MABARACIYAH Daga Bara Zuwa Firgitar Masu Iko by Auwal sadiya

Author :  Auwal sadiya Category :  Free Novels Online (Read & Download)

Chapter   4 / 33

9K to 12K   out of 96.8K words

kafin kowa ya cire hijabinsa ya ajiye.
Ɗakin da aka kwantar da Dr. Bukar suka nufah,gefe kuma duka daƙuna ne kowanne da ɗan gado a ciki da banɗaki,saidai kofar a rufe take,wani daga cikin wanda suke ɗakunann yafara buga ƙofar yana magana.
Kallon zainab khamriyyah tayi tareda tambayar wanene a ciki.
"Uhm ɗan gidan minister ne da aka kawoshi jiyah"
"Egnr Aisha Eemran?"
"Eh itace,tun ranar yake ta......."
"Bashshi dama dole yayi saboda bai san wahala ba ko kaɗan,yayi sa'a ma da iyah ajiyeshi akayi kawai a ɗakin,hmmm naji labarin itama yanda hankalinta ya tashi ai,ƴan rainin hankali,saina kai mata kansa naga tsiyah"
Wucewa tayi ɗakin da suke aikin Dr bukar ɗin,yana kwance a jojjona masa wayoyi a jikinsa yana fitar da numfashi da kyar da kyar.
Wani file dr nawwarah ta miƙawa khamriyyan tareda cewa,
"Duk wani abu daya kamata ayi an zartar shugaba,buƙata shine a bashi ruwan zuwa anjima idan ya farka,daga nan kuma aiki ya kammala"
"Sai ki dunga ƙirana da shugabarki duk kuwa da yanda kika girmeni a matsayi da kuma shekaru"
"Hmmm dan bakisan yanda kike a zuciyarmu bane shiyasa kika faɗi haka,ke tamkar zinariyah ce da muka tsinceta a lokacin da muke tsaka da neman ko kwandala ce wacce zamuci abinci.
Kin bamu ƙwarin gwiwa da kuma muradin yin abinda ko namiji bai isa bamuba,keɗin tamkar ɗayace da dubu,dan haka bake kika samemu ba mune muka sameki"
Ɗan murmushin gefen baki tayi tareda cewa
"Ki daina irin wanann zancen nawwarah,kin fikowa sanin na tsani abinda za'ayi ko a fadamin dazai jawo min karayar zuciya,yanzu dai aiki yayi kyau ina miki jinjina,barina je na ɗan ji da wancan ɗan gidan minister,dan in ba rufe masa baki akayi ba bazayyi mana shuru ba sam,"
Fita tayi daga dakin tareda saka wata fuska ta nufi ɗakin dayake.
Can kaman wajen karfe shabiyu saƙo ya shiga mata kan cewar dr. Bukar ya tashi daga aikin da'akayi masa na cire ƙoda.
Ɗakin ta nufah inda ta ganshi a zaune,kwana ɗaya har ya rame yayi baki,daga ɗan kansa akayi da pillow sai nishi yake bakinsa ta bushe.
A gabansa ta tsayah tareda kama kunkumi tana dariyah,shima kuma sarai daga gani ya ganeta,buɗe baki yayi a hankali da kyar tareda cewa
"Mmmmai ya ......fffaru dani a a anan wajen?"
"Aiki mukayi maka yallabai,gani mukayi baka dace ace kamar ka kana amfani da ƙoda ba,ta roba zata fi maka kyau shiyasa muka ciresu muka saka maka na roba,to yanzu sai kayi mana godiya"
"Ammmm..."
Shuru yayi yama kasa cewa komai,babu abinda yake sai zubar da hawaye,dan a yanda yake bashida karfin halin aikata komai,hannun ya kai dayake rawa ya ɗora akan babban bandejin dayake kan ruwan cikinsa,tabbas ba mafarki yake ba hakane,sun cire masa ƙoda,dan ga alama nan ta nuna har a bakinsa najin kishirwa dayakeyi.
"Oh sorry ba manta bari a kawomaka ruwa kasha,karka margaya tun yanzu"
Ruwa ta tsiyanyo a kofi daga cikin butar faro,da kaman baxai karba ba,amma ganin ruwan mai kyaune kuma yana buƙata yasa ya buɗe bakinsa ta zuba masa.
Kwat kwat yafara shan ruwan da kansa ya kawar da kai.
Dr nawwarah ce tashigo ɗakin tareda cewa
"Shugaba yasha ruwan ?"
"Ehhh yasha fiyeda yanda nake tsammani ma kuwa,aiki yayi yanda muke so,yanzu kafin ya fara birkicewa ya kamata mu jefarshi su tsinceshi"
Zaro ido yayi jin abinda suke faɗa,musamman da idonsa ya sauƙa kan fuskar dr nawwarah,wacce take masa kallom tsana.
"Dr. To yanzu ya gaka yanda abun ya juyah,kasan ruwan da muka baka kuwa,ruwane mai dauke da sinadari mai karfi wanda temporary kidney baxata iyah excretion ɗin sa ba,mai kake tunani zai faru to a matsayinka na likitan ƙodar,nasan basai na fadamaka ba kasan result ɗin dazai haifar?
