Chapter 13 Reading SAFARA A TAƁO Kunya Ba Tausayi By FATIMA MUHAMMAD | Hausa Novel READ HAUSA Novels

SAFARA A TAƁO Kunya Ba Tausayi By FATIMA MUHAMMAD | Hausa Novel

Author :  FATIMA MUHAMMAD Category :  African Stories & Novels

Chapter   13 / 62

36K to 39K   out of 184.1K words

min haka? Me nayi ne nikam? Don Allah"

"yayi ha™uri ya yafemin..."""

"""Mahaifinki ba ya cikin yanayin da za ki iya magana da shi Hibbah! Ki yi ha™uri"""

"Momma ta faWa tana janyota ta rungumeta saboda ta samar mata natsuwa don duk jikinta babu inda baya rawa, kuka ta sake fashewa da shi don bata tsammaci hakan ba tana kuma son sanin dalili"

"""Da gaske ne kenan Daddy ne ya hana aurena Momma? Da gaske ne ya rabani da Najeeb? Shikenan ni kuma haka za'a yi ta zuwa ana fasawa ana bari na da ciwo cikin zuciyata?"

"Momm..."""

"Numfashinta ke yankewa hakan yasa maganan ma daukewa hankali tashe Momma take kiran sunanta tana jijjigata amma tuni ta fara haki da kokarin janyo numfashin sai dai bata da control Win shi tuni ta kai ™asa a sume, salati da ihun kiran sunanta da Momma ke yi ya fito da Hudah da ta Soye kanta Wakin Momma tana kuka sossai don tana fitowa ta samu labarin wurin Aina'u, ta kasa komawa Wakin ne saboda bata san yadda zata fuskanci 'yar uwarta ba, ashe da gaske abin da take ji a jikinta ba alkhairi bane? Ita kanta ta rasa dalilin da zai sa Daddy ya hana Najeeb auren Hibbah, halin da ta isko su ya sake Waga mata hankali da gudu ta zo ta kama"

hibbar ta taya Momma suka yi ™asa.

"Mumtaz da Aina'u da suke zaune cikin jimami da damuwa a tare da Nadiya da ta zabga tagumi itama tana jimamin al'amarin Hibbah ganinsu yasa duk suka mi™e suka dunguma waje, Daddy Zubair ne da ya fito shima fuskarshi babu walwala ganinsu a hakan ya sa ya taho da sauri ya buWe musu motar shi suka shiga basu tsaya ko ina ba sai asibiti tuni Daddy Rabi'u da matanshi biyu a tare da Aunty husna ma suka rufa musu baya cikin damuwa da jimamin Al'amarin da ba'a"

taSa zato ko tsammani ba.

****

*BARI DAI MU DAKATA A NAN. LITTAFIN NAN YANZU MA AKA FARA TAFIYAR SHI DON DA SAURAN RINA A KABA... ME KUKE TUNANI YA SA AKA YANKE HUKUNCIN RABA

NAJEEB DA HIBBA? SHIN WANI AZAL NE AKAN HIBBAH DA TAKE GANIN BATA DA SA'AR

SOYAYYA A RAYUWARTA? ME ZAI FARU A GABA? WA ZAI KARYA MATA RECORD? WA KUMA ZAI FUSKANCETA YA BUŠE BAABIN DA TA RUFE KIRIB A RAYUWARTA NA SOYAYYA KO AURE? MUTANENA KU BIYO NI DON JIN YADDA ZA TA KAYA! ME ZAI

FARU DA AMAL A KAUYE? SHIN HAJIYA ZA TA SO HUDAH KUWA?

"*Littafin nan na kuWi ne ki biya Naira Šari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faWakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun"

0545475847

Gt bank

Fatima Muhammad Gurin

Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763

Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi.

Sai na ji ku*

Note: Da dare ne zan dinga posting da rana zan bi in dinga karanta comments naku so please a

ba ni haWin kai mu tafi lafiya kaman yadda muka fara lafiya. Na gode sossai.

Gureenjoh

16

"Kanshi a jingine jikin katifan nashi da tunda ya zamar da wayan bai sake ko da motsi ba har lokacin wasu hawayen da bai taSa tsammanin zai iya zubarwa ba yake zubarwa cikin zafi biyu da ya haWe mishi, ji yake kaman kanshi zai tsage saboda girman abin da ya ji a yammacin ya shallake duk tunaninshi, sunan Allah yake ta ambata cikin neman sassaucin birkiceccen"

yanayin.

"Tura ™ofan Wakin nashi aka yi, bai motsa ba don rudanin da yake ciki bai sa ya ji ma ™arar da"

"kofan yayi a sadda aka turon ba. Dafa shi yaji an yi tare da ambaton sunanshi ""Najeeb!"""

"Wani kakkauran miyau ya haWiye yana jan zuciya, Muryar kowa baya son ji ciki har Ummar tashi... Meyasa? Meyasa ta aikata mishi abin da ta aikata? Shi me yayi da ya cancanci karSar"

hukuncin laifin da bai san an yi ba?

"""Ka yi ha™uri Najeeb..."""

"Umma ta faWa tana zubar da hawayen da tun dawowar su Abba basu daina zuba mata ba, rayuwarta na baya take tunawa tana jin ina ma da zata iya mayar da hannun agogo baya? Ina ma tana da iko akan rayuwarta? Da bata zaSi ™addarar ta ya kasance a haka ba. Da bata bari rudin soyayya ya kwasheta ta tafka kuskure da ya shafi har Wan ta mafi soyuwa a ranta ba."

"""Umma ta yaya? Ta yaya hakan ya kasance? Ya kuke tunanin zan yarda da maganganunku sama-ta-ka? Me nayi da ba za ki iya sanar da ni abu mai girma haka a rayuwata ba sai yanzu da na gama sallamar da soyayyata wa Hibbah? Umma ba ni nake ji ba sai ita...bata fa da lafiya! Zuciyarta already a karye yake taya kike tunanin zata sake karbar wani namijin kuma a"

"rayuwarta ba tare da fargaba ko damuwa ba?"""

Kai take girgizawa ba tare da ta kalleshi ba hawayenta na ™ara gudu tace

"""Ka yarda da ni idan na ce maka ina jin kwatankwacin abin da kuke ji a raina nima, sam ban zata ta haka komai zai bayyana maka ba, na zaci komai ya wuce, na yi zaton na shafe baabin duk wani taSo ko gibin da rayuwa ya darsar mini a baya ashe ba haka abin yake ba ashe da sauran rina a kaba!"""

"""Umma ta ya Mahaifin Hibbah ya zama Mahaifina? Ta ina?"""

Ajiyar zuciya ta sau™e tana goge hawayenta da bai daina zuba ba kuma har lokacin bata kalleshi ba don bata ™aunar ganin mummunar yanayin da Wan nata yake ciki ta shiga cewa.

"""Ka san yanayin rawuyar gidanmu, Dukda mun kasance ba masu hali ba mahaifinmu mutum ne mai zafin gaske da tsananin a™ida hakan ya sa gidanshi komai yake a tsare bisa ra'ayin da yake so ba son ran Wa ba, ina aji biyu na secondary na haWu da Mudassir da ya zo bautan ™asa makarantarmu inda sabo ya shiga tsakaninmu kasancewa ta Waliba mai kwazo da haza™a, tun muna sabo har soyayya ya zo ya kullu a tsakani ko kan ya gama shekara guda cikin Daura ina jin cewa ba zan iya rayuwa ba a tare da shi ba, shima kuma yana ™aunata sossai Dukda ya faWa min su ma fafutuka suke da iyayensu don karatun ma da yayi under scholarship ne saboda kwazonshi kuma idan ya gama wannan bautan ™asa bashi da takamammen aikin kamawa haka"

na ji na gani na tura shi wurin mahaifina.

