Author : Auwal sadiya Category : Free Novels Online (Read & Download)
yanda zanyi ne,soyayyar data shayar dani ne tariga ta kama dukkan ilahirin jikina da kuma jijiyoyin jikina,har takai bazan jure rashinta ba,ka taimakeni......."
"Karkasake min wanann roƙon sadeeq,lokaci yayi dazaka dawo hankalinka,Da Detective Khaleel Muhammad kake zance.
Wanda akan aikinsa zai iyah harbe kowa nasa indai akan aikinsa ne,jiya aikin ba a hannuna yake ba,amma yanxu a hannuna yake,dan haka sai inda ƙarfina yaƙare wajen ganin sun kankari hukuncinsu kaman yanda suka manna laifinsu.
Wannan alƙawari ne,shawara ɗayah zan baka shine kanada damar ganinta a yanxu kafin bincikena yafara akanta.
Gargaɗina shine karka barsu su gudu,damin kasan hukuncin matar data gudu koh,kai zan kama a matsayinta"
"An faɗamusu ɗaukar doka a hannu dan anyi maka abu shine daidai,inda hakane da na daɗe da aikata fansata shekara goma da suka wuce"
Ya karisa magana yana cije baki tareda fasa kofin glass ɗin dayake hannunsa.
Jinine ya fara ɗiga akan tiles ɗin,amma ko kaɗan bai kulada shiba,saboda hankalinsa baya kan wajen..
Takan glass ɗin ma yataka yabar wajen.
Zare ido dec sadeeq yayi yana jin furucin Dec. Khaleel ɗin,duk da bayyi mamaki ba na halayyar tasa amma kuma yayi mamakin yanda ya ɗau zafi akan lamarin.
Har ya juya zai koma ɗaki saikuma wata zuciyar tace masa gwara yaje.
Saboda kobai je bama a cikin lokacin da khaleel ta ɗeba masa zasu ƙare,dan tunda yace zai tabbatar anyi musu hukunci to babu mai hanashi.
_____________________
Ɗan wake tasaka a gaba tanaci wanda inno tayi mata,da badan ɗan wake bane,yanda take cikin jimamin rashin mijinta ko kallonsa bazatayi ba,amma tunda sunsan bazata iya jure ganinsa bataci ba shiyasa sukayi mata shi.
Fadeelah ce tashigo da gudu dr nawwarah ta ɗaukosu daga makaranta,saboda kusan inda yanxu take aikine bayan tabar asibitin dr. Bukar.
"Anty Sabrah mijinki yana waje wai fadamki"
Zumbur sabriyyah ta miƙe tareda kallon dr. Nawwarah,da alama neman ta gasgata mata zancen take.
Daga kanta tayi tareda murmushi,da alama kenan gaskiyane..
Yatsun hannunta masu maiƙon mai da yaji ta suɗe tareda ɗaura ɗan kwalin kayanta .
"Har cikin zuciyata inaso yazo,amma fargabar zuwan tafi son zuwan yawa.
Gani nake kamar zai sakeni Anty nawwarah,banason narasashi inasonshi sosai"
Hawayene yafara zaryah akan fuskarta,wanda hakan yasa sauran jikinsu yayi sanyi,ji suke kaman su tariyo baya karsu yaudari Sadeeq ɗin.
Khairiyyah ce tazo da wayah a hannunta suna video call da khamriyyah,a wajen wani ruwa take mai kamada lambu,da alama inaga hostel ɗinsu ne.
"Sabrah gashi inji khamrah,tace ki nutsu karki saka damuwa a ranki,ki cigaba da addu'a sannan ki je kiji da mai yazo"
Karbar wayar tayi a hankali suna kallon juna itada khamriyyan.
"Sabrah nasan zaki iyah,ki dunga saka hakan aranki,kije karki bata masa lokaci,idan wani abu yafaru ki ƙirani zanyi magana dashi kinji"
Ɗaga kai tayi,kaman wata kurmiyah,yau kam surrutu da kwainane sun kau babu su.
Hijabinta ɗauka fuskarnan a kode tayi hanyar kofar gidan,kirjin ta sai dukan tara tara yakeyi
Daga nesa ta hango motar tasa a ɗan gaba gidansu.
Cikin sanyi take tunkararsa kanta a sunkuye har ta isa wajen motar.
Murufin ƙofar takama ta buɗe,amma kuma jura ƙafar zuwa cikin motar shiya gagareta.
