Author : Auwal sadiya Category : Free Novels Online (Read & Download)
ramgwameba,sai dan idan nadawo aiki,aikina ne,wanann karon alƙawarina da ƙasata na gaskene babu ƙaryah cikinsa"
Daga haka tayi musu sallama tafice daga office ɗin.
Tana fita sadeeq ya zarowa khaleel ido tareda cewa.
"Kasan mai kayi kuwa? Dawo da ita aiki fah kayi,bayan kasan maita aikata,ma kake tunani"
"Hmmm karka damu ɗan uwa,babu abinda zatayi,tariga tasan munsan komai akanta,dan haka bazatayi wani gigin yin komai ba,kuma zata taimaka sosai wajen kama mabaraciyah,saboda ance mugu shiyasan makwancin mugu"
"Eh kuma wannan hakane,Allah ya taimakemu toh"
Washagari kuwa kaman yanda sukayi da dec. Khaleel,ba kunya Khamriyyah ta dawo aikin ta na bincike.
Kusan sati guda ta ɗauka bata ga su dec. Sadeeq,kasancewar tana ta ƙoƙarin gyara abubuwan data tafi ta bari,gashi tasan wani lokacin da gangan Dec. Khaleel yake aikowa a kawomata takaddu,idna taga hakan murmushi kawai takeyi.
Har dare wani lokacin take kaiwa tana aiki a ɗakinta.
Bironta ne yauma da safe tana cike wasu takaddu kafin taje office,ɗakin su khairiyyah tashiga domin dubawa,dan tasan bazasu rasa takardu ba.
Drawer ta farko ta jawo bata ganiba,tasake jawo ta biyu babu,har zata mayar kuma sai taga wata takarda.
Ƴar dariyah tayi tareda buɗewa tana cewa.
"Hmm yanxu haka khairiyyah ce tayi kasuwa,barinaga kalaman soyayyah,tunda mu babu wanda ya taba bamu sai....."
Cak ta tsayah da maganar ganin abinda takardar ta ƙunsa.
Maganganu aka caccakawa sabrah akan rashin fitowa duniya ta faɗi ita wacece.
"Kan buhun ubancan,mai akayi akai madeena,yarinyar nan tasanni kuwa,ba ƴar gidan sarkim katsina ba,inma ƴar sarkin duniyace zata gane shayi ruwane.
Sabrahhhhh khairiiiiiii inakuke kuzo nan?"
Da gudu suka shigo cikin ɗakin dan ganin mai yake faruwa.
Turuss sukayi ganin ta dunƙule hannunta tareda cize baki,jikinta yana vibrating,ta mutsitstsike paper a hannunta.
"Kinsan me khamriyyah bawai......."
"Yaushene ɗaurin auren?"
"Yaune za'a ɗaura auren idan taso daga masallacin juma'a"
"Meyasa toh banga kunje kun nuna kanku a gaban kowa a cikin gidanba,mai kuke a zaune a cikin gida,lokacin daya kamata ace kunacan kuna maida martani.
Da bangani ba shikenan haka wannan cin mutuncin zai tafi a banza.?"
"Am khamriyyah ......"
"Shshshsh karkuce komai,ku saka kayanku mutafi yanxu nan,wlh sai anje,idan kuman bazakuje ba zanje ni kaɗai.
Badan kina kunyar ubaba kika ƙi nuna kanki,batun in kinason mijinki kuma bai tasoba,dole saikin nuna mata ke macece,kuma indai zata shigo gidanki dole tazo a ƙasanki ba a shugabarki ba.
Shiryawa sukayi cikin kaya iri ɗayah dukkansu su ukun,farida tana kallonsu ,taso binsu amma babu dama,saboda kar a gano tana tareda su a cibiyar bincike.
Fatan nasara tayi musu lokacin da suka shiga motar khamriyyan takece raini sai gidan masarautar katsinan.
................see you next.........
Taku
_sadi-sakhna_
Ƴar mutan jama'are.
*MABARACIYAH*
_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)
51••52
Jan motar tayi bayan sun gama shiga sai gidan su madeena.
A lokacin ƙarfe tarane na safe,tundaga bakin kofar mutane maƙil anata shirye shirye,dan madeena itace ƴa tabiyu daza'ayi aurenta a fadar.
A bakin kofa sukayi parcking motar su,dan babu wajen shiga koda sunyi niyyah.
