MABARACIYAH Daga Bara Zuwa Firgitar Masu Iko by Auwal sadiya

Author :  Auwal sadiya Category :  Free Novels Online (Read & Download)

Chapter   32 / 33

93K to 96K   out of 96.8K words

wasu shekarune shazali ya koma garin daura da zama,a nan kam ban zauna a wajensa,saina tafi inda nake ƙira da gidanmu,wato wajen su sabriyyah.
Sunyi murna sosai da ganina,anan kuma naji abinda ya faru da maryam,banyi mamaki ba dannasan bai wuce aikin saifuddeen ba,zai aikata sosai.
Hakan bai isa ba ya biyo gida yaimana cin mutunci,tareda ketawa anty juwairah zarafi.
A lokacin banso su sabriyyah susan wannan ɗaukar fansar ba,saidai daga yanayin halin dasuka shiga irinnawa,yasa naja ragamar ɗaukar fansa,domin su samu salama a ransu,wanda suka aikata hakan kuma suma su samu hukuncinsu daidai da abinda suka aikata.
Bani na tashi komawa garin Kankia ba,sai lokacin danayi cuku cuku ogah sadeeq ya turani garin aiki,dan dama hakannne burina.
Abinda na gani ne ya girgizani sosai,hajiyah Gaji tayi kuɗi sosai,yayuna kuma yahuza da yusuf ta maidasu tamkar karnuka,a cewar ta wai sonsu take bayan iyayenmu sun rasu,ta sake musu kuɗi suna yanda suka so,shaye shaye da kuma aikin tantiranci,kowa zai zaginsu yake a gari.
Wannan abin yafimin komai ciwo daga cikin abinda akayi min,gwanda iyayen mu su kashesu akayi,ba ɗauke su daga hanyar gaskiya ba.
Yayanta mata su ta ɗorasu akan harkar kasuwanci,sukuma yayuna kashewar kawai ta nuna musu,tareda bata musu gobensu.
Amma dayake Allah ba Azzalumi bane,sai ya zamo jikokinta dukka yawanci hanyar dasuka bi kenan,abin yana damunta amma kuma takasa yin komai akai.
Tsara kamen ƴan iskan garin na shiryah,batareda na faɗamusu nice ba na kawosu garin katsina wajen horon matasa shashashu,har yanzu suna ciki,ina zuwa musu ziyara lokaci zuwa lokaci,tun basu san wacece ba har na sanar dasu.
A nan ne sukayi kukan nadama na abinda suka faɗa ciki,saidai har yanzu ban bada izinin a sakesuba,dan har yanzu ƙwayar bata gama sakinsu ba.
Hmm Hajiya gaji kuwa ta bayan fage na biyo mata,malamminta dayake mata aiki,take yiwa mutane sharri,da kuma zalunci,na ɗauke dukka yayansa,sannan nasa akayi masa dukan kawo wuƙa.
Zabi na bashi akan yayi mata hukuncin dadai yanda yake ganin yayi daidai da ita,na kashe mutane dayawa,bana ma buƙatar itama nata jinin ya hau kan hannuna,dan bata kai ma matsayin hakan ba.
A daren ya ɗauki alkalumansa ya turamata baƙin sammu.
Manyan ƙuraje suka cika jikinta ta ko ina,ga hauka tanayi.. Bayan zama a cikin wanann azabar kuma,a sati na gaba gabobin jikinta sukayi ta gundulewa suna faɗuwa.
Mutuwar walaƙanci tayi da Allah wadai,sannan kuma babu wanda ya je kan gawarta,jikokinta ne ƴan iskan suka je suka binneta.
(Labarin abinda tayiwa Hajiya fulani da kuma su dr. Bukar tayi,har zuwa lokacin da Tazo gaban Alƙalin).............


____________________________

Numfasawa tayi bayan ta gama labarin kafin ta kalli idanuwan mutanen wajen,zuwa lokacin fuskarta tayi shabe shabe da hawaye,saboda fama tsohon gyambon daya warke.

"Wannan shine abinda yafaru a cikin rayuwata,kama daga haihuwa ta ,kashe iyayena,haɗuwata da su sabriyyah,kashe wanda sukayi min haka,bayan najira kotu taƙi daukar mataki,haɗuwata da iyalan gidan sarautar katsina,harma da soyayyarmu da ɗan gidan.
Sannan inaso mutane wajenanan su sani,ko kaɗan bana nadamar abinda na aikatawa wannan mutane,dan haka a shirye nake naji hukuncina daga wajen alƙali"
Shuru wajen yayi kaman babu mutane,kowa jikinsa yayi sanyi jin labarin abinda khamriyyah ta faɗa.
Masu kuka sunayi,masu tausayawa sunayi,haka masu mamaki da shiga ruɗu.
Alƙaline yayi gyaran murya tareda cewa.
"Uhm uhm munji abinda kika ce,to shin kinada shaidu akan abinda kika faɗa,idan bakida shi kotu zata yanke miki hukuncin rai da rai a gidan yari"
"Hmmm shaidu kake buƙata daga labarina,dan kaji ban ambaci sunanka a masu laifi ba a ciki? Duk wajennan kafi kowa sanin abinda na faɗa gaskiyane.
Sannan idan naga dama bazan tsayah a gabanka na buƙaci hukunci daga alƙali irinka ba,karka manta duk rashin adalcin da akayi kaine ka zartar dashi.
Batun ɗaurin rai da rai kuma bana buƙata,wata shida kawai zanyi,badan komai ba saboda nasan an min hukunci,kuma mai shirin yi a gaba shima karya tafi haka batareda hukunci ba.
Idan kuma kanaganin abinda kaga dama nima zakamin,to zan bankaɗa mummunan lafinka kaima,sannan duk manyan garinnan dana gani a wannan gidan tsafin saina faɗi sunansu ɗaya bayan ɗaya a wajennan,dan kar nake kallonsu,kuma ba tsoronsu nake ba.
Na baka minti talatin kayi tunani"
Shuru nan ma kowa yayi,saidai daga ganin idonta kasan ba tsoro take ba,kuma zata aikata abinda tayi niyyah.
Ko minti talatin ɗin ba ayi ba,saiga ƙiran daga babbar gwamnati akan a saketa yanzu nan,inkuma hukuncin takeso,to a tabbatar babu abinda ya faru da ita har zuwa ta fito,sannna ranar fitowar a shiryah gagarumar tarbarta.
Wani murmushi khamriyyah tayi tareda kallon alƙalin tace.
"Hmmm ƙasarmu najeriyah da baci,Allah ne kaɗai zai mana gyara a cikinta,ka bugamin takardar laifina kawai,su kuma wanda suke bayana ka wanke sunan su tass,su koma gida cikin koshin lafiya.
Sannan kaman yanda nace,ka shirya bada order a fitarni nan da ƙarshen shekara"
Ihune ya kaure a cikin kotun,lokacin da alƙali ya zartarwa deejah kuma khamriyyah hukuncin data buƙata.
Wasu suna baza'a ɗaureta ba wasu kuma sunata zagin manyan ƙasa da abinda suke a ƙasar.
Kafin su khamriyyah su fito daga kotun labarinta har ya zaga ko ina,mutane sai cewa suke tayi daidai,musamman da suka gano gaskiya ta faɗa.
Fitowa akayi da ita da ankwa a hannunta,mutane sun cika hanyar da ƙyar ake wuce wa da ita..
Dec. Sadeeq ta gani shida khaleel a tsaye,kana ganinsa kamar an yi masa mutuwa.
Excuse ta karba a wajen ƴan sandan ta nufi inda suke.
A gabansa ta tsayah,tana zuba masa ido shima yana zubamata,zubewa tayi akan gwiwoyinta tareda sakin kukan da ita kanta rabonta da irinsa ta manta..
"Kayi haƙuri ka yafemin khaleel,nayi hakane saboda shiyafi dacewa,idan banyi haka ba hankalina a ƙarshe bazai kwanta ba.
Ka yafemin fatali danayi da taimkonka a gareni kayi........"
Ɗagota yayi shima yana ƙoƙarin maida hawayen idonsa.
