MABARACIYAH Daga Bara Zuwa Firgitar Masu Iko by Auwal sadiya

Author :  Auwal sadiya Category :  Free Novels Online (Read & Download)

Chapter   8 / 33

21K to 24K   out of 96.8K words

wanke,kin manta wajen wankinne kike shirin wucewa"
"Iye na'am inno dama ......uhm anty juwairah ce zata ɗan tayani na wanke"
"Zaki kaimata dai irinna wancan satin,banace ku dunga wankewa ba,shine zaki kai mata saboda kinda tana wanke miki koh,to ƙaro dana khairi itama ki wanke mata"
Tsalle nafara da dira kafa ina kukan tsiyah.
"Kai inno kai inno ya za'ayi ace ni zam wanke mata wandon datake fitsari a jikinsu,ni wlh....."
"Ke wlh me?...bazaki wanke ba ko mai,ba ƙanwarki bace,keda ba wata zaki kai ta wanke miki ba,ashe babu daɗi kenan....."
Katsewa tayi da maganar jin muryar baba shehu yazo yana mata magana.
"Shatu maza kizo wata yarinyah aka kawo,wani mutum ne ya kawota amma munyi munyi tayi magana taƙi,gashi mutumin ya riga ya tafi"
"Toh ikon allah,yarinya ce ƙarama har haka?"
"Ahah ba ƙarama ba ce,dan zata fi su khairi da kaman shekara guda koh fi ,saidai daga ganin yarinyar kaman taga rayuwa sosai"
Juyawa inno tayi tabi bayansa domin ganin wacce yake magana akanta,nima ina za'a barni a baya gulma tana cina,da sauri nabisu dan ganin wacece,musamman danaji ance sa'armu ce,rabon da'akawo mutum mai ɗan girma tun muna ƙanana,hakan mazane guda biyu,shiyasa abin yabani mamaki.
Binsu nake a baya batareda sun ganni ba,har muka ce office ɗin baba shehun,a bakin ƙofar na labe ina leƙawa kaɗan kaɗan,yarinyace kam kaman yanda ya faɗa,sanye da wata riga iya gwiwarta,da alama rigar ta daɗe a jikinta saboda dauɗar da rigar take tattare da itah.
Gashin kanta dogone ya zube gaban goshinta wanda yana ganin fuskarta sosai,saidai duk da haka mutum sai ya hando farar fatarta datayi baƙi saboda dattin jikinnata.
Babu takalmi a ƙafarta,duk ta farfashe kaman wanda tayi tafiyah akan ƙaya,a takaice dai in ka haɗu da itah a jeji zaka iyah rantsewa fatalwa ce.
Saurin rufe bakin nayi domin karnayi babban motsi lokacin danaji baba shehu yana yiwa inno magana.
"Gata nan Shatu ki shiga da itah ciki,nasan akwai yara a wajenki haka itama maryamu(maman yara),nayi niyyar kaita wajen Hajjah,saidai zamanta wajenta bazai yiyuba,saboda yarinyar tana buƙatar kulawa da ƙwantar da hankali idan ana so da dawo yanda take,kafin sannan ki kaita ciki ki shiryata ko kayan sabrah ta saka,zumuje asibiti a dubata,koda juwairah sai mu tafi.
Ganin inno taja hannun yarinyar zasu fitone yasa na koma cikin gidan da gudu.
Da deen mukayi karo a bakin ƙofah zai fita,saurin riƙo hannunsa nayi jikina har rawa yake wajen faɗa masa mai ya faru.
"Kai dallah zokaji wata magana,bari kaji munyi sabuwar ƴar uwa,saidai kama take da fatalwa idan ka ganta"
"Ƙaryah kikeyi,nasan ƙaryarki fah sabrah"
"Mtsww bana son raini,ina maka ƙarya ne,ta barika ga yanzu inno zata shigo da ita,in da gaskene sai nayi maka duka uku,ko kayi bacci kuwa"
