Author : Auwal sadiya Category : Free Novels Online (Read & Download)
gado mai kyau da laushi,kaman gaske.
Cije le'ben bakina nayi na ƙasa kafin na isa inda take kwancen,ba laifi kam daga gani muna saka ran tashinta lafiyah.
Mun kwana kana mun waye amma har yanzu inno bata tashi ba,hankalinmu ya ɗugunzuma ya tashi,saidai kuma masu zuwa dubata akai akai sunce babu matsala sosai,zata tashi inshaallah.
Mu huɗune a zaune da deen khariyyah sai kuma mu dama muna nan,maman yara kam munce ta zauna saboda ƙafarta,kulada gidanma da takeyi ya ishemu komai.
Khairiyyah ce ta shigo ɗakin tana haki tareda sauƙe ajiyar zuciya,yatsanta kuma yana nuna waje,saboda kiɗima har ta gagara cewa komai.
Dukkanmu kallon ta mukayi harda khamriyyah wanda fitowarta kenan daga banɗaki.
"Bbbbaaaban su fadeelah,wlh shi nagani ya shiga wani office a cikin asibitinnan yanzu nan"
"Ke khairiyyah kalau kike kuwa,ai wanann tsinannan mutumin kika gani kuwa,dama yana duniyar"
Na faɗa da alamar tambaya.
"Kutt harna kasa ganeshi,taya kike zaton zan manta da wanann fuskar a yanzu,kaman su ɗayah dasu fadeelah idan kika ganshi,yafi kama dasu musamman idan kinganshi da rana,shida wani ne mai baƙin glass.
Da alama kuma sunada matsayi a asibitin,dannaga kowa yana gaishesu"
Tashi nayi da gudu zan fita khamriyyah tayi saurin riƙoni tareda cewa.
"Bakida hankaline sabrah,me kike shirin yi haka,kinsan wane irin garaje kike ƙoƙarin aikatawa kuwa?
Da manyan mutane kike ƙoƙarin haɗa sabga,wanda shari'ah ma ta kasa yi musu komai,(wani murmushi tayi bayan ta ɗauke hannunta daga kan kafaɗata). Kibar komai a hannuna sabrah,cikin sauƙi da dabara zamuji da komai,bilahillazi jinin maryam da kuma budurcin anty juwairah harma da ranta da kuma hakkin su fadeelah bazai tafi a banza ba,sannan kuma inna gama dashi na dawo fansar ƙodar inno,babu wanda zai sha a hannuna daga cikinsu,zamu nuna musu muma mun iyah dabanci da iya shegen"
Dukkan mu shuru mukayi muna jinta har tafita daga ɗakin,komai zata iyo allah masani.
Ganin wasi wasin ina zataje bazai kaini ba yasa na bita da sauri,amma ina fota babu ita babu alamarta,waige waige na fayi ko zan ganota,can na hangi wata mai shara da goga na ƙoƙarin shiga office ɗin MD ,har tazo shiga ta tsaya tareda juyowa inda nake ta ