Chapter 37 Reading SAFARA A TAƁO Kunya Ba Tausayi By FATIMA MUHAMMAD | Hausa Novel READ HAUSA Novels

SAFARA A TAƁO Kunya Ba Tausayi By FATIMA MUHAMMAD | Hausa Novel

Author :  FATIMA MUHAMMAD Category :  African Stories & Novels

Chapter   37 / 62

108K to 111K   out of 184.1K words

motar"

"ya kwana, Abdul na chan wurin aiki bayan ya sau™e Jadwa ya wuce."

"Tana isa gida wanka ta yi da ruwa mai zafi sossai ta sake gasa jikinta ta fito ta fara shiri a hankali har ta gama cikin cotton doguwar riga, ko motsi tayi kamshi ne ke tashi jikinta haka ta kwanta ta lumshe idanu babu irin tunanin da bata yi ba har bacci ya sureta a haka, ™arfe huWu da 'yan mintuna ta farka taje tayi alwala ta zo ta gabatar da sallah a lokacin Jadwa ta shigo ""Na le™o ai Wazu kina bacci"""

"""Ina kwanciya baccin ya sureni fa ba shiri"""

Ta amsa fuskarta a sake

"""Eyyaa sannu! Allah ubangiji ya kara sau™i ni zan wuce"""

"Mi™ewa tayi sanye da hijabin Jadwa na ce mata ta bari ma ba sai ta raka ta ba ita kuma tana cewa ba komai ai zata mi™e kafa ne har gaban motar gidansu da ya zo daukanta ta raka ta ita da Zaitoon, sai da ta shiga Zaitoon ta ajiye mata leda da mommy ta bayar a bata tayi godiya"

kan suka fice.

"""Tana da hankali sossai na yi wa yaya Abdul murna"" Hibbah ta faWa da 'yar murmushi expression Winta blank."

"""Aikam dai tana da hankali sossai, saura mu ga ta Yaya Nasir"" ""Allah ya sa kar ya kwaso mana baturiya to"""

"Suka yi dariya a tare, ko da suka shiga Zaitoon wurin Mommy ta yi yayinda Hibbah ta nufi Waki, tana shiga taji ringing na wayanta kan ta Wauka ma ya yanke, dayake sabon waya ne bata yi setting na silence unknown caller ba tukuna, ta buWe tana kokarin duba number Win aka sake"

™ira.

"""Hello"""

Ta faWa tana zama.

"""Hibbatullahi Mudassir Madaki kin tsira a karon farko, amma ba komai a juri zuwa rafi dai...by"

"the way na ™ira ne in yi miki gargaWi..."" Ta mi™e tsaye"

"""Wanene kai? Kuma me kake nema da ni?"""

Dariya yayi da alama Muryar an sauyata ne ko ta hanyar na'ura ko kuma daga ma™ogoro.

"""Kin riga kin san me nake nema ai, na san babu abinda yake baki tsoro irin sake bayyanar hotunan da kike tunanin sun ™are, ina da su har da waenda aka yi amfani da irin jikin da fuskar tsaff aka haWa kyawawan videos da maza daban-daban..."""

Idanunta ta Wan zaro sun rine tuni

"""Me kake so da ni? Meyasa za ka Wauki alhakina? Me na yi maka?"""

"""Duk kin san amsar yarinya, abin da ya kamata ki tambaya shine... In faWi sharudai na za ki bi, kuskuren bin sharaWina daidai yake da ki wayi gari da ganin videos Winki na playing automatically a billboard na matsiyaciyar kamfaninku, sai kowani ma'aikaci yayi Allah wadai da ke, sai kin zaSi mutuwa fiye da rayuwa. """

"Hawaye ne suka shiga zubo mata babu shiri, waye ne zai yi Blackmailing Winta bayan yunkurin mugun nufinshi gareta?"

"""Me me kake so?"""

"""Yauwa 'yar gari, ina so ne ki saka wanchan bastard boss naku ya daina bincike a kaina, ina so ya zare hannunshi a lamarinki you will never fool me a tafin hannuna kuke duka, wallahi idan"

"bai dakatar ba za ki sha mamaki"""

Kitttt aka katse ™iran.

"""Hasbunallahu wani'imal wakeeel innalillahi wainna ilaihi rajiun"""

Ta Yi ta maimaitawa idanunta zube wuri guda na tsawon mintuna talatin kan ta sanya kanta cikin pillow ta fashe da wani kukan.

