Author : Auwal sadiya Category : Free Novels Online (Read & Download)
so kenan,wasu mutane ya ƙira maza uku mace daya sai kuma wanann ma'aikaciyar asibitin.
Dukkansu tambayarsu akai ɗaya bayan dayah,amma amsa iri ɗaya suke bayarwa kan cewar dagaskene munje mun faɗamusu kashe mutane ake a asibitin.
Wasu kanma hadda ƙarinsu,kanaji kasan ƙaryah sukeyi,dan ko ganinsu bamu taba yi ba sai yau,idan aka cire nurse ɗin
Duk da bamuda hujjah ko guda ɗayah,amma mun ƙi karbar laifin da bamuyi ba,wanda hakan yasa aka ɗaga ƙara sai gobe da safe.
Turamu aka sake yi zuwa wanann baƙin ramin,muna kallon idonsu inno,baya khariyyah da idonta yayi luhu luhu kaman garwashi.
Bayan mun koma wani garin kwaki aka bamu babu ƙarago babu suga,haka muka cusashi a cikinmu.
Can kaman misalin karfe shabiyu mukaji motsin mutum yashigo cikin cell ɗin.
Saurin tashi nayi na ƙanƙame khamriyyah wacce itama ta buɗe ido.
Mai aikin wajenne da fitila a hannunsa da kuma wayah.
Bayyi magana ba sai haskamu dayayi tareda nuna mana gaban wayar,brr shehu ne a zaune akan kujera,gefens kuma dr bukar kana ganin wajen kasan aljannar duniyane.
"Nasan kunyi mamaki koh,toh muna so gobe ku amshi laifin da'aka ɗoramuku a gaban kotu,idan ba haka ba kuma,sai mun halakar da duk wani rai dayake wanann gidan marayun,sannan kuma kubi bayansu,saiku zabi ɗayah,idan kunada wayo kuyi yanda mukace muku,abubuwan dakuka sani kuma ku zama makafi sannan kurame akai,idan ba haka ba kuma hmmm gargaɗine ƴan yara,ku tuna bakuda ikon yin komai akai"
Suna gama faɗin hakan wayar ta mutu,mutumin ko magana bayyi mana ba yafita daga cell ɗin tareda maida wajen ya rufe.
"Khamriyyah anya kuwa ba wani abu suke nema daban ba,ba iya wancan ba"
"Sai yanzu kika sani sabrah,hmmm da iyah wancan ne da yanzu sun kashemu har lahira,yanzun ma inaji a jikina suna gama wannan abin zasu kashemu,saidai in dabara zamuyi.
Gobe zamuyi musu abinda suke so,amma karmu yadda mu shiga motar dazasu kaimu gida a cikinta,idan ba hakaba kuma kinsan sauran"
Zaro ido nayi ina kallonta sai kuma yanzu nakulada hakan.
Washagari da'aka bamu laifin bamiyi taurin kai ba,ta inda mutum zai gane shari'ar ta son kaice ba'a tambayemu dalilin daya saka mukayi ba,ko suwaye suka aikomu,saima wani batu da mukaji alƙalin ya zayyano,wanda shiya bamu tabbbacin shima ɗan cikinsu ne.
"A bisa shaidu da aka kawo da kuma yanda masu laifi suka amsa lafinsu,kotu ta yanke zasu biya tara naira miliyan 60,saboda abinda sukayi mai girma ne sosai.
Amma kasancewar a ƙarƙashin gwamnati suke itace iyayensu,toh gwamnati keda alhakin biyan wanann kuɗin,lawyarn gwamnati ko kanada tacewa?"
Wani ne ya tashi a jerin lawyoyin tareda matsowa gaba.
"Eh wato ranka yadaɗe,madadin biyan kuɗin gwamnati da bawa dr bukar wanann gidan marayu a matsayin tarar daza'a bashi,saboda bisa la'akari da abubuwan dasuke faruwa a wajen dama,ministern kulada fili sai yasaka hannu"
Tafi suka ɗauka manyan wajen tamkar suna ɗakin taron siyasa.
Da saurinsa ministern yazo yasakaa hannu a takardar tareda miƙawa alƙali.
Shikuma ya miƙawa dr bukar takardun filin,wanda ko mahaukaci yasan wanann shari'ar wasace kawai.