"Ki shigo mana,ko anan zaki tsayah"
Dec. Sadeeq ya faɗa cikin dakewa,wanda hakan yaƙara sakata cikin razana.
Sakin murfin motar tayi tareda shigowa kana ta maida shi ta rufe.
Sun ɗau kaman minti shida babu wanda yace komai,shine idonsa kyam yana kallonta,amma ita kam glass ɗin gefenta ta zubawa ido.
"Yaushe kika zama kurmiyah ko gaisuwa babu"
"Iyee na'am uhmmmm......ina wuni,ya hanya"
"Lafiyah kalau,ya gida dasu khairiyyah"
Shuru tayi naya amsa masa ba,dan tasan yayi ne dan tasan ya karanta littafin.
"Mai yasa danazo gida a ranar na tarar bakya nan,shin nabaki izinin tafiyah gidanku ne?"
Maganar ce tazo mata a bazata,wanda hakan yasa tarasa mai zatace masa.
Kafin ta bashi amsa wayar dake kan cinyarta tayi ƙara,tana dauka taga sunan khamriyyah,da kaman bazata dauka ba saikuma ta ɗaga,bata bari tafara magana ba tafara magana ba tace.
"Sabrah ki bashi wayar zamuyi magana!"
"Naji amma kiɗan......"
Kafin tagama magana khamriyyah takashe wayarta tareda ƙiran ta sadeeq ɗin.
Ɗauka yayi domin yaji mai zatace masa.
"Malam Sadeeq barka da rana,kana magana ne da Khamriyyah ƴar uwar matarka Sabriyyah.
Batun abinda ya faru a tsaninmu nasan zakaji babu daɗi,amma kayi haƙuri bamuyi niyyar cutarwa a gareka ba,sannan ina mai tabbatar maka da gaskiyah sabriyyah take zaune dakai,duk da shi auren dawata manufah tayi.
Duk wani laifi da mukayi maka harda na wanda ya fada kansu duk laifina ne,kuma nayi maka alƙawarin ina gama abinda nake zai miƙa kaina gareku,ammma dan allah karkace zaka saki sabriyyah kamaidata ƘARAMAR BAZAWARA,(littafin ƙawata Ummu najma) na roƙeka"
"Naji to idan kingama magiyar,batun kamaki kuma yanzu case ɗin yabar hannuna,kiyi iyah ƙoƙarinki,domin ina mai tabbatar miki kin kusa zuwa hannu"
"Wannan ba abin damuwa bane idan har bazaka yanke alaƙarka da sabriyyya ba,dama ni na shiryah ranar ƙin dillanci"
Kashe wayarta tayi daga haka.(bazata sanja ba dai)ya faɗa aransa.
Kallon sabriyyah yayi wacce tayi zuruzuru.
"Shin waye yacemiki zan sake kine,kowa yake tamin magana akai,dama haka kika ɗauki alaƙarmu,ta warware a abu irin wannan?,bazan rabu dake ba Sabriyyah,saima nayi alƙawarin taimaka miki,amma bazan iyah sake yadda kimin irin wannan ba,kinyi na farko kinyi na ƙarshe,kin yarda?"
Maimakon bashi amsa faɗawa tayi kansa tareda ƙanƙameshi tana shaƙar ƙamshin turarensa wanda tayi mungun kewa.
"Kayi haƙuri mijina farincikina,hakiƙa yanxu nasan kayi nisa a zuciyata da bazan juri rashinka ba sam"
"Sunanki yayi min daɗi SABRIYYAH,mai haƙuri yake nufi,amma tawa sabrar dai a hankali"
Dariyah tasaka tareda haɗe bakinsu waje guda da sauri,dan dama tayi kewarsa ba kaɗanba.
Sake rungumeta yayi bayan yaraba bakinsu,bayajin zai iya rabuwa da ita.
"Duk da nasan bazan aikata daidai ba,amma zanyi iya ƙoƙarina wajen kubutar dake daga tarkon ɗan uwana.
Inasonki sosai sabrahhh!!"
Dec. Sadeeq ya faɗa a cikin zuciyarsa lokacin dayake shafa bayan ta.
Taku
_sadi-sakhna_
Ƴar mutan jama'are.
*MABARACIYAH*
_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)
31••32
Da safe da deejah ta tashi aiki suka hau na wanke wanken da salaha tace ta tayasu.
ita dai har yanzu bataga Hajiyah saratu ba,saboda lokacin da suka zo ranar ta tafi gidansu masarautar Gombe,Babanta wanda shine wazirin garin ya rasu,yayanta ya hau,yau ake bikin naɗashi da kuma rabon gado.
Yau zata dawo shiyasa su salaha ma da basa girki yau zasu taya su lami.
Bayan sun gama wanke wanken ma wani aikin daban suka fara na gyara kayan miyah.
Deejah ce ta kalli salaha tareda cewa.
"Masarautar nan ta bani mamaki,banga ɗa ko guda ɗayaba wanda yake ɗan sarki a gidannan tunda na shigo,bayan an san gidan sarauta da yara"
"Akwai yara duk da ba sosaiba,abubuwan daya faru shekaru goma da huɗu da suka wuce sune suka haddasa rashin wasu daga yaran gidan.
Hajiya Fulani ƴaƴanta dama huɗune,babban shine Yarima Junaid,a ranar da abin yafaru aka nemeshi ƙasa da sama aka rasa,wasu suna cewa ma ya mutu,wasu kuma sunce mahaifinsa ne ya turashi karatu ƙasar waje,amma dai kowa yana zaton ya mutu ɗinne.
Sai mai binsa Nana Khadija,itakuma tayi aure a masarautar zaria,da yayanta huɗu.
Na uku shine yarima mubarak,wanda tun a ranar ya faɗi har yau bai sake motsawa ba, kuma da ransa.
Ɗan autanta shine Jalal,hmmm faɗan nace miki halayyarsa,karki so ki tona ma,yarone mai ji da kyau sarauta sangarta da kuma ƙururciyah,duk abinda zai miki a gidannan babu wanda zai kallah bare ya ɗau mataki,ciki kuwa harda mai martaba.
Zaman lafiyarki shine karki shiga harkarsa sam.
Saikuma ƴaƴan Hajiya Saratu,ita ƴaƴanta guda ukune kuma dukka mata ne sai autanta shine namiji,daga Madeena sai kuma mai sunan mahaifiyar sarki wato Ruƙayya,ana cemata Amal.
Ita madeena tana makaranta a Buk,aji biyu,ita kuma Amal tana secondry ss2.
Saikuma ɗan autanta Abdussalam mai shekara goma sha biyar,yana jss 3.
Dukkansu suna EMIRATE NURSERY,PRIMARY AND SECONDRY SCHOOL.
Shida Amal tare suka tafi da hajiya saratu masarautar Gombe,garin kakanninsu kenan,yau idan suka dawo zaki gansu"
"Uhm naji batunki,amma baki faɗamin ita Hajiya fulani daga wane gari takeba,ko kuma wace masarauta"
"Ita ba jinin sarauta bace,saidai mahaifinta babban malamine kuma hamshaƙin mai kuɗi a garin maiduguri,suɗin ainihin ƴan shuwa ne masuji da kyau da kuma kuɗi.
Naji ance a Dubai suka haɗu da sarki lokacin yana karatu a can,yana gabanta a makarantar,acan suka zauna bayan anyi aurensu har suka haifi Junaid a can.
Jijjiga kai deejah tayi tana ajiye dukkan wani silin bayani dataji daga bakin salahan.
Sai wajen ƙarfe ɗaya na rana tukunna suka gama shirya komai.
Warwas deejah tayi a ɗakinnasu tana sauke ajiyar zuciya,dan daga gani bata saba irin aikin ba yau ya kamata.
"Kai wlh dolema nagama abinda ya kawoni natafi,irin wannan wahala"
Ita kaɗai take mitar,babu kowa a wajen bare ya tayata.
Daga bayane salaha tazo musu da abinci sakuci ,kafi Sukayi sallah.
Cikin ɗan bacci daya ɗauketa ta jiyo hayaniyar algaita da kuma ƙarar motoci.
Tashi tayi kana ta leƙa window,wanda yayi dadai da shigowar motoci guda shida cikin farfajiyar gidan.
"Inaga tawagar Hajiya saratu ne,ta dawo kenan"
Deejah ta faɗa a ranta.
Tashi tayi ta fito daga ɗakin tareda tsayawa a corridor ɗin shiga sashen hajiya saratun.
Fitowa tayi daga mota zata shiga cikin gidan,Bakace ba sosai ba kuma katuwa,amma hakan bai hana mutum yaga kyan taba,murmushi take suna gaisawa dasu yadiko lami suna mata sannu.