"Sai yaushe zaki daina wannan bada haƙurin,bayan kinsan baki taba burgeni ba irinna yau,kinyi abinda maza ma ba lallai su iya ba,ke jajirtacciyah ce kuma majingina khamriyyyah,Allah yabaki sa'a rayuwarki ta gaba,yasa hankalinki ya kwanta kiyi rayuwar farinciki.
Zan dunga zuwa koyaushe ina miki ziyara,har zuwa lokacin dazaki dawo gareni,kisa a ranki kowa yana tareda ke"
Jijjiga kai take tana murmushi hawaye bai daina zuba a kan kumatunta ba.
Su fadeelah ta hango a gefe tareda su sabriyyan wanda suma kukan suke.
"Haba my family,menene kuma na kukan,babu abinda zai faru,ku ɗauka naje karatu kaman koyau she,kunji twin ɗina,mommy zata dawo gareku"
Rungumesu tayi a jikinta tana sauraren ƙaramar muryarsu ta kuka.
Miƙewa tayi tsaye tareda karbar su sultan suma a hannun amal.
"Dukka zanyi missing ɗinku kuma,Amal kiyi haƙuri da abinda na miki kinji,banyi miki dan inajin haushinki ba,nayi mikine saboda ki gyara halinki,sannan wannan takardar nine nasa kawarki ta zugaki akan ki tura,saboda a dakatar da auren sadeeq da madeena.
Abubuwa dayawa nayisu batareda saninku ba,duk ku yafemin.
Ku kulada kanku sosai,ke sabrah ki kwantar da hankali a gidan mijinki,kuma ƴan matana kanna dawo naji kyakykyawan labari kunji"
Dukkansu sakin kuka sukayi,danji suke kaman tana musu wasiyyah.
"Khamriyyah meyasa?"
"Saboda banason kusha wahalar danasha,kokum labarinna ya bata muku rai,kudaina wannan maganar ya wuce haka"
Mahaifiyar saifuddeen ta nufo wajen itada wata yarinya mai kamada su fadeelah,da alama kanwarsa ce.
Sunkuyar dakai matar tayi tana kallon su fadeela..
"Tabbas kowa ya gansu yaga jininmu yarannnan,zanceki babu ƙarya a ciki,kuma kaman yanda kika faɗa zayyi nadamar abinda yayi yaran mutane tabbas yayi.
Dan yanxu mu shiya turoni nabaki haƙuri akan abinda yayi muku,dan bashida ikon fuskantarku a yanzu,yara kuma komin sonsa daganinsu dole zai haƙura,kuma zancenki haƙƙun saidai yagani a wajen wasu"
Tana maganar muryarta tana rawa ,itama kana ganin danasanin sangarta yaron datayi.
"Babu komai hajiya,dama wanda yayi ba kyau dole zaiga ba kyau,naji dadi daya gane gaskiyah,koba komai shiɗin ubansune ko an so ko an ƙi,sannan kice masa dukiyarsa nina ɗebe ta,diyyar hajja da kuma anty zuwairah,sannan kuma nayi amfani da sauran a rayuwar ƴaƴansa"
"Zaiji wannan saƙon,inshallah zaki ganmu ranar da kika fito daga gidan yari"
Iyalan sauran wanda abin yashefesune suma suka zo inda khamriyyah take,harda mrs. Shehu wacce ta mareta,kana ganinta yanzu kasan cikin kunya take dakuma tirrr da halin mijinnata,tana ta yaba halinsa,batasani ba ashe shiɗin makashine,kuma masifah a cikin al'ummah.
Haka ma dr. Bukar,a ranar aka rufe asibitinsa da kuma wasu abubuwansa,domin kwakwkwaran bincike.
Bayan an gama neman yafe yafenne khamriyyah ta juya zuwa motar daza'a tafi da ita,mutane kowa na faɗin albarkacin bakinsa.
Suma su khaleel mota suka shiga zuwa gida,haƙika shari'ar tazo masa a bazata ba yanda ya tsammata,amma hakan ma yayi,koba komai yaji farinciki da kwanciyar hankali daya gano tsagwaron murna jinjina a idon mutanen wajen,hakan ya ƙara tabbatar masa da masoyiyar tasa ta musammance.....