Muna cikin maganar ne muka hango inno ta kamo hannun yarinyar sun nufo hanyar shigowa gidan,haɗa ido mukayi da yarinyar,duk da lokacin banida wani hankali amma kuma naga wani abu wai tashin hankali a cikin ƙwayar idanuwanta.
"Ku kuma mai kukeyi a nan wajen,yar butan uwa ina kallon idonki ai kina leƙowa,wato kinzo kina yafa masa tun kafin mu ƙariso koh?"
Tun kafin ta dungureni na shige gida ina dariyah,dan dama mun sabayi nida inno tawa takaina.
Shashenmu suka shigo lokacin na koma wajen wankina,amma ban ɗauko na kharin da'akace ba,saboda naga inno ta manta da zancen.
A bakin baranda suka tsayah da yarinyar wacce take ta rarraba ido a gidannamu,kaman wanda ta daɗe bata ga gida ba,ni inaga ma daga jeji aka ɗaukota.
Maganar da inno take matane ta katsemu dukka dagani har itan a tunanin damuka faɗa.
"Yarinyah menene sunanki?"
Shuru tayiwa inno tana kallonta,da alama taji mai tace amma kuma bata mayar mata da martani ba"
"Da alama kinji mai nace,ko bakya magana ne?"
Jijjiga wa inno kai tayi,da alama tana maganar kenna ba kurmiya bace,amma menene haka ya hanata yin magana,allah ya tsaga maka baki dan kayi magana amma ka rufeshi kirif mai yasa?,mu gamunan sai anyi da gaske muyi shuru,amma ita maganar ce taƙiyi
Ɗan karamin murmushi inno tayi mata wanda zaisa ta kwantar da hankalinta,
"Ki saki jikinki kinji,nan gidanku ne kema kaman sauran yaran dasuka tsinci kansu a gidan,ki kwantar da hankalinki babu abinda zai sameki,ki ɗaukeni kaman uwar data haifeki,nikuma nayi alƙawari zan riƙeƙi tamkar ƴar cikina kaman yanda na riƙe sauran yaran"
Ɗan murmushi itama yarinyar tayi amma har sannan akwai zullumi kwance a cikin idanuwanta.
Rigar jikinta inno ta ɗaga zata ciremata tayi saurin riƙewa tana zare ido.
Nida inno ƴar dariyah mukayi da muka gani mai take nufi,wato tana kunyar a ciremata riga,da gaskiyar ta muma tun yaushe inno ta daina yimana wanka,sai ita za'ace za'a yiwa wanka,ganin dariyar danake yimatane yasa ta ƙara sunkuyar da kai,inno ce ta kaimin duka tareda nuna min hanyar barin wajen.
Fita nayi na nufi wajen su khairi,zuwa lokacin labarin zuwan yarinyar gidan ya zagaye ko ina na gidan.
Saida aka kai ruwa rana kafin ta bari inno tayi mata wankan nan,a tunanina kunya takeji kaman yanda muke idan za'ayi mana,saidai kuma da alama hasashena ba daidai bane,mai yiyuwa tana boye wani abune a jikinta,wanda yazama sirrinta da take so ita kaɗai tasani.
Komadai menene naga kaman ta yadda da inno,daga yanda ta ɗan sake da ita.
Gyara mata jikinta tayi,tareda bata kayana ta saka,duk da ta ɗan fini a tsayi,saboda na ɗan fi khairi jiki amma kayan sun shigeta saboda yanda halin rayuwa yayi da itah,da alama idan bata tsinci kanta cikin hakan ba zata iyah fina ƙiba.
Wanki mai kyau inno tayiwa gashinnata kafin yasamu damar yij kalar irinna bil'adama,haka zalika fatar jikinta wanda yanzu ta nuna kalar ta ba fara ba,kana kuma ba baƙa ba.