Tafiyah suke a tare,ga kayansu ma masu uban daraja da khamriyyah tazo musu dashi,takalman da gyalen ma iri ɗayah,sai gwalagwalai da suka yi ado dasu,(ayar tambaya,a ina khamriyah ta samo kuɗi haka)kana ganin shigar kasan da gayyah sukayi.
A hankali suke takawa saboda cikin sabrah daya tsufah har yah ɗago riga.
Wata mai aikice zata wuce khamriyyah tayi saurin tareta.
"Ke sashen hajiya Saratu muke nema"
Kallonsu salaha tayi daga sama har ƙasa,dan ita a ranta tayi zaton saƙƙowarsu kenan a jirgi"
Nuna musu wajen tayi,tai gaba abinta da kuloli,wanda hajiya saratu tace a kaiwa su khaleel da suke sashen Yarima jalal.
Bin yatsanta sukayi da kallo zuwa sashen data nuna musun.
Aikuwa khamriyyah ce a gaba ta zasu zuwa wajen..
Shiga sukayi suna rarraba ido,babu wanda suka kula,suma masu binsu da idon basu kulasu ba.
Amal ce ta fito daga ɗakin da madeena take tana ta magana a wayah.
Katsewa tayi tareda kallon su khmariyyah tace.
"Ku ƙawayen anty madeena ne,ku shigo nan tana ciki"
Binta sukayi a bayah,dan dama abinda khamriyyah takeso kenan.
Ƙarewa wanda suka ɗakin sukayi da kallo,wato kawayen madeenan.
Ɗaga ido khamriyyah tayi tareda mintsina baki tace.
"Ina amaryar ne,kaman yanda ta bada takadda kan cewa uwargidan Sadeeq tazo ta bugi ƙirji tace itace matar sa wacce yafiso,tofah dama ance rana bata ƙaryah saidai uwar ɗiyah taji kunya.
Ka sabrah tazo tabbatar miki kan cewar ba kunyar uban kowa takeba wajen fitowa duniyah ta amsa sunan matarsa,kuma rashin cika magana sai ƙaramin mutum,dan haka gata a gabank8 bataji tsoron fitowa ba tazo har gidan naki uban"
Dukkan ƙawayen amaryar harda amaryar ma tsayawa sukayi baki sake suna kallon khamriyyah wacce take zazzga masifah kaman bakinta zai cire.
Tun anayin hayaniyar a ɗaki har manya suka fara zuwa neman ko lafiyah.
Kowa idan yaxo yaji matar sadeeq ce tazo tabbatarwa madeena magana sai ya juya yakai gaba.
Kafin awa ɗayah da zuwannnasu har kaf gidan ya ɗauka da zuwan su khamriyyan.
Har sannan madeena kuwa kanta ya kulle,tarasama bakin maganar mai zatace da lamarin.
Hakiya Daada yayar hajiya saratu ce taƙirasu falon hajiya saratun domin jin mai yake faruwa.
Daidai lokacin shima sadeeq ya shigo falon shida su ahmad,khaleel da kuma saleem.
Sai sauran wasu abokan.
Hakuri aka bawa wasu suka fita,abinka da gidan sarauta dama yayah.
"Ke wannan da kike magana,kince zuwa kikayi tabbatarwa amaryah cewa Sadeeq yafi son Uwargida,menene ma'anar wanann magana,kinfi kowa sanin nan ba gidan ƙananan mutane bane inda kuka saba yin haka nan gidan sarsutane.
In wani abu madeena tayi muku ma bai kamata kuzo har gida wajenta ba,saboda matsayin da ubanta yakeda shi.
Batun matsayi kuma wannan kafin a ɗaura aurene,ana ɗaurawa dole itace zata jagoranci komai,sha'anin jagoranci ai sai wanda ya gada.
Zakuce tazagi ubaku,shin kunada ubanne ƙaryah tayi,duk wajennan kowa shuru yayi,amma babu wanda zaice ga ubanta a garinnan sanda sadeeq ya aureta. Inba shiririta irinta yaroba,shima yanzu gashinnan abin ya dameshi yazo biɗar ƴar asali"
Har khamriyyah ta buɗi baki zatayi magana inno tashigo wajen,da lullubin gyalen babba,kana ganinta kasan sauri tayi kafin ta iso.