Kafin nan ka more guntun lokacinka wajen tunanin,takaici,razana ,zullumi dadai sauran abubuwan dazasu kara worse ɗin ciwon,kan ka farga babu damar komawa da baya,saidai ka tunkari mutuwarka"
Tunkafin ta gama maganar ma jikinsa yafara tsanani,kana ganinsa kasan ba karamin mawuyacin hali ya shiga ba sosai.
Khamriyyah ce ta kalli su maryam wanda har sun shirya dama fita dashi.
"Vl3(maryam) deen ya ɗaukeku a motah,ku kaishi gefen gidan Dec. Sadeeq ku ajiyeshi"
"Shikenan V- lady,amma kince zaki tafi gidan,mai zai hana mu fita tare?"
"Mashin ɗina aikin mai yake,beside ma banda ra'ayin zuwa,kudai kuyi yanda nace"
Fita sukayi tareda nufar gidan dec. Sadeeq ɗin bayan sun saka shi a cikin boot,zuwa sannan har ya suma bai san inda kansa yakeba.
A gefen wata katanga da take nesa kaɗan da gidannsa suka ajiye gawar.
Har sun taka motar sun fara tafiyah,saikuma suka ga wata mata tazo kan gawar,da kaya a jikinta jajaye,babu abinda suke ganin a jikinta idonta kawai,ganin sun haskata yasa ta fasa yin komai a wajen ta zura da gudu bayan wasu gidaje wanda aka farasu ba'a gamaba.
Maryam ce ta fita da gudu tabi bayan ta yayinda shima deen yabi bayan ta da sauri.
Sun zuwa bayan wajen babu ita babu alamarta gashi kuma ba wani wajen da mutum zai buya a gurin.
"Deen inaga fah aljana ce,dan baka ga kayan jikinta bama,ni wani iri nakeji ma"
"Kefah kin faye tsoro,babu abinda xai faru,mutum ce daga gani kaman kowa,ina ruwan aljani da wani dr. Bukar toh,kawai dai inaga bacewa tayi"
Saurin komawa mota sukai tareda barin wajen,gudun karsu dade a kamasu a wajen.
Akwance yake Amrah tayi pillow da kirjinsa sai bacci sukeyi,dan jiya da daddare ma amai ta dungayi dakyar suka samu ya tsayah,shiyasa sunayin sallah suka koma bacci.
Ƙarar wayarsa ce ta tasheshi daga baccin dayakeyi,itama kuma amrah ta motsa daga kwancen datake.
Dayake tafi kusa da wayar ita tamiƙo masa wayar cikin magagin bacci,sunan data ganine yasa ta jan tsukah mai karfi.
"Kekuma keda wa haka kike jan tsaki?"
Ƙarbar wayar yayi,ganin sunan khamriyyah yasashi yin ƴar ƙaramar dariyah,yana shafah kanta wanda ta mayar ta sake kwanciyah tana tura baki.
"Hell............what?,a gefen gidana kuma meyasa? Ganinna fitowa yanzu nan,ku tabbatar kun kula sosai"
Saurin zame jikinsa yayi tareda jura rigarsa yafita da sauri.
A bakin ƙofar gidannasa yasamu dandanzon ƴan sanda,sai ƙokarin ture mutane suke.
Khamriyyah ce ta nufoshi da wata takarda a hannunta.
"Barka da safiya ogah,ga can gawar yanzu muka samu bayani daga wani ɗan anguwar daya ganta,babu wanda yaje wajen isowarmu kennan"
Ta gefenta ya wuce ba tareda yabawa abinda take faɗa muhimmanci sosai ba,burinsa ya isa ga gawar kawai.
Tsugunnawa yayi a gaban wajen yana kare mata kallo,wata ƴar takarda ya ciro a gefen gawar fara,daukowa yayi tareda buɗewa.
Rubitune irin na almajirai na warash,saidai kuma bana larabci bane,in ba wanda yayi zurfi a karstun nasu ba ba zai iyah karantawa ba bare rubutawa,dan dasu ake amfani ake ƙiran aljanu da kuma siddabaru.
Duddubawa yake saidai ya gagara karantawa sam.
Khamriyyah ce ta iso wajen tana kallon takardar a hannunsa,mikamata yayi tareda cewa
"Duba ko zaki iya ganewa?"
"Ahah yallabai,(ɗaga muryah tayi tareda nunawa mutanen wajen),akwai wanda zai iyah karanta mana wannan yaren kuwa"
Shuru akayi sai daga baya wani almajiri ƙolo ya fito tareda ƙarbar takarda,a dole an ƙirashi wajen bincike.
Duddu bawa yake alamar mai son gano wani abun,koda ba duka bane daga tasa fahimtar.
Ɗagowa yayi tareda nunawa dec. Sadeeq wani waje a jikin takardar ta ƙasa.
"Eh to nima ban iyah rubutawa ba amma kuma nakan gane harafi kaɗan kaɗan ba masu wuyah ba...........nan dai ta wajen ƙarshen MABARACIYAH aka rubuta dan na san na kalmar mabarata,nan mabaraciyane a rubuce.
Amma nasan malamina zai iyah karanta muku wasiƙar.