"Tashin farko Babanmu ya ™i amincewa a cewar shi ba zai kai ni har Kano ba tare da ya san wani kwakwarar sana'ar Mudassir ba, bautan ™asa ba abu bane da zai rike mace shi kawai baya ma so, ya fi kaunar yayanshi suna kusa dashi idan ya juya zai gansu kuma ya ga halin da suke ciki don haka Mudassir yayi hakuri ina da manema a cikin dauran zai turo su in zabi Waya daga ciki yayi min aure tunda abin da nake so kenan, nan na daka tsalle na dira akan sai Mudassir tun ma bai san rigimar da nake yi ba har ya isa kunnen shi, an kai ruwa rana don har makarantar ma an hanani zuwa, nayi kuka har da ciwo kaman ba zan rayu ba amma na kasa fawwalawa Allah in bi maganar iyaye duk saboda SO wanda bashi da tabbas! shi kanshi Mudassir bai ha™ura ba yayi ta zuwa ana mishi wulakanci iri iri a karshe na tubure bisa goyon bayan mamana na tafi wurin danginta a mai aduwa kawunaina suka Waura aurena da Mudassir"""

Hawayenta ta sharce

"""Ban san cewa kofar wani ba™ar kaddara na buWewa rayuwata ba sai da muka baro Mai aduwa zuwa daura mahaifina ya hane ni shiga mishi gida, ya kuma yi rantsuwar babu shi babu ni har abada ya sallama wa Mudassir, ban sani ba ™addarar shan wahala ne, rabon samunka ne ko sharrin dake bibiye da wasu soyayyar ne amma tunda muka shigo cikin Kano na ji auren ya fice"

min daga kai.

"Iyayensu mutanen kirki ne, Yaya Rabi'u a lokacin shi ke ciyar da gidan kasancewarshi dan kasuwa yayinda Zubair yake ma secondary a lokacin na gomnati, idan an samu abincin safe to babu na rana dare da kyar ake ci ga jinya mahaifiyarsu na kwance Dukda ba ranga ranga ba amma suna yawon asibiti, farkon aurenmu akwai sauran kudin service nashi da ya tara ya fara business amma a je a je bukatu ga iyaye ga iyali ya zo ya karar da kuWin tas ya shiga buga bugan inda yake bin 'yan siyasa, ban shekara biyu ba mahaifiyarsu ta rasu shima mahaifinsu da watanni takwas ya bi bayanta ba jinya ba komai sai Rabi'u ya janye ciyar da mu dama chan saboda iyayenshi ne da ya Wauke su dole, yana dai taimakawa amma ba komai da komai ba shima kuma da nashi iyalan kwatsam muna cikin wannan hali na samu ciki kai tsaye Mudassir ya nuna baya so lokacin ba na ciki bane saboda yaushe ya gama fama da ni bare ya fama da harkar yara, ban damu ba na biye mishi muka barar har aka sanya min tsarin iyali da yayi ta sakani jinya iri iri yayinda hankalin Mudassir ya komawa siyasa bai damu da halin da nake ciki ba, ina son zuwa gida amma mahaifina ya riga ya yi min katanga da shi sai dai a waya da mahaifiyata da naga zan iya mutuwa da jinya ga jini da nake zubarwa a koyaushe na tafi aka je aka cire min ba tare da sanin Mudassir ba, watanni uku bayan nan na samu juna biyu kwatsam sai laulayi na fara a sannan har Mudassir ya samu kujerar member saboda irin kwazonshi da zafin nama, nuna min yayi ban isa ba mun yi rigima sossai akan cire wannan tsari kan muka zo kan batun zubar da ciki akan har yanzu bai shirya ba, na ja ya ja nan ya ce min sai dai in zaSa"

"Wan ko auren..."""

Shiru tayi tana tuna irin halin da ta shiga a lokacin kallonta kawai Najeeb ke yi yana sake jin gabaWaya zuciyarshi na ba™i da Waci.