Dukkanmu sakin baki mukayi muna kallon abinda yake faruwa,kaman an haɗa drama,su kuma ko kunya basaji a gaban mutane lallai sunyi nisa basajin kira..
Yanzu ina zamu shiga kenan,nidama nasan akwai abinda suke so shiyasa aka yi mana haka,tamkar tumaki gaskiya idan bakada galihu ka shiga uku a rayuwar nan.
Dayake sun samu abinda suke so nan da nan aka sallamemu harda motar dazata mayarmu gida.
Mutane sai kallon banza ake mana,wasu suna allah wadaran naka ya lalace,wasu kuma na laifin iyayenmu ne,kowa da abinda yake faɗa.
Duk baƙin jinin dazasu jawo mana bai damesu ba,mu tamkar dolly muke a wajensu su wana yanda suka ga dama,saboda babu wanda zaibi bayanmu kowa nasa ɗan yasani ba marayu ba.
Anzo fita a garin katsinan kuwa mukayiwa direban wayo akan cewar zamuje wani waje,duk yadda yayi damu mukaki komawa motar bayan fita,ƙarshe ma guduwa mukai cikin jeji,da alama bai san wani abu za'ayi mana ba dam haka bai takuraba yaja motar ya koma cikin gari.
Mu kuma muka Hau motar garinnamu.
Bamiyi garajen zuwa gidaba sai muka tafi wajen a anguwar tamu,saboda tsaro.
Kafin dare kuwa labari hatsari direban ya haɗa gari,ashe dayar motar tasa a since take,hmmm kisa baya yimusu wuyah,gashi motar kamawa tayi da wutah saboda abinda aka saka a cikin man motar.
Dan haka babu wanda yasan mun mutu ko kuma munyi rai.
Ko sati ba'ayiba dr bukar yakori dukka yaran gidan da kumamu gabaɗayah,dayake nida khamriyyah bama son a gane muna raye ,iyah su deen ne suiayi ta ƙoƙarin maida yaran zuwa gidan wani marayun.
Maman yara ma tafiya tayi,itama inno da mukace mata makaranta zamu tafi sai tace zata ɗauki su fadeelah su tafi kyauyensu,
Khamriyyah ce ta hana ta akan itama fama take da kanta,tunda gidanmu na katsina da muyi an gama acan zamu zauna kawai sai a samo mai kulada su idan khamriyyah ta tafi makaranta,tunda acan zatayi karatun.
Jin haka yasa inno tace zata zauna dasu wanda hakan yasa mu yin murna,dan dama abinda muke so tace kenan kada ta tafi.
*****______*****______*****
Haka muka cigaba da karatunmu cikin jajircewa saboda cika burinmu na ɗaukar fansa musamman yanda dr bukar yagina asibiti a filin gidanmu yana more rayuwarsa kaman bayyi komai ba.
Bayan khamriyyah tashiga tawagarka ne nikuma nayi amfani na salona najawo soyayyarka gareni saboda aikin yayi mana sauƙi,amma bayan wannan zamana dakai da kuma soyyayata duka gaskiyace a gareka Sadeeq,ina sonka har raina,sanann banida nufin cutarwa a gareka ko kuma ɗan mu dayake cikina,ka yarda dani akan hakan.
Wanann shine abinda zan iya sanar dakai daga cikin rayuwarmu,abinda ban gaya maka ba kuma toh wanann sirrinmu ne.
Sauran masu yi mana aiki kuma duk yawanci mun haɗu dasune a cikin wanda suke gidan saifuddeen, irin yanda ya kama maryam.Dr nawwarah ce kawai muka haɗu da ita a asibitin dr bukar,dama tana neman fansa akansa na mutanen dayake kashewa,cikinsu harda ƙaninta.
Kayi haƙuri da abinda nay imaka,bazan iya fuskantarka yanxu ba har sai ka gane gaskiyata,idan ka fahimceni to ka nemeni mijina,a shirye nake na karbi duk abinda zaka yimin matuƙar ba saki bane.
Ina sonka sosai,daga matarka Sabriyyah (Amrah).
To mutane back to business inda muka tsaya😀😀😀
Taku
_sadi-sakhna_
Ƴar mutan jama'are.
*MABARACIYAH*
_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)
27••28
Lokacin da dec. Sadeeq ya gama karanta littafin rayuwar sabrah shuru yayi ko motsin kirki ya gagara yi,tamkar ba a duniyar ba haka yake jinsa.
