Author : Auwal sadiya Category : Free Novels Online (Read & Download)
ƙiramin ruƙon danayi miki shamsiyyah?...karki manta fah kebada madara na raineki ba da nonona na shayar dake ,jinki nake tamkar ƴar dazan haifah a cikina,sannan lokacin dana shayar dake bana tuna ke ƴar sunnah ce ko kuma ƴar gabada fatiha,kawai ni ke yarinyah nake gani ƴata kuma mai neman taimakona,sannan wacce zan raina na bata tarbiyyah,to barikiji abinda baki saniba,tun lokacin dana karbeki nasan duk wacce ta haifeki ba musulma bace,sannan kuma bada aure ta haifeki ba ,hasalima ubanki dayake matsayin saurayinta ne ya gudu yabarta,itakuma da ajiyeki a gaban coci ta gudu.
Baba shehu zaije aikin shinkafah kogi da asuba yaganki,ba wanda yagani ya lallaba ya ɗaukoki ya kawoki nan dan kwaɗayin ki tashi cikin musulmai.
Lokacin daya faɗamin mai yafaru,ban taba farincikin rainon ƴa ba kaman yanda nayi akanki,saboda ina hango riba biyu zan samu,na rainonki da kuma na nabaki tarbiyyha irinta ƴaƴan musulmai,amma shine kika faɗin anbiyani albashi na rainonki koh?.......hmmm ki fice ki bani waje bana buƙatar sake ganinki a rayuwata har abada"
Shuru tayi bata tafiba,da alama jikinta yayi sanyi da zancen inno,
"Uhm ko ban riƙesuba zan tafi dasu na kaisu gidan marayu a katsina,saina dunga zuwa ina dubasu......"
"Ni zan riƙesu na rainesu,kuma zan fara sana'a da neman aiki domin siyan madara da kuma abincin dazasu ci,inshaallah jinin anty juwairah bazai tagayyara ba indai ina raye"
Dukkanmu kallon khamriyyha mukayi wacce tayi maganar cikin dakewa,kuma babu alamar zata canja maganar tata.
"Ke kuma shamsiyyah kaman yanda inno ta faɗa ki tashi ki tafi gidan mijinki,daga rana mai kaman tayau bamason ganinki a cikin gidannan koda wani abune ya faru,muna so ki manta damu a rayuwarki,ki ɗauka tamkar daga sama kika faɗo,kokuma kishiga duniyan neman uwarki,nasan ita zatayi daraja a wajenki tunda ita ba'a bata kuɗi ba sanda ta haifeki ba"
Cikin muzanta da kunyah shamsiyyah ta zari jakarta ta bar gidan ma gabaɗayah.
Jinake kaman na shaƙeta saboda haushinta danakeji,dama ni bama shiri da itah tun muna yara.
Bayan fitarta daga ɗakinne inno ta kalli khmariyyah wacce take jijjiga fadeelah ta tashi daga bacci.
"Amma aikin dakika karba zakiyi da kamar wuyah khamriyyah,inaga zai iyah tana rayuwarki"
"Bazai taba rayuwata ba,in ma yatana babu damuwa,inda nice a madubin rayuwar anty juwairah haka ta faru dani dole na riƙesu,dan haka yanzu da bata nan sun zama ƴaƴa na,zan riƙesu tamkar ƴayan da allah zai bani a cikina"
"Bazai gagara ba ma khamriyyah ,kina damu,zamu zama tamkar tsintsiya guda ɗayah,yaran nan gidan ma zamu cigaba da kukadasu kafin muga ya allah zayyi"
Ina gama faɗin hakan na rungume khamriyyan,ita ma khariyyah tabi bayanmu tana sha ƙawallar idonta.
Daɗi naji a raina ganin murmushin inno ya dawo ba kaman ɗazuba da ranta ya 'baci.
Idan akace kana rayuwa toh saidai fa kawai kace mashaallah,dan lallai kaga yanda ranka yakeso ba.
Da daɗi da babu haka muka cigaba da rainon ƴan biyun anty juwairah,sun wayo sosai dan sun doshi wata biyar yanzu. Ba wanda suka fi sabawa da itah kamar khmariyyah,dan tafi kowa shaƙuwa dasu,a wajenta ma suke kwana,duk da ma bata fiye zama a gidanba.