"Mabaraciyah kuma?"



_sadi-sakhna_




*(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)*

*MABARACIYAH*
(mai harshen damo)

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιε.


_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)



Paid book #400
3131951977
Auwal sadiya
First bank

Mai turo kati kuma ta wanann number MTN
09035784150

Mutanen niger su tuntubi wanann number
+227 97 21 16 15

Naƙara shafin free har zuwa page 20,zuwa lokacin inka shiryah kazo a fara dakai ranar juma'a.

_____________________
Assalamualaikum barkan mu da wannan lokaci *ABMAR COLLECTION* ina nan na kawo muku kayana masu kyau da sauki👌🏻
KAMAR SU:-
Atamfa, Atamfa Mai golden,💁‍♀️
Lace ,Shadda lace
Yadi, Shadda
Abayas💥
Kids wear
Takalmi, jaka, mayafai💥
Sleeping dress, kananan kaya na gayu🔥kayan kitchen,
DA DAI SAURANSU ina Sokoto ina tura kaya ko ina da izinin ubangiji mai son kayana pc ina maraba daku siyan daya ko sari👏🏻domin neman karin bayani sai ku neme ni ta wannan number waya👉08101521252
nagode kwarai da gaske💃💃







Free page
7••8



"Okay mun gode bawan allah,inshaallah zamu tuntubi inda malaminnaka yake domin sanin abinda yake jiki yanada matukar muhimmanci"
"Bakomai ofisa ba nisa layin bayannan ne,kana zuwa kace Shazali mai almajirai,kowa ya sanshi sosai"
Motar ambulance ceta iso wajen sai kara take na nuna bayyanarta,wasu mutanene suka fito daga cikin motar sanye da kayan aikinsu.
Wajen inda gawar dr. Bukar take suka kariso domin tafiyah dashi checking,sanadiyyar alamomi daya nuna kala kala.
Ɗagashin dasukayi ne yayi sanadiyyar bayyanar babban bandage din dayake cikinsa,da alama an kasheshine da hanyar yimasa wani abu a cikin.
Saurin ƙarisawa wajen dec. Sadeeq yayi tareda cewa,
"Kudan dagata pleace kaɗan"
Buɗe cikin yayi tareda ɗora hannunsa akai,
"Me'akayi masa a ciki to,lallai wannan lamari yafara bani mamaki yanzu.
Maza a tabbatar an ɗauki hoton cikin"
Ahmad ne yazo da sauri ya ɗauka da camera kafin aka sakashi a motar zuwa asibitin.
"Kai Ahmad kabi bayansu asibitin muna zuwa yanzunnan,akwai wani waje dazamuje,ka tabbatar anyiwa gawar bincike yanda ya dace"
"Yess sir"
"Ke kuma dec. Khamriyyah zoki rakani,yakamata mu samu masaniya gameda wannan takardar,dan abin akwai ɗaure kai ciki"
Binsa tayi a baya suka shiga motarsa tareda nufar gidan da ɗan saurayin yayi musu kwantancensa.
Basu wani ɗade ba suka isa,kasamcewar a anguwar ne gidan.
Maƙil suka samu gidan cikeda almajirai sai karatun maraice suke a jikin allansu,iyah muryarsu kakeji baka isa ka banbamce muryah wani ba da abinda yake faɗa.
Wani yaro suka ƙirah daga cikin masu karatun,da kaman bazai zo ba saikuma yadai taso da allonsa a hannu.
"Kai yaron malam ya karatu?"
"Lafiyah kalau"
"Yawwa idan malaminku yana nan kace muna sallama dashi kaji?"
"Toh"
Yana faɗa ya ruga cikin gidan da gudunsa.
Suna nan tsaye sai kashi ya dawo tareda cemusu su shiga yana cikin zaurensa.