Taya ake tunanin kwakwalwarsa zata ɗauki abubuwan daya ke ganin tamkar a cikin film suke gudana,duk tsawon zaman dayayi da matarsa da soyayyar daya nuna mata shida danginsa ashe ita bai ma santa ba kwata kwata,ta aureshine badan allah ba saidan wani kuɗuri nata.
Duk da ta fadamasa soyayyarta ta gaskiyace amma taya zai yarda da wanda yayi mada wanannan karyar,gashi ƙarin abinma cikinsa ne a jikinta.
Sannan soyayyar sa gareta tasa yakasa ganin laifinta a cikin lamarin,duk koda daukar fansane to sunada laifinsu suma.
Anya ma kuwa zai iya cigaba da wanann binciken,yace ya kama wa to,ƴan uwar matarsa,saboda nayi musu laifi sun ɗau fansa,kokuma yakama matartasa wacce take ɗauke da cikinsa ya kaita kotu,wacce yake mutuwar so,inaaaa bazai iyah hakan ba gaskiya.
Inama zai saka kansa yaji daɗi da wannan lamarin mai cikeda hargitsi.
Jefar da littafin yayi idanunsa yana zubar da hawaye,gabaɗaya duniyar da juya masa baya a ƴan wasu daƙiƙu.
Murza gashin kansa yayi tareda zamewa ya kwanta akan gadon,bacci barawo ne ƙadai yasamu damar sanɗawa kusada shi ya ɗaukeshi.
Saboda yasamu yasamu salamar tunanin da sukayi masa kwanya a cikin kansa,wanda kashi mafi tsoka na tunanin duk na sabriyyah ne.
****_____*****_____*****
Khairiyyah ce a zaune inno sai faɗa takeyi,ta inda take shiga ba tanan take fitaba,dan dawowarta kenan daga garinsu bayan wata biyu da tafiyarta.
Daren jiya ta dawo nan taji labarin wai ƴan bincike sun kama khariyyan a wajen didi,wacce take kulada su fadeelah.
"Kai ɗiyannan kun iyah jawo magana,kuba maza ba ba komai ba kusaka burin daukar fansa a kanku,kowa yasan abinda akayi muku da ciwo,amma inaku ina faɗa da gwamnati,idan an kasheku akwai tsiyarsu ne a ciki,"
Daga ido tayi ta kalli sabriyyah wacce tashigo tana sunne kai,da alama itama tasan zata kwashi rabonta.
"Ke kuma me kike a gida da tsakar rana haka,ina sadiqun?"
"Hmmm dama inno ya gano cewar ni ƴar uwar khariyyahce lokacin daya kamata a wajen aikinsu,shiyasa na taho saboda karyaje ya sameni a gidan"
"Tabb me na fadamuku tunda farko,amma kuka ɗauki aure a wasa kuka kitsa komai,idan na nuna bana so ma sai anyi a bayan idona,yanxu toh kike nufi,ya sakeki ko kuma kin taho shikenan ki zauna da aure a kanki,yanzu ya kuke tunanin zuciyarsa zatayi kenan,ita waccer ta yaudareshi suna aiki tare,ke kuma matarsa ya gano bakinku ɗayah,kya taho ai saiki zauna kiji mai zaice koh?"
"Inno kiyi haƙiri banaso ya sakeni ne idan yaje gidan,ina sonsa sosai"
"So? Mai so bazatayi abinda kukayi ba sam,yanzu tunda anyi haka sai ku sake yin wani abun kuma,gaki da ciki,mezaku faɗawa danku toh"
Zugum zugum sukayi inno tayi ta surfah faɗa har tayi ta gaji tukunna ta shige ɗakinta,saida ta bar wajenne tukunna sabrah ta matsa kusan khairiyyah tana kallon fuskarta wacce tayi jaa saboda mari
"Ke khairiyyah ya jikinki"
"Kai sabrah sai kace wata khariyyan da,babu komai zai sabe,amma kaman yanda inno ta faɗa yakamata mu daina fansar nan haka,duk wanda yayi ma yake shida allah yanzu"
Warwara ido sabrah tayi tareda cewa
"Wlh dan sun ƙarene,da badan haka ba suma sai sunji a jikinsu tsabb,tunda babu wanda yayi saura a cikinsu bai ƙarbi hukunci ba shiyasa aiki ya ƙare,Sadeeq kuma karki damu zamu sasanta,duk inajin tsoro sosai,amma bakomai na bar masa littafin tarihina a ɗakinmu zai san komai da ake ciki,daga nan sai ya yanke hukuncin tsakaninmu dashi"
Tashi sabrah tayi ta nufi ɗakin khairiyyah da ƴar jakarta ta kayah.
