Chapter 21 Reading SAFARA A TAƁO Kunya Ba Tausayi By FATIMA MUHAMMAD | Hausa Novel READ HAUSA Novels

SAFARA A TAƁO Kunya Ba Tausayi By FATIMA MUHAMMAD | Hausa Novel

Author :  FATIMA MUHAMMAD Category :  African Stories & Novels

Chapter   21 / 62

60K to 63K   out of 184.1K words

ta mishi abin da kika ga dama da tutiyar ke mahaifiya ce a gareshi? Wallahi ki gode Allah ma kin samu Wan mai biyayya a irin yaran zamani babu mai zuba ido kina yi mishi hakan, ita kanta Hudar kin ci sa'ar samun 'yar arziki amma kin nace lallai sai kin ga karshen zaman lafiyarsu to ya zo """

Da sauri ta kalleshi

"""Eh ya zo! Ki kalleni da kyau iyayenta sun kafe lallai lallai ya sakar musu 'ya don ba daga sassake ta faWo ba da gatanta, shi karan kanshi Mu'azzam din ya dawo a susuce amma ya tabbatar min ganinku shine karshen abin da zai zo ranshi a yanzu don baku kyauta mishi ba! Kuma ban ga laifinshi ba don tunda kuka nunawa 'ya'yanshi kiyayya shima bakwa sonshi ya min daidai sai ku rungume gidan ku sha zamanku"""

Yana kai nan ya juya ya fice yana cigaba da masifa don sossai ranshi ya Saci musamman da

Mu'azzam din ya je mishi yana zub da hawaye.

"Mi™ewa Hajiya tayi ta nufi ciki jikinta duk a sanyaye, da kyar take tafiya har ta shiga cikin uwar daka tana kiran Falmata ta kawo mata mayafi ta tafi gidan Yayan ta samu Mu'azzam ita Allah ya gani bata so kashe 'ya'yan cikinshi ba kai ko Hudar ma bata yi mata fatar mutuwa ba sai dai ta"

tarar da Falmata a bayi tana ta sheka amai.....

"*Littafin nan na kuWi ne ki biya Naira Šari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faWakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun"

0545475847

Gt bank

Fatima Muhammad Gurin

Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763

Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi.

Sai na ji ku*

Gureenjoh

27

"""Falmata? Dama baki da lafiya ne?"""

"Tana wanke fuska tace ""Zazzabi ne kawai Mama"""

"""Sannu taho ki ga mu tafi gidan Yaya ina son Magana da Mu'azzam"""

Tana fitowa jikinta duk a mace take cewa

"""Mama dama ya zo shine ba zai nemeki ba sai ke za ki neme shi?"""

Girgiza kai tayi

"""Falmata wani irin zuciya ce a kirjinki? Yanzu a duk abubuwan nan da suke faruwa baki ji kaman ni ce mai babban laifi ba? Ban kyauta wa Mu'azzam ba, idan ya ce ya rabu da ni kuma ta har abada ai dukkanmu mun kaWe wa zai cigaba da kula da mu da rayuwarmu?"""

Zama tayi tana share hawaye

"""Wallahi ban ™i Huda da wani dalili mai girma ba, sharrin shaidan ne shine ya nuna min cewa muddin na zuba ido duk wani dukiya ta Mu'azzam da kulawarshi a kan Hudar zai tsaya, ina ganin kaman za ta saka shi mantawa da mu sai ita kaWai da ΄a΄anta dalilin kenan da ya sa na hana su zaman lafiya amma yarinyar nan bata taSa min komai ba..."""

Tana magana tana zubar da hawaye.

"""Na san wahalar Waukar ciki, na san na raino na san me ake cewa nakuda amma don rashin imani mun kasa tallafa mata, ta nemo mai tayata mun kore ta, kuWi wannan idan ta ba ni dayawa sadda Mu'azzam ba ya nan cewa nake dama dayawa yake aiko mata tana so ta talauta shi ta mallaki komai nashi, idan ta ba ni kaWan in ce ai dayawa ya aiko ta choge sauran saboda ba™ar zuciyarta, wace macece za ta juri abin da Hudah ta jure a zamanta da ni? Kaico na ni Tani wallahi ban kyauta ba"""

Sossai take kuka tana tuna duk abubuwan da tayi ta yi wa Hudah.