Tunda daga nan zakaga fahimtar juna da kyautatawar datayiwa ma'aikatan nata.
Su amal ne ke binta a baya,ita tana sanye da wani yaɗi maroon doguwar riga,shikuma Abdussalam ƙananan kayane a jikinsa,dukkan yaran kuma fararene,saikuma suka ɗauko kamanninta,ubansu mai martaba suka iyo a farin fata.
Wayace a hannunta tana dannawa tana yatsina fuska,irinnasu na ƴan masu iko,su yadiko lami sai gaisheta suke suna washe baki,amma ko kallonsu batayi ba,shima Abdul ɗin bai kulasu ba ya wuce,kaman wanda suke jin haushinsu.
Takaicine ya shaƙi deejah datake gefe,batasan lokacin data ciji fatar bakinta ba.
Dawakai aka shigo dasu uku da wani matashi mai kuladasu,yana ɗaya daga cikin gadonta da aka raba musu.
Bayan komai ya lafane yadiko lami ta shigo ɗakin su deejan.
"Ke deejah zo muje ki gaida Hajiya tadawo daga gidansu"
Toh kawai tace tareda bin bayan ta.
Koba komai dama tanda buƙatar ganin wajen sosai.
Falo na biyu suka shiga bayan na daya wanda tun farkon zuwanta tasanshi.
Waya take tana zaune akan kujera,kan amal kuma yana cinyartata tana wani turjewa,wai sai an bata mota tafita wajen ƙawayenta tacemusu ta dawo.
Sauke wayar tayi bayan tayi sallama tareda kallon amal ɗin.
"Ke banason sakarci fah Amal,babanku bayason wannan fitar akai akai,hakanma ki ɗauki mota,idan zakije driver ha kaiki toh,ina kuma bazaki je ba karki ƙara yimin maganar.
Dirvern mu ya tafi garinsu,kije saleem da muka taho dashi drivern su ummah a can ya kaiki,tunda yace yasan garin"
Tashi tayi tana turjewa ta fice a falon duk abinda suke deejah ta zuba musu ido tana kallon ikon allah.
"Amm Lami mai kikace ma"
"Eh dama hajiya yarinya ce nazo da itah,tanason aiki a nanne sai muka taho tare"
"Ayyah ba laifi ai,yafi zaman banza,bata iya gaisuwa bane?"
Sunkutarta lami tayi tana haɗe fuskaa,wanda hakan yasa deejah murmushi tareda cewa
"Ranki ya daɗe baki bani damar gaisuwar bane,ina jiran ki bani izini ne,.....ina wuni ya hanya,an dawo kalau?".
Ta fada tareda durƙusawa a kasan carpet ɗin.
Mamaki abin yabawa su hajiya saratu,amsa gaisuwar tayi cikin sake murya kafin deejah ta koma ta zauna.
"Sannunki da zuwa,dama Amal tana neman mai kulada sashenta,idan zaki iya sai ki dunga gyara mata,dan naganki kinada tsafta da kuma hankali,da alama zaku shiryah"
Daga kai deejah tayi tareda cewa.
"Ba matsala zan iya inshaallah"
Kallon ta yadiko lami tayi da mamaki,ba itace tace bazata yi aiki anan wajen ba,mai kuma yakawo ta wajen.
_______________
Wani ne zaune akan bakin mota ya naɗe hannu sai zuba surutu yake ga wanda yake sunkuye yana ɗaure dawaki a rumfarsu.
Shina tsugunnen kaɗan kaɗan yake bawa nakan motar amsa,kana ganin fuskarsa kasan surutun ya isheshi,sannan kuma bai saba dashi ba,koƙari kawai yake.
"Wai eemran bakajin mai nake cewa ne?"
"Ina jinka mana mai kake so nace,nida yanxu nazo masarautar taya zansan mai kake faɗa,kaida kasha zuwa bayaune zuwanka na farko ba"
"Hakane kam nasha zuwa wajennan sosai,amma nayi mamaki da aka cemaka ka dawo aiki daga gombe zuwa nan kuma ka yarda"
"Aikin kuɗi nake a can ma ba garin mu bane,nan ma kuma ba garinmj bane aikin kuɗi zanyi,menene banbanci a ciki?"
"Ahah babu kam,idan ka gama gyara musu muhallin zamu ɗan zaga gari?"