Ita kuma khairah ta bita da kallo tareda jijjiga kai.
Deen ne yashigo gidan hannunsa riƙeda nasu fadeelah ya ɗaukosu a makaranta,kallon juna sukayi shida khariyyah ya kashe mata ido.
Ganin hakan yasa tayi masa hararar wasa tareda shigewa ɗakin da sabrah tashiga.
Ƙwalla mata magana yayi daidai tana shigewa ɗakin.
"Masoyiya ya zanyi da yaran kuma kika tafi"
"Kasan yanda zakayi dasu,dan rainin hankali ai kasan nafi ƙarfinka"
"So baruwansa da yaro khari tah,ko kinfini ma zan iya sonki bare koda watannine ai nafiki"
Juyi tayi masa tareda shigewa ɗakin tana murmushi,shima ƴar dariyah yayi tareda fita waje can baya inda nasa part ɗin yake.
Duk abinda suke akan idon fadeelah wacce ta cuno baki tana naɗewa a kwanyar kanta
Hanyar dakin inno sukayi,tunda sunsan ta dawo kuma antynsu bata nan sai wajen inno.
Da daddare su khairi ne da fareedah sukayi abincin dare,didi itakuma ta huta,dan itama dayake dun saba da wanda ba iyayensu ba sai sukejinta tamkar su maman yara.
Shirya abincin sukayi amma inno bata fitoba tana ɗaki,da alama tayi fushi kenan.
Sabrah ce itada khairi suka shigs ɗakin innon,dan baƙaramin damunsu fushinnata yayi ba.
A zaune take akan sallaya tayi gama sallahr magriba,tsugunnawa sukayi a gabanta har ta gama addu'ar.
Sabrah ce tafara magana kanta yana sukunye
"Inno kiyi haƙuri,wlh bazamu sakeba daga yau,zamuyi yanda kikace,amma don allah kidaina wanann fushin"
"Ni ba fushi nake dakuba,fushi nake da taurin kanku,amma tunda kunce bazaku ƙara ba na yarda wanann karon,ke ki shirya da mijinki kuyi zamanku lafiyah,kada ki ƙara tashin tashina ko kuma cutarsa,ki riƙe maraicinki da kuma tarbiyyar dana baki,harkema ki bawa ɗanki.
Ke kuma autah,nasan kuna soyayya da deeni dan dazu ma fadeelah ta faɗamin mai kukace ɗazu,idan kema kinasonsa yakamata kuyi auren,zamannan ya isa haka,kun girma yanzu.
Ita kuma wancar munyi wayah da itah tacemin ƙarin karatu ta tafi na wata shida,allah ya dawo da ita lafiyah,da alama kam aikinku ya ƙare tunda bata nan,nasan dama itace shugabar komai.
Yanzu abinda yafi damuna shine shari'ah,kunsan bazaku kashe manyan gari ku tafi a banza ba koh?"
"Hmmm inna karki damu da wannan,tunda kin huce shikenan,muje muci abinci kar yayi sanyi"
Tashi tayi daga kan sallayar suka fita zuwa cin abincin.
Khamriyyah kam tunda asirinta ya tonu tsakaninta da deen da daina cewa komai,sai hararar fadeelah take tana cewa munafuka kawai.
_____________________
Dec. Saddeq ne a zaune a falon hajiyah Indo ( mahaifiyarsa kenan)
Mata mai kawaici kana da tsoron allah..
Tunda dazu yasaka kwanon cin abincin a gabansa amma ya gagara yin loma ko guda ɗayah,kwana uku kenan dayin abin aamma har yanzu bai koma normal.
Zabura yayi jin muryar ammin a kansa tana magana,bai luraba ashe tayi kusan minti talatin akan sa.
"Sadeeq mai yake damunka ne kwanann,sannan ina ita amratun kace min tayi tafiyah yau kwana uku,anya kuwa ba faɗa kayi kaƙi faɗamin "
"Bamuyi fadaba ammi,kawai.....kawai dai uhm ta tafi gidane"
"Zancen banza,haka kawai zata tafi gida,saikace a wani gari take,ka faɗamin mai yafaru a tsakaninku,nasan fah zuciyarka,karka cutar da ƴar mutane ban sani ba "
"Allah ammi babu abinda ya faru,zata dawo kwanannan,ba wani abin dakuwa bane,au na manta ban fadamiki ba,khaleel gobe zai dawo daga china,yace ki shirya masa abincin daya fiso"
Dec. Sadeeq ya faɗa yana kawar da zancen sabrah da ammi takeyi.
Aikuwa yayi nasara,dan tanajin dawowar ɗannata hankalinta ya koma kai,na mai zata yi masa dazai faranta masa rai.
Kowa ya kalli idon ammi yasan tanaji dashi kodaga magana ma,jijjiga kai dec. Sadeeq yayi yana murmushi,danshi kansa yayi kewar abokinnasa sannan kuma dan uwansa guda sosai.
Fakar idon ammi dec. Sadeeq yayi ya shige ɗaki,dan dama neman yanda zai ajiye abincin yake,kan gadon sa na gidan ya faɗa ya kwanta tareda riƙe cikinsa wanda yake barazanar fashewa.
"Amrah why,you i love you more than you can imagine,meyasa zakiyimin haka,meyasa zaki barni ni kaɗai,bayan kinsan bansaba rashinki a kusada dani ba,bazan kamaki ba dan allah kidawo gareni,zanyi komai domin nunawa duniyah keba mai laifi bace mai ɗaukar fansa ce,ki taimakeni ki dawo gareni mu raini ɗanmu tare,rashinki zai iyah yimin illah amrah "
Zuwa lokacin zuciyarsa ta karye matuƙa,wanda hakan yasa shi dole yasaki kukan kewar matar tasa har bacci ya ɗauke shi.
Itama sabrah a bangarenta hakan ce take faruwa,zata nunawa su khairiyyah ko nace sauran gidan babu komai,amma da daddare har kukan tsoron rasa mijinnata takeyi.
Koyaushe khairiyyah ce ke rarrashinta akan zai dawo gareta,amma kwana uku har ta sare da zuwannsa.
"Please sabrah ki daina kukannan dan allah,dare hutun bawa amma ke yazama na kuka a wajenki,ki kwantar da hankalinki na tabbata shima yana kewarki kaman yanda kikeyin tasa,komai zaizo da sauƙi inshaallah."
"Nikam khairi gobe zanje wajensa na bashi haƙuri,nace masa ya yafemin na koma ɗakina"
"Kai sabrah,anya kuwa so bai kwashemiki hankaliba,yanzu fah kukayi waya da khamriyyah tace miki ki ɗan dakata,shine zakije ki ruguza komai,ta faɗamiki zata san yadda za'ayi,inta kama zuwane zataje akan gyara tsakaninku,idan kika dulmiya komai wlh kinsan halinta banza zatayi dake kiyita kukan rashin mijinnaki,muda bamu dashi ma ai mun haƙura muna zaune"
"Ke khairi dan ina faɗamiki shine kika tsigeni kaman kin samu kaza,ya isheki to haka,tun farko kinsan daɗin mijinne dazaki san zafin rashinsa"
Tana gama faɗar hakan ta juya ta kwanta,ta bar khairiyyah a zaune da baki buɗe,mai kuka tabar kukan ta mayar martanin faɗa,ashe dama na tsiya ne.
Tun safe ammi take ta jirjirgan taryar ɗannata wanda take ji dashi sosai.
Meenah sai cunbuna baki take ammi ta hanata zuwa makaranta,a dole sai ta tsayah tayata aikin abincin ranar,gashi suna shirin zana jarabawar fita.
"Ke meenah yi sauri ki ɗauko min shinkafar nan dana jiƙa ki markaɗa ta,a fara ɗana masar"
"Kai ammi yanzu harda wata masa za'ayi,mutumin da rabonsa da ƙasarnan tun muna ƴan ƙanana,ni ban ma sanshi ba ko a hoto,haka alaƙarmu dashi babu wanda ya faɗamana"
"Ke meenah inabaki kiyayeni ba saina karya kashinki,dahaka zaki tarbi yayannaki karon farko a rayuwarki,sanann yanayin aikinsa ne haka shiyasa bai faye zuwaba"
Tafiya tayi zuwa makarden,badan tana so ba sai dan anyimata dole.