Mashaallah tana da kyau dadai misali,wanda yanzu yasamu damar fitowa,saidai kuma ramar datake jikinta itama wani abune daya yi mata cikass.
Hannunta inno ta riƙo suka fito daga ɗaki zuwa harabar gidannamu,inda kowa ke haɗuwa idan ya fito daga sashensu.
Kallo ɗaya tayi mana tayi saurin sauƙe kanta,ganin yanda tarin yara suka kafeta da kallo,tunda suka fito wajen idona yake kanta,haƙiƙa naji daɗi da'akace a sashenmu zata zauna,koba komai na samu abokiya idan mukayi faɗa da khairi,dan haka kawai nakejinta a raina tamkar ƴar uwata.
Baba shehu ne yafara magana,dan dama duk sanda aka kawo wani indai yanada wayo to zai faɗi sunansa muma mu faɗa masa.
"To alhamdulillah,godiya ga Allah daya bamu wannan rayuwa mai albarka,kaman ko yaushe bama rasa amsar ɗaya daga cikin al'ummar musulmi zuwa wanann gida wanda ya tara yara marasa galihu,to yauma mun samu baƙuncin wata baiwar allah wanda aka kawomana ita an sameta a jeji a zaune.
Muna fatan masu riƙon gidanann zasu riƙeta kamar yanda suka saba ga kowanne yaro idan ya faɗo hannunsu,duk da cewa ana biyansu amma hakan bashine yake nuna an biyasu dukkanin ƙoƙarinsu ga yara marayu ba,wannan sakamako ne da sai allah ne kaɗai zai biyata a ranar ƙarshe.
Sannan ku kuma ina fatan zaku rungumeta tamakar ƴar uwarku,ku rayu tsintsiya maɗauri ɗayah"
Dukkanmu haɗa baki mukayi wajen amsawa,cewar zamu karbeta a matsayin ɗayarmu.
Bayan an gama jawabi ɗaya bayan ɗaya muke zuwa muna faɗamaata sunanmu,har aka zo ƙaina.
Tashi nayi na isa gareta tareda kama hannunta.
Kallona tayi da mamaki,inda ta sauƙe idonta akan hannunnamu kafin ta kuma mayarwa zuwa cikin idona,murmushi nayi mata mai nuna mun karbeta zuwa cikinmu kafin na yi mata magana.
"Sunana sabriyyah ana cemin sabrah,ni ƴan biyun khairiyyah ce,nasan kinga kamarmu koh,ke kuma fah menene sunanki,har yanzu baki faɗamana ba?"
Da gangan na tambayeta duk da nasan ba amsamin zatayi ba,dan inno ma ta tambayeta ɗazu amma bata amsa mata ba,ga mamakina sainaji tayi magana cikin dashashshiyar murya mai nuna ta daɗe batayi magana ba.
"Banida .......ssssuna,bansan sunan ba"
"Khamriyyah ,sunanki khamriyyah daga yau kinji"
"Khamriyyah.....?"
Sunan nata ta faɗa,amma kuma saitayi kaman tambayata takeyi,dariyah abin ya bani wanda hakan yasa ni yin dariyar.
"Sunanki mai daɗi khamriyyah,gashi yana kama da namu,mai yasa kike tambayata,nasan zai miki kyau shiyasa nafaɗa miki,ki dunga amfani dashi kafin kisan naki kinji?"
Ɗaga min kai kawai tayi amma
,Bata sakemin magana ba,da alama bata shiiyah yin surutun danake shirin jan ta dashiba.
Juyawa nayi na kalli su deen tareda cewa,
"Ku sunnan ta khamriyyah daga yau,ya kukaji yana kama da namu koh"
Hajjah ce ta harareni tareda kauda kanta tana mita
"Mtsww yarinya sai shegem iyayi,daga ganin baƙuwa harkin saka mata suna dan kinga bata dashi,uhm"
Inno tana jinta kuwa ta cafe,