Muhaɗu a chapter ta gaba wanda kuma itace ta ƙarshe inshaallah.......





Taku
_sadi-sakhna_
Ƴar mutan jama'are.








*MABARACIYAH*


_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)






65••66






_Bayan wata shida_

Wani mutum ne ya nufi taron mata guda shida suna zaune da uniform ɗin prison a jikinsu..
Khamriyyah ce a tsakanin su tana ɗoramusu karatu,wasu acikinsu sun fita ma a haife.
Gaisawa sukayi kafin yace.
"Madam shugaba yana ƙiranki a office,yaune ranar tafiyarki,har na kawo takarda daga sama,da kuma mota da kaya na rakaki gida"
Ɗaga masa kai kawai tayi batareda tajiyo ta kalleshi ba,tundaga yanayin fuskar matan zaka san cewa sun saba da ita sosai,basa son fitarta daga wajen,saidai hakan shine mafi alkhairi ga duk wanda yashiga irin wannnan gidan.
Tashi tayi tareda yimusu murmushi.
"Karku damu yan uwa,zan dunga kawo muku ziyara har ku fita,idan kun fita kuma ku taho gareni,zan taimaka muku idan inada dama"
Ɗaga kai sukayi,daga haka ta bar wajen zuwa inda mutumin yabi..
Cike ciken takarda akayi a office ɗin,daga nan shugaban ya ɗago kansa ya kalleta.
"Madam yau kin gama wa'adinki na zama a gidannan,an wanke sunanki daga dukkan wani laifi da kika aikata,yanzu kina da damar dazaki koma ga dankinki domin kafa sabuwar rayuwa tareda su"
"Nagode sir"
"Babu komai,yanxu ki shiga nan lubna zata baki kaya ki saka,daga nan familynki suna jiranki a waje"
Ɗaga kai khamriyyah tayi tareda bin inda ya nuna mata da yatsa.
Wanka tayi da sabulu mai kyau ba irin wanda suke amfani dashi ba a banɗakin,kafin ta fito ta saka kayan ta taimakon matar da ya ƙira da lubanan.
Doguwar rigace baƙa sai gyalen shikuma ja,irin adon rigar.
Kayan sunyi mata kyau sosai,dan ma tayi looosing farinta ba kaman da ba.
Fitowa sukayi tareda matar zuwa bakin get ɗin,inda take hango motocin masarautar katsina a wajen.
A hankali take takawa kirjinta yana bada sauti mai ƙarfi,rabonta da kasancewa a waje,tun wata shida baya,ko zuwa akayi mata saidai ta kallesu ta bayan labule..
Da ɗaɗdai da ɗaɗɗai mutanen cikin motocin suka fara fitowa.
Sabriyyah,khairiyyah,khaleel,sadeeq,inno,jalal,amal,madeena,hajiyah saratu,hajiyah deejah,meena,yah yusuf da yah yahuza,maryam,farida,balki,doc nawwarah,twins ɗinta(fadeelah,fadeel,sultan,sultana),saifuddeen da ahalinsa dukka.
Su biggy,da wasu dukka mutane daban.
Kuka khamriyyah ta saka tareda zubewa a ƙasa,lokacin dataga ɗumbin mutanen da suka zo taryarta.
Su khairi ne suka rugo da gudu tareda rungumeta,da a tsaye take da sai sun jefar da ita.
Dariyah suka sa ganin suma abinda yabasu dariyah,hakika sunyi missing ɗin ta sosai,tareda jiran sauraran zuwan wannan ranar.
Idonta ta ɗaga ta sauƙe akan khaleel,wanda ya ɗan rame yayi duhu,bayyi kama da wanda yayi jinya ba,tasan bazai wuce tunanin halin da take cikiba.
Idonta tasake sauƙewa akan yayunnata gudan jininta,wanda suke tsaye cikin nutsuwa kaman basuba,murmushi suke yimata mai cikeda nuna alamar nasara a ceto hankalinsu.
Wajen da khaleel yake ta nufah tana sake masa murmushi,amma sabanin haka ɗan turbune fuska yayi,bazata ce kai tsaye da ita yake ba,tasan bai wuce tace ita hankalinta kwance ba,bata missing ɗinsa,dan abinda yake faɗa kenann kullum idan ya ƙira wayah an bata.
Wajen su yah yahuza ta nufa tareda rungumesu batareda tace komai ba.
Suma sakata sukayi a jikinsu suna jinjina ƙoƙarint,a,da kuma tausayawa halinda tashiga,domin gani suke kaman komai laifinsu ne,da suka kasa kulada ita,har wahalar rayuwa tayi mata yawa.Saidai alhamdulillah yanzu komai yayi daidai.
