MABARACIYAH Daga Bara Zuwa Firgitar Masu Iko by Auwal sadiya

Author :  Auwal sadiya Category :  Free Novels Online (Read & Download)

Chapter   30 / 33

87K to 90K   out of 96.8K words

zargi,dan lokacin ku tun bayan minti biyar yayi"
"Am sorry DOP,wani abune ya tsayar damu,amma yanzu zamu iya tafiyah inshaallah"
Fitowa akayi dasu khamriyyha daga cikin police station ɗin,kana ganinsu kasan babu abinda ya samesu.
Mutane da ƴan jarida sai bi suke,yau sunga wadanda suka kaɗa hantar gwamnati da manyan gari a shekarun baya.
Tun kafin su isa kotu tayi maƙil da mutane,ana shiga ba bata lokaci lauyoyi suka fara gabatar da kansu.
Iyayen Saifuddeen sun dau nasu lauyoyin,hakama iyalan dr. Bukar da kuma barr. Shehu.
Kowa idonsa cike da muradin mai za'a yiwa waɗannan yara yakeyi..
Sukuwa su khairiyyah musamman khamriyyah,kallonsu take babu alamar firgita,dan dama tasan ranar zatazo,musamman daya zamo a kotun aka yankewa musu hukuncin sun yi kazafi ga Dr. Bukar,sannan kuma aka kasa samarwa mahaifinta hakiƙinsa lokacin da kawunta yazo wajen su..
Wani tafarfasa kirjinta ya fara,kana ganinta zaka hango tsagwaron bakin ciki a cikinsa.
Duk ta ɗau fansa ta huce,amma kuma har yanzu zafin ranta bai gama washewa ba,dubawa tayi a cikin ranta amma bata gano mai tayi missing ba daga cikin abinda ta aikata.
Ta gano mai tayi missing tabbas ta gano.
Maganar alƙalince takatse mata tunani inda taji yana jawo labaran ƙarya daya saba a koda yaushe,hmmm su khaleel basu san komai ba,amma tana ganinsa ta tabbatar a siyeshi kaman ko yaushe..
Tabbas su khaleel sunada harkar tsaro a hannunsu,amma kuma basu da harkar shari'ah a hannunsu.
Tasan burin khaleel shine a wanke ta a matsayin khamriyyah,daga baya kuma idan tazo a matsayin mabaraciyah saita yadda a yanke mata hukunci,shikuma sai ya fitar da ita ya ƙona fuskar datake sawa a matsayin mabaraciyah.
Kenan deejah zata rayu a matsayin azzalumar datayi laifi ta gudu.
Inaaaa batayi aikinnan dan tayi irin wannann sunan ba mai sunan matsoraciyah.
Tayi wannan aikinne dan ta ɗaga martabarta,da kuma irin wanda akayiwa mutane kamar ta.
Zuwa lokacin idonta yayi jawur saboda muryoyin da suke safara a cikin kunnenta,kuma dukkansu zugata suke ba bata hakuri ba.
"Kayi haƙuri khaleel da alkawarin danayi maka,bazan iya ture sunan deejah ta irin wanan hanyar ba.
Idan nayi haka ban cika burina ba,ban nuna musu kuskurensu ba.
Wannan shine abinda nayi missing wanda yake cin zuciyata,idan har kuma nabari tsoro yahanani ɗaukaka sunan mabaraciyah a zukatan mutane,to zan rayu cikin danasani da takaici.
Dan haka bazan taba bari hakan ta faruba.
Bude idanunta tayi akan alƙalin dayake shari'ar tareda cewa.
"Objection mu lord,babu wani ɗaga ƙara daza'ayi.
Ayita ta ƙare anan wajen kowa ya huta.
Zan faɗamaka duk abinda kake buƙatar ji,kafin sannan kasaki wannan na bayana ka wanke su na laifinsu.
Saboda babu abinda suka aikata,dukkansu umarni na suke bi"
Kallon ta kowa yake da mamaki,shima alƙalin dubanta yayi tareda cewa.
"Amma kuma wannan mutane guda uku na gefenki su yaran mabaraciyane kina nufin harda su"
"Ƙwarai kuwa kana shakka ne,to bari kaji abinda baka sani ba.
Khamriyyah itace mabaraciyah sannan kuma mabaraciyah itace khamriyyah.
Ba kaiba har kowa dayake wajennan ya tsaya yaji labarina,da kuma dalilina nayin abinda nayi"

Kallon idon khaleel tayi,tana ganin tsantsar gargaɗin kada tayi,amma kuma inaaa ba maida hannun agogon baya,dole tayi yanda ya dace.