Falmata da ta samu sanyin tiles ta kwanta tace

"""Ni kuma dan banzan dukan da ta min ta kyauta kenan? Kin san Hajiya dukan nan ne ya sa na shiga Wakin ma na samu tana nakuda ko na bi ta kanta don dama na yi alkawarin rama wa. Ta saka min ido akan samarina har da guntun wa'azinta alhali ta sani na sani soyayyar idan ba da"

"haka ba mazan gudu wa suke"""

"""Falmata dama kin shiga kin ga tana nakuda kika yi tafiyarki? Kin kuwa san me zai faru idan da ta mutu? Nakuda fa??"""

"A Wan tsorace Hajiyar tayi tambayar, baki falmata ta turo ""Innalillahi wainna ilaihi rajiun..."""

"Hajiya tayi ta maimaitawa zuciyarta na cigaba da tsinkewa, duk abin da falmata tayi ba laifinta bane nawa ne, koma menene da bata ga ina yi ba da bata yi ba, wace iriyar uwa na zama ni"

Tani? Tana maganan a ranta tana kuka.

Da kyar ta danne zuciyarta ta Wauki mayafi don tafiya gidan Yayan Juyowa da zata yi don

"tayiwa falmata magana su tafi ta ga ta yi bacci, bata kawo komai ba ta fice daga gidan sai dai ta je chan Win ma bata samu Mu'azzam ba haka ta gaji da zama ta tattara ta dawo."

****

"Amal kam tunda ta sau™a tana zaune ne babu abin da take son gani irin iyayenta, a firgice take"

"kuma a razane don haka ana turo kofa ta zabure sai ta ga Daddy ne, da sauri ta sau™o tazo ta"

"faWa jikinshi tana kuka sossai da neman yafiya, daga shi har zubair ta basu tausayi ta ™are kaman wacce tayi ciwon yunwa duk ta yi ba™i kaman ba Amal ba, ko da labarin bayyanar Amal ya je ga mahaifiyarta kaman za ta zauce haka itama ta sa aka kawo ta asibitin sun yi kuka sun kuma gode Allah da bai ba Qasim dama a kanta ba inda tuni aka yi musu kyakyawar Wauri"

kuma ana shirin tura su kotu don shari'a.

"Satin Hudah biyu da haihuwa aka sallameta, ba zata ce zaman asibitin bai mata daaWi ba don a kullum tare suke da danginta da 'yan uwanta ana kulawa da ita tamkar Gimbiya, yaranta sun warke garas tana cigaba da kulawa da su da taimakon su Momma, idan ka ganta ba za ka ce ita ce ta haihun ba don tuni ta mayar da kyaunta dama aikin ake kulawa da da kuma jininta, Mu'azzam ya mayar da asibitin gida tun yana zuwa basa kula shi har dai ya shiga ba Momma da Daddy tausayi don ranan kawai zubewa yayi yana ro™on su su yafe mishi wallahi ya amsa"

laifinshi su barshi ya ga Hudah da yaranshi.

"Da kyar Daddy Z ya kyale suka fita a Wakin, gaban Hudah ya nufa ya ri™o hannunta"

"""Na tuba Hudah! Wallahi na tuba ki yafe min don Allah! Na tafka kusakurai dayawa a zaman mu ina ganin don ni ban saSa miki ba ai don mahaifiyata ta saSa miki hakan ba zai zama cusgunawa a gareki ba, na sani tayi abubuwa masu yawa na kasa magana bare Waukar mataki ban san cewa har a irin wannan lokaci na rayuwa ko mutuwa za su iya aikata abin da suka aikata a gareki ba! Wallahi a yanzu a shirye nake da daukar mataki tuni na chanza miki gida kayakinki ma suna chan ko hanyar wanchan gidan ba za ki sake kallo ba bare ki zauna da Hajiyata. Na ma nemi mai aiki da zata dinga miki aiki kina kula da yaranmu kuma kina zuwa"

"makaranta duk abinda kike so ki faWa wlh zan yi miki"""

Zame hannunta ta yi ba tare da ta ce komai ba don Daddy Z ya riga ya mata gargaWi kuma ba

zata tsallake maganar iyayenta ba a kan 'yancin da suke son samar mata.