"Ta Yi kuka har ta ji ba daaWi kan ta mi™e ta Wauko wayan ta shiga duba Layin MB MUSTAPHA sai dai bata da shi kasancewar ranar da ya kira bata yi saving ba, ta duba Layin Raliyat ta kirata sai dai a kashe. Babu irin tunanin da bata yi ba Usaib ne da bai samu cikon burinshi a kanta ba yake son tarwatsata? Raliya ce ta cigaba da ri™e tsanarta a zuciyarta take son ganin bayanta?"

Ko Sagir ne har ya fito daga prison yake son ™arasa kasheta?

"Director ta ™ira shima not reacherble, ta sake gwada Layin da ya ™irata yanzu switch off wayan ta jefar tana binne kanta a tsakankanin kafafunta tana sake fara sabon kuka, ko da Allah zai sa ta bar aiki kamfanin MB MUSTAPHA bata fata ko da wasa ta barshi a tozarce, tana tuna irin ba™in ciki, damuwa da Wimuwa da ta shiga a baya na irin Blackmailing Winta da Sagir yayi da watsa hotunanta, zubewar ™imarta da na gidansu idan irin hakan ya sake faruwa ya zata yi?"

Dole ne ta samu MB MUSTAPHA a yau din nan.

"Layin Nasir da rabon da su yi magana har ta manta ta duba sai dai ashe na Nigeria ne da sauri ta mi™e ta nufi Wakin mommy, suna zaune da Zaitoon suna duba wasu kaya don shirye shiryen auren Abdul ake sossai saboda ya ™arato."

"""Mommy Don Allah ina son numbern Ya Nasir"" Ta faWa tana iya kokarinta wurin Soye damuwarta ""Me ya samu idanunki haka Hibbah?"""

"""Mommy bacci na tashi ne"""

Ga wayan duba ki dauka.

Da sauri ta Wauki wayan ta fice tana gujewa idanun Zaitoon da ta san ba haka ta barta yanzu ba.

Ringing na ™arshe yayi picking

"""Yaya Nasir.."""

"""Hibbah?? Ke ce kike kira na da Layin Nijeriya kai tsaye? Mu je WhatsApp mana"" ""No ba sai mun je ba, Layin MB MUSTAPHA nake so ka turomin"""

"""Lafiya kam?"""

"""Lafiya ™alau pls yanzu don Allah"""

"Tana kai nan ta katse ™iran, cikin mintuna ta ga Layin tayi copying kawai ta shiga kiranshi."

"""Ya ilahi.."""

Ta ambata tana Mi™ewa tsaye layinshi not reacherble da alama a DND ya saka.

"Duk yadda zata yi ta yi amma ta kasa samun shi, tayi kuka har ta gaji ko da bayan isha ta sha magungunanta don kirjinta da yayi mata nauyi bata san ta yi bacci ba."

"Washegari har makara tayi don magungunan akwai na saka bacci sossai saboda ta samu isasshen natsuwar zuciya, wanka tayi ta shirya cikin shirin zuwa office don dole ta samu MB MUSTAPHA ta dakatar da shi akan binciken da yake, ta gwammaci ta bar kamfanin gabaWaya akan sake shigar hotunanta duniya, ko da ta fito a shirye tsab mommy ta dubeta"

"""Ya dai? Sai ina?"" ""Mommy office"""

"""Haba Hibbah, yaushe kika samu lafiyar zuwa office? Ba Za ki huta sossai ba?"""

"""Mommy Don Allah kar ki hanani zuwa wallahi na ji sau™i babu abin da zai faru"" Mommy dai bata so ba amma magiyar Hibbah ya sa dole ta ha™ura."

"Sai da ta fita ta tuna motarta ma ba ya gidan yana kamfani, tana shirin juyawa ta karSo keyn mommy Abdul ya yi mata Horn."

"Kaman kar ta je sai kuma dai ta nufi motar ta tsaya daga gefen da yake ""Ina kwana"""

"""Lafiya ™alau Hibbah ya jiki?"" ""Alhamdulillah da sau™i"""

"""Ko in ajiye ki office Win? Na kula chan kika yi kuma kaman Motarki bai dawo ba ko?"""

Kaman ta ™i amincewa sai kuma ta tuna idan ta tafi da motar Momma wa zai dawo da shi har ta

samu ta Wauko nata?

Zagayawa tayi ta shiga ta zauna ya kunna suka Wauki hanya.

"""Hibbah"""

Ya ™irata jin shirun motar yayi yawa kwarai.