A wani ɗan ɗaki yake zaune kafin a shiga cikin gidan,wanda muke kirada zaure a yaren hausa.
"Salamu alaikum"
"Wa'alaikumus salam"
"Malam barka da safiyah,sunana Decetive Abubakar sadeeq,wananm kuma abokiyar aikina ce Khamriyyah.
Wani abune na bincike ya taso wanda ya shafi sani da kuma ilimi irin naku a ciki,wanann ne yasa muka nufo nan tareda baran roƙon malam ko zaka iyah fayyacemana mai takardar nan ta ƙunsa?"
Ya ƙarisa magana yana miƙawa malam shazali takardar.
Ƙarba yayi yana ɗan duddubawa kafin ya ɗago ya kalli su khamriyyah.
"Toh malam mai bincike nima lamarin yaɗan shamin kai,dan alƙalamin macece tabbas ya rubuta wannan kalmomi,abin mamaki anan shine ya akayi mace ta ƙware a rubutunnan,ko ɗaliban mu na nan,yanzu suka fara koyah basukai matakin wannan ƙwarewar ba"
"Hmm ba kai kaɗai wanann abin ya ɗaurewa kai ba gafarta malam,kai yanzuma kasan da abin,mudai yanzu buƙata ka faɗa mana mai wannan takardar ta ƙunsa in akwai dama"
"Bi'zinillah bazai gagaraba barina sake dubawa"
Wani ɗan madubi ya ɗauko ya saka a kan takardar tareda nuna musu su matso su gani.
Kaman dama jira suke,da sauri suka matso,matsowa yayi da sauri tareda saka idonsa akan takardar.
Kallon malamin yayi da alamar tambaya akan fuskarsa.
"Kagani rubutune na ajami da rubutun warash,amma kuma a juye yake,baya karantuwa sai tacikin madubi ga wanda bai iyah karantashiba da rubutashi,abinda kaga nasaka masa madubi saboda abune na bincike wanda kuna buƙatar ku sani dakanku"
Miƙawa dec. Sadeeq madubin yayi da kuma taakardar,ga mamakinsa kuwa saiyaga tacikin madubin yana gane abinda aka rubuta akan takardar.
Tashi yayi malamin tareda cewa
"Barina baku waje ku karanta,zan zagaya almajiran can dama"
Kallon khamriyyah yayi sanann ya ƙara kallon takardar.
"Akwai biro da takarda a wajenki kuwa?"
"Eh akwai ogah,bana tafiya babu jotter saboda rubuta bayanai"
"Okay yayi kyau,idan na karantomiki ki rubutamin"
_Mai kake tunani malam sadeeq mai bincike,a zatonka wanann harbin da abokiyar aikinka tayimin zayyi ajalina ? Lah lah,tabbas salo irinna aikina sukayi amfani dashi,amma bani bace nake aikatawa,kai kanka nasan kana tunanin nice,saboda nasan duk abinda suke shiryawa dama abinda kaima kake saƙawa,ni tamkar inuwa nake,ina a ko ina in ka wulga mai bincike.
Sannan wanann kisan da akayi karma ka ambaci sunana,dan wanann ƙodarsa aka cire tareda maye gurbinta da ta roba.
Dan haka inkana da hankali zaka san cewa wanann ba aikin mabaraciyah bane,aikinta da hanyoyin gargajiyah take amfani,sanann kuma ta wargaza wanda ba'a tsammanin wargajewarsa.
Kasan ance *idan mikiyah tayi kuka kaza gudu take ta buyah*,to kaman hakane wacce take kisansu yanzu zasu gudu su buyah,kayimusu gargaɗi su tsimayi fasowata,dan akwai gagarumin aiki dazan gabatar a garinnan,in ka isa ka iyah bincike ka dakatar dani malam sadeeq.
Abar nemanka MABARACIYAH._