Tana zuwa aiki da yamma bayan mun dawo daga makaranta,a gidan wani chairman.
Duk da haka idan zata tafi saita ɗauki ɗayah daga cikinsu ta goyeshi,nikuma naji da ɗayah.
Nima ba zama nakeba nasamu koyarwa a islamiyar anguwarmu,ita kuma khariyyah tana shagon computer su,sai yamma take dawowa.
Yanzu gidan shuru ba kaman da ba,dan ma maman yara tana nan bata tafiba tukunna,tace ya ɗanta yaƙara bata lokaci tukunna,to hakanne yasa muka ɗan samu dama daman abin.
Muna zaune dani da deen muna hira,dayake anyi hutun ss3 kafin a zana paper ya dawo gida,wani satin zamu fara jarabawa.
inata tsokanarsa yayi tsayi muryarsa kuma ta zama ƙatuwa,wata yarinya ce tazo wajen da fadeelah a gefenta tana biyeda itah,ta cune bakinnan kaman na kifi,yarinyar dariyah take bani sosai,kwata kwata bata iyo mahaifyarta ba mai sanyin rai.
"Yah deen wai kazo inji maman yara zata aikeka"
"Ohh yanzu fah nadawo,kice ganinna zuwa yanzunnan"
Harara ya dokamin lokacin daya tashi zai tafi.
Nasan ƙiran bazai wuce na abinda zata siyaba zata koma asibiti wajen inno,wacce safi ɗaya kenan da'akayi mata tiyatar appendix a katsina,wani asibiti suka fara yin ayyuka kyauta na tsawon wata shida saboda marasa lafiyah,inda ana haka da an huta.
Kallon fadeelah nayi wacce tafiyar tayi ɗan kwari sosai,dan dama itace mai sanyin yin abu da wuri ba kaman fadeel ba,shekara biyu amma bata daɗe dayin tafiya ba.
Kallonta nake tana wasan kasa,kaman ba itace maimin kukan dareba tana ƙiran khamriyyah,yau kwana huɗu amma jinake kaman shekara,allah allah nake sudawo daga asibitin,dan naji ance aikin yayi kyau har banɗaki takezuwa ta dawo da kanta.
Gaskiya khamriyhah tana ƙoƙari sosai,mai riƙe fadeelah ai saiya shiryah,batada daɗi ko kaɗan.
Tashi nayi daga wajen na ajiye novel ɗin dayake hannuna,ganin lokacin tafiya makarantar islamiyyah yayi.
Wanka nayi suma su fadeel nayi musu,dan suna zaune a gidanne amma basa cikin yaran gidan,dan haka mu muke musu komai ba ƴan aikiba.
Ɗan maman yarane da wasu wanda aka rainesu a wajen suka ɗauki masu aiki guda biyar wanda zasu dunga kulada wajen. Sannan su dunga taimakawa da aikin yaran.
Nafi minti biyar ina zaunar ta amma taƙi zama nayi mata wankan,shi fadeel tun ɗazu nayi masa wankansa har ya bushe ban saka masa kaya ba.
"Yanzu fadeelah dan butar ƙaniyarki bazaki tsayaba koh,zan kaiki wajen karen madugu ya cinyeki kuwa"
Shuru tayi tana zare ido,ga tsoron tsiyah dama.
Da haka na samu dama na gama mata wankan na shirya su,sashen maman yara suka nufah ni kuma nafice daga gidan.
Kwana biyar su khariyyah suka sake sai gasu sun dawo gida,anata murna aiki yayi kyau,saidai ance ta samu hutu sosai da sosai.
"Inno shikennan yanzu kam anyi aiki,muna fatan kisamu lafiyah sosai"
"Ah jiki kam yayi kyau sosai,banda ciwon wajen tiyatar babu abinda yake damuna,sunce kada na dunga shan ruwa mai datti,sanann kuma idan wani abu kona matsala yafaru to kada na naje ko wane asibiti sai can.
Dama appendix ɗin waje biyune yake?"
Da alamar tambaya na kalleta,wajen biyu kuma
Nuna gefen cikinta tayi bangaren dama sanann ta nuna kusan mararta ma,wai duk ciwo takeji a wajajen idan bata sha magani ba"
Ware biyu kuma,sanann sunyi gargaɗin kar a sha ruwa marar kyau,idan kuma matsala tafaru kar a je asibitin ko ina sai nasu.