"""Na'am"""

"""Hibbah ina so don Allah ki yi ha™uri, ina mai baki ha™uri bisa abubuwan da muka yi ta yi a baya zuwa Wauke miki da muka yi, hakan ya faru ne bisa dalilin nemawa kaina sau™i ba don na tsaneki ko na daina daukar ki matsayin kanwa kuma jinina ba, kin riga kin haramta mana a"

"dokance ina mai ro™on ki da ki sake ba ni damar kasancewa Wan uwanki kuma abokin shawara kaman yadda muke a baya"""

Kanta ta sau™ar tana hadiye hawayen da suka cika mata idanu.

"""Na zaci ka tsaneni yaya Abdul hakan ya sa nima na tsani kaina na amincewa da nayi na biyo"

"Ya Nasir Lagos gashi na rusa kyakyawar ala™a da zamantakewarku..."""

"""Kin taSa ganin inda aka tsani jini? Ke fa kanwata ce Hibbah komenene ya faru babu mai chanza wannan matsayin, mu ne muka yi miki laifi amma yanzu a wurina komai ya wuce Ki yi"

"ha™uri da tsatsauran hukuncina na yi hakan ne don in warke ciwon rasaki"""

Numfashi ta sau™e

"""Shiekanan Ya Abdul Allah ya cigaba da haWe kanmu ya kara mana karfin zumunci"""

Yayi murmushi

"""Na gode kwarai kanwata"""

Basu sake wani hira ba har ya sauketa gaban company sam basu kula da gate Win a rufe kirib ba sai da har ya tafi ta nufi gate don shiga ciki....

49

"Da tsantsar mamaki take kallon gate Win, me ya faru haka da shutting down company gabaWaya?"

Ta tambayi kanta sai dai babu amsa kuma babu kowa a arear.

"Luckily tana nan tsaye sai ga motarshi, har sun Wuceta kaWan sai ta ga an tsaya, bai fito ba driver Win shi ne ya sau™o ya zo wurinta."

"""Good morning"""

"Ya gaisheta ta amsa da turanci don yoruba ne baya jin hausa, ya sanar mata oga ya ce wai ta zo."

Har ya Wan juya tana tsaye tana kallon motar sai ta tuna ma irin neman da tayi ta mishi da kuma abin da ya kawota tuni ta kau da tunanin dalilin ganin kamfani a rufe kuma ranar aiki da safe ta nufi motar dama ya riga ya buWe mata driver Win tabbacin Site da yake ta Wayan Sangaren ne

don haka ta zo ta shiga.

"Wani daddaWar kamshi da kuma sanyi na Ac da har ya yo over ne ya bugeta, ta Wan sau™e ajiyar zuciya duk sanyin da ake zabgawa gari bai isheshi ba? Ta Wan muskuta don hankalinshi na kan system kuma bai kalleta ba Dukda haka kwarjininshi duk ya cika motar dama ta saba duk suka fita tare a mota guda a takure take, a haka Win ma yawan zaman nata gaba ne idan"

sun fita sha'anin aiki P.A ke zama da shi a baya.

"""Good morning Sir"""

"Ya Wan gyaWa kai, seconds huWu ya ™ara kan ya Wan waigo sai suka haWa idanu don kallonshi take, ta Wan sau™ar da idanunta ™asa tana jin tambayar da ya watso mata."

"""Me kike yi anan?"""

"Ta kalli kanta ta kalli companyn, wani irin tambaya ne wannan? Me kuwa take banda ta zo aiki?"

Ko dai ya koreta ne already?

"""Aiki na zo"""

Ta harhada ta faWa don har lokacin idanunshi da suka fitine ta suna kanta.

"""Aiki?? Yaushe kika warke?"" Ta Wan bata fuska kaWan ""Na warke Sir"""

"Sai a lokacin ya kawar da idanu bai ce komai ba ya yi wa Driver Win umarnin su tafi. ""Si...r"""

Maganan ya ma™ale saboda kallonta da yayi har sai da gabanta ya faWi Dukda ba Harara ba ne

"ko mugun kallo, ta rasa courage ne kawai kafafunta har sanyi suka yi, yanayi ne da bata taSa ji ba a rayuwarta."

"Duk yadda ta so mishi magana ma ta kasa, sai da suka yi nisa driver ya tambayi ina za su je?"

"Shiru ya yi abin shi ta fahimci da ita kenan ake, ina kuwa zata je tunda ya sakota gaba daga kamfanin shi banda gida?"

"""Victoria Island"""

"Ta faWa chan ™asa babu abinda bata sa™a ba, ganin sun haye gada sun fara shiga ciki ta faWa mishi Layin da zai bi har kofan gidansu."

