma bai taSa manta halin da ya jefaki ba sanadiyar hakan zuciyarshi yayi rauni da ake tunanin ya kamu da ciwon zuciya, ya rasa kwanciyar hankali da natsuwa daga matanshi kullum ana rabon faWa kullu yaumin rigima har sai da ya auro Fatima kin ganta nan, itama bata tsira ba don ma ba rigimamma ba ce amma biyun chan sun haWe mata kai ha™uri da kawaicinta ya ajiye ta har yanzu. Wallahi wallahi a sadda ya sake ki da a ce kin fara nemana da ba zan taSa bari ki tafi ba amma a ba yadda na iya na hakura gashi bisa kuskurenshi 'ya'yanshi biyu sun fada soyayya ba don Allah ya sa da yayanki da ya san Mudassir Win aka zo ba da Allah kaWai ya san irin kwabar da za mu yi ko hakan ya ishe mu"

"ishara"""

"Kanta na kasa hawaye na diga a hannunta dake kan kafafunta, ko Waya ba maganar da ya WaWata da ™asa don duk bata ma ji zata iya kallon Mudassir ba bare batun

14 / 62