Dukkan su garzayawa akayi fadar,inda aka shiryah gagarumin biki na taryarta zuwa gida..
A ranar khamriyyha taga soyayyar dasuke mata ya wuce yanda take mamaki,a tunaninta da ƴayan hajiyah fulani ateeka zasu tsaneta idan suka gano abinda tayiwa mahaifiyarsu,ga mamakinta ma sai haƙuri suke bata tareda roƙar ta manta abinda ya faru.
Tunda suka dawo bata samu kona mintin ɗaya ta zauna ba,mutanen datayi rayuwa dasu harda na makarantarsu sai zuwa ake mata barka da fitowa,harda iyalan wanda tayiwa tsiyah,sune yanzu a cikin kunya,dan wasu daƙyar suke haɗa ido da ita.
Dare mahutar bawa,saida magriba tayi kafin aka fara raguwa da mutane,wasu sai cewa suke sai wani sati kuma,bata gane mai suke nufi ba,itama kuma bata samu lokacin tambayarba.
Ɗakinsu ta shiga tana yada kai na gajiyah.
Kayan jikinta ta cire,wani yadi mai tsadar gaske,wanda sukayi anko da dukkan matan gidan,walima akayi wacce ta kayatar sosai.
Banɗaki ta wuce tasakewa kanta ruwa mai sanyi,saida ta tabbatar sanyin ya ratsata kafin tashiga bahon wanka ta gasa jikinta sosai.
Lokacin data fito duk an idar da sallahr magriba,dan haka haɗawa tayi da isah tayi,wacce ta taddata tana addu'a.
Amal ce tashigo hannunta ɗauke da kwanon abinci ta ajiyemata.
"Anty ga abinci,nasan baki samu kinci dazu da yawa ba"
"Hmm kaman kuwa kin sani,duk jikina a mace yake"
"Tabbb gashi kuwa yah khaleel da ina shigowa yace yana jiranki a wajen dakuka saba haɗuwa"
Wata kasalalliyar ajiyar zuwa khamriyyah tasake tareda ɗaga kanta kawai,yazatayi tasan bata isa kawo masa uzurin bazai samu ganinta ba,bayan tafi kowa sanin yanda ya ƙagu ta dawo gareshi.
Riga marar nauyi tasaka ta murza humrah kaɗan,daga nan tasaka hijabi tafita inda suke zama lokacin yana eemran tana deejah.
A zaune ta hangoshi yana daddana waya da alama ya ɗan dade yana jiranta.
Sallama tayi masa ya amsa ba tareda ya ɗago idonsa ba.
Itama bata sake cewa komai ba tasamu waje ta zauna.
"Fushi kake dani yah khaleel,mai nayi haka?"
"Hmm khamreee nayi kewarki sosai,bansan iya adadin lokacin dana zauna tunanin fitowarki ba,gani nayi kaman shekara shida nayi ina jiranki ba wata shida ba. Kiyi haƙuri ba fushi nake dake ba,kawai ganin yanda mutane suka tarene suka hanani ganinki ni kaɗai na more"
Yar dariyah khamriyyah tayi,soyayyarsa tana ratsata tace.
"Nima nayi kewarka sosai,saidai alhamdulillah,yanxu duk wani abu daya tsayamin a zuciya na tsawon shekaru ya tafi,na yiwa wanda suka aikata ba daidai ba hukuncinsu,sannan nima kuma na karbi nawa hukuncin na gama,sai nake jina kaman wata sabuwar mutum a duniyar"
"Ina fatan kuma wannan sabuwar halittar ta fara sabuwar rayuwa tareda ni,ta zauna a gefena har zuwa lokacin da Allah ya zai rufe mana ido,ta kasance abokiyar rayuwata sannan kuma uwar iyalina.
Shin wannna halitta zata amince nazama mijinta kuma sirrinta,sannan farincikinta?"
"Wannan halitta ta amicewa masoyinta ɗari bisa dari,batareda na nadama ko dana sani ba"
Murmushi khaleel yayi najin daɗi tareda cewa.
"Mashaallah,alhamdulillah bi ni'imati hi,dama ke ake jiran dawowarki na nemi amincewarki,anriga an gama shirin bikin da kuma inda zamu zauna,saidai mu bazamu dade ba,zan koma ƙarin karatu china,inda nayi karatu,tare zamu tafi wani watan.
Amarya saiki shiryah ɗaurin aurenki wani satin,wani watan kuma barin ƙasar ya kamaki,kafin sannan saiki samu ki huta gajiyah,bazamu zauna a kasarnan ba yanzu"
" umm Amma kuma naji ana cewa mai martaba zai ɗoraka akan sarauta koh,yana buƙatar hutu"
"Ahah bazan kama zaman basirr ɗinnan yanzu ba,bangama cin gashin rayuwata ba,shima saida ya shaƙata kafin ya hau mulki,beside ban tara yara ba nayi rayuwa dasu irinta ko wane uba,saina fara zaman fadanci,inaaa there is time babyy,before let we chill okay?"