Yaran yake kallo yana zub da hawaye sai yanzu ya samu ya Wauke su ya rungume cike da farin

cikin da ke sau™a mishi tamkar ruwan sanyi a ranshi.

"""Alhamdulillah! Alhamdulillah!!"""

Murmushi ya saki ya kalleta

"""Kun yi musu huduba ne? Na ji Hibbah na kiransu da Amna da Yumna"""

"Girgiza kai tayi bata ce komai ba, sai ya fahimci inkiya ce kawai a take ya yi musu huduba, ya ajiye mata yumnar"

"""Allah ya raya mana Kubrah"" Yayiwa Amna ma kan ya sau™e ta ""Allah ya raya mana Fatima"""

"Bata ce komai ba don dama ta san a yanzu ba zai yi gigin saka sunan mahaifiyarshi ba sai dai bata yi tunanin zai saka Aunty kubrah ba, ya matso yayi pecking goshinta"

"""Sannu da ™o™ari Allah yayi miki albarka Hudah"""

Idanu ta lumshe kawai tana hawaye bata ce tak ba.

"Shigowar su Aina'u ya sa dole ya fice, dole kawai yake rayuwa shi kadai a sabon gidan da ya"

"saya saboda Hudah Win, gida ne mai kyau don ba karamin shigo mishi kudi ke yi ba, Dukda ba"

"za'a ce babban gida ba madaidaici ne amma mai kyau da Waukar ido komai na gidan kaman ka sace don kyau da walwalin gidan, ya kashe kudi sossai a kan gidan ba kuma don komai ba sai don ya wankewa Hudah zuciyarta da hakurinta, Mahaifiyarshi duk yadda ta so ta ganshi abin ya gagara ya ™i bari sam, ya dai san ya tura musu kayan abinci da kuWin cefene ta hanyar Wan"

Kawunshi amma bai je gidan ba sam.

"Ko da aka sallami Hudah Daddy Z gidanshi ya kaita ya sa Aunty husna ta shirya mata Waki na musamman, akwai dattijuwar 'yar uwarsu da ya je ya daukota musamman daga kauye kasancewar mijinta ya mutu kuma bata da 'ya'ya Yadikko suke ce mata ya ajiyewa Hudar don"

Aunty Kubra zata koma ita da Hibbah.

"Sai da ta dawo gidan Daddy Z aka yi suna na ji da gani raguna bibbiyu aka yanakawa kowacce yarinya duk fa mahaifinsu ma bai sani ba, Dukda an riga yin sunan Amal da ba kowane ma ya sani ba bare ya je ta sakawa danta sunan Mahaifinta Mudassir tana kiranshi Ayman, sai gata ta"

zo sunan Hudah.

"Dayawa sun yi mamakin ganin yadda Amal ta chanza, bata iya ta daure ba ta nemi yafiyar Hibbah da Hudah dama ta jima da neman na Momma, ita kanta mahaifiyarta jikinta ya yi sanyi da abubuwan da suka faru, yayinda Hajiya Zakiya kuma gani ga wane ya zama mata ishara ta"

fara rage ba™ar kishi da musgunawa Momma itama da take.

Yara da mahaifiyarsu sun samu sha tara na arziki daga 'yan uwa da abokan arziki bayan suna

da sati daya Hibbah da Aunty Kubra suka koma legos saboda school na Hibbah.

"Shi kam Mu'azzam ko da ya je asibiti bai sameta ba ya sake jin tashin hankali, gidansu ya je sai dai aka ce mishi bata nan, ya sake susuce wa yaje wurin Daddy Rabi'u yayi ta ro™onshi gafara akan zai gyara zai chanza ya yi alkawari tausayinshi ya sa Daddy Rabi'u yace ba komai za su yi"

"shawara da 'yan uwanshi yanzu ya tafi kawai, haka ya tafi cikin tsammanin wa rabbuka."

*****

"""ke falmata! Falmata ke!!"""

Hajiya Tani ke kiranta tana ture ta.

"Idanunta da suka yamushe ta Waga take kallon hajiyar ""Wai menene Hajiya?"""

"""Lafiyarki kam? Wani irin ciwo ne wannan da kullum safiya kina nan kina bin sanyin tiles? Abinci wannan sai kin zaSa kike ci me yake damunki ne?"""