Mai hakan yake nufi,anyah kuwa babu wami abu a ƙasa kuwa.
Hmmmm. Dama fah ance araha bata ado. Allah dai yasa lafiya kawai shi ake fata.
Taku
_sadi-sakhna_
Ƴar mutan jama'are.
*MABARACIYAH*
_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)
23••24
Da farko naso nazarin wannan tiyata ta inno,amma kuma ganin an samu abinda ake nema wato sauƙi,saikawai na bar zancen. Uwa uba kuma naga khamriyyah tayi shuru da zancen.
Mun fara zana jarabawa,karatu ya fara zafi,dan kowa burinsa da mafarkinsa ya ɗauka akan sai ya cimma burinsa akai.
Koyaushe idan kaga ɗaya daga cikinmu to da littafi a hannunsa yana karatu,shima deen dayake makarantarsu nasan hakanne a wajensa,munsan iya karatunne muke dashi dazamu dogara dashi, shiyasa bazamuyi da wasa ba.
Waec muka farayi a makarantar daga nan bamu komaba,dan bamuda wanda zai biyamana kuɗin neco mu zana,sai allah ya dafamana muka ci guda ɗayar da muke da damar yinta.
Musamman khairiyyah da deen sun fimu cin paper.
To hakan ma gwanda ni da khamriyyah kam,taci math kam sosai amma english kam sai a alhamdulillah.
Kallonta nayi lokacin da mukaje cirowa paper,ina ƙunshe dariyar datake cina,duk da nasan ta ganni.
"Anty khamriyyah"
Harara ta watsamin wanda hakan yasakani sakin dariyata,dan dama tasani idan na ce mata anty to tsokana naso yi.
"Wace makaranta yanzu zaki tafi,naga subject ɗin da kika zaba ma wasu kala daban"
"Suna ga damar yi,shiyasa na saka,ko kinaso nasaka wanda banajin zasuyi min amfani?"
"Ahah ban ce ba,wace makaranta zaki tafi toh"
"Ba ruwanki,kiji da taki makarantar kawai,kowa yayi nasa bangaren dayaga yafi masa"
"Uhm ni inason karantar physicology,amma bangaren behaviour nakeso,saboda abin yana burgeni ga dunga ganin mutum kana gane ɗabi'unsa,yakika ce abin khamriyyah"
"Hmmm kike min dariyar math kema fah naki bawani ƙoƙari kikayi sosai ba,kuma kinsan ana buƙatarsa sosai"
"Eh dai yafi naki,khairiyyah kam naga taci nata,kodayake tana buƙatar sanin computer dole ta dage,shikuwa wancan mai engineering ɗin yanada aiki a gabansa sosai"
"Menene aiki a ciki,sa kaine fah abin,gani yayi zai iya shiyasa yayi"
"Uhm hakane kam,amma ba'a nan gizo yake saƙarba,kuɗin yin karatun shine aikin"
"Kin fiye hasashen nesa sabrah tun baki ga farko ba,ke kam ki zubawa sarautar allah ido mana"
"Uhm muna ta surutu yamma fa tayi gwanda mu hanzarta komawa gida"
Na faɗa ina ƙara saurin tafiyata,itama khamriyyah dana faɗa sai a sannan ta kula ashe ta bar inno da rainon su fadeela,gashi ba lafiyace da itaba,ciwo yaƙi ci yaƙi cinyewa,anyi tiyata amma har hanzu kukan ciwo take da daddare,musamman idan tasha wani ruwa ba na pure water ba.
Ƴar tsokana muka cigaba dayi a hanya na yau da kullum har allah ya kaimu gida.
Ɗakin inno muka shiga dan mun hango takalmin maman yara a wajen,da alama kenan tana ɗakin,gabana ne ya buga,wanda suma sauran daga ganin kan fuskarsu kasan hakanne a ransu,dan daga ganin yanayin bana lafiya bane.
Shiga mukayi da sauri can uwar ɗakin inda muke jiyo nishin inno maman yara tanayi mata sannu.
A kwance take akan katifar hannunta yana dafe a mararta,jijjiga kai takeyi da alama ciwon yana matuƙar cin jikinta.