"Abune mai kyau ai hajjah,yarinyar dama tanason wanda zai jata a jiki,saboda halin da take ciki"
Tafiya akayi da itah zuwa asibiti kaman yanda aka faɗa,yayinda mukuma muka nufi yin wanka domin tafiyah islamiyah,bamuje ta safe ba saboda ranar lahadi ne amma ta yamma kam dole sai munje.
A hanya na kalli maryam wanda tayi shuru tana zazzare idanu,
"Uhm maryam amma ya kike gani musami wata ƙawar,kinga mun zama mu huɗu kenan koh,farida dama mun fita,maman yarace take cusata a cikinsu"
Farida tana daga baya tana jin abinda nake cewa,aikuwa ta cafe.
"Eh in kun fini kuma wacce aka kawo ɗin ai tafiku,dan haka idan kukayi mata raini kuma nayi muku"
Binta nayi da gudu na buga mata jakar makaranta ta a bayanta,duk abinda ake deen,khairi,da maryam basu tankaba.
Ganin abin yayi yawane ma deen ɗin ya kallemu tareda yin magana cikin faɗa,
"Ku dallah ku kyalemu da zancen wata yanxu,ke sabrah wato kin manta da dukan malam garzali koh,hmmm sai ya kamaki kiyi ta ihu kaman an kasheki,amma kinfi kowa manta mai zamu tarar,gashi bamuje wajen anty juwairah haddaba,hmmm yau akwai duka"
Tashi ɗaya abin ya faɗomin a rai,tunda na manta da hakan sai yanzu,idona ne ya fito nayi firi firi ina tuno yanda yake zambaɗamin bulalar idan bankai haddarba,kallon su maryam nayi wanda tun ɗazu su sun tuna da hakan,nikaɗaice na manata,nake biye farida wacce iyah haruffah ake koyamusu,kar'bar haddar ma tare suke bayarwa.
Tuntsurewa da dariyah deen yayi yana bubbuga takashinsa wanda yake bada ƙarar wanduna da yawa.
"Ihuuuu wasu zasu sha duka,nayi ciko tamau,kaya za'a daka,ku kuwa idan ya kamaku kowa sai tayi fitsari"
Munji haushi abinda ya faɗamana saidai yau babu damar maida martani,dan cikin kowa ya ɗuru ruwa da tsoron malam garzali.
Haka mukaje kuwa yayi mana duka,har aka dawo gida muna kuka,musamman khairi,tun inno tana rarrashinta har tagaji ta bari dan haushi.
Basu anty juwairane suka dawo gidab na har wajen magriba,saboda saida akayi mata ƙarin ruwa tareda gwaje gwaje,iya maleria ce kawai take damunta sai typhoid saboda gurbataccen ruwa da tayi tasha.
Ba laifi ta sauƙi sosai,dan iyah magani suka rubuta mata wanda zata dunga sha.
A ɗakinmu aka ce zata dunga kwana kusada katifata.
Tare mukaci abincin dare,saidai babu wanda tacewa komai har muka gama,muma bamuyi mata magana ba sai binta da ido kawai da muke,ganin sabon abu.
Bayan mun shiga mun kwanta inno ce ta tofamaana addu'a kafin ta kashe mana wutar ɗakin,duk da yanxu mun iya addu'ar da kanmu amma kuma sabon yimana harda yaran da suka zo kafinmu yabi jikinta.
........cikin dare naji an tsala wani uban ihu mai masifar firgitarwa,zabura mukayi dukka muka tashi,musamman ma ni da nake kusada ihun.
Khamriyyah muka gani a zaune har sanann bata bar ihunba amma dai ƙarar ihun ya ragu.
Dukkan ilahirin jikinta rawa yake ga wani gumi daya rufeta shirkif kaman an watsa mata ruwa.........













