Author : Auwal sadiya Category : Free Novels Online (Read & Download)
kyau,kaifah kace min kanaso kaɗan danɗana,yanzu kuma bakaso ne,tsorona kake kake ja da baya,jarumin masarautar katsina?"
"Dadddan ALLAHHHH kiyi haƙuri ki taimakeni,wayyo allah nah,bansan ke aljana bace da bazan yimiki haka ba"
"Allah ko baka sani ba?.....in faɗama wani abu dazai rikita ka,yayanka junaid yana raye,kuma yana kusada kai,sannan shima ɗaya yayannka yana daff da farkawa daga dogon baccinsa,taya zan taimaka maka kayi sarauta toh,so kake na kashesu dukka kokuma me?.
Ka daina wanann mafarkin,babu inda zai kaika sai halaka,kai a duhu kake baka san komai ba.
Ka gyara rayuwarka ka tsaya iya haka,idan kuma nasake ganinka da wata macen a gidannan,ko kuma kayi shaye shaye,.........hmmm don't imagine."
Daga haka ta sau masa tattausan murmushi tabar ɗakin.
A bakin ƙofar fitowa daga sashen nasa ta haɗu ta sumail yana jiranta.
"Oh harka tsoratani,yaushe ka dawo"
"Minti biyu baya.
Taya zan tsorita aljana kuma?"
Yafaɗa ta sigar zolaya.
Dariya tayi tareda cewa.
"Kajini kenan dashi,hmmm yanada rawar kai ne.Yanzu tunda munyi nasarar ɗaukar akwatin,kana ganin zata iyah gane inda yake,nifah nasan sharrin matar nan"
"Hhh karki damu,na kaishi ga shugabana wanda nake ɗaukar karatu a wajensa akan ya buɗeshi,lokacin dana tahodai yana ƙoƙarin budewa,zai iya ɗaukarsa wataƙil kwana biyu ya bude,amma idan ya buɗe dole zata san baya nan,duk da cewar bazata san inda yake ba"
Jinjina lamarin deejah tayi,inba an haɗa da mutanen boyeba taya zata iya wanann abin ita kaɗai.
Wajen la'asar sakaliyah hajiya fulani ta dawo daga meeting itada ta hannun damanta,surayyah wacce aka fi sani da silver.
Koda ta shiga ɗakinnata razana tayi,domin a jikinta taji cewar am buɗe mata ma'ajiyar sirrinta,saurin ɗaga gadon tayi tareda duba akwatin.
Ganin yana ciki yasa ta sau ajiyar zuciya tareda ɗagowa ta kalli silver.
"Huh komai normal,duk cewar ko ɗaukarsa akayi ma mutum bazai iya buɗewa ba,idan ya buɗema da sakanni zan gano inda yake.
Ki ƙiramin deejah naji mai ta bincika a yau"
Waya silver ta ɗauka ta dannawa deejah ƙira,akan suna nemanta.
Babu bata lokaci kuwa tazo,dan dama hakan yana cikin tsarinta,an kulle gidan babu shiga babu fita ana bincike.
In bada ƙwaƙwƙwaran dalili ba mutum bazai fitaba.
"Ranki ya daɗe gani"
"Uhm mai kika samo gameda yarima junaid,ko har yanzu bakiga wani ba wanda kike zargi?"
"Eh banga komai ba,amma akwai wasu baƙi da akace sunzo jiya cikin gidannan da yamma samari,kuma suna zaune a bayan gidan galadima.
Naso naje na duba,to kuma an saka matakin rashin fita,shiyas........"
"Shiyasa me,ina ruwana da wani rashin fita na batan yarinya,saratu ma ta bace mana ba ƴar ta ba,ki shiryah yanzu zan aika a barki ki fita injini,ina son ganoshi da gaggawa,nagaji da riƙe wancan mai kama da gawar,dole ɗayam biyunsu zai mutu,ɗayan kuma zan mallakeshi na ɗorashi akan mulki"
"Toh ranki ya daɗe,barina je na shirya nazo"
"Yanzu zan aika saƙo,in kinzo fita ki wuce kawai,babu wanda zai hanaki,sannan ki tunada gargaɗina,karnaji plan ɗina a bakin kowa,idam ba haka ba ki shirya ganin ki babu harshe"
Jiki yana rawar ƙarya deejah ta bar sashen hajiya fulanin.
Cikin rashin sani suna ta sauƙaƙa mata shirinta hmmmm.