See you next in deejah's history.........



Taku
_sadi-sakhna_
Ƴar mutan jama'are.








*MABARACIYAH*


_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)






59••60










Kowa dayake cikin kotun saida ya girgiza dajin abinda ta fada.
Hatta su sabriyyah saida abin yabasu mamaki,inaga kuma sauran mutane.
Ganin yanda fuskar kowa tacika da zullumine yasata fitowa daga akwatin dasuke tareda sauran..
Gaban alƙali tazo ta tsayah tareda kallon al'ummar mutanen wajen.
Da ɗaɗɗai take ganin tsana da kuma tsangwamar da mutane sukeyi mata.
Alƙalan da wanda suke ƙara ne suka tashi tareda cewa.
"Yah shugaba mai adalci,wacce ake ƙara ta bayyana cewar ita ke aikata wannan abubuwan,bama ga iya ɗaya ba,gabaɗaya mata biyun ta bayyana cewar itace,kuma ga shaida nan na hoton fuskar wacce ake ƙirada mabaraciyah a hannunta.
Yakamata Alƙali ya gaggauta yanke mata hukuncin mai girma,ta yanda zai zama izina ga sauran masu muradin aikata laifi irinna ta"
Ihu ne ya kaure mutane suna cewa Eh hakane a kasheta.
Shuru alƙali yayi yana rubuce rubuce,wanda hakan yasa lauyoyin da sarki ya ɗauka suka tashi domin cewa wani abu.
Hannu khamriyyah ta nuna musu na su zauna tareda cewa.
"Karku saka kanku akan abinda bakuda masaniyarsa,duk da nasan kunyi ƴa dani sannan kuma kunsan aikinku,amma ina mai baku haƙuri kan cewar ku hutasar da kanku akan wannan lamarin.
Da inada damar barin nahiyar ma zan bari na tafi,amma kuma inaso mutane su san dalilina nayi abinda nayi,dan haka bana buƙatar wani ya matsi bakina kokuma ya tari numfashi na.
Kowa a yau ya saurari labarina da kuma abinda mutanen suka min,ban kashe kowa ko na lahanta kowa ba sai su"
Sauƙe idonta tayi akan iyalan su dr. Bukar da brr. Shehu,saikuma na DOCTOR ALAWIYYAH(wacce takashe ta rubuta mata sunan ta a duk jikinta da karfen wuta)
Sannan kuma da hajiyah fulani da saifuddeen,wanda suke zaune akan keken marasa lafiyah sun tsiramata ido.
Suda Allah ya ƙaddara basu shiga list ɗin mutuwar ba.