"A waje yayi parking sai ya fita ya bar su, motar ya Wauki shiru sai kamshin junansu dake dukar hancin kowannensu, ya haWu da unguwar very quite, weather Win kuma very cool da ya saukar da wani warmness yanayi mai sa natsuwa da bacci."

"Jin kaman ba zai yi magana ba ta buWe baki tace ""I called yo..."""

"Daidai ya juyo shima yana cewa ""Me kika je yi company?"""

Shiru duk suka yi.

"""You should go First"" Ya faWa calmly."

"""Na je aiki"" ""Sure??"""

Ta Wan kalleshi

"""kika ce you called me? Me kike so?"""

Ta ma rasa me zata ce duk miyaun Bakinta a kafe ta rasa dalili.

"Wayanta dake hannunta ya zare, Luckily ba password shima dayake bai yi saving number Winta ba bashi da shi, abin da ya bashi mamaki ta kirashi sau talatin itama bata yi saving ba, da Wan hanzari ya kalleta."

"""Me ya faru?"""

"Yadda yayi tambayar sai ya sa hawaye cika mata idanu. ""Dama...Da..ma akan wannan abu da ya faru ne..."""

Kallon Bakinta da take motsawa yana rawa a hankali ya cigaba da yi

"""Idan dai har akwai wani bincike da kake yi sir don Allah a barshi ba sai an yi ba...!"""

Tana fahimtar kallon nashi a sadda ya juye zuwa tamkar Harara

"""Me kike nufi? Ni Almustapha a yi ™o™arin tozartani in zuba idanu? Never..."""

Hawayen da take rikewa ne suka zubo ya zura musu idanu.

"""Hibbah!!"""

"Wallahi har cikin kanta sai da ta ji ™iran, ta kasa kallonshi banda hannayenta da take ta wasa da"

su.

"""Look Hibbah... Kalleni nan ki faWa min menene? Is someone threatening you?"" Cikin Muryar lallashi yayi maganan kaman mai magana da Jasrah."

Ta girgiza kai

"""Haka kawai ne bana so, bana son abinda zai dawo ya Wagawa iyayena hankali"""

"Shiru ya Wan yi yana kallon waje kan ya waigo ya kalleta ""Ok na ji... Zan daina bincike don ke!"""

Lumshe idanu tayi tana sau™e numfashi a hankali sai ya ce

"""Amma zan cigaba don kaina da kuma company Wina, da a wani wurin ya faru kila bai shafeni ba amma cikin company Wina har cikin office Wina? No i must fish out the culprit."""

"""Sir """

"""Save it ko ma menene kike son cewa You can go home company na break sai monday za'a"

"dawo aiki"""

"Ya cire wayanshi a DND ya ™ira layinshi sai da yayi ringing ya kashe, ya shigar da contact Winta favorite kan ya mayar DND don numbobin da suke favorite ne kaWai za su iya samunshi kuma daga Mum sai Jasrah sai Abbanshi sai ita na ™arshe."

Wayanta ya mayar mata kan kafafunta bai ce komai ba.

"Ta kasa cewa komai haka ta fito daga motar don ko kallonta bai sake yi ba bare ya nuna alamun yana sauraronta, gida ta shiga kaman zata saki ihu."

"A parlor ta samu Mommy da wasu aunties dinsu Zaitoon ta gaishe su zata wuce mommy tace ""Ya dai har kin dawo? Ko jikin ne?"""

Ta girgiza kai

"""Ashe wai kamfani suna break sai monday za'a koma"""

"""kai gaskiya yaron nan yana da kirki, wani ma'aikata ne ake ba wa ma'aikata hutu haka? Ya"

"kyauta wallahi za ma ki ™ara jin karfin jiki kan Litinin din"""

Ita dai ta wuce bata ce komai ba kaman zata saki kuka.

"Ko da ta shiga Waki sako ta sake gani da wani layi daban ba na jiya ba, shima gargaWi ne."

"""Na shiga uku ni Hibbah... Yanzu ya zan yi?"""

Tayi magana hannunta Waya na bisa kanta.

"Ba zata ce ga yadda ta karashe sauran kwanakin ba, tun tana iya bacci har ta daina runtsawa saboda fargaba, a farko message sau Waya ake mata amma ya zama kullum yana ™aruwa"

yanzu sau biyar take ganin gargaWi da jan kunne.

"Tana zaune ranar Lahadi a waje hannunta bisa kumatunta aka wangale gate mota ta shigo cikin gidan, tana mamakin waye a taxi sai ga Nasir ya buWe kofa ya fito."