Taku
_sadi-sakhan_
Ƴar mutan jama'are.





*(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)*

*MABARACIYAH*
(mai harshen damo)

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιε.


_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)



Paid book #400
3131951977
Auwal sadiya
First bank

Mai turo kati kuma ta wanann number MTN
09035784150

Mutanen niger su tuntubi wanann number
+227 97 21 16 15

Naƙara shafin free har zuwa page 20,zuwa lokacin inka shiryah kazo a fara dakai ranar juma'a.

_____________________
Assalamualaikum barkan mu da wannan lokaci *ABMAR COLLECTION* ina nan na kawo muku kayana masu kyau da sauki👌🏻
KAMAR SU:-
Atamfa, Atamfa Mai golden,💁‍♀️
Lace ,Shadda lace
Yadi, Shadda
Abayas💥
Kids wear
Takalmi, jaka, mayafai💥
Sleeping dress, kananan kaya na gayu🔥kayan kitchen,
DA DAI SAURANSU ina Sokoto ina tura kaya ko ina da izinin ubangiji mai son kayana pc ina maraba daku siyan daya ko sari👏🏻domin neman karin bayani sai ku neme ni ta wannan number waya👉08101521252
nagode kwarai da gaske💃💃











13••14









Dukkan mu kallonta muke yanda take nishi numfashinta yana sama da kasa,kaman da alama yana mata wahala wajen shagarsa.
Gashi dukkanmu dagani har khairi da kuma sauran yaran an rasa mai matsawa kusada itah,ganin hakanne yasa na jawo khairi tareda yimata raaɗa a kunne ,na taje ta ƙira inno a ɗakinta.
Bata daɗe da fitaba sai gata tashigo itada innon.
Saurin ƙarisawa wajen ta tayi,wanda har yanzu razanar bata bar jikinta sosai ba.
"Khamriyyah lafiyah kuwa,kinga ɗago ko kalleni,menene ya faru"
Tana yi mata magana tana tofamata addu'o'i a jikinta,dan abinnata yayi kama da wanda aljanu suka ra'esu.
A hankali take sauƙe sautin kukannata,har ya zamo iya ajiyar zuciya kawai takeyi,kallon inno take da kuma su sabrah,sai a sanann ma takula asheda mutane a kanta.
Da alama kenan duk tambayoyin da inno tayi mata batasan tanayi ba.
Mamaki abin yabani,wai dama haka masu aljanu sukeyi,danni ban taba ganin mai yiba,tunda mu iyah rayuwarmu to ta ƙarene dag makaranta sai kuma gida.
Bamuda buƙatar yawo yawo irinna yara,dan idan wasanne har ma munyi yawa inaga.
"Kalleni khamriyyah,yanzu kinajin mai nakecewa,in kinaji ki ɗagamin kanki"
Ɗaga kan khamriyyah tayi,wanda hakan yake nuna taji abinda inno ta faɗa kenan.
"Mai yafaru dake,ki faɗamin idan har kin ɗaukeni a matsayin uwa,kaman yanda na ɗaukeki a matsayin ɗiyata"
Jijjiga kai khamriyyah tafarayi tana ƙara dawowa da kukannnata,saidai yanzu a cikin hankalinta takeyi,bana razana bane,
Yanda take kukan da kuma abinda yake kan fuskarta,ya isa shaidawa mutum batason amsa tambayar da inno tayimata.
"Kiyi haƙuri inno.....in in in ?"
Daga haka ta gagara sake cewa furta wata kalmar bayan haka.
Ganin tambayar bazai haifar da wani ɗa mai ido ba,saima ƙara saka ta kogin ɗimuwa,yasa inno sauke ajiyar zuciya tareda dafa kafaɗarta
"Kiyi shuru ya isa haka to kukan,ki kwantar da hankalimki,inshaallah babu abinda zai faru,daga ni har sabin ƴan uwanki a shirye muke da mu tarbeki a cikinmu,sannan mu saurari kukanki,a duk lokacin da kika yi ra'ayin sanar da mu,in allahh ya kaimu gobe zan yi ƙoƙarin sanar dake wasu addu'o'i kafin a salak8 kema a islamiyyah."
Ɗaga kai khamriyyah tayi,alamr taji abinda innon ta faɗamata,sannan ta koma ta kwanta tareda rufe jikinta ta mayafi.
Juyowa wajenmu inno tayi tareda yimana magana muma,ganin yanda mukayi tsuru tsuru muna kallonsu
" yanzu dare ya fara ku samu ku kwanta gobe da makaranta."
"Toh"
Shine kawai abinda bakimmu yasamu ƙwarin gwiwar fada.
Da safe tashi mukayi har khamriyyan kaman babu abinda yafaru jiyan.