Tafiyah take tana ƴar waƙa,bata luraba taji tayi karoda mutum a gabanta.
Ɗaga kai tayi suka haɗa ido da Junaid wanda ya sarƙe hannayensa a ƙirjinsa yana kallonta.
"Dama kina waƙa,ya naga kin fito daga sashennan,har yanzu kina yi mata aikin duba shi ne"
"Ɗaga kai tayi,dan tasan mubarak yake nufi,duk da tanaga a alamar tausayawa ɗan uwanna sa a idonsa,amma yana ƙoƙarin boyewa.
"Kanaso ka ganshi ne"
"Uhm,amma bazan iyaba koda na samu dama,bansan a yanda zan ganshi yanzu ba,rabona dashi tun shekara sha huɗu baya,da farko nayi zaton ya mutu,sai akace wai yana raye,doguwar suma ya shiga"
"Amma daga yanda kake magana,kaman kun shaƙu dashi sosai"
"Mun shaƙu sosai,a lokacin iya mu huɗune,khadija sai mubarak da kuma khaleel,sai kuma mubarak shine ƙarami lokacin.
Tare muka taso da khaleel,saidai shiya fini da watanni,mahaifiyarsa itace Babba,wato Hajiya Fulani maryama.
Bayan rasuwarta ne mahaifiyarmu ta karbi matsayinta na fulani.
Sannan hajiya saratu tana amarya,da tsohon ciki,ita kuma mahaifiyarmu tanada cikin jalal.
Kusan a tare suka haihu,hajiya saratu ta haifi yara biyu mata,ita kuma ta haifi jala,tsiransu kwana biyu.
Ranar Sunan jalal,su kuma kwanan su biyu aka nemesu aka rasa.
Hayaniya ce ta kaure a gidan,ga mutanen kowanne bangare sun zo domin taya su samun ƙaruwar haihuwa.
Babu irin shiga yanayin tausayi da hajiya saratu bata tsinci kanta ba,saidai kaman maye yaci shirwa haka zance ya shiririce,tun ana nemansu har aka haƙura aka zubawa Allah ido akan sarautar sa.
Da farko kasamcewar babu wanda yasan abinda mahaifiyata take,babu wanda yazargeta akan abinda ya wakana a wannan lokacin,saidai da ta aikata na shekara sha huɗu baya,sai komai ya fito fili na halayenta.
Deejah nayi bakin cikin kasancewata ɗa a gareta,saidai koma menene babu yanda zanyi,ita ɗin uwata ce Allah ya zana hakan.
Dan haka banajin zan iya saka kafata a wannan sashen dana fado duniya na buɗe idona a wajen,sannan shigata daidai yake da zuƙewar jinina,wanda inajin wani abu yanzu ma yana fizgar ƙirjina ta ciki"
Ya faɗa yana dafe ƙirjinsa ta bangaren hagun.
Saurin saka hannu deejah tayi taja shi zuwa can kusan sashensu nesa da inda suke.
"Kuma kasan hakan meyasa kazo kusada wajen,duk da hakan zai iya cutar dakai"
"Saboda naga shigarki sashen,haka kawai hankalina yaki kwanciya ganin baki fito ba"
Numfasawa deejah tayi tana kallonsa,yanda yake ƙoƙarin saita numfashinsa.
"Saboda me kake nunamin irin wannan kulawar Junaid,a ganina kaman yayi yawa,tunda har zaka iya saka lafiyarka a hatsari saboda ni"
"Saboda ina sonki ne,ina ƙaunarki,ina miki so tsakani da Allah har can ƙasan zuciyata,ia yimiki son da ni kaina idan na tambayeni bansan iya adadin zurfinsa ba.
Allah ya jarrabeni da azabtacciyar soyayya,sanann kuma makahuwa,da bana ganin komai idan bakeba a bangaren bege,kewa soyayya da kuma sahihiyar ƙauna"
Runtse ido deejah tayi tanajin yanda maganganunsa suke huda dodon kunnenta har izuwa can ƙarƙashin zuciyarta,tunda take bata taba jin kalaman da suka girgizata irin wannan ba..
Inda a satin bayane kafin ta gane shiɗin ɗan makiyyartane,da tuni ta karbi soyyyarsa,amma a yanz duk da cewa tana masa kwatankwacin soyayyar dayake mata,batajin zata iyah karbar wannan tayin.
Domin bakomai zai haifar mataba sai kawomata cikas a cikin Kuɗurinta.