Nice na kalli khamriyyah ta sauri kana nace,
"Khamriyyqh barinaje na nemo mota mu koma asivitin,dama sunce idan wani abu ya faru to a koma da wuri"
"Ahah bazamu koma can ba,asibitin garinnnan zamu kaita,munada buƙatar musan mai yake damunta da farko"
Kallon alamun tambaya nayi mata,sai kuma nayi shuru,dan wanann ba lokacin magana bane.
Fita nayi daga gidan zuwa gidan maƙwantanmu,yanada motar dayake haya,watakil zai iyah taimaka mana.
Ina zuwa kuwa nayi sa'a yana nan,saidai yana shirin fita,dawowarsa kenan daga aikin,uzurina na bashi wanda hakan yasa ya amince.
Tare muka shigo gidan na wuce ɗakin domin nuna masa,lokacin khamriyya ta aza kanta a cinyarta tana shafa mata ruwa.
General hospital muka nufah da farko,amma ganin sunan asibitin da sukayi mana aiki yasa furr suka ƙi karbarmu,a cewarsu dole saidai mukoma inda akayi mana aiki.
Kallon khmariyyah nayi wacce ta cije bazamu tafi katsinnan ba,to ina take so muje.
"Dan allah yaya Sale ta ɗan kaimu Ali Maibara hospital mana"
Karkara motar yayi zuwa can ɗin,dayake suma 24h suke buɗewa.
Da sauri aka turata zuwa ɗakin gaggawa,saboda ganin yanda ta galabaitah sosai.
Katinmu suka baƙaci mu bayar,nice nake riƙe dashi dan haka na fitar zan nuna musu,saurin maida hannu khamriyyah tayi tareda ɗan ƙaryar dakai tace,
"Uhm dama ranki ya daɗa bamuje wani asibitin ba,jiya ta fara ciwon to dayayi tsanani shine muka kawota nan"
Da kaman bazata yarda ba saboda ganin ɗinikin dayake kan cikin inno,amma kuma saita basar saboda ciwon ya warke garau,zata ɗauka maybe ba ciwonsa bane.
"Toh shikennan yanzu zaku jiramu anan za'a kaita ɗakin scanning,zanyi ƙoƙarin saka file ɗinta da wuri saboda ganin halin datake ciki,kuna iyah zama kafin a fito da sakamakon.
"Mun gode sosai"
Shine abinda muka faɗa dukkanmu a tare,waya ƴar nokia ɗinnan khamriyyah ta daga tareda faɗawa maman yara inda muke,dan itama girma yafara kamata ciwon ƙafa take fama dashi,bazatayi mana sauri ba shiyasa muka taho,inyaso tazo daga baya.
Ƙiran sallahr magriba ne ya tashemu a wajen muka shiga ɗakin da inno take kwance.
Anyi mata scan ɗin amma dole saidai mujira gobe da safe kafin muji sakamakon,sun yimata allurar kashe zafi dai ɗazu,wanda hakan yasa ta samu bacci takeyi.
Muna idar da sallahr ne maman yara ta shigo itada khariyyah da kular abinci a hannusu,sai a lokacin ma na tuna ashe fah inajin yunwa.
Khamriyyah da maman yarane suka koma gida,inya so gobe da safe saisu dawo.
Dan su fadeelah sai kuka suke suna ƙiranta,gashi babu kowa a sashennamu sai yara.
Bacci dai rabi da rabi mukayishi,ga yanayin ƙasar tamu na sauro,ga kuma tashin da inno takeyi,wasu sunaye take ta ambata in mukayi magana ma bata ganemu kwata kwata.
Wajen misalin ƙarfe bakwai khamriyyah ta dawo asibitin,hannunta ɗauke da flask ɗin kunu,ita kaɗai ta dawo maman yara tana gida .
Nan muka cigaba da zaman tagumi bayan mun karyah,har zuwa lokacin da likitar ta turo muje mu sameta.
