MABARACIYAH Daga Bara Zuwa Firgitar Masu Iko by Auwal sadiya

Author :  Auwal sadiya Category :  Free Novels Online (Read & Download)

Chapter   28 / 33

81K to 84K   out of 96.8K words

musulunce aure tsakanin su babu shi a addinance.
Sannan dalili na biyu kuma dana taraku anan wajen shine,inaso dani daku da kowa aji labarin mai yafaru bayan barin su gida da kuma yanda sukayi rayuwa.
Dan haka muna sauraranku"
Kowa ido ya zubawa su inno,wanda suke gefe guda kusada mai martaba ,domin maƙasudin taron akansune.
Gyaran muryah inno tayi,cikin nutsuwa ta zayyano masu duk abinda yafaru,daga tsintar su khairiyyah da tayi,da irin ƙalubalen datayi harma da abinda suka aikata bayan cin mutuncin da akayi musu na fansa akan manyan gari.
(Labarin da sabriyyah da bawa Sadeeq a cikin kundin tarihinta).
Wajenne ya kaure da hayaniya,wasu na tausayinsu khairi,wasu na cikin mamakin abinda ya faru,yayinda wasu ke ganin ƙaryahne mutanen bazasu yi haka ba.
Gyaran murya mai martaba yayi,wanda hakan yasa kowa yayi shuru.
"Toh duk munji abinda ya faru,haƙiƙa abinda aka yi muku a garin daura abune da kowa akayi masa abinda zayyi kenan idan ya samu dama.
Saidai kuma da zai zamo mutane suna ɗaukar doka a hannunsu to dokar bazatayi amfaniba kenan.
Za'ayi bincike,idan ya zamto gaskiya kuka faɗa,nida kaina zan tsayah muku a kotu,duk da hakan ba ƙaramin abu bane,dan su kansu wanda kuka aikatawa haka manyan mutanene.
Zaku zauna a cikin gidannan a matsayin kowane ɗa a cikin gidannan,ke kuma Sabriyyah zaki koma gidan mijinki ki zauna kafin muga yanda Allah yayi,idan wani abune ya taso duk zakiji mai ake ciki.
Ku kuma sauran za'a tura mota ta ɗebo muku kayanku zuwa nan gida.
Toh idan da mai tambaya kowani abu ya faɗa za'a rufe waje da addu'a,mai buƙatar ganinsu ko magana dasu a matsayin ƴan uwanku saikuje sashensu,nizan tafi fada ana jirana"
Taronne ya watse daga haka,kowa na faɗin albarkacin bakinsa.
Hajiya saratuce taza inno zuwa sashenta,dan ko barinsu su koma gida taƙiyi,a cewarta basai sunje ɗaukowa kayan bama,za'a ɗakkomusu,idan an gama shirya musu inda zasu zauna sai suje yiwa kaƙwantansu bankwana.
Abinci aka shirya musu nagani na faɗa,duk wanda yaga hajiya saratu a lokacin yasan tana cikin farinciki sosai da sosai.
Mutanenta kuwa da abokan arziƙi kowa sai taya murna yakeyi da bayyanar ƴaƴanta.
Su khairiyyah sunga gata kam sosai a wajen danginsu da basu sansu ba sai yanxu.