Wajen misalin ƙarfe shabiyu baƙar mota ta faka a ƙofar gidan su dec. Sadeeq ɗin,kana ganin motar kaga new mordern wacce ake ji da itah.
Buɗe ƙofar yayi da sauri tareda bayyanowa daga cikin motar,lallausan murmushi yasakewa ammi wacce take bakin baranda tana jiran ƙarisowarsa.
Hannu ta buɗe masa ya taho da gudu tareda shigewa jikinta yana ƙanƙameta .
"I really miss you my beloved mother,nayi murna da ganinki farincikina"
"Nima nayi kewarka ɗan ɗana,ya ƙasar wasu da zaman haƙuri da aka yi,dafatan an samu abinda akaje nema"
"Inshaalllah ammi,ina bro nah ban ganshi ba"
Ya faɗa yana waigawa hagun da dama.
Sakin baki meenah tayi tana ƙaremasa kallo,yayinda kirjinta yake bugawa fat fat saboda tsagwaron kyau da kuma kwarjini datayi arba dashi a jikin wanann bawan allah.
Shin wanann balarabene ko kuwa baturene mai kyau,dan bayyi mata kama da ƴan nigeria sosai ba sam.
Manyan idanunsa ne suka sauƙa akanta wanda sai a lokacin ya kulada itah.
Murmushi ya sake mata daya sakara ƙara narkewa cikin begennasa.
"Little ɗin ammi kece kika girma haka,ya makaranta,banga big anty ba,shine kotazo taryata koh"
"Uhm. Uhm. Yah khaleel ina wuni ya hanya"
"Lafiyah kalau,barina je ɗaki na huta zan kawomiki tsarabarki,kayan kam inaga sunyi miki yawa,dan kinfi yanda nake hasashenki sosai"
Itadai meenah rasa bakin magana tayi kwata kwata ta faɗa cikin kogon tunanin da ita kanta bata san na menene ba.
Duk abinda suke ammi tana kallo,babu abinda tayi sai murmushin manya kawai.
Duk yanda dec. Sadeeq ke ƙoƙarin boye damuwarsa na rashin sabrah a gaban ƴan uwan saida khaleel ya fahimceshi.
Suna gama cin abincin kuwa yajashi lambu tareda nuna masa da yatsa alamar menene yake faruwa.
Jijjiga kai shima Sadeeq ɗin yayi alamar ba komai.
"Karka cemin haka ɗan uwa,ka faɗamin abinda yake faruwa,shin kun kama wanann matanne,sanann kuma miye yasakaka a damuwa haka"
"Bamu kamasu ba yanzu ma sun subuce,saidai wannan karon ba guduwa tayi ba,nine narasa ƙwarin gwiwar killaceta khaleel"
"Kamanya kenan ban fahimta ba"
"Da kabar zancennan khaleel,bai kamata daga dawowarka ka saka wannnan acikin abubuwan rayuwarka ba"
"Hmmm yaushe ka fara tunanin abinda ya shafeka bai shafeni ba sadeeq,tukunnama ina Amrah ban gantaba?"
"Abubuwa dayawa sun faru a kwana uku kacal bayan wayar da mukayi.
Abubuwan sun karyar min da gwiwa,sun sakani ruɗani kana da shiga cikin wasi wasi.
Kaman yanda ka faɗa yakamata nasamu wani na faɗamasa kuma ba kowa bane kaine,yanxu kuwa zakaji.
Khaleel matata ......wacce na yarda da itah,na amince mata na bata ragamar farincikina,itama tana ɗaya daga cikin su"
"Mai kake faɗa sadeeq ban fahimta ba"
"Bazaka fahimta ba kaman yanda na kasa fahimta,amma yanxu zakaji mai yake faruwa kuwa"
Cikin ƙanƙanin lokaci dec. Sadeeq yafaɗawa khaleel halin da ake ciki na kama khairiyyah harma da gano kamarsu da Sabriyyah da kuma tarihin rayuwarsu kaff.
Shuru khaleel yayi yana