Kallon rubutun khamriyyah takeyi bayan dec. Sadeeq yagama karantowa abinda yake cikin takardar,daga yanda take nazartar talardar kasan ta afka kogin tunani,sanann kuma daga gani mai saƙon ba iyah dec. Sadeeq aka turawa saƙon ba harda ita kanta.
Sunyi kusan minti biyar babu wanda yayi magana a cikinsu,da alama suna ƙara tariyo abinne a cikim kansu,dan kowa danasa damuwar gameda saƙon dayake cikin takardar.
"Sir mun riga mun samo abinda yake cikin takardar,yakamata mu koma asibitin nan,zaman haka babu abinda zai haifar"
"Eh zamu koma,amma daga iyah takardar nan mun gano wasu satar amsa guda biyu a ciki"
"Ogah satar amsa kuma?"
"Eh,abun na farko mungano ba iyah ita kaɗaice take aikata mugun aikin da ake nemanta dashi ba,sannan abu na biyu mungano ita ɗin dole tayi makaranta ne a wata tsangaya ta almajirai,inba batayi makarantarba to lallai tanada alaƙa da wata makaranta irin tasu.
Yanzu binciken mu dole zai haɗa da wurare na tsangayar almajirai,sannan dole kuma muƙara bincike wajen gano sauran masu aikatawar ma"
"Amma.... Ogah ka yarda da abinda ta faɗa,anyah ba wasa takeson tayi da hankalinmu ba kaman yanda ta saba?"
"Nima nayi tunanin hakan,ta farko ban yarda ba,amma kuma idan abinda tafaɗa gaskiyane ba fah,ya kikega zamuyi kenan,inaga idan har wanann ma na gagara gano wani abu akai to dole zan miƙa case ɗin nan zuwa gaba"
"Baza'ayi har haka ba ogah zamuyi iyah matuƙar ƙoƙarinmu inshaallah"
"Nan da wani satin inaga zan shigar da takardar tafiyah ƙarin karatu,danni ma na fara tantamar aikinnawa tundaga yanzu"
Shuru khamriyyah tayi tana jinsa,dan tarasa abin cewa ma itah,duk abubuwa sun juyah lokaci ɗayah.
Tashi sukayi suka tafi bayan sun yiwa malamin godiya.
Asibitin suka nufah,dan tun a hanya ahmad yake ƙiransu wai result ɗin binciƙen ya fito.
A bakin wajen yasamu iyalan dr. Bukar ɗin suna zaune sunyi jugum.
Kallon su yayi a ransa yana cewa
Yanzu su basuda aiki sai dauko gawar mutane sukai wa masoyanta,abin takaicinma sun gagara gano waye yake kisan,
Wucewa sukayi ciki inda office ɗin likitan yake,a bakin wajen ya samu ahmad a tsaye da file ɗin a hannunsa,yana ganinsa ya miƙo masa.
Karba yayi jikinsa har rawa yake wajen ganin menene a ciki.
Idonsa ya zaro lokacin dayaga an rubuta yayi loosing kidney,kallon likitan yayi tareda neman ƙarin bayani.
"Eh kaman yanda ka gani Detective sadeeq hakane ya faru,munyi bincike a gameda a cikinsa,inda muka gano bashida ƙoda ko guda ɗaya duk an ciresu,sannan kuma an maye gurbinsu da temporary,bayan hakan kuma an bashi ruwa mai ɗauke da sinadarin acid a ciki,wanda kuma ƙodar roba bazata iya taceshi ba,ko ƙoda normal ma mutum bazai iyah tsallakewa ba batareda yasha magani ba,sanadiyyar hakanne ta tsayah da aiki,shikuma ruwan ya shiga cikin jikinsa,wanann ne yajawo kalar duhu da jikinsa yayi.