Ɗaga masa kai khamriyyah tayi tana dariyah,dan itama tana buƙatar adjust ɗin rayuwarta kam kafin ta fara cuɗanya da sha'anin mulki.
Daga nan akalar hirarsu ta sauyah zuwa ta masoyah masu begen junansu.
Tundaga ranar da labari ya jagaya khamriyyah ta amince a haɗa a aurensu dana su khairiyyah da deen,madeena kuma itada wani lecturer su da yake sonta,saleem ma yaso a haɗa nasu shida amal,amma firr taƙi,a cewarta saita shiga jami'a tukunna ta fara,kuma ma bata son a haɗa bikinta dana wasu,bazatayi shagali a bikinba inda ita aka haɗa.
Biki aka fara ba kama hannun yaro,inno ta taka rawar gani wajen yi musu gyaran jiki ta kuma bangaren tasirin turare da sauransu.
Ita kuma hajiyah saratu takanass tashiga jirgi ta nufi dubai itada hajiyah deejah sayo kayan ɗaki,iri ɗaya akayi musu,kala ce kawai ta bambamta.
Rana bata ƙarya kuwa,sati yana zagayowa aka ɗaura auren ƴan matan gidan,abinka da hannu da shuni,nan da nan akayi shiri da kuma yin duk abinda ya dace.
Dukkansu kowacce sarki yabata alƙyabbar daza'a kaita,khamriyyah surukarsa,su khairiyyah kuma yayansa na jini,dan haka dukkansu sun cancanci samun Al'adar sarauta kafin kaisu gidan miji,duk da kana gani kasan yafiji da matar Babban ɗannasa na jini,surukarsa ta farko wacce aka kawo basu suka kai ba.
Bayan haka kuma aka haɗasu da kyaitukansu dasuka samu daga manyan gari.
Dan har dangin Hajiyah Ateek ma sun ƙarbi khamriyyah hannu bibbiyu,tunda sunsan yar uwarsu ce take da laifi,sannan kuma mai ya faru ya zasuyi,soon zasu haɗa jini da khamriyyahn,dan haka babu abin wani boye boye.
Bajinta suka zage suka nuna a nasu na matsayin shuwa,kakan Khaleel kam harda kyautar Dadduma da kuma Alqur'ani mai kyau ya aikowa amaryar tasa.
Madeena kano aka kaita,khariyyah kuma ana cikin katsina,haka ita ma khamriyyah.
Da farko mai martaba yaso khaleel ya zauna a cikin gidan,amma ya ƙi yadda sam,shiyafi son rayuwar privacy da kuma rashin hayaniya.
Duk wanda ya kalli gidajen amaren dole zai sake gani ya jinina,domin kowa anyi bata barin dukiyah da kayan alfarma.
Masu kaiwa khmariyyah harda sabrah a ciki,wacce yayanta suke ta mata kukan zazzabin haƙori sun rame kaman basu ba.
Bayan kowa yayi hanyar falo sabrah ta kalli khamriyyah wacce take zaune tana game a wayarta,babu alamar damuwa ko kaɗan.
"To da farko dai ƴar uwa kinsan aure shi ba abin wasa bane......."
"Sai kuma nace abin wasane,kinga dan Allah karki dameni da surutu kacan danki yanata kuka a falo kije ki karbeshi,wannan abubuwan sau nawa za'amin bitarsu ne,batun yin biyyaya dama ni nace ina so,dan haka basai kowa yacemin nayi ba,"
Dariyah sabrah tasaka tareda dungure goshin khamriyyah wacce take ta zuba kaman yayan kanya.
"Ke dallacan,daga yin magana harkin fara masifah,wato missing ɗina ma. Bakyayi koh"
"Innayi missing ɗinki saina zauna nayi ta kuka koh,idan ina kewarki zaki ganni a gidanki,yanzu dai ki tattara mutanen falon can ku tafi,dare yayi gasu matane kusan dukkansu da goyo"
Daga haka khamriyyah tazari kayan baccinta ta nufi banɗaki.
Sakin baki sabrah tayi tana kallonta,daga nan ta jijjiga kai tana zaki ƙwala a ranta.
Bayan khamriyyah tayi wanka,saida ta tsaya tayi na turare yanda Anty yagana ta faɗamata,ƴar autar su hajiya fulani ateeka.
Ta daɗe kafin ta fito daga banɗakin tana gyara igiyar rigarta.
Turus tayi ganin mutum akan gado sanye da pyjamas shima ya zuba mata ido.
"Uhm miye na tsoron,kicigaba da tafiyarki mana"
Ya faɗa yana ƙaremat kallo.
Kafesewa tayi

32 / 33