Wajen misalin ƙarfe takwas na dare khaleel ya shigo gida daga wajen aiki,dan yanxu wani lokacin sai daren yake dawowa,gabaɗaya abubuwa sun masa zafi,ga kewar masoyiyarsa,ga fargabar kamata dayake koda ya ganta,sannan kuma aibantata da mutane sukeyi ko yaushe acikim kunnuwansa,tun yana ƙoƙarin boyewa har sadeeq yafara gane akwai abinda yake faruwa tsakaninsa da ita.
Shikaɗaine yasan yanda mutane suke ɗaukarta ba haka takeba,saidai kuma taya zai fahimtar dasu hakan,bayan ko abinda yake tsakanin su babu wanda yasani,dagashi sai saleem ne kaɗai suka sani.
Gashi yanemeta yarasa a wannan duniyar,ko numberta yasamu,yasan jin muryarta zao rage masa damuwa,tayi masa abubuwan da koda baya sonta bazai manta da itaba.
Itace mace ta farko bayan hajiya deejah da tasan lalurarsa,kuma ta tsaya a wajensa lokacin dayake bukatar taimakonsa,karshe ta ajiye muradinta ta nema masa lafiyar da tun yana da ƙananan shekaru ya rasata,saidai ya gani a wajen wasu,amma yanzu shine yake rayuwa ba fargabar wani ciwo zai shigo rayuwarsa a kowanne irin lokacin.
Maizaice da wannan halitta ta ubangiji,wacce ransa yake matuƙar muradin ya rayu da ita,ta gujeshi da kunyar bazata iyah zama a matsayin surukar mahaifiyarsa,bayan abinda tayi mata.
Batasan cewar shi ko kasheshi takeyi tana dawomar da ransa baya tunanin ciwon sonta zai bar ruhinsa ya samu salama.....
Hajiyah deejah ce ta ƙatseshi da tunanin daya zame masa ci kana da kuma sha a kullum.
"Ibrahim khaleel"
Saurin juyowa yayi da sauri,dan duk sanda tayi masa wannan ƙiran toh fa abin yanada muhimmanci.
"Tun ɗazu nake ta kiranka baka jini ba sam,mai yake damunka ne haka,gashi kaƙi sanar da kowa abinda yake faruwa.
Dama mahaifinka ne yake faɗimun cewar kaje yana son yin magana dakai yanzu"
"Toh ummah,barina cire kayan aiki tukunna"
Duk da ba uniform yake sawa kamar su Sadeeq ba,amma kuma akwai yanayin shigar dayake wanda ita ta aikice kawai.
Shiryawa yayi lokacin ana ƙiran isha,dan haka kawai daya tafi masallaci tacan ya wuce gidannasu. Ko abinci bai tsaya ci ba,dan dama bashida ɗanɗanon cin abincin.
Dayazo shiga sashen mai martaban,dogarawa ne suka tsayar dashi,wanda da alama basuda labarin shine yarima junaid ɗin,(dan duk gidan sarautar kowa cewa aka cemusu yarima junaid ya dawo,wajen aikinsa kuwa da kuma wanda suka sanshi a waje,kowa da Khaleel ya sanshi.
Tsayawa yayi yana kallonsa,shifa abinda baya cikin ra'ayinsa kenan,wato sha'anin sarauta,abune da tun yana gidanma baya so,inaga kuma daya tashi badashi ba,bai saba ba kwata kwata,bashshi a rayuwarsa ta freedom da privacy.
Har ya buɗe baki zayyi magana,saiga waziri ya fito daga wajen sarkin.
Alhaji Musa Malam,yanada yawan yan shekaru,dan ko a fuska ma yafi sarkin ɗan manyanta.Shine yayan Mahaifiyar ainihin Khaleel ɗin daya rasu,wato Hajiya fulani Ameena.
"Ahh junaidu kaine,mukan da aka saba koba shigo nan ba aikazo mu gaisa koh"
"Eh dama kuma bana kasar ai,Abbah yana cikine?"
Yafaɗa a hankali cikin ladabi.
"Eh yana ciki ka shiga,naga kuwa kaman dama kai yake jira,dan da yanzu ya shiga cikin gida"
Cikin sanyi da nutsuwa Khaleel yasaka kansa cikin turakar mai martabar,bakinsa ɗauke da sallama.
"Assalamu alaikum"
"Wa'alaikassalam Junaidu"
"Abbah khaleel ne fah"
Yafaɗa cikin dan ɗaure fuska.
"Kai nikarka min sakarcin dakakewa uwar taka,yaka matso tanan kazauna,akwai abinda zamu tattauna,duk sunan daka ɗauka daga cikinsu ma ai ba bu damuwa,dukkansu jinina ne,kuma ko kaine kaɗai a raye ko kuma shine,dukka ina ganin kune a jiki guda ɗaya,koyaushe saina tuna lokacin dakuke shigowa gaisheni nan wajen ku biyu a kowacce safiyah"
Daga yanda yayi maganar kasan abin yana sosa masa zuciya sosai,da alama yayi kewar ƴayannasa.