Tayi maganan da damuwa

"""Me kuwa zai dameni Hajiya? Malaria ce fa da typhoid"" ""Ban yarda ba ki tashi mu tafi asibiti"""

"""Ni dai don Allah ba sai mun je ba bana son allura ki kyaleni"" ""Wallahi sai kin je, tashi mu tafi"""

Ta janyo mayafin ta ta tura falmatar a gaba gabanta sai faWuwa yake suka tafi asibitin da suke

da kati.

Bayan falmata ta yi wa likitan bayani aka bata gwaji suka je suka yo.

"""Masha Allah, tana dauke ne da cikin wata biyu dama irin wannan ciwuka a First trimester normal ne sai da """

"""Ciki Dr.??"""

"Daga falmata har hajiyar suka faWa a razane ko kan yayi wani magana Hajiya ta yanke jiki ta faWi ihu falmata ta saki shi kam bai san bata da aure ba sai salati yake tuni aka yi emergency da ita, falmata kam banda kuka babu abin da take ta ™i magana sai wayan hajiyar suka Wauka suka kira Yayanta a lokacin ma yana tare da Mu'azzam hankalinsu duk ya tashi suka yo asibitin sai"

dai su ma da mummunan labari suka ci karo tuni Mu'azzam ya rufeta da duka.

"Da kyar aka kwace ta, da kyar da gaske aka samu Hajiya ta farfado sai kuka."

"""Ai ba kuka ne ya kamata ki yi ba duk laifin waye Tani? Laifinki ne shiyasa wasu mazan ke ganin auren 'yar da ta tashi gaban mace sai jarrabawa, irin ku ne ke sa ake yi wa single mothers kudin goro, kin kasa saka idanu akan yarinyarki amma kin kafawa surkarki karan zu™a,"

"kin bar huruminki kin shiga na Allah dole ki ga ba daidai ba"""

Cikin kuka tace

"""Innalillahi wainna ilaihi rajiun...! Allah na tuba Allah... Sai da Hudah ta faWa tana ro™ona akan rayuwar falmata da irin tara samarinta na ce hassada ce take mata da ba™in ciki da sharri ashe duk gaske ne! Na shiga uku"""

Sossai take kuka da ya so ba wa su Mu'azzam tausayi Yaya yace

"""Shiyasa harshe ma abin kiyayewa ne kaman yadda annabi ya ce, baki bashi da kyau"" Tana tuna irin aibatawar da tayi ta yi wa Hibbah da zargin gidansu Hudah din cewa duk 'yan"

iska ne ashe ga Wiyarta na lalace wa gabanta bata sani ba.

"Fasalta irin tashin hankalin da suka shiga ma ba zai rubutu ba, falmatar ta nemi ko a zubar suka sake shigar jikinta da duka Kawun nata ya cigaba tsawatar mata"

Babu zancen zubarwa tunda haka ta zaSa ta raine shi har ta haife kila idan suna ganin Wan ya

"zame musu ishara, haka suka tarkata jiki a mace zuciya na cigaba da kuna suka yi gida, Mu'azzam bai zauna ba yayi tafiyar shi."

*****

"Hibbah da Usaib a wannan dawowartan wani irin ™auna ne ya kullu tsakani don tuni ta ba da kai bori ya hau, Usaib in dai kalamai ne a bar mishi yana kula da ita sossai da riritata, kuma daga ita har Aunty Kubra da Zaitoon suna jin daaWin ganin yadda yake nuna mata ™auna ko a gaban waye."

A tsakankanin ne ma aka zo tambayar auren Zaitoon wanda hakan ya ™arawa family Win farin

"ciki ™warai kasancewar zaitoon rabon ya Wan yi nisa, tuni shirye shirye ya kankama na bikin"

inda Hibbah ita ce kanwa kuma kawa na kusa don ˜awayenta dayawa ma basa ™asar...

"*Littafin nan na kuWi ne ki biya Naira Šari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faWakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun"

0545475847

Gt bank

Fatima Muhammad Gurin

Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763

Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi.