_____________________________


_GARIN KANKIA wasu shekaru masu yawa baya_

Sunana Khadija Abdullahi kankia,nikaɗai ce a ƴa mace a wajen innata.
Mahaifina malam Audu yanada mata guda biyu.
Magajiyah,wacce muke ƙiranta da iyah Gaji,saikuma mahaifiyata wacce HAUWA muna ƙiranta da Innan deejah.
Iyah gaji auren Saurayi aka yimusu itada mahaifina,ƴayanta guda biyu ne. Daga harira sai Murjah,kuma dukkansu anyi aurensu kafin a haifeni.
Innata kuma ƴayanta guda biyarne,yayuna maza uku,Hamza,Yusuf da Yahuza,saikuma ɗan autanmu umar,wanda da shekara ɗaya na fishi saboda yanayin rashin tsarin iyali.
Kuma daga kan wannan inna bata sake haihuwa ba,saboda wani matsanancin ciwo ta gamu dashi lokacin haihuwar umar,anyi anyi takasa haihuwa da kanta,dole sai asibiti aka kaita.
Nan ma daƙyar aka fitar dashi daga cikinta. Tundaga wannan lokacin ta gamu da ciwo a mararta,kasancewar babu kuɗi sannan babu wayewa,haka ciwon yacigaba da cinta har mukayi wayo,idan ya tashi saidai mu karbo mata jiƙo a wajen malam musa.
A haka tacigaba da rayuwa cikin wannan halin har mukayi wayo muka gane mai yake faruwa a gidannamu.
Iyah gaji irin mutanenne da babi ɗigon tsoron Allah a ransu,basayin komai sai abinda malamin dubansu ya faɗamusu,dan da wayonmu munsan iyah gaji bata Sallah.
Ga baƙar mugunta da take yiwa innarmu itada ƴaƴanta su Harira.
Babu dama mahafinmu yayi magana,inaga kuma innah,dole haka kowa yake nuna kaman babu komai,bayan kowa yasan yana faruwar.
Ina kowa yana jurewa nikam saina fara maida martani,iyah gaji bata isa tayimin na ƙyaleta ba,duk ranar da nayi mata rashin kunya ranar bazata bani abinci ba,dan dama inna jijyarta yanata iya yin komai,kullum tana ɗaki tana fama da ciwo.. Gashi ta saka Malam yamin dukan tsiyah,dan zugashi take ta kalallama zance,wanda nikaina ban sanshi ba.
A lokacin danake karama babu wacce malam yafiso fiyeda ni,amma yauda gobe ta wuce wasa,saida yazamo babu wacce ya tsana kamanni.
Gashi yanzu dagani sai umar a gidan,ankai su yaha yahuza Almajiranci.
Duk wani aikin wuyah saiyah dawo kan umar,lokacin ma shekararsa bakwai nikuma takwas,wani abin idan tasaka mu saboda ƙankantar shekaru bazamu iyaba,amma babu uzuri sai duka.
Wata rana ina wanke wanke,umar yashigo gidan sai tangal tangal yakeda robar ɗiban ruwa,yajiƙe jikinsa jarab da ruwa,ga uban sanyi da ake a garin.
Dukkanmu sanyi ya hudamu dagani har shi,dan wani lokacin ko muryarsa bata fita saboda mura.
Magana yake cikin shaƙyƙyƙyiyar muryarsa.
"Iyahh gaji na debo ruwan a sauƙemin"
Magana yaketayi amma tana jinsa bata fito ta kalleshi ba.
Ganin hakanne yasa na nufeshi tareda karba robar ruwan.
Iyayine irinnawa,amma nasan baxan iya sauke masa ba,wahalar dayake shane zuciyata bazata iyah juraba.
Dagani harshi ruwan kwaremana yayi a jikinmu,kaman anyi mana wanka a garin saukewar.
Masifah iya gaji ta fara kaman an aikota,amma haka nayi biris da ita nazashi cikin ɗakinmu wajen innah,wacce take kwance tanajin abinda yake faruwa,ko a lokacin baya ma batada abin cewa bare yanxu.
Cire kayan jikina nayi nasaka wani bushashshe,yayinda shima umar ba cillah masa marar jiƙa ya saka.
Muryar iyah gaji na jiyo tana cewa.
"Shegiyar yarinyah,to wlh bari kiji,idan kika kuskura kika sanja kayan jikinki sai na miki lahani a gidannan,kuma ruwane kin jawo masa,saiya ɗebo sau ashirin yau"
Dataji hakan bai isheta ba ɗakin ta nufah da sauri tareda foncikoni nida umar,shikam sai ihu yake,amma idona ni a bushe yake kaff da tsanar matar ubannawa.