Shima khaleel ɗin lokacinne yadawo masa tamkar sabo a cikin kansa,yanda mahaifinnassu yake matuƙar nuna musu soyayya.
Karisawa wajen ubannsa yayi tareda rungumeshi a jikinsa,dan idan yatsaya kwatanta jin kewar mahaifinnsa bazai yiyu ba.
"Abbahhhh kayi haƙuri da rashin sanar dakai ina raye,akwai dalilin hakanne shiyasa,ammafa nayi kewarka sosai,sannan nayi kukan rashin ɗan uwana"
Dafa bayansa yayi tareda yin murshi irinna manya kafin yace.
"Nima nayi kewar rashinku kusada ni,a cikin wannan satin gani nake kaman nafi kowa farinciki,ƴaƴana har guda uku sun bayyana gareni.
Inaso ka dawo gida da zama kaima,ga nan sashenka nasa a gyaramaka,yakamata ka dawo gida da zama,ka fara sanin sha'anin mulki,domin ni lokaci gaba yake min,dama kuma sanda na karbi mulki nafara girma,inaga kuma yanzu.
Sannan ga mata kai har yanzu naga babu"
Shuru khaleel yayi yanajin abinda mahaifinsa yake faɗa,a tsarin dawowa gidan ya cigaba da rayuwa kaman da, kwata kwata baya cikin tsarinsa,saidai kuma bazai iya cewa mahaifinnsa ahah ba.
Sannan idan yace bazai karbi mulkinba to wa za'a baiwa,mubarak bai daɗe da tasowa daga doguwar suma ba,yanayin magana ma har yanzu bai gama ganeta ba,sannan iya kacinsa secondry kawai abinda yafaru dashi,kwakwalwarsa irinta wancan shekarunce har yanzu.
Shiri turashi saudiyyah akema yayi karun addini ko hakan zai ƙara taimaka masa,saikuma jalal,wanda yanzune aka samu yafara nutsuwa ma tukunna. Shikuma shiyafi cancanta ya karba,amma kuma bayada ra'ayin hakan,saidai babu yadda zayyi dole ya dawo gidan kaman yanda mai martaba yace,ko yaƙi ko yaso shine babba yanzu a gidan.
"Shikenan Abbah zan dawo gida da zama,amma ba yanzu ba tukunna akwai case ɗin danake running,banason haɗashi da sha'anin gidannan tukunna,inaso a barni idan nagama tukunna"
"Shikennan babu matsala,kanada damar dazaka gama tunani akai,bari ninashiga cikin gida,amma kafinnan kaje ka gaida Hajiya saratu tukunna,dan kunsan a wajenta kuke kafin wannan abin ya auku.
Ga gaida mahaifinnaku,(mahaifin Sadeeq),yaki zuwa mu gaisa wato,nadaɗe rabona dashi"
"To shikenan zaiji Abbah,naji ummah tana cewa wai bayada lokaci,sha'anin zabe ya matso"
"To shikenan Allah ya taimaka,kazo gobe da yamma idan kanada lokaci,domin zan nunaka gasu manyan gari"
"Amma abbah da an bari tukunna,a yanayin aikinmu ba'a fiye son bayyana Ahali ba sosai"
"Ohh to na fahimta"
Daga nan Khaleel yafito daga sashen mahaifinnasa ya nufi cikin gidan.
Tafiya yake yana kallon wajajen dayafi zuwa lokacin yana matsayin Eemran,wani wajen yayi murmushi,wani wajen kuma saidai ya jijjga kai,musamman idan ya tuna rayuwar dasukayi da Deejah,idan wani ne yabashi labari bazai gasgata shiba.
Sabuwar kewartace ta dawo masa cikin kansa,yanda take abubuwanta sakk yanda yake muradin mahaɗin rayuwarsa ta kasance,mace mai juriyah jajircewa da kuma tsayawa akan ra'ayinta.
Wata mace yagano a zaune akan dutsen da suke zama shida Deejah idan yanason yin magana da ita.
A yanda tayi zaman da kuma jikinta sak irinna deejah.
Gabansane ya buga giff,sannan haka kawai jikinsa ya bashi kaman itace.
A hankali yake takawa zuwa wajen har isa tabb da inda take.
Khamriyyah ce a zaune da waya a hannunta tana game ɗin bubble,sai fash fash suke cewa.
Jin kaman da mutum a bayan tane yasa ta saurin juyowa tareda zaburah.
"Ohhh Subahanallah yallabai ashe kaine,wani abune yataso na case ɗin muke aiki?"
"Uhm uhm ahah,kawai yanda kikayi zamanne na ɗauka ko wanda nake nemane a zaune,am sorry barina shiga ciki wajen Umman su Madeena"
Daga haka cikin diri dirice da alamar rashin cikar buri ya bar wajen.