"Kiyi haƙuri hajiya kibar wannan tone tonen,abin yarane shiyasa suka tashi hankalinsu,amma hakan bazata sake faruwa ba,batun mahaifi kuma ance kam shine yake ado,amma fah bashine yake numa kimaba,ko ɗan sarki ko talaka,mai uba da marar uba,hakan baya shafar duka gaba ta rayuwarka,ita kanta kima kai kake siyawa kanka,haka kyautatawa da kuma samun soyayyar mutane.
Duk da ƴa ta batada gata irinnaku,haka ɗanku yaji ya gani yace ita yake so,bamu sayeshi da boka ko malam ba Allah ne ya dubi maraicinta yabata zuciyar mijinta,sannan ko kusa bana bakincikin ya auri ƴar uwarsa Fatana shine Allah yabasu zaman lafiya.
Abinda yafaru anan kuma dan Allah a tufeshi,karya shafi auren daza'ayi"
Wata harara hajiya Daada ta zabgawa inno tareda cewa.
"Aikin banza wace kima za'a samu a wajen ƴaƴan gidan marayu,ko talaka bakowane zai auresu ba bare jinin sarauta.
Ƴaƴan shegu na titine fah,wanda matan banza sukeyin cikinsu su zubar,ku kuma akai muku su a baku kuɗi ku rainesu.
Ke kanki nasan bazakiso ɗan ki ya auri wannan kazamar ba ,amma haka kuka laƙanawa ɗanmu domin zalunci,wannan karyar wann............."
Fasss kakejin ƙarar mari inno ta ɗauke mata fuska cikin zuciyah.
"Kada ki kuskura kisake ƙiramin ƴaƴa ƙazamai,saboda ban shayar dasu da haram ba ban ciyarda su da haram ba,da taribiyya da kuma hanyar daidai na rainesu.
Babu ruwana da iyayensu,da kuma abinda sukayi suka haifesu,walau su musulmai ne ko kuma akasin haka,abinda nasani shine tuna ranar 7 ga watan mayu na shekarar 1999 na ɗora idanuwana akansu suna tsumman goyo.
A ranar nayi register su a matsayin ƴaƴana ba riƙon gwamnati ba,sannan da gumina na rainesu bada ƙwandalar gwamnatiba,ba madarar kanti na basu ba,madarar jikina suka sha suka rayu.
Ina musu son kwatankwacin yamda nake yiwa ɗan da na haifa,dan haka karki ƙara ƙazantamin yara a gaban idona,babu uwar dazata juri haka"
Hannun su khamriyyah taja da niyyar fita dasu daga wajen,amma sabrah ta fizge hannunta.
Hanyar inda sadeeq yake tsaye taje ta zuba gwiwoyinta,kana ta kama ƙafafunsa tareda sakin wani zurfaffan kuka mai dulmiyar da zuciyar duk wanda ya saurara cikin duniyar tausayi.
"Duk da cewar haramunne kuma bai daceba mace ta nemi saki a hannun mijinta,saidai babu yanda zanyi ya zamemin dole saina tambaya Sadeeq,ka sawwaƙemin ka auri ƴar uwarka,niba sa'arka bace a rayuwa yanda ta faɗa,ko talaka saina ƙasa ne zai zauna dani,hakan ma zan rayu cikin tsoron ranar dazai min gori.
Ka taimakeni ya fitar dani daga wannan ruɗi daga nan,abinda yake cikina ma kabarmin shi zan raineshi ni kaɗai,ta haka ne zai rayu cikin salama.
Karka damu mun ƙware a rainar wanda bashida mai tallafarsa."
Kuka take rusawa wiwiwi wanda hakan yasa khairiyyah durƙusawa itama a wajen tareda juyota zuwa gareta.
Shikuwa dama sadeeq tunda yazo wajen yaji abinda ake faɗa ya sandare a wajen bai sake motsiba na kirki.
"Rabinah,meyasa kike wannan kukanne haka,kullum yau daban na gobe daban,kisakawa ranki salama kodan lafiyarki,nikam kinsani bazan iya jure rashinki ba koh,ke kaɗaice wacce na haɗa alaƙa da ita a duniyarnan.
"Inji wa ɗin,waye ya faɗamiki haka?"
Dukkansu kallon hajiya saratu sukayi wacce take tsaye idonta yana zubar da ƙwallah tana ganin abinda yake faruwa.