Shirin mu mukayi kaman kullum cikin kayan makarantar tamu,har zan fita zuwa wajen karyawa khairi ta riƙe hijabina ta bayah.
"Wlh baki isaba sabrah,haka kawai jiya ki sakawa hijabinki manja shine yanzu kuma ki ɗauki nawa,wlh ki ciremin"
Juyawa nayi na kalleta,duk da nasan banawa bane,ammafah babu alamar zan karbi laifin ko kuma na cire hijabin saima ƙoƙarin ƙwace riƙon datakemin nakeyi.
"Dallah ki sakeni,a gidan uban wa na saka manja a hijabinnawa,wannan ne nawa,saidai idan ke kika saka manjan"
Faɗa muka fara har hijabin yana ƙoƙarin yagewa,inno ce ta fito daga ɗakinta da ɗan ƙaramin yaro a hannunta wato Abdoul wanda take riƙo,ɗaya hannunnata kuma da naira goma guda biyu na taran mu.
Sakin baki tayi tana kallon yanda muke ta faɗa bayan ita kuma tana ciki tana nemo mana kuɗin break fast..
Ranƙwashi ta saki mana a kai kowa guda ɗayah,take kuwa khairi ta fasa ihu tana tsaramata abinda nayi mata.
Kallona tayi nayi saurin kauda kai ina jiran mai zai biyo baya.
"Hmmm wai sabrah nikam wannan faɗannaki na rashin gaskiya yaushe zaki daina ne?"
"Ba nata bane hijabin nawa ne fah inno"
"Wlh ƙarya take,ga can nata ita taci ɗan malele a wajen su Umaimah,ni banci ba"
"Yi shuru nasan ita taci ai,to cire hijabin ki bata,ki dau naki ki saka,wani ne yahana ki kaishi wajen wanki,gashi yau monday,kai sabrah allah ya shiryeki"
Cun'buna baki nayi bayan wulga mata hijabunnta,tareda fasa kuka ina zama a wajen.
"Ni wlh to inno bazan je makaranta da nawa hijabinba,malam Ɗahiru dukana zayyi, koroni zayyi kona jema"
Hijabin khairi ta ɗauka ta saka tareda ƙarbar nata kuɗin tayi waje,tunda an ƙwata mata hijabinta shikenan.
Shigewa ɗaki inno tayi bayan ta zabga min harara,alamar aiki bai isheni ba.
Bayan tashige nikuma tsayawa nayi ta burburwar ganin yanda khamriyyah ta tsiramin ido tana kallona,ashe tun sanda muka fara faɗan ma tana ɗakin tana kallommu,amma baxaka ce da mutum a wajen ba.
"Meyasa kika yi shuru kina kallonmu"
Banyi zaton zata amsamin ba sai naji tayi magana
"Saboda sha'awa kuke bani sosai"
Tunani na tafi a raina,
"Sha'awa kuma,muna faɗa kice sha'awa?"
Bata mayarmin amsar ba inno tafito daga ɗakin tareda kallona
"Dallah tashi ki ciremin kayan nan inba so kike kiyi datti dasu ba,dama burinki kenan ki zauna a gida ai,in kika kuskura baba shehu ya ganki baki je makaramta ba bada ke zayyi ke kika sani"
Jikina ne yayi sanyi,dan na tsani jin an ambata min kalmar za'a bayarni.
Tashi nayi na cire riga da wandon na mayarda doguwar rigata wacce na cire.
Komawa nayi kan kujerar da khamriyyah take na zauna mun kallon juna.
"Khamriyyah meyasa bakya yin magana sosai?...."
"Saboda bana buƙatar yin hakan,idan naji buƙatar hakanne nakeyi,saidai bawai buƙatar hakan yana daga cikin abinda nake so bane,saidan yana daga cikin kaɗdarata"
"Ƙaddara kuma?....meyasa kike magana kaman manyan mutane,kowani babban ma da ƙyar zai gane"
"Kamawa tayi shiyasa,sannan yawan magana ko yin magana bashi yake sakawa ka iya magana ba,saidai idam ita maganar tasoka da iyata"
"Amma....."
"Sabrah ke kuma kin kasance mai yawan tambaya sannan da manta damar da kike da itah rahama ce.
Duk da kina gidan marayu amma kuma kinada uwar da ko ita ta haifeki iyakaci,kina da ƴar uwar da kuke jini ɗaya,sanann kinada kwanciyar hankali babu fargaba,uwa uba sunada muradin baki ilimi wanda zakije ki dawo kina gaban idonsu,meyasa kike wasa da hakan?..."
"Kin ban mamaki,yanxu fah kika ce muna burgeki da muna faɗa,yanzu kuma kina cewa meyasa mukeyi?"
"Kina burgeni saboda kin samu damar yin faɗa da ƴar uwarki,kina ban takaici saboda kin bari kina faɗa da ƴar uwarki"
"Kinada abin mamaki,dole kiyi shuru,dan idan kikayi magana babu mai cewa ke yarinya ce"
"Kema kinada abin mamaki da kika

8 / 33