Kisa akayi masa na rashin galihu,sanann duk wanda yayi kisan nan ƙwararrene wajen bangaren ƙoda,sannan kuma masani a wajen tiyata,wanann case ɗin ba ƙarami bane detective sadeeq,wannan shine iya abinda muka gani a binciken da mukayi dai"
"Nagode dr. Da ƙoƙari,in ba damuwa za'a iyah bawa iyalinsa gawarsa,mukuma muna buƙatar tafiyah"
"Ba matsala hakan,zaku iyah tafiyah,Allah ya kiyaye gaba "
Musabaha sukayi da dr kafin ya juya ya fito daga wajen likitan.
Da hajiya salah yaci karo a bakin ƙofar idonta yayi jawur da hawaye,gefe kuma ƴaƴantane guda shida,maza biyu mata huɗu,kowanne kagani a cikinsu kasan yana cikin halin jimami,mai dauriyar cikinsu ma iyah dr. Muhseen ne wanda yanzu yake matakin shakarar farko na aiki a asibitin ubannasa.
"Ya ake ciki,menene yace yayi sanadiyyar mutuwarsa?"
Shuru dec. Sadeeq yayi ya gagara yi mata bayani sannan yarasa ƙwarij gwiwar miƙa mata file ɗin tagani da kanta.
Ganin hakanne yasa khamriyyah karbar takardar t miƙa mata ,saboda taga ogananta yarasa ƙarfin gwiwarsa a lokacin.
Dubawa takeyi amma takasa gani ko manene,ganin an saka case ɗin ƙodane yasa ta mikawa babban ɗan nata,saboda shima fannin wajen ya karanta irinna ogansa.
Ƙarba yayi tun kafin ya gama karantawa hannunsa yafara karkarwa,idanuwansa suka firfito,kana ganin tashin hankali da razana a cikin idanuwansa cike fall,zafar da takardar yayi batareda yaƙarisa karantawa ba,domin hannunwasa ma bazasu iyah cigaba da riƙe takardar ba.
"Menene muhsin mai ka gani a cikin takardar?"
Shuru yayi shima ya runtse ido,ko buɗe ido ya kalleta ya gagara ballantana ya faɗa mata mai yayi arba dashi a cikin file ɗin.
Kama rigarsa tayi tana jijjigawa,zuwa sannan tafara kasa riƙe kukan dayake cinta tun farkon faruwan ɗauke mijinnata,
"Kayimin magana muhseen,idan shi yakasa yimin bayani kai bai kamata ka boyemin mai ka gani ba,kasan nafi kowa hakkin nasan mai yafaru da mijina!"
"Ummah da kin....."
"Karka fara wannan wasan dani,ka faɗamin mai ya faru yanzunnan,basai anjima ba"
"Abbah ba haka kawai ya mutuba,sannan ba duka bane ko harsashi ya kasheshi ba ummah,ya mutune a sanadiyyar ɗauke dukkan ƙododinsa da akayi,sanann kuma aka maye gurbinsu da dana roba,ba'a barshi haka ba aka kuma shayar dashi ruwa mai ƙarfin acid da temporary kidney bazata iyah excretion ba,sanadiyyar hakan yakwana cikin azaba kafin safiyah ya mutu batareda wani ya kawomasa ɗauki ba......!"
Sakin rigar muhseen ɗin tayi tareda zubewa akan tiles ɗin wajen,mai kuma zatace da irin wanann mummunan labari dataji,wanda gwanda ace a gabanta ya faɗi ya mutu dataji labarin abinda yafaru dashi,kuma batasan yafaruba bare tana wajen tayi wani abu.
"Tabbas wannan zaluncine ummah,mai abbah yayimusu suka yimasa wannan ɗanyen aiki,a iyah sanina dashi bashida abokin gaba ko guda ɗaya,to menene dalilinsu na aikata hakan,wacece wanann mabaraciyar,sanann mai yasa take aikatawa manyan mutane wanann ɗanyen hukuncin?"
"Uhm haƙiƙanin gaskiya muhseen ba mabaraciya bace ta

4 / 33