Shuru mukayi dukkanmu muna sauraren mai zata zo mana dashi,
"Kuyi haƙuri jiya lokaci ya ƙure shiyasa muka barku a duhu,maganar gaskiyah tiyatar da akayi mata a baya ta ƙoda tayi kyau sosai,saidai kuma rashin bin ƙa'idoji kafin ta warke ne ya jawo hakan,kasancewar yanzu ƙoda ɗaya ce da ita,dole sai tana kula,to saba dokar yasaka dole sai an mayar da ita anyi mata wankin wajen,mu bamayi a nan,zan rubuta muku takarda ku tafi katsina"
Me mai take cewa,jinayi gabana yayi dummm data ambaci ƙoda,amya kuwa result ɗinmu ta faɗa,duk da ina zargin akwai wani a tiyatar amma ba har haka nake zargaba gaskiya.
"Likita anya kuwa result ɗinmu kika faɗa"
"Kwarai ma kuwa,akwai wani abune dayafaru?"
"Ahah babu komai ,inaga tana cikin halin ruɗewane"
Khamriyya ta faɗa tareda jana waje,kallonta nake ita kanta da mamaki,da alama tasan wani abun daban wanda ban sani ba ni.
"Ke sabrah ki nutsu mana,kinaso ta gano asibitin da sukayi mana aikine,idan ta gano duk wani abu zatayi domin riƙemu a nan wajen"
"Me kike nufi khamriyyah"
"Hmmm abubuwa da yawa,bakiyi mamaki ba da daga kallon takardar asibitin general suka ƙi karbarmu,saboda zasu fuskanci barazana mai kyau idan sukayi hakan.
Suna amfani da sunan wani ciwo si dunga ciran sassan mutane batareda saninsu ba,wanann dalilinne yasa suke iya ƙoƙarinsu wajen boye bayanan su,sannan suna da ƙarfi shiyasa kowa yaja bakinsa yayi shuru da aikin da,sukeyi"
"Inna lillahi,muma muna ɗaya daga cikin wanda sharrinsu ya faɗa kanmu kenan,gashi sunfi ƙarfin hukuma inaga mu kuma,yanzu ykk ganin zamuyi"
"Yanda zamuyi a fili yake,zamu koma asibitinne a yau"
"Kuttt suyi mana wannan zaluncin kice mu koma kuma?,tabbas abinda zafi sosai,yana cinmu a zuciya,amma bazamuje ba su sake kashemu"
"Bazasu kashemu ba,hasalima zasuyi iya ƙoƙarinsu wajen yiwa inno magani,kin manta su suka sakata a cikin halin,kuma sannan abinda sukayi suna iya ƙoƙarinsu wajen binneshi,shiyasa ma basaso wani asibitin su shiga cikin zancen.
Karki damu zasuyi manaagani,sannan kuma zamu kokarin bin diddigi a can,abu ɗaya zamuyi shine .
Karmu sake mu nuna musu cewar munje wani asibitin,kuma munsan abinda yake damunta,idan suka san hakan kuma dagani har ke mun zama shaƙaƙƙu"
Tashin hankali kenan! Hantata ce ta kaɗa saboda jin bayanan da khamriyya tayimin,wannan wace irin rayuwace,mutum yana fama da talauci,ga kuma wahalar rayuwa,amma hakan bai isheshiba sai an ciremasa wani abin da allah ne yayi masa,bashida kuɗin sayarsa,amma su dasuke da watada naka ma bazasu bar maka ba saisun ƙwace,zuciyata ce tafara tafasa da kwakwalwata ta fara tunomin abubuwan da akayi ta mana a shekarunnan,kana ganinsu kasan tsagwaron zaluncine kaɗai,mugunta da kuma son zuciya.
Komawa mukayi ɗakin inno,idonta biyu tana kallon silin,saidai bata jijjigar da cije baki irinna jiya kafin mu kawota,tausayinta ne yakamani da irin zaluncin da akayi mata,wanda kuma nasan ba iya ita kaɗai akayiwa ba harda dubunnan mutane bil'adama,inshaallah zamuyi iya ƙoƙarinmu wajen ganin bata san abinda ya faru da ita ba,dan hawan jininta zai iya tashi murasata gaba ɗaya a kowanne irin lokaci idan taji labarin.
Karkatowa tayi a hankali tana kallon mu,yayinda wani siririn hawaye yake bin gefen kuncinta,babu abinda yake kan fuskarta face tsoron tafiyah ta barmu a wannan duniyah babu kuladamu,karisawa nayi da sauri na gurfana gwiwoyina a gaban gadonnata,nima zuwa sannan karfina ya kare na riƙe kukan.
Jijjaga kai nake tareda furta magana cikin dashashshiyar murya.