"Ahah bazan je ba,inaso na ɗan huta kafin gobe na nemo musu abinci"
Amal ce ta tunkaro inda suke tareda sauƙe idonta akan saleem ɗin,hakanne yasa yabada hankalinsa gareta,tareda barin zancen da suke da eemaran.
"Ran gimbiya ya daɗe,ƴar sarauta jinin sarauta,gaba salama baya salama,tafatan gajiyar tafiya tabi jiki"
Ya faɗa yana ɗaga hannu.
Wani murmushin jin daɗin yabon tayi masa tareda kallon eemran wanda ko ɗagowa daga aikin dayake bayyi ba bare ya kalleta.
"Wannnan kuma fah,shiba baya gaisuwa ne yayi banza da mutane"
"Gimbiya kinsan sabone a gidan,shine mai kulada dawakan da aka taho dashi"
"Kuma shine dan yana sabo yafi ƙarfin gaisuwa,koba komai ai a ƙasan mu yake"
Miƙewa yayi daga wajen dawakan tareda kallon saleem wanda har yanzu yake kan motar.
"Saleem ni zan shiga ciki,saina ganka"
Da yazo wucewa ma ko kallon amal ɗin bayyi ba kaman an ajiye masa dutsi.
Tsuke baki tayi tana binsa da kallo,kyakykyawane ajin ƙarshe,da badan wahalar duniya da kuma halin rashi ba,bayyi kama da wanda zai kulada dawakai ba.
Saleem ne ya kaɗa mata makulli kafin ta dawo daga kallonsa.
"Ɗan rainin hankaline,shib kowa ba amma yake nunamin taƙama"
"Ki rabu dashi,nida nasanshi bada daɗewa bama haka nake zama dashi"
"Aikuwa saina koyamasa hankali"
"Bazaki iyaba,kibar zaka cikin gashinta gimbiyar garin katsina"
"Okay manta kawai,dama anguwa zaka kaini,idi bayannan ya tafi gidansu,barina je na shirya nan da minti talatin"
"An gama ranki ya daɗe"
Juyawa tayi ta bar wajen tana jujjuya ɗan karamin kunkuminta,a dole sai an ganshi ko bayanan sosai.
Duk abinda suke akan idon deejah,wacce tazo wucewa zata koma muhallinsu daga wajen hajiya saratu,murmushi tayi ganin abinda wanda aka ƙira da eemran yayi wa Amal.
Haka kawai taji ya burgeta da halayyarsa ta ƙin ɗaukar raini,dan ta tsani ganin mutum yana ƙasƙanta kansa dan bashida komai,ya manta darajar da allah yayishi tayinsa mutum kuma iri ɗaya da wanda yake kwantar dakai garesu.
__________________
"Ke zainabu kin tabbatar watace a cikin gidannan ta faɗamiki cewar maganin ya baci,ba malaminne ya faɗa miki ba"
"Eh ranki ya daɗe na rantse da allah watace tafaɗamin,kuma a gidannan take,saboda na gasgata zargin hakan yasa na je ga malamin,shima kuma haka ya faɗamin.
Hatta wanda ya bata maganin saida ta faɗamin,kuma bayanin dadai yayi ta wanda Malam Malafah ya faɗamin"
Numfasawa Fulani Ateeka tayi tareda ƙara miƙe jajayen kafafunta wanda wasu mata guda uku suke matsa mata.
"In hakane zanso naga wacece wanann yarinyar,indai a ranar data shigo gidannan zata iya faɗan wanda ya bata magani bayan ba mutum bane,to lallai tanada baiwa a jikinta wanda muke buƙatarta.
Ki tabbatar kin kawomin ita nan naganta,sannan naji mai take takama dashi,duk da nasan itaɗin bakomai bace a kaina"
"Angama saurauniyar Katsina"
"Mtsww wani banza mulkin katsina mai za'ayi dashi,nida nake mulkar tsibiri nawa na kaina a ƙasar Australia mai zanyi da wani takurarrnen mulkinnan,duk da haka kuma matsayinna na sarauniya ko ban karba ba babu wata mahaluƙiyar da take doron duniyar nan dazata iyah karba,walau aljanace ko mutum,saidai idan bana numfashi"
Ƙirari matan wajen suka fara mata,wanda hakan yaƙara kambama mata kai.
"Ki ƙiramin ita da daddare,dan gobe nakeson barin kasar,zafinta ya isheni haka,akwai meeting danake dashi"
Cikin sauri jiki na rawa zee-zee wacce sunanta zainabu ta tashi tana cewa.