Takawa take a hankali har inda su khairiyyah suke zaune,kama hannayensu tayi na dama tareda dubawa
Abinda take nemane Allah ya nuna mata a tsakiyar hannunsu.
Tawadace iri ɗayah,saidai ta khariyyah a ɗan saman ta sabriyyah.
"Hmmmm dama naji a jikina sune ,zoki gani daaaaadddda,wlh sune sune fahhhh,tun ɗazu nina kulada yanda suke kama da Innar mai martaba,dan dama ita suka iya fitik lokacin da aka haifesu,amma ke baki kulaba sai masifah kike marar amfani"
Hannun su sabrah takama ta matse a kirjin ta sai surutai takeyi,wanda ba'a rabasu dana farinciki.
Ba iya su sabrah ba,kowa ma nawajen kallon mamaki yake mata.
Tashi tayi da sauri ta nufi turakar mai martaba da take sashenta.
da saurinta sai gata ta dawo da hoton Halimatussa'adiyyah,wato mahaifiyar mai martaba,wanda ta ɗauka irin marar kalar nan na da.
Miƙawa mutanen wajen tayi kowa yana gani,wanda suka santa sai a sannan suke tunowa kumafah hakane,saidai ance wanda ya mutu dole sai an matashi.
Banbancinta dasu khairiyyah a hoton ɗayane.
Ta ɗan fisu manyanta,kuma kanaganinta bazaka ga wayewa irintasu ba.
Hajiya saratuce ta ƙara dacewa.
"Kai abdul je kace ana naman mai martaba a cikin gida saboda wani muhimmin Al'amari"
Har sannan babu wanda yasake cewa komai,har itama hajiya saratun,kowa yana jiran yaga shigowar mai martaba a ga yanda zayyi.
Shida fadawa guda biyu suka shigo,yasha sabuwar alkyabba na ɗaurin auren ƴar sa daza'ayi yanxu.
"Hajiya ƙarama lafiyah kika ƙirani,ga kuma mutane a gida haka an taru"
Da hannunta ta nuna masa su sabrah batareda tace komai ba.
Ɗan zare ido yayi tareda sakin baki,
"Daga adamawa suke?,ƴaƴan waye a cikin su baffah modibbo?"
"Ahah ko ɗayah,acikin ƴayan da aka taba haifah a gidannnan waye yayi kama da marigayiya inna?"
"Hmm ke kuma menene na tuna wannan labarin,ƴaƴa biyu Allah ya azurtani dasu masu kaman innata a lokaci guda....."
"Suma wannan ƴan biyune,sun rayune a gidan marayu dake garin daura,sannan an tsincesune a hannun wata mata zata sakasu a kogi,ranar da tayi daidai da rasa ƴaƴana danayi,wanda suke da kwana biyu a duniya....."
Sakin kuka tayi tareda durƙusawa a ƙasa,dama tana maganar muryarta tana rawa,kana gani kasan abin yana cin zuciyarta matuƙa.
Kama kafaɗunta mai martaba yayi tareda ɗagota.
"Addu'a zakiyi da nuna mafarinciki da Allah ya nuna miki su,ba kuka irin haka ba"
Ɗaga kai tayi alamar ta fahimta,kafin ta kalli inno wanda itama idonta yake kanta.
Takawa take a hankali har inda take tsaye,hannyenta ta ɗaga tareda cewa.
"Nagode nagode,duk da nasan dan kina sonsu dakuma kyakykyawar zuciya yasa kika rainesu,amma duk da haka na godemiki yake wannan jajirtacciyar uwa.
Duk da cewar na gano su sabrah sune ƴaƴana dana rasa a shekara ashirin da huɗu bayah,hakan bashine zaisa na rabaki dasuba,ƴayanki ne halak malak,Alhamdulillah naji daɗi,zuciyata ta samu nutsuwa dana tabbatar cewar suna cikin koshin lafiyah kuma cikin ingantacciyar rayuwa"
Kama hannunta inno tayi tareda cewa.
"Nice da farinciki da Allah yabani ikon nayi tozali da iyayensu,masu daraja da kuma mutunci,ba irin wanda mutane suke tunani ba.
Nagode da kyautar da kikamin,amma kuma bazan iya ɗauke ƴayanki na tafi dasuba,dole kina buƙatar fahimtarsu,dan haka zasu zauna a wajenki na ɗan lokaci kafin kowa idan Allah yayi mata miji ta tafi ɗakinta.
Wani daɗine ya jiyarci hajiya saratu da taji batun da tayi.
Tun kafin tayi magana khariyyah tace.
"Inno me naji kina cewa,ai tafiya zakiyi mu zauna a gidannan,ahah nikam bazan zauna a nan ba,ƙafarki ƙafata"
Harararta inno tayi,amma tayi ƙiƙam da kai alamar babu inda zataje.
"Dukkanku ku dawo nan da zama,akwai sashen Hajiya Marigayiyah,wato mahaifiyar Khaleel,saiku zauna a wajen,tunda ba namiji a inda kuken zaman ma hatsarine kuna mata"
Ɗaga kai inno tayi da alama taji mai yace,a ranta taso ta koma garinsu idan sun dawo nan,saidai kuma wacece ita dazata ce bataso,koba komai gata ga ƴaƴanta ma.
"Shikenan ranka ya daɗe mungode sosai,Allah ya ƙara martaba"
"Ameen ameen,ke kuma madeena gwanda dakikayi wannan maganar,da yanzu abin ya ƙazanta yanda ba'aso,matarsa ta farko yayarkice ta jini uwa ɗaya uba ɗaya,dayanzu ba a saniba sai yayi rayuwar aure da yaya da ƙanwa"
"Nifah baba dama bani natura wata wasiƙa ba,bansan ma mai suke magana akai ba"
"Toh in bake bace waye ya tura,ga wasiƙar ƙarya zamuyi miki"
Khamriyyah ta faɗa tana miƙa wasiƙar wajenta.
Karba tayi tareda warewa ta karanta.
"Amal,wannann rubutun amal ne ba nawa ba,ita ta tura baniba"
Kowa juyawa yayi ya kalleta,yayinda ta sunkuyar da kai tana murza hannu.
Dungureta hajiya saratu tayi dama tana kusanta.
"Ja'irar ƴah,da badan wannan sabon lamarin ya fitoba da shikenan kin jawo husuma da tashin hankali koh"
Tsawa mai martaba ya daka mata tareda cewa.
"Ai wannan bai ishetaba,gobema idan aka barta zata sake,dolene ta fuskanci hukunci"
Baba nima wlh vanice nayi haka kawai ba,deejah ce tace na rubuta lokacin data saceni,kuma tace inna faɗawa wani itace tayimin wannan dukan saita yankani,wai kashe hajiyan su anty khadija tazoyi babu ruwanta da kowa.
Da nace meyasa zata sa a rubuta wannan takardar kuma sai tace wai ina ruwana"
"Wacece deejah kuma?,kowa shuru yayi wanda suka santa kuma suka fara kame kame"
"Uhm Aiki tayi a gidannan na wata huɗu a sashena,ranar da aka sace hajiya har yau babu wanda yasake ganinta"
Amal ta faɗa bakinta yana rawa dan tsoro.
"Me masu tsaron gidannan suke har tazo tayi hakan,waye yake taimaka mata a gidan"
"Eh tareda ake ganinsu da yaron shamaki mai kulada dawakan Ummah,kuma data tafi bayan ta gama shima ba'a sake ganinsa ba,harda drivern ma"
Dunƙule hannu mai martaba yayi tareda ƙiran dogarawa sukayi waje,domin neman ƙarin bayani.
Har yazo fita idonsa yakai kan khaleel wanda yayi saurin kawar da kai.
"Wannan fah,kaman yayan gidannan,wanene shi"
"Yah khaleel ne wanda yake wajen su hajiya Deejah,bai daɗe da dawowa daga ƙasar china ba"
" Khaleel kuma,ba ance sun mutu ba shida junaid.
Mai yake faruwane a gidannan a rufe tsawon shekaru,sannan ......
Wannan ba khaleel bane,kama yakemin da ƙaramin junaid,kudai faɗi gaskiya,kuma kunsan gaskiya"
"Eh Abbah nine Junaid,amma nasake suna da khaleel nake amfani bayan abinda ya faru.
Kuma inaso na cigaba a matsayin khaleel har sanda numfashina zai ƙare"
Kallon mai martaba yake lokacin daya faɗi hakan,kana kallon tsagwaron bakin ciki a cikin idanuwannasa..
Hajiya deejah ce tashigo itada meena,dan yanzu labari yaje mata wai an soke ɗaurin auren Sadeeq da Madeena.