"""Ka kwatanta yadda macen da ta sadaukar da iyaye, karatu, gata, lafiya da kuma yarantarta akan namijin da a karshe ya juya mata baya zata ji cikin zuciyarta, na razana da kalamanshi sanin cewa ya san bani da inda zan je da ya wuce gidanshi tunda da shi na rufe ido zan yi rayuwa, ganin halin da na shiga ya sa ya fice ya kyaleni, na sabi mayafi na tafi gidan Yaya Rabi'u inda na kai mishi karar komai don har lokacin da yaranta ta don ma na daina makaranta tun daga auren da har a lokacin ban ™are secondary school ba, ya ajiye mu yayiwa Mudassir faWa sossai inda bai ce komai ba har muka dawo gida daga nan ya Wauke min, ba zan iya wassafa maka irin zaman doya da manjan da muka dinga yi ba har sai da cikin ka ya kai watanni biyar inda na gaji, na lalace na ™are a sannan shi kuwa kudi ya fara zama mishi sossai, har gida ya gina amma ya ™i mayar da ni saboda bama shiri don kawai ina dauke da jininshi a jikina na kuma nace sai na haife, na nemi da ya sakeni zan tafi don na gaji, ya nuna min ga mata dayawa a gari a yanzu yana da kuWin auro hudu in na tafi babu abin da zai same shi, zuciyata ta gama karyewa haka na haWa kayakina ya ba ni kudin mota da takardar saki na da"

kuma gargaWin har abada kar na neme shi tunda ba zan bi ra'ayinshi ba.

"Na yi kukan da ban san adadi ba na shiga tashin hankali a sadda mahaifina ya nuna ba gidanshi ba kuma ai sai dai wani gidan don shi a 'ya'yan shi ma babu mai kalan sunana ya jima da binne ta a karkashin kasa, ro™on duniya da magiya na yi bai saurareni ba na wuce wurin dangin mamana su Win ma ba wani karfi bane amma na zauna da su har na haihu damuwa, yawan kuka ya haddasa min hawan jinin da da na zo haihuwa kaman ba zan rayu ba don jijjiga a sannan ne nake ta ro™on a tayani neman yafiyan Babana mutuwa zan yi, ganin fa jikina ya fi"

karfin mai aduwa aka kaini Katsina a sannan ne mahaifina ya zo kaina daga nan ma Kano aka

"tura mu na azabtu kwarai kan na haifeka, ya ri™e ka ya yi maka Adu'a a lokacin tausayina ya fi komai yawa a ranshi, ya amince cewa rabon samun ka ne ya sa na tubure mishi a yanzu gashi na shiga cikin nadama mai yawa don Sunan Mudassir ya tumbatsa matashin dan siyasa mai kuWi a hannu, tuni ya sake aure ma ya manta ma da ya taSa rayuwa da ni A yawace-yawance"

"jinyata mahaifina yayi hatsari Allah ya amshi abin shi hanyar Kano zai koma daura na tsani mahaifinka fiye da komai da kowa a duniya saboda a ganina shine sanadin komai, ya wargaza min rayuwa ya wargaza min farin ciki saukin ta ma ba ta yadda kuka yi kama so bana ganinka"

matsayin danshi sai dai nawa.

"Na koma daura bayan tsawon jinya muka cigaba da rayuwa a gidan gado karkashin mahaifiyata itama ta rasu baka wuce shekaru uku ba, Abbanku abokin yayana ne ya kan je Daura ziyara yana matukar kaunarka, tun ma bana sakewa da yadda yake kaunar naka har na fara sakewa muna hira da gaisawa kan ya nuna yana so na, na so na ™i don tabon muddasir wallahi da shi zan mutu a rayuwata amma sai su Yaya suka hane ni, a karo na biyu ba zan iya kin bin umarnin na gaba da ni ba haka ya auroni ya dawo da ni kano ranar da na dawo na yi kuka marar adadi don ina tuna sadda na biyo son zuciyata na zaSi Muddasir akan komai da kowa nawa a ™arshe"

na haifi da marar ido.

"Abubakar na kaunarka wane shi ya haifeka Dukda bashi da arziki amma mutum ne mai zuciyar yi sannan yana da rufin asiri ya nuna min soyayya har na haifi duka ˜annenka uku, wallahi ban san Hibbah ta ala™anta da muddasir ba, ban san cewa zata iya zama Wiyar shi ba, na kuma Soye maka komai ne saboda ina so ka cigaba da rayuwa cikin farin ciki ba tare da tuna akwai wani da yayi abandoning Winka a baya ba, sannan tuna komai da ya faru kaman tono wani miki"

"ne mai wayar warkewa"""

"A hankali yayi hugging na mahaifiyar tashi ganin har jikinta na rawa saboda kukan da take yi,"

lallai dole wasu su tsani So! Wasu mazan sai ka rasa menene a zuciyoyinsu su kan manta duk wani hallaci na mace da sadaukarwarta...