Tari innah tayi ganin ta dage sai ta fitar damu a cikin ɗakin.
"Yaya gaji ki ɗan bari rana ta fito mana kafin su cigaba da aikin,naga garin da sanyi sosai"
"Ihuuuu ina kake malam maza fito gaji mai akemin anan wajen.
Wai nice kulu takemin gorin dan ban haifi namiji ba bazan aiki ɗantaba,zo kaji malam,to wlh koni ko ita saika zaba,dama ba uwar komai take ba a gidan banda ci dakuma kashi"
Masifa take kan gari ya gari da sanyin safiyar,fitowa yayi jin abin yayi yawa yazo bakin ɗakin.
"Menene gaji da safiyannan kuma?"
"Oh bakaji mai nace ba,to wlh sai tabar gidannan,tunda ina kulada ita bata ganiba,saika yanke hukunci yanzu,ko kuma abinda yaxo bazai maka kyau ba"
Duk abinda suke ido kawai muka zuba musu,har yagama lallashin iyah gaji suka fita daga ɗakin.
Tundaga wannan kaman an zuga iyah gaji wajen gana mana azaba,kowace rana da abinda zatayi mana.
Shiryen shiryen tafiya sarin kayah malam ya fara zuwa kano,dan dama aikinsa kenan koyaushe,idan yaje kuma yakan ɗauki watanni bai koma ba,ina murna da neman kuɗi zaije,saidai kuma ina bakinciki da zai tafi ya barmu da uƙubarmu.
Bye mukayi masa nida umar bayan mun rakashi har bakin tasha,umar sai kuka yake akan yatafi dashi.
Tsugunnawa yayi daidai tsayinmu tareda yin murmushin takaici.
"Hmmm nafi kowa jin zafin rayuwar dakuke ƴayana,saidai babu yanda zanyi kuyimin uzuri,a duk lokacin dana yanke zan gyara komai,ina shigowa sai kasa yin komai,mahaifiyarku ina sonta sosai,ina tausayawa rayuwarta sosai,saidai bazan iyah ɗaukar mataki ba.
Da nayi tunanin na sawwake mata aurena,saidai kuma hakan ma ba shawara bace,domin batada kowa iyayenta duk sun rasu,ƴan uwa kuwa a wannan lokacin sai addu'a kawai.
Kece kaɗai mace,kuma mai ƙaramin shekaru akan yayunki,amma kuma Allah yabaki zuciyar jurewa da kuma taimako,ki kulada ƙaninki da mahaifiyarki kafin na dawo kinji uwata"
Muryarsa tana rawa ya ƙarisa maganar tareda zuyawa dan kada naga hawayen daya zubo masa.
Tausayin iyayennawa ne ya kamani,gashi banida abinda zan iya akai.
"Malam zanyi iya ƙoƙarina,amma ka dawo da wuri kafin ta kashemu kaji malam"
Saurin shigewa mota yayi bayan ya jefo mana jaka biyu (400).
Muna kallon motar har ta ƙule kafin muka dawo gida,kowanne yaro murna yake idan ya doso gidansu,amma mu fargaba ce take ziyartar zuciyoyinmu a duk lokacin da muka doso gidan.
A hankali muka raba zuwa ɗakinmu saboda kar iyah gaji da ganmu.
Allah ya bamu sa'a kuwa har muka shiga batagani ba,dan tana ganin kuɗin zata ƙwace da dakemu.
Bayan an gama abinci munata jira tace ga namu sai mukaji shuru,har wajen la'asar bata bamuba,umar kam tun dazu yayi kukansa ya ƙoshi yayi shuru.
Nima dauriyah kawai nake,amma cikina yanaji a jikinsa,ga inna ma batada lafiyah,dole zata buƙaci abinci.
Kallonsu nayi dukka biyun wanda babana yace na kulada su,tun ba'a je ko inaba har nakasa kulada dasu ɗin.
Tashi nayi da sauri na nufi ɗakin iyah gaji tareda zubewa a gabanta ina kuka.
"Iyah gaji dan Allah ki bamu abinci,kar inna da umar su mutu"
"Toh mutu mana ina ruwa na,in kina tunanin hakan da kikayi zaisa na baku abinci to ki sanja tunanin yar yarinya,babu ku babu abincin gidannan har abada,in zaki iya ki ciyardasu,ba ana zugaki ke mai zuciya ba,da yarintarki,to zuciyar ta basu abinci"
Bansake cewa komai ba nafito daga ɗakin iya gajin,dan nasan komai zana sake cewa bazata sanja hukuncinta ba.
Kayan jikina na kalla,dama duƙu duƙu suke da datti,kama skirt ɗin nayi na yaga shi,hakama rigar na yage hannunta.
Zancen karshe dai na koma tamkar MABARACIYAH.