"Me nakejine a gari marar daɗi,mayake faruwa?"
Idonta ta ɗorah kan su inno da suke tsaye suna kallon abinda yake faruwa tsakanin mai martaba da kuma ɗannasa junaid.
"Kukuma mai kuke a gidannan,ko kune kuka wargaxa auren kai?"
"Hadeeza ba sune suka wargaje aureba,nina dakatar dashi,saboda matarsa ta farko ɗaya daga ƴan biyun da aka rasane shekarun baya,wato ƴayan Hajiya saratu.
Kinga babu auren daza'a ɗaura da madeena kenan.
Sannan ba wannan bama,ya akayi junaid yazama khaleel,kincemin kincemin dukka sun mutu,mayafaru iyeee?"
"Habaa Yaya,yazaka dawo da abinda ya wuce,komai yafarune saboda laifinku kaida matarka Hajiya fulani,ta kallameka kazama sai abunda tace,wato hajiya Fulani.
Sannan niba nice nace ya rayu a matsayin khaleel ba,shine yace bayason zamansa a junaid sai a khaleel.Nikuma idan nace maka khaleel yana raye dole zata sani ,gashi shima hatsarine tasan yana raye,hatta kusancinsa da inda yake hatsarine,shiyasa nida mijina muka raineshi shida Sadeeq a tare,a ƙasar china,da muka tashi dawowa kuma sai muka barshi a can saboda tsaro.
Batareda kowa yasani ba ya cigaba da rayuwa,khaleel shiya rasu bayan sun sha mintin da junaid ya ɗaukomusu na tsafinta,shine kaɗai ya rayu,shima sai bayan shekara biyu yana jinya a cam kafin ya tashi.
Da har mun fidda rai da rayuwarsa,daya tashi yaji ɗan uwansa dasuka shaƙu wato khaleel ya rasu sai yace da sunansa zai cigaba da amfani,anan muka sanja masa suna bisa shari'a,muka barshi a can yayi karatun bincike a can"
"Toh amma meyasa kika boyemin tsawon wannan lokacin"
"Dolene yasa nayi hakan,an sace yara jarirai a tsumman goyo,Hajiya fulani Ameena,matarka ta farko ta rasu,kowa yasan shanye jininta akayi,amma ba a yi komai ba.
Yarannan sunsha guba a ɗakinta,wani yaron ha ilau yafaɗa doguwar suma ta tsawon shekaru mai akayi akai,bayan doguwar jinya,ɗaya ya mutu ɗaya ya rayu,sai na faɗamaka,tabishi ta kasheshi shima.
Duk da ɗantane amma ransa take nema saboda buƙatar duniyarta,yanzu ma da badan alkadarinta ya karye ba bazan faɗamaka ba.
Ni wannan deejah da akace tayi mata aika aika tayimin daidai,duk da hakan bai kamata a ɗau doka a hannun ba"
Taku
_sadi-sakhna_
Ƴar mutan jama'are.
*MABARACIYAH*
_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)
53••54
Babban falone na mai martaba an cika shi maƙil da mutane,kowa ka ganshi dangine ko kuma shaƙiƙin amini na masarautar,kaman irinsu inno da khamriyyah da saleem,wanda sun haɗu da wajen ta wani dalili.
Dukkan dangi dana kusa harma dana nesa an hallara a wajen domin jin mai mai martaba zai sanar dasu.
Hajiya fulanice kawai bata wajen,ita tana caliponia wajen magani.Saidai wasu ƴan uwanta kawai.
Kowa a wajen a carpet yake zaune,iya babban gayyar ne kawai a hakimce akan kujera.
Farawa yayi da addu'a,bayan an gama sannan yafara da cewa.
"Toh wasu sunsan abinda ya taramu a wajennan,wasu kuma basu saniba,saidai kuma suna mamakin yanda jiya har an hallara za'a ɗaura auren ƴa ta da kuma ɗan kanwata hajiya deejah,amma kuma aka fasa saboda wani dalili.
Tohh babban dalilin shine,bayyanar ƴaƴan yan biyu mata wanda suka bata shekara kusan ashirin da huɗu da suka wuce,yau Allah da ƙudurinsa da kuma hikimarsa ya bayyana mana su lokacin da bama tsammanin hakan.
Sannan wani abin mamakin ashe ɗaya daga cikinsu itace matar shi wanda madeen zata aura,kunga kuwa a