Sauke idanuwanta tayi akan sa wanda suka sanja kala zuwa na emotion zalllah.
"Ina sonka emran,ina sonka junaid,koma A wanne suna ka bayyana ina sonka,saidai kayimin uzuri da lamuni akan wanann babban ragama dakake burin na karba daga wajenka.
Bazan iya karbar soyayyarka ba saboda wani dalili,kayimin haƙurin hakan"
"Babu komai,saidai kisani ko yanxu zuciyata ta samu nutsuwa dana san cewar na amayar da abinda yake cin zuciyata,koda baki amsa ba nidai ya fita daga gareni.
Zan cigaba da yin soyayyar bangare ɗaya har zuwa ranar dazaki amshi soyayyata deejah"
"Nagode daka fahimceni,saidai nayimaka alƙawarin bazaka ga sanji daga gareni ba,yakamata ka shiga cikin ka huta,domin har yanxu jikinka bayyi ƙarfi sosai ba"
Jijjiga kai yayi tareda yunƙurin miƙewa,dan matsawa tayi ya tashi,tareda kallonsa har ya shige sashensu.
Hawayen dayake zarya a idonta tasaka hannu ta share,ita wacece a cikin mutane dazata ce batason yin rayuwa irinta kowa da wanann bawan Allah.
Saidai ita kaɗai tasan mai zai faru idan har ta amince masa,kuma ya tarar abinda tayiwa uwarsa daga baya.
"Kayi hakuri Junaid,ina sonka amma bazan iya ganin fuskarka a matsayin masoyiba bayan ina koƙarin kashe uwarka"
Daga haka tashiga ɗakinsu tasaka wasu kaya baƙaƙe,riga da wandone amma rigar har ƙasan gwiwarta,jagaye kanta tayi da gyale kafin ta kalli salaha wacce take cin tuwo.
"Salaha hajiya fulani ta aikeni Waje,zan fita koda yadiko lami tazo nemana,kice bazan dade ba"
"Saikin dawo"
Shine kawai abinda tace,daga nan tai hanyar waje.
Tana zuwa kama. Yanda ta faɗa mata suka buɗemata kofah ta wuce.
Wani layi tashiga ta baya,saiga wata mota tana jiranta,shiga tayi aka ja sai bayan gari.
_______________________________
Khariyyah ce a zaune da system a gabanta tana wani aiki,sallama takeji amma ta gagara tashi daga abinda take.
Fadeelah ce tazo wucewa,zata shiga kitchen.
"Yawwa ke zokije ana sallama a waje,kijiyo ko waye"
"Wai anty khairi har yanzu anty khamriyyah bazata dawoba ne?"
"Ke ni rufemin baki,tujarar da kikayiwa deen dazu bata isheki ba saikin karamin wata,akwai wata khamriyyanne bayan wacce kukayi waya da ita,tace muku wani watan zata dawo,me kuma kike so kiji.
Watan gaba zasu gama training ta dawo ƙasar.
Yanzu dai maza jeki kiga wanene yake zuba uwar Sallama tun ɗazu"
"Uhm da ayita cemana masifaffu nida twincy nah(khmariyyah),ashe ke masifarki tana hanyar zuwa,gashinan kin ishi mutane da hayani"
Itadai khairiyyah bata dago kanta ba bare ta kula sabrah,wacce take rike da kofin cornplacks.
"Hmmm ni mai yasa ma na zauna a gida nake aikine,da ina can hankalina kwance"
"Yanzu ma waya riƙeki,tafi mana"
Fadeelah ce tashigo riƙeda wata wasiƙa a hannunta.
Sabrah ta mikawa dayake tafi kusada ita.
"Gashi inji wani,wai daga madeena amaryar Uncle Sadeeq"
"Amarya kuma,an ɗaura auren ne,kajimin ƴar iskar yarinya"
"Wace yarinya kike magana sabrah,wai tukunnama mai aka turo a saƙon?"
"Hmmm wai madeena matar Sadeeq,bariki ji mai tace a ciki.
_assalam antynah ta wucin gadi,ina mai sanar dake cewa kifara sakawa zuciyarki hakurin rashin mijinki daxakiyi,dan daga zarar na nashigo kisani fita zakiyi.
Idan kuma kina ganin zaki iya zan baki wani abu,idan kin isa har kika aikata,nikuma ina mai tabbatar miki da cewar ba bar miki shi halak malak.
A yau an saka ranar aurena dashi,wani watan a daidai wannan lokacin.
Idan har kin isa kuma zaki iya soyayyarki har ta kai haka.