Mi™ewa tayi ta nufe shi

"""Sannu da zuwa Ya Nasir"""

"Yayi mata murmushi don shima sun shirya bayan ta karSi Layin MB MUSTAPHA yana tambayarta jikinta a WhatsApp daga baya ya nemi afuwarta kuma ta yafe komai ya wuce. ""Yauwa Hibbah..."""

Kayanshi ya fitar ta tayashi ja Dukda ba murna take ba amma tana ta murmushi saboda surprise ne da ta san mommy karan kanta zata ji daaWi musamman da yace mata ai ya dawo ne

yayi attending auren Yayanshi tayi murnar shiryawarsu wane.

Su mommy da ba™in da har sun fara zuwa saboda auren wani sati ne suka shiga mishi maraba

da murnar ganinshi ita dai ta koma inda ta taso don bata manta nightmere Winta ba.

"Bata jima da zama ba aka sake wangale gate sai ta ga motarta, Mi™ewa tayi ta tsaya har drivern yayi parking ya fito, shine wanda ya dawo da ita ranar da taje company ta hadu da su, gaisheta yayi ta amsa tana mishi godiya ya mi™a mata key"

"""Boss ne ya ce a dawor miki da ita"" ""na gode sossai"""

Ta karSa ya mata sallama tana ma ya tsaya ko ruwa ya sha ya ce mata ai boss na jiranshi

yanzu.

"Motar ta je ta buWe ta ga handbag Winta na ranan da ta bari ta Wauka ta sake rufewa ta nufi ciki, Washegari mutanen Kano za su iso amma bata wani farin ciki saboda gudun abin da zai iya"

"faruwa, har rama ta yi tsabar faWuwar gaba."

Washegari monday da safe ta shirya mommy na ce mata ba zata je tarbar su Momma ba? Tace a'a tana da ayyuka bata karSi izinin fashi ba yau haka mommy ta barta ta fice duk kuma

damuwarta ta ga MB MUSTAPHA.

"Yau kamfanin ya Wauki hada-hada na jama'ar cikinta saboda sun dawo ne da karsashi da kuma karfin su saboda dan hutu da aka samu wanda har yau babu wanda ya san dalili banda MB MUSTAPHAN kuma shi bai huta ba don duk kwanakin ya yi aiki, kai tsaye elevator ta shiga zuwa office nasu an share duk an goge komai banda kamshi babu abin da ke tashi, zama tayi"

tana harWe hannayenta cikin jiran ya zo kawai ta sake ganin wani sa™o

"""Ba kin yi kunnen uwar shegu da gargaWina ba? Toh ki jira zuwa gobe da misalin karfe 10 na safe kowani ma'aikaci na kamfanin nan sai ya ganki a mummunan yanayin da sai kin"

"gwammaci mutuwa da rayuwa"""

"Sa™on kawai take kallo zuciyarta na racing, bata ji Shigowarsu ba shi da driver da ya ri™o mishi jaka sai P.A har sai da P.A Win yayi mata magana ta mi™e tsaye da sauri sai idanunta suka shige cikin nashi."

A hankali ta sau™ar tana gaishe su fuskarta cike da damuwa.

"Ya amsa a kan lips ya wuce office nashi, P.A na biye da shi, zama ta yi hannayenta a goshinta duka biyu har P.A ya fito ya Wuceta zuwa office nashi, kiran landline daga office na MB ya sa ta mi™e ta nufi office Win ta Wan yi knocking ta shiga, tana shiga wayanshi na ™ira..."

"""Yes..."""

Ya amsa call Win.

"""Oh Yeah! Ga ni nan zuwa..."""

"Ya faWa yana Mi™ewa tsaye ya nufi waje, har ya Wan Wuceta ya waigo ""Give me a second pls"""

Yana kai nan ya fice.

"Zama tayi akan three seater Win, tun tana jira har bata san ta zame kwance ba bata san kuma bacci ya sureta ba saboda rashin bacci da bata samu a kwanakin don kwana mi™awa Allah lamuranta take a duk sadda damuwar wannan da bata san wanene ba ya hanata runtsawa."

Shi kam ™aramin meeting yayi da Securities dinshi na companyn ya manta ya tara su tun

"sassafe sai da aka kirashi aka tuna mishi, bayan ya gama ya dawo office Win ko da ya tura ya shigo kai tsaye idanunshi kanta suka yi."

"Hannayenshi ya zube a aljihu ya nufota ya tsaya daga gefen kanta

37 / 62