kwano na ɗauka a tsakar gidan na nufi bakin tashar garinmmu,inda masu bara suke zama harma da almajirai dayawa.
Tafiya nake hawaye yana bin kuncina,ko gabana bana gani sosai.
Zama nayi ina bin bakin abin almajiran suke faɗa a gaban Manyan dasuke zaunen.
Bani nasamu wani yabani guntun abinci ba har sai wajen la'asar,amma kuma nayi sa'a,domin dayawa ya bani.
Gida na nufo da sauri murna fal cikina,koba komai nayi nasara.
Ɗakinnamu ba shige tareda ajiye kwanon a gaban umar,barin kukan yayi tareda saka hannunsa a cikin jallof ɗin wacce tasha manja sosai.
Kallon alamar tambaya inna tayi min,wanda hakan yasa na faɗamata abinda yake faruwa.
"Innalillah,duniya ina zaki damu,kunyar kallonku nake deejah,nakasa kulada ƴayan dana haifa har sai sunyi bara"
"Karki ce haka inna,babu abinda zaisa ki barmu a cikin wannan halin inba uzurin jinya ba,ki daina fadin haka"
Turamata abincin nayi gabanta muka fara ci,duk da bamu ƙoshiba amma kuma mun kashe yunwarmu sosai,ganin yanzu umar ya daina kuka,inna ma ta daina riƙe cikin yunwa,yasani ƙara samun ƙwarin gwiwar komawa wata barar gobe.
Zanci gaba da zuwa har lokacin dazan iyah yin aikin ƙarfi sannan sai na daina.
Ga mamakina iyah gaji zata hanani zuwa bara,amma kuma sainaga bata hanani ba,abinma dadi yamata sosai,ace ƴar kishiyarta tana bara,mai yafi haka yimata daɗi.
Wasa wasa har nafara sabawa da almajiran da muke bara dasu,don kullum tare muke,har nafara iyah sana'arsu da shoe shiner,wani lokacin kuma har tsangayarsu nake zuwa muna karatu tare.
Shikansa malamin har ya sanni,domin nima allo ya bani yake doramin karatu da kansa.
Yanda babban ɗan sa malam shazali,shine mai biya mana karatun.
Ganin na fara koyane yasa na fara zuwa da umar ma,saboda shima yayi karatu,idan mungama kuma kowa ya ɗai robarsa ya fita nema.
Nima sai bi cikinsu mu tafi.
Duk inda na wuce zakaji ana cewa ga mabaraciyah a cikin Almajirai ga mabaraciyahh.
Tun inajin kunyar sunan har yazamo ina amsawa da dariyah,sanadin haka ma wasu ke bani sadaka ko basuyi niyyaba..
Malam shazaline yanuna min cewar nadaina binsu bara,amma naƙijin sa,saboda ni baxan iyah fitowa na fada masa mai yake faruwa a gidanmu ba,sannna kuma bazan iya dainawa ba.
Ciwon innarmu ne yafara tsanani sosai,wanda hakan yasa naje gida wajen kawunmu wato ƙaninta wanda suke uba ɗaya na faɗamasa..
Da farko banza yayi dani,saida nayi ta magiya tareda zubewa ƙasa kafin ya jini.
Yana zagina yana aibatani haka yabiyoni muka dawo gidan,yazanyi dole na jure ko mai zaice,abin takaicin bansan garinda su yahuza suke ba,inna sani ma da nisa sosai,dannaji ance a ƙauyen Bauchi suke.
Baro irinna masu ruwa aka samo muka sakata a cikin zuwa asibiti,lokacin magriba ta kusa.
Inna laraba ma maƙwanciyarmu ta taimaka mana sosai,dan ɗanta ne ma ya tura mana baron.
Lokacin da mukaje asibitin da suka gwadata cewa sukayi abin ya fi ƙarfinsu,domin Cancer mahaiface taci ƙarfinta sosai.
Tun sanda ta haihu yakamata ayi mata magani,amma kuma ba'ayi ba,abin yanzu bazayyiyu ba.
Ya mutum zaiji ace masa iyayensa ciwo yaci ƙarfinsu bazasu warke ba,saidai ya tsaya yayi kallon mituwarsu,haka naji a cikin ƙoƙon rai na.
Da farko sun barmu mun zauna a asibitin suna mata allurar kashe zafi,koba komai zata koma ga Allah bata sha wahala sosai ba..
Amma daga baya sai suka ce dole sai mun kawo kuɗin daza'a dunga siyan magani.
Matsawa nayi wajen kawunnawa wanda zuwansa kenan dubamu.
"Kawu ka faɗawa su yaya yahuza dasu yusuf su dawo gida,a siyar da gonar inna a kaita katsinan da sukace muje"