To kizo cikin gidanmu na masarautar katsina ki bayyana cewa kece a ransa,shima kuma ya faɗamin da bakinsa cewa ke yake so bani ba,idan har hakan ta faru,nikuma na barmiki mijinki..........naji ance kina tsoron bayyana kanki ga dangin miji Saboda bakida uban dazaki nuna ko dangin uban,taya wanann zata zama MATAR SADEEQ?_
Ajiye system ɗin khairiyyah tayi,tareda sake karanta wasiƙar da kanta bayan ta fizgeta.
"Kutt kan ubancan,kiji ƴar iskar yarinya,mai take nufi kenan,anya kuwa bata san ke wacece ba"
"Inma tasani zan nuna mata cewar nima ƴace,meye laifina dan bansan iyaye naba khairiyyah,sai tayi dana sanin wannan maganar kuwa,Allah ya kaimu ranar auren"
Cikin kuka ta ƙarisa maganar,tana gama faɗa kuwa ta juya tashige ɗakin data fito daga ciki.
Hmmm zata koma gidan jiya na kuka kenan.........
Taku
_sadi-sakhna_
Ƴar mutan jama'are.
*MABARACIYAH*
_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)
45••46
Duk gari da nepa,amma inda suka nufa da motar babu alamar haske sai duhu ƙirin.
Gidane kaman kango,amma kuma taciki madaidaicine sosai.
Fita deejah tayi a motar,idonta a toshe da glass baƙi,alamar babu mutunci..
Zare glass ɗin idonta tayi tana kallon amal wacce ta jigina da bangon ɗakin tana bacci.
Zama deejah tayi akan kujerar da take gabanta tareda shurarta ta ƙafarta.
"Ke tashi dallah,nan ba gidan ubannaki bane da zaki yimin bacci anan wajen"
Sautin numfashi tayi na alamar wanda yayi wahalallen bacci.
Da sauri ta murtsike tareda ja da baya tana kallon deejah wacce take zaune a gabanta.
"Ke kuma mai kike anan wajen,bakiyi kama da wanda aka ɗaukeba,in aikoki akayi ki ƙwatoni to ki sinceni mu tafi"
Zabga mata mari deejah tayi guda biyu a kowanne gefen kumatunta,kafin ta nuna mata yatsa a baki,alamar tayi shuru da bakinta.
"Yimin shuru,kinga nayi miki kama da wacce zaki dunga magana a haka?"
"To ke wacece bayan yanda na sanki"
"Hmmm banda nashiga gidanku domin neman wani abuba,ke kin isa ko ido ki ɗaga a gabana,bare harki ɗaga hannu ki mareni?
Yanzu zan zartar miki da hukuncin rashin kunyarki kafin gobe nasakeki ki tafi gida.
Idan kuma koda wasa naji zancen a bakinki kokuma kika nuna alama kafin na gama abinda nake,hmmmmm.
Zanga tsakanin keda jalal waye zai iyah riƙe tsoronsa gareni bai bari wani ya ganiba.
Dagake harshi,idan naga kun cigaba da abinda kuke saina murƙusaku."
"Tttto amm.....amma meyasa kike haka ko ku........"
"Shhsh inayine saboda ɗan tausayina daku na wani dalili,yayanku yanajin haushin yanda kuke,nikuma bazan juri ganin yana kallon ƙannensa a haka,shiyasa zan gyaraku ku koma saiti.
Hukuncin dazaki ɗauka kuma yanzu nayimin rashin mutuncine"
Dariyah ta sheƙe da ita tana kallon yanda jikin amal yake rawa.
"Bigggy,zo ki mata bulala ashirin,gobema da safe kiyi mata goma,ki bata abinci taci,nima iyayenta basu barni da yunwa ba.
Sannan wajen misalin ƙarfe goma ku rufe mata fuska ku kaita gefen gidansu.
Nizan koma,idan aka kaiki gidan naje gyaramiki jikinki gobe,saiki sakemin rashin mutunci,zan sake nuna miki yanda akeyi wanda yafi naki"
Daga haka deejah ta mayarda glass ɗinta ta bar ɗakin.
Tun kafin ta fita tafara jiyo ihun deeja biggy tana dukanta.
Sai wajen misalin karfe goma kafin ta koma gidan,bayan tagama wasu uzururrukanta.
Har tashige taga kamar alamar inuwar mutum yana kallon,tsarguwa tayi wanda hakan yasa ta ta nufi wajen.