Kallonsa khamriyyah take,da tunanin mai yake damunsa,amma kuma babu wanda zai bata amsar hakan,kallon wajen da take xaune tayi,tareda sake kallon inda yabi.
"Wa kuma yake nema anan wajen,hmm you are in my target.
Danasha cikin salaha kan abinda tasani gameda deejah,tace anan wajen suke zama itada eemran suna hira,yanzu kuma Ogah khaleel yazo yana neman wata a wajen,yayi zaton nice ita ,mai hakan yake nufi,shida ance bai daɗe da dawowa daga ƙasar ba,taya yasan da wata anan wajen yazo nemanta?"
Kaɗa kanta tayi itama ta bar wajen,ganin babu wanda zai bata amsa koda ta tambaya.
Tun dawowarsu fada su khamriyyah basu taba fitaba,saboda yawan mutane dasuke zuwa kallon su sabriyyah,sannan dakuma zagawa dasu gurin yan uwa.
Dan jiyama suka dawo daga gombe gidan su Hajiya saratu.
Khamriyyah ce a gaban tangamemen madubin ɗakinnasu tana shiryawa cikin kayan haka normal,kayan aikinnata kuma tasakasu a cikin jaka saboda gudun abin magana a gidan.
Tare suka gama shiryawa itada khairiyyah wacce itama zata wajen nata aikin.
Sabrah kuwa tana zaune da tulelen cikinta tana kallon,da yau zata koma ɗakinta,Hajiya saratuce ta dage akan a barta ta zauna a gida,don koda tana gidanma dole zata dawo gidan,tunda cikin farine.
Bori kaɗai sadeeq bai tayarba dayaji zancen hakan,gani haka yasa hajiya saratu cewa zata koma toh,amma mahaifiyarsa tazo akan cewa ta zauna a gida kawai,tunda tashiga wata na tara,ana saka ran haihuwar ta nanda sati uku masu zuwa.
"Uhm kunji ɗadinku zaku fice kusha iskar waje,ni duk zamannan ya isheni ga nauyin jiki,duk da har yanzu ban warware da gajiyar zuwa gombennan ba"
"Ko aiki kike kinsam ai bamai barki kifita daga gidanann da wannan cikin,gwanda ki kwantar da hankalinki"
Har sabrah zata sake magana madeena tashigo ɗakin,da fara'arta ganin yayunnata sun tashi.
"Anties ina kwannan ku ya gajiyar tafiyah?"
"Lafiya kalau sis kin tashi lafiya?"
"Alhamdulillah,Anty sabrah wai kije inji Hajiya saratu kisha maganin sassafe"
"Toh,nimaganinne banajin daɗinsa a baki,duk da inajin daɗin sa sosai"
"Kinga tashi yanzu haka tana jiranki,inkuma so kike na ƙira ogah SAdeeq ya goyeki kuma toh,duk munsan jiyama a gidan ya kwana a sashen Jalal,aimu da turaki akayi muka huta da ma'auratan zamani"
Khamriyyah ce mai zuba wannan surutun tana shafa mai a ƙaramin bakinta mai shegen surutu.
Dukkansu dariyah suka sa harda madeena wacce itama tasamu waje ta zauna tana kallonsu,Alaƙarsu baƙaramin burgeta yake ba,haka ma faɗansu.
A iya sati ɗaya da sukayi a tare tajita gurbin data rasa yau ya cike,a dajinta take kaman batada yaya mace,saboda Antyn tah Khadija sanda tayi wayo anyi aurenta,kuma bata jansu a jiki.
Amma yanzu zamanta cikin ƴan uwannnata yanasakata nishaɗi.
Ji take kamaar karta koma makaranta wani satin.
Suna gama shiryawa dama driver yana jiransu a waje..
Bayan sun gaisheda inno,suka wuce sashen Hajiya saratu ma.
Sabrah tana zaune da magani a kofi sai yamutsa fuska take.
Basu daɗe ba a wajen suka fita,hajiya saratu musu fatan Alkhairi cikin fara'ah,a cikin idonta zaka hango kaunar datakewa ƴan matan.
Khairiyyah aka fara a jiyewa a wajen aikinta,kafin aka wuce da khamriyyah headquatersu.
Drivern yana ajiyeta ta wuce rest room na mata domin saka kayan aikinta,sai sauri take dan tasan halin shugabannata.
Kwankwasa ƙofar tayi,amma shuru ba'a amasa ba,hakanne yasa ta tura kofar ta shiga,dan a tunaninta bayanan.
Turus tayi jin abinda yashigo kunnenta.
"Duk da nasan ke mai laifice,kuma nine keda alhakin miƙaki ga alƙali,na minti biyar kacal ki yarda na ganki deejah,batareda kowa yasami ba,akwai abinda nake son muyi magana akai,sann......."
Da sauri ya juyo suka haɗa ido da khamriyyah,wacce itama shiɗin take kallo.........