"Hhh yarinya kenan,bakida labarin gonar innar taku harda ita gwamnati ta karba a garinnan,duk wanda kuka je siyarwa babu wanda zai siya,saboda suna ƙarƙashin gonakin da brrr. Shehu Babban chair man ya ƙarba"
"Amma meyasa ya ƙwace wa inna ginarta toh"
"Ance sun shiga kan hanya za'ayi titi a wajen,ana saka ran zasu bayar da wani kuɗi amma har yanzu babu abinda suka bayar,amma dai tashi muje muyi masa magana a gidansa,ƙila ya taimaka mana"
Tashi nayi tareda sake kallon inna wacce take kwance na bi bayan kawu,dan ma muna sa ran dawowar babana daga sarinsa a satin gaba.
Gidan babu nisa sosai da asibitin dan haka bamu dade ba muka isa.
Ni tsayawa nayi a gefe,suna magana da kawu,saida ya gama tsaramasa kafin yayi murmushi.
"Kai Babannan,gona fah ba iya takuce ta shiga hannu ba,harda ta sauran mutane,an ce kuyi haƙuri kuɗinku zasu fito bada daɗewa ba"
Ƙarisawa nayi gabansa tareda zubewa a ƙasa ina kuka.
"Dan Allah baba ka taimaka,innata tana buƙatar aiki,gashi bamuda abinda zamu siyar,ka ara mana kuɗi inyaso idan suka fito saika ɗauka"
Jefar dani yayi daga jikinsa tareda kaɗe kafarsa.
"Ke wace irin yarinya ce,da wannan dattin kike tabamin farar shadda,nabaki kuɗina saboda nina damu uwar taki ta tashi,ki cemata tayi ta jira idan suka fito ta samu maganin"
Haushine yakama kawu wanda hakan yasa ya cakumi kwalar brr. Shehu.
"Ya isheka haka azzalumin banza,kowa yanada labarin cewa akwai wata manaƙisa dakayi,akan kuɗin mutane"
"Hhhhhh ashe kanada wayo ka gano gaskiyah,kuɗi na cinyesu sun zama nawa,kuma babu abinda za'a iya min,ni lauyane zan kare kaina,bazan bada kuɗi ba,idan ka isa ka ƙwacesu a wajena"
"Haka kace,shikenan kazuba ido ka gani,nikuma zan tsaya tsayin daka na ƙwato musu haƙƙinsu,shari'ah daga nan har katsina a shiga"
"Ka gwada ka gani,basai kakai goben ma bare kayi shari'ar ba"
Ture kawu yayi tareda ƙare mana kallo ya bar wajen.
Bayansa nake kallon yanda yake tafiyah hankalinsa kwance kaman babu abinda yayi.
Kawune ya ɗagani muka koma asibitin,har sannan kuka nake.
Mai zan gani a wannan duniyar da yanzu ma nake fahimtarta.
Lokacin da muka koma likita ne ya aiko kan cewa kawu yaje ana nemansa,komai zaice dashi oho.
Bayan kaman wasu mintuna ya dawo fuskarsa ɗauke da damuwa.
"Deejah sunce zasu koreta a asibiti idan bamu bada wani kuɗi ba,nikuma banida wani kuɗi a yanzu,iya gona tace ɗaya tal danake nomawa iyalina,amma karki damu akwai lambuna na hayin kogi,zan je nabada shi jingina na wannan shekarar,inyaso sai a basu wani kuɗin.
Godiyah nafara yimasa bansan adadinta ba,da nayi zaton bashida mitunci,sai daga baya na gane ashe fadane dashi kawai.
Abinci yasiyomana nida umar,taliyah da manja kafin ya tafi.
Washagari dai jiya i yau,saidai sabanin kowanne lolacin,yau abinda yafaru yafi kowanne girgizani.











Taku
_sadi-sakhna_
Ƴar mutan jama'are.








*MABARACIYAH*


_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)






61••62






Wani irin abu kunne na yake jiyomin a bakin mutane.
Kawuna wai ya rasu,jiya da daddare wasu sun shiga sunyi masa yankan rago,ya mutu muss har lahira.
Gari ya ɗauka da hayaniya,nidai ina zaune a gaban mahaifiyata wadda taketa murkukusun ciwo,na yau kamma yafi na kullum,gashi wanda na kwana da tunanin zaizo ya tallafemu shima wasu sun kasheshi.
Nurse ce ta shigo ɗakin tana duba wata a gefenmu,duk abinda inna takeyi ko juyo kanmu batayi ba.
Karisawa nayi gabanta tareda jan hannunta,amma ban

30 / 33