A hankali take tunkarar wajen,har ta isa inda inuwar take.
Haɗa ido sukayi da junaid wanda shima kallonnata yake.
"Meyasa kika ƙi dawowa da wuri,bayan kinsan akwai wanda bazai iya bacci ba har sai yaga kin dawo gida cikin koshin lafiya?"
"Kayi haƙuri,naje wani wajene amma bazan sake yin daren ba"
Ta faɗa cikin ƙaramar murya,kaman mai son nuna rashin laifinta.
"Amma da bai kamata ka fito yanzu ba,bayan kaima bajin daɗi kake ba"
"Babu komai yanxu zan kwanta,mu ƙwana lafiyah"
Juyawa yayi cikin sanyin jiki,deejah tana kallonsa har ya kule.
Itama nasu bangaren ta nufi,tausayi da kuma soyayyar junaid sun ƙi barin zuciyarta sam.
Washagari kaman misalin karfe goma yanda deejah ta faɗawa su biggy,suka saketa bayan sunyi mata bulalarta guda goma,kuka kam da azaba babu wanda bata shaba.
Since mata hannu suka,sanann suka tafi,na fuskar kuma ita tasaka hannunta dasukayi tsami ta buɗe.
A bakin ƙofar gidannasu ta tsinci kanta,amma tacan nesa da mutane,yanda mutane basu kulada su ba.
Takawa take a hankali jikinta yana rawa har ta isa bakin ƙofar.
Wani dogarine yakula da ita,da sauri ya nufi wajen tareda duddubawa.
"Subhanallah gimbiya Amal ce a wani yanayi,maza ana buƙatar suturtawa domin kaita sashensu"
Wasu dogarawane suka matso da sauri akan tareda da babbar riga,yayinda mata biyu kuma suka kinkimeta zuwa sashen hajiya saratu.
Kan kaceme dawowar tata ya zaga ko ina,wasu na barka wasu na Allah yakyauta.
Salaha ce tazo da gudu ta ƙira deejah akan taje ta taimakawa amal ɗin.
Tun ɗazu suka fadamata sun ajiyeta,ƙiran dama take jira.
Ajiye wayar tayi akan katifarta,tareda tashi ta nufi sashen hajiya saratun
A zaune take madeena a gefenta ɗayan wajen kuma hajiya saratu,dukkansu sai duba jikinta suke suna tambayarta me akayi mata,wanene ya ɗauketa? Amma taƙi cewa komai,sai kuka take kawai kaɗan kaɗan.
"Shikenan yi shuru,munji daɗi ma da babu abinda yasami darajarki,basuyi miki fyaɗeba,ki daina tunawa ya wuce kinji.
Daga yanzu za'a ƙara tsaro idan zaki fita sosai,tunda abin yazama haka,banason sake rasa wani yaron a yanzu"
Gyaran murya deejah tayi,tun ɗazu tana tsaye tana kallonsu.
Suna haɗa ido da amal tayi saurin sunkuyar da kanta,jikinta yafara rawa,duk da tana ƙoƙarin saitawa karsu gane.
Ita deejah ta kulada hakan,shiyasa tayi saurin gyara murya tareda cewa.
"Sannu gimbiya amal ya jikinnaki,sai mukaji kyakykyawan labari na dawowarki,Allah ya ƙara tsarewa,muje in taimaka miki ki gyara jikin,,kafin mutane sufara zuwa"
"Hakane kam,jeki deejah ta taimaka miki ki gyara jikin"
Itadai amal tana son cewa kar a barsu da deejah su kaɗai,amma kuma batada ikon faɗan hakan,dan kamar mala'ika haka take ganinta a yanxu.
Tashi tayi ta bita a baya har suka isa ɗakinnata.
Saurin tsugunnawa amal tayi ganin sun bar kan idon mutane.
"Dan Allah kiyi hakuri,wlh baxan ƙaraba na rantse da......."
"Dakata! Nafi kowa sanin bazaki karaba ai,nima kuma banca zan sake yimiki wani abunba,tashi muje banɗaki na taimaka miki ki gyara jikinki.
Kiyayyata badaku bane dukka,dan haka ki kiyaye shiga gonata daga yau,nagama abinda ya kawoni na tafi"
Da sauri amal ta shiga banɗakin tayi wanka sosai bayan deejah ta haɗa mata ruwan wankan.
Lokacin data fito deejah tana zaune a bakin gadonta tana kallonta.