"""Na fahimceki Umma! Ki yi ha™uri na ganin laifinki da na yi ashe kema a kaddararki akwai bautawa So da kuma cin amana mai zafi, umma na fi jin Hibbah fiye da kowa tambarin Mahaifinta sai ya sa ta sake tsanan maza don za ta tabbatarwa kanta da cewa lallai namiji ™anin ajali da ake cewa gaskiya ne.."""

"Šagowa umma ta yi tana Wan murmushi da bai mamaye fuskarta ba ta mi™e kawai don Allah ya gani a yanzu ko maganar hibban bata so bare mahaifinta, shima kuma Najeeb Win ya ji cewa har abada ba zai sake shiga huldarta ba Dukda ™anwarshi ce kuma bata da laifin komai amma"

shi bai karSi Alhj Mudassir matsayin uba ba.

****

"A chan asibiti kuwa da kyar aka ceto Hibbah, ko da ta farka ta cigaba da kukan da maganganu sai da suka yi da gaske ta natsu amma da Momma tayi mata bayanin komai saboda babu abin boyewa a yanzu gwara kawai ta sani a maimakon ta samu hujjar yi wa Najeeb sai ta sake"

"samun hujja a kan maza ashe duk halinsu Waya ne, ashe yaudara da son zuciyar bata bar kan"

"kowa ba...tana tuna umma da irin kirkinta sai taji duk lamarin mazan ya sire mata, ko da Daddy ya shigo duba ta bayan gaisuwa bata sake magana ko kallonshi ba, shi karan kanshi ya zabge a kwana Waya jal saboda bai taSa tunanin ta nan Allah ya kama shi ba, babu abin da yake son sake gani a yanzu irin fuskar Najeeb, babu kuma wacce yake son yafiyarta kaman Mahaifiyar Najeeb a wannan duniya, ha™i™a ya zalunceta amma Allah ya gani ya jima da yin nadama kuma"

ya neme ta bai sameta bane ya ha™ura.

"Jiki a sanyaye suka tarkata suka yi gida don Hibbah ta nace a sallame ta, Mu'azzam ma ya zo ya Wauki Hudah da tayi wani iri saboda damuwar 'yar uwarta, ko da ya tambayeta an gama"

komai na Hibba ce mishi kawai tayi eh don ba za ta iya dogon jawabi ba.

"A chan Sangaren Amal kuwa sai da ta gaji da zama a wurin da kuka da komai Dukda ita kaWai ce a tsakar gidan don duk sun share ta haka ta mi™e don fita daga gidan ta nemi yadda za ta yi ta koma gidan mahaifinta sai dai ji tayi kaman an Waure mata ™afafu, wani ™unci da damuwa ya sake ziyartar zuciyarta, Innar Qasimu da ta fito jin motsinta ta nuna mata wani Waki"

"""Ga chan Wakin ki ki shiga ki huta kan a gama tuwo"""

Ga mamakin ta kasa Musa mata tayi haka ta nufi Wakin jiki a saSule.

"*Littafin nan na kuWi ne ki biya Naira Šari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faWakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun"

0545475847

Gt bank

Fatima Muhammad Gurin

Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763

Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi.

Sai na ji ku*

Gureenjoh

17

Wanka ya fito sai dai tunda ya zauna da niyyar shafa mai bai motsa ba har Momma ta shigo

"Wakin bayan ta gama kintsa komai da yayi amfani dashi na abincin dare ganinshi zaune cike da damuwa a yanayinshi, zama tayi gangarshi ta shiga cewa"

"""Daddyn yara tunani ko damuwa ba su ne mashalar halin da duk muke ciki ba, ya kamata ka"

"™arfafa wa kanka ko don

13 / 62