Sai na ji ku*

Gureenjoh

28

"A yau Hudah ke cika arba'in daga ita har yaran sun yi kyau abinsu suna samun kulawa sossai daga Aunty husna da Daddy Z bata daka ta rigimar Amaryarshi sam don asali ita ba mai kaunar rigima ba ce, tana zaune tsakar parlorn Aunty husna tana ba Yumna abincinta ta jiyo sallama, sai da gabanta ya faWi jin Muryar da ko a mafarki ta ji zata iya gane mai ita cikin seconds, da sauri ta Wago tana kallon Hajiya Tani da ta shigo parlorn tana amsa sallamar a kan labbanta,"

"Aunty husna ta mi™e ri™e da Amna itama tana kallonta ""Lafiya?"""

"Murmushi ta yi mai ciwo, dole a ce mata lafiya tunda ta yi girman hoti-ho ta zub da daraja da"

kima da Allah yayi mata kaico rayuwa! Kaiconta da ta kasa fayyace gaskiya da daidai sai da komai ya chaSe mata.

"""Lafiya ™alau na zo wurin Hudah ne"""

Hudah da kyar tace

"""Sannu da zuwa Hajiya, bismillah ki zauna"""

Gaban Hudah ta matso ta zauna gangarta kawai sai ta fashe mata da kuka

"""Hudah ki yiwa Allah ki yafemin alhakinki da na Wauka, ki yafe min uzzura miki da nayi ta yi na hana ki zaman lafiya a dakinki, na yi nadamar duk wani furuci a gareki a yanzu haka kunyar kaina nake ji..."""

Hannunta Hudah ta ri™o Dukda zuciyarta rawa yake tana tsoron kar ma shigo shigo ba zurfi

hajiyar ke shirin mata

"""Hajiya ba zan ce ban ri™e ki ba a wannan karo, ba zan ce baki kuntata mini ba amma wallahi ban taSa ganinki da wani ido ba bayan na uwa hakan ya sa duk kalamanki kan zama masu kuna tamkar garwashi a zuciyata, ban auri Mu'azzam saboda in raba shi da ku ba, na aure shi ne saboda ina son shi kuma ina so in tayaku sonshi, na zaci zan samu wata uwar da zan iya shearing damuwata mu yi kuka da dariya a tare kamar wacce ta haifeni, na rabu da 'yar uwata"

"da tunanin Falmata za ta zame min twinee a sabuwar rayuwar aurena sai dai kash duk mafarkina ya sauya daga mai kyau zuwa mummuna har nake jin bana sha'awar sake zama da Mu'azzam bare mu haWa Inuwa. Idan da iyayen miji masu ™iyayya ga sirikansu za su fahimta wallahi babu macen ™warai 'yar gidan tarbiya da za ta so raba Wa da iyayenshi saboda kawai tana aurenshi. Matsayinki na uwa Hajiya wallahi na yafe miki, ina fata komai zai wuce a wurinki,"

"idan akwai inda na saba miki nima ina ro™o ki yafe min..."""

"Kuka sossai Hajiya Tani ke yi lallai ta ga ishara ji yadda yarinyar da zata iya yin jika da ita ke faWa mata gaskiyar rayuwa, bata san me ya hau kanta ba da ta kasa ganin good side of Hudah a kullum sai son ganin laifinta, da ta bi shawarar Hudah tun farko da falmata bata lalace mata a gida ba, ita kam ta ga illar furuci."

"""Na gode sossai Hudah! Na gode ™warai Don Allah ki yafe wa falmata ma, tana chan tana fama"

"da azabar laulayi wanda ta janyo mana da zuri'armu magana a kanshi yau fari gobe tsumma kullum kuka da nadama bata isa fita ko kofar gida ba sai cin mutunci"""

Hudah ta ji tausayin falmata saboda ta san zafin da ta taya Hibbah ji a sadda rudin samarin

zamani ya rinjayeta wurin aikata kuskure a rayuwarta tana tuna yadda ko fita ya gagari Hibbah sai da niqabi ko facemask saboda mutane da bakinsu.

Aunty husna tace

"""Allah ya kawo mafita ya sa silar shiryuwar kenan, mun kasa gane samarin zamani a koyaushe bukatarsu Waya ce ga mace, matukar baki bari suna taSa ki ko kina tura musu hotunan jikinki ko ma kuna aikata laifin musayen kalaman da basu chanchanta ba to ba soyayya ba ce ko kuma baki son su ne, mata dayawa saboda suna so su yi auren gani suke ba komai bane sai bayan saurayi ya yaudari mace sai ya gudu ya barta wasu ma

21 / 62