"Ɗauke nata idon tayi tareda sunkuyawa,in tace zata daina tsoron deejah to tayi ƙarya"
"Ga kayana ɗauki ki saka,nasan dukan baikai yanaki yin komai ba,na saka miki magani a ruwan wankan,nan da nan zai warke"
"Nnnagode"
"Hhhh godiya kike min,daina wannna zancen,kin kusa daina ganina ma a gidannan,watan gobe iya yanzu nabar rayuwarku gabaɗaya"
Daga haka deejah ta fita daga ɗakin bayan ta tabbatar komai ya daidaita.
Kwana uku kenan da dawowar amal,yau kamma har makaranta taje,jikinta da sauƙi sosai.
Ta ɗan rage tsoron deejah yanzu,data san ba komai zatayi mata ba,amma fah ko da ido ta bata umarni yi take babu tsayawa.
Hankalin deejah kwance yanzu,dan yanzu batada matsala da yarima jalal da kuma amal,madeena kuwa ita bashiga shirgin mutane take ba sosai.
Wani satin zata koma makaranta zasu fara jarabawa,tana dawowa kuma za'a yi aurensu da Dec. Sadeeq,dan dama an saka rana.
Hajiya fulani ce ta kalli deejah tareda cewa,
"Na jaki jikina a lokacin da bai wuce wata guda ba,kin samu damar da ba wanda ya samu,yanzu zan tambayeki na ƙarshe,kin gano shi kokuwa baki ganoshi ba"
"Na ganoshi ranki ya dade"
Tashi hajiya fulani tayi ta zauna daga kwance da take.
"Me kika ce,kin ganoshi yaushe"
"Eh naganoshi,zan faɗamiki amma da sharaɗin bazaki kasheshi ba,sannan kuma zakiyi amfani da damarki kicire masa gubar dakika saka a ƙirjinsa.
Idan kikayi haka toh zan nuna miki shi"
"Well well yarjejeniya kikeyi dani,ke wacece?"
"Ba yarjejeniya bace,shiɗin saurayina ne,kuma zan iya komai domin kareshi,kiyi amfani a jikinki ki kareshi nikuma zan faɗamiki a ina yake"
"Nikuma bazan yimasa maganin ba saikin dawomin da akwatina da kika ɗauka,jiya nagane an ɗaukeshi,sannan jalal ne ya ɗauka,kuma nasan ke kika Sakashi.
Abinda yasa bandamu ba saboda nasan duk innda kika kaishi dole zaki dawo dashi,idan kuma kika ƙi toh zaki karni kanki a gabanki"
"Hhh bana tsoron abinda zaki ce Hajiya Fulani,idan na kawo nasan zaki kasheni idan ban kawo bama zaki kasheni,dan haka idan kinaso na dawo miki dashi,to dole saikin yi abinda nace.
"Ki cire aljanin dayake kan jalal wanda yake sakashi yin shaiɗanci,sannan ki cire aljanin dayake yiwa Nana khadeeja aiki akan kishiyoyinta.
Ki ɗauke gubar da take kirjin Junaida,sannan kuma ki nemi a saki ruhin mubarak.
Idan ba hakaba,to bazan taba faɗamiki inda akwatinnan yake ba,idan kika kasheni ma kin rasa har abada."
Zaro ido hajiya fulani tayi tana kallon deejah,batayi zaton yarinyar har takai haka ba.
"Ya akayi kika yi nasara tsallaka kasarnan da akwatin bayan kina nan? Dan inaji a jikina yana nesa sosai"
"Hhhhh wani abokina nabawa dazashi wata ƙasa ya tafi dashi,yana shirin dawowa,zabi yana gareki,ko kiyi abinda nace ya dawo dashi,ko kuma nace ya jefashi a teku a hanyar sa ta dawowa"
Gumine yafara tsatstsafowa hajiya fulani,dan tasan idan babu akwatinnan duk matsayinta da dukiyar data mallaka duk sai sun salwance.
"Shikenan naji zan cire abinda kikace,kafinnan saiki faɗamin a inda yake koh?"
"Uhm wannan ba matsala bace,tunda kin yarda da abinda nace.
Wanda yazo a matsayin mai kulada dawakan Hajiya Saratu,shine ɗanki yarima junaid."
"Yau juma'a bazaiyu aikin yayi yanda ake so ba,amma gobe zan sa a ɗebeku harke dasu zuwa gidana na sirri,inda nake duk wani aiki.
Sannan zan wanke kaina a wajensu,na nuna nice nakeson yin