See you next......😊







Taku
_sadi-sakhna_
Ƴar mutan jama'are.








*MABARACIYAH*


_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)






55••56





"Ahh ogah ba komai fah kacigaba da wayarka kawai,barina je wani waje na dawo,bansan kana cikiba dama,nayi ta magana ba'a amsaba"
"Dakata,amma kinji mai nace,sannan kinsan dawa nake wayah?"
Juyowa tayi ta kalleshi tareda ƴar yin dariyah tace.
"Ahhh batun waya kam ai dole naji tunda inada kunne,yanayin wayarma ya tabbatar dawa ake yinta,abin mamakin kuma shine a ina kuka haɗu da har kuke wannan maganar da ita.
Duk da dama na zargi hakan tun daren jiya"
Fesar da numfashi khaleel yayi tareda cewa.
"Okay okay naji kingane abinda yake faruwa,amma please karki faɗawa kowa mai yake faruwa"
"Uhm hakan bai daceba,amma duba da yanda ka damu zam taimakawa ogana nayi ƙus da bakina,amma nima da sharaɗin zaka daina min wanan faɗannaka,dan ya isheni,idan kana buƙatar taimako ma ƙofah a buɗe take,koba komai zan ɗan ja lokacin ba'azo kaina ba kenan,tunda sai angama da ita kan azo kaina,itakuma mai kafcen soyayyarta ya kafeka"
Da dariya taɗan karishe magana tareda barin office ɗin.
Binta yayi da kallo tareda sauƙe ajiyar zuciya,haka kawai shakkarta yakeyi,domin itama wajennnata ba sauƙi,inaga kuma shugabar.
"Oh ya Allah gani gareka,inama zan iya mantawa da wannan baiwar taka"
Daga haka ya koma jiki a sabule ya cigaba da abinda yake.
Can kusan misalin shabiyu na rana khamriyyah ta shigo ɗauke da tea cup a hannunta,yanxu tunda itace mataimakiyarsa duk wani abu itake kula dashi..
Da sallama tashigo office ɗin ta sameshi yana rubuce rubuce akan paper.
Zama tayi a kujerar datake facing ɗinsa ta zuba masa ido.
Tsarguwa yayi da halayyarta ta wanda yakan yasashi cewar.
"Menene kika zuba min ido haka kaman wanda yau kika fara kallona"
"Uhm tausayi kake banine sosai,tun zuwana wajennan koyaushe sai kowa ya tafi ya barka,bawai dan kana aikiba saidan kana tunani.
Kowa yana kulada ramar dakake a kwannan ,duk da kowa bai san ciwon so ne yake ɗawainiya dakaiba.
Soyayyar data ke abinda kunya a gareka,wacce bazaka iya fito duniyah ka bayyana ta ba.
Hmm waye zai iya cewa ya kamu da soyyayar wacce aka bashi ragamar yakama ta da laifi,shin wane suna za'a ƙirashi?......i am sorry ogah for this burden life"
"Ba kunyar soyayyartace tasakani hakaba,dana sani nake da nadamar meyasa bab nuna mata kulawa fiyeda yanda na bata ba,har ta kubuce ta buya a duniya tareda kunyar kanta kanta.
Inaso na haɗu da itah na nuna mata a shirye nake naji uzurinta da dalilinta,sannan kuma na fahimceta akai,idan nema mata kariyahne a gaban Alƙali zan iya domin taimakonta.
Ita ɗin ba yanda kowa ke tunaninta bace,tana da halin na juriya,tausayi da taimako wanda bakowa zai gane hakan ba,saboda idan tayi niyyar taimakon tana nuna shine kamar zalunci take.
Alhali ba haka bane.
Khamriyyah inaso na haɗu da itah yau batareda kowa yasani ba,zuciyata tayi kewarta sosai?"
Wani irin tashi khamriyyah tayi daga kan kujerar da take tareda kallon Ogannta,anya kuwa ba zaucewa yayi ba yake wannan bayanin haka.
"Ogah anyah kuwa ƙalau kake?"
"Ina za'a samu ƙalau a gun wanda yake irin wannan soyyayar,ina za'a samu a kalau a gun wanda yake kwana yake tashi da fargabar shin masoyiyarsa ta samu wajen kwana mai kyau ko bata samuba,sannan wacce take kwana da zullumin cewar za'a kamata saboda ta kashe wanda sukayi mata laifi"
Sadeeq ne ya banko ƙofar ya shigo,idonsa cike fal da hawaye har yana zuba.
Zaro ido khamriyyah tayi itda khaleel suna kallonsa.
"Duk tsawon wannan lokacin kana cikin irin wannan halin amma baka taba sanar dani ba Khaleel,Anyah kuwa ka ɗaukeni ɗan uwa yanda na ɗaukeka,babu wanda na fara faɗawa sirrina saikai,amma kai naka sirrin bansan dashi ba,kullum ina cikin wasiwasin mai ya sameka,yanzu da banji ba shikenan haka zakayi ta zama babu mai taimaka maka,koma wacece kake so yakamata kasanar dani"
Juyawa sadeeq yayi zai bar office ɗin,saikuma ya tsayah saboda abinda yaji Khaleel yana faɗa,
"Sadeeq Deejah nakeso,wacce kafi sani da mabaraciyah!!!
Ita nake yiwa son da bazan iya misaltashi ba a cikin raina,taya zan iyah sanar dakai irin wannan labarin ɗan uwa,taya zan buɗi baki nacemaka ina son wacce yakamata na tsaneta,taya zan iya cemaka inason wacce takeda laifi a idon duniyah,bayan kowa ya sanni da dannne abinda nakeji indai yazo a bangaren aikinah?!!!
Bazan iyaba Sadeeq,badam kajiba zanyi ta jurewa har ya kaini ƙasa,domin abune dana kasa jurewa irin wanda na saba a koyaushe.
Inason sanar dakai amma kuma na banida ƙwarin gwiwar hakan"
Rungumeshi Sadeeq yayi ƙam a jikinsa tareda shafa bayansa.
"Hmm khaleel kenan,duk duniyar nan babu wanda zaka faɗawa wannan labarinnaka ya fahimceka kamanni,saboda karka manta nima ina cikin irin koman da kake ciki yanzu.
Koda yakasance ita mai laifi ce,sannan kuma zaka kamata,to karka yi wasa da wannan lokacin wajen fuskantarta,da kuma fahimtarta,ta hakane abin zai zo maka da sauƙi.
Bansan a inda kuka haɗu ba,amma hakan yasa naji da akwai wani abu a ƙasa itama daya sata aikata hakan,saboda nasan bazaka faɗa soyayyarta ba idan ta kasance yanda kowa ke zatonta,dan haka ka haɗu da ita tun kana da damar hakan,ka haɗu da ita a matsayin masoyinta,lokacin daka fito da shaidu kuma ka haɗu da ita a matsayin Dedective IBRAHIM KHALEEL na tabbatar zata fahimce ka"
Sauƙe ajiyar zuciya khaleel yayi,duk da ya yarda da abinda sadeeq ya faɗa masa,amma har yanzu yana kunyar sa sosai akan abinda ya faru
Lallai bai kamata mutum ya faɗi abu kokuma ya zartar ba,alhali bai san mai yake faruwa ba.
Gyaran muryah khamriyyah tayi ganin sun manta da ita a wajen,
"Allah yabaka sa'a a soyayyarka ogah,kaman yanda kake sonta ina mai tabbatar maka itama tana sonka da zuciya ɗayah,kawai dai akwai dalilin hakan"
Tana fita daga office ɗin khaleel ɗin ta hangi royal driver yazo ɗaukarta,anan ta tuna ashefah yanzu a can suke zaune.
Shiga tayi suka nufi gida,tunani da tausayin Khaleel fal a ranta.
Da yamma yau khaleel ya tafi gida yau,kirjinsa sai bugawa yake da tunanin taya zai fuskanceta a yau ɗin.
Tun a motarsa kafin ya isa gidan yake ƙiranta amma batayi picking ba,hakanne yasashi turamata massage,akan inda zasu haɗu.
Bayan ya fito daga wanka ne yaga massage ɗinta na addess ɗin inda zai sameta.
"Bakin ruwa?"
Yafada a ransa,mai kuma zai kaisu

28 / 33