"Angama ranki ya daɗe,zan cika aiki yanda kike sonsa,da sannu Yarima mubarak zai tashi da kafafuwansa"
Deejah a tafito daga banɗakin amal ta wanke mata,sa'arta ɗaya ma babu datti sosai,da batajin zata iyah.
A falon hajiyah saratun ta haɗu da Ita amal ɗin ta dawo daga anguwar wajen magriba.
"Ke makikeyi a dakina kuma batarda izini na ba"
"Ki tambayi hajiya zata faɗamiki dalilin shigata ɗakin"
Deejah tana gama magana Amal ta ɗauketa da mari.
"Har ina miki magana mai kike a dakina kina cemin wai na tambayi hajiya,ni ban isa na tambayeki ba kenan"
Jakadiya ce tashigo falon,da alama sarki ne ya aikota wajen hajiya saratu.
"Uwa uwar sarakai mai yafaru naga kina fushi?"
"Banni jakadiya,wanann yar rainin hankalince take gayamin magana mana"
Kallon deejah jakadiya tayi tareda ta'be baki.
"Ke kuma wane gangancinne ya ɗebeki da dayin hakan,hala ke sabuwa ce bakisan gidan sarauta ba"
Daga haka ta shige turakar hajiha saratun bayan ta nemi iso.
Kallon amal deejah take tareda dafe kuncinta,babban abin takaicin tasan tafi amal nesa ba kusaba,amma kuma ta daga hannu ta mareta dan rashin tarbiyyah.
Hmm kawai tace tareda gocewa ta gefenta ta bar wajen.
A hanyar komawa sashensu ne tana cikin duniyar tunani kawai ji tayi ta bugi mutum a gabanta.
Saurin razana tayi tareda ɗagowa idonta dan ganin waye.
Zee-zee ce take murza goshinta tareda cewa.
"Ina kike gani haka,tun dazu nake gabanki amma baki ganni ba"
"Yi hakuri,amma mai kike a sashennan hakanma dare ya fara"
"Wajenki nazo,kin tuna maganar da mukayi jiya,har kike fadamin magani baci?"
"Eh na tuna menene"
"To dakika fadamin ban yadda dake ba,saina tafi wajen mai maganin daya bayar,abinda kika faɗamin shima haka ya faɗa,shine abin yaƙi barin raina har saida na faɗawa Hajiya fulani.
Shine tace na faɗamiki tana nemanki da daddarennnan,tanaso taji wace irin baiwa kike ɗauke da ita"
"Nikuma,ba wata baiwa,kawai naganshi ne,shiyasa na faɗamiki"
"To idan ba baiwa bace nima na ganshi mana ko wani a cikin gidan?,dan allah ke wacece daga ina kika zo"
Ɗaure fuska deejah tayi ganin yanda ta takura mata,dama kuma ga bakincikin abinda amal tayi maga,tunani take yanda zata koyawa yarinyar hankali ,sai ita kuma wannan ta bayyana da nata buƙatar,ga kuma wasu tambayoyi wanda batada da dalilin amsa mata su.
"Shikenan kice ina zuwa idan nayi sallah"
"Lallaima yarinyar nan,har mai girma sarauniyar katsina zakisa tana jiranki a turakarta?"
"Eh idan bazata jiraba,shikuma allah daya haliccetane zai jirani kenan saina gama da ita kafin nazo nayi sallahr?"
Daga haka tawuce tabar zee-zee a tsaye yauma da mamaki.
Itakuwa deejah tasan dama dole zata nemeta idan zee-zee tabata labari,saboda zatayi zaton wani abin hajiya saratu take ƙullamata da ita,to duk yanda zatayi zatayi domin ganin ta maidata sashenta.
Duk da deejah tasan hajiya fulani tana jiranta amma saida tagama abinda zatayi kafin taje shashennata.
Wasu body guard ne bakin ƙofar sunsha baƙaƙen kaya,kana ganinsu kasan ba a nan ta samosu ba.
Ƙiƙama sukayi babu wanda yakeda yunƙurin barta ta shiga wajen.
Zee-zee ce tafito tazo shiga sashen taga deejah a tsaye.
"Lahh ku kubarta tashiga baƙuwar hajiya ce,ita ta bata damar zuwa."
Matsamasu sukayi itada deejah suka wuce,batareda sunce komai ba.
Duk wanda yayi yunƙurin haɗa shashen Hajiya fulani dana hajiya