"Ahah ki daina irin wanann kallon,babu inda zakije inno muna tare,zaki samu sauƙi kawannan da izinin ubangiji"
Khamriyyah ce ta shigo da paper a hannunta tana jingine da jikin ƙofah.
Kallonta nake ganin tayi shuru batayi magana ba,inaga so take nazo muyi magana a waje.
Sanin hakanne yasa na muka fita waje.
"Sabrah na ƙarbo mana takardar sallama,sign sukayi akan sun turamu DR BUKAR INTERNATIONAL HOSPITAL,na karba amma bazamu tafi da takardar ba saboda kada sugane mun san mai ya sameta,zamuje kaman yanda sukace muje idan wata matsala ta faru"
Ɗaga mata kai nayi kawai,danna san zata iyah ji da lamarin fiyeda mu gabaki ɗayah.
Komawa ɗakin mukayi domin shirye shiryen tafiyah garin katsina a gobe,duk da munsan wajen amma ba ƙaramin aiki bane,ɗan kuɗin da muka ajiye na aikin da khamriyyah tayi da kuma zuwa shagon khariyyah,yanzu ma dole muka lallameta ta tafi,ogansu sai kiranta yake saboda ƙwarewarta a shagon.
*****______******_______******
Karfe shaɗayah a asibitin tayi mana,da wurwuri muka fita danma mun tsayah a kan hanya abinka da motar hayah.
Cikin sauri babu bata lokaci akan shirya mana dubata,dayake sunsan abinda suka shuka,masu dubatan jikinsu har rawa yake wajen yi da sauri,idan baka saniba ma dole sai kayi mamaki,duk wannan rawar jikin a banza babu ko sisi a Nigeria kuma,hakan ma mutum yasan bazaiyiyuba sam.
Duk inda sukayi binsu kawai muke da ido ganin yanda suke aiki babu tsayawa.
Wata matace zatayi shekaru talatin dai ta fito daga wani office mai daraja a cikin asibitin,idanuwanta jajur sukayi tana share hawaye,duk da tana iyah ƙoƙarinta domin kar a gane halin data ke ciki.
Khmariyyah na kallah wanda ashe itama hankalinta yana kanta,duk wanda suka kawo marasa lafiyah harma da wanda suka dawo kamarmu sai murna suka suna sakawa asibitin albarka,mu kaɗai idan mai hankali ya kallemu zai gano munsan wani abu,amma dayake bakinmu a rufe muke shuru kakejinmu,dan gano munsani tamkar zama matattune.
Wata nurse ce ta nufomu bakinnan a washe kaman gonar auduga. Munafuka na faɗa araina.
"Sannuku yan mata,aiki ya kammala yanda akeso,munyi nasarar gyara mata tiyatar,yanzu babu matsala,amma duk da haka a kiyaye ka'idojin shan ruwanta da kyau"
Tunda tafara maganar shekeke muke kallonta,jinake kaman na doketa,a wajen khamriyyah kam ma yafi haka.
"Amma tiyatar appendix akayi mata,shin mai haɗin appendix da abinda mutum zai sha ma'ikaciyar jinya?"
Ɗan murmushi tayi,amma daga gani na shiga zullumine.
"Ehh....toh dama hakane mana,tunda akwai ciwo a cikinta tana buƙatar kare lafiyarta wajen cin abu mai kyau"
"Amma kuma da farko kince abinsha,yanzu kuma abin sha,munyi bincike babu abinda ya haɗa tiyatar appendix da kuma shan ruwa marar kyau malama"
Waigawa gefenta tayi,ganin babu wanda yake kallonta yasa ta jamu da sauri zuwa wani corridor,har gumi ya fara tsatstsafowa a jikinta na razana.
"Kunga...nnnasan kuna cikin ruɗani gameda ciwon mahaifiyarku,amma ina rokonku da allah ku tsayah daga binciken dakukeyi,dan bazai haifar muku da ɗa mai ido ba.
Wani abin zaifi kyau ka barshi a duhu daka haska da fitila kaga menene"
Tana gama faɗin hakan ta dafa kafaɗar khamriyyah tareda yin murmushin takaici ta bar wajen.
Ɗakin innon mukaje domin ganin aikin da sukace mana yayi kyau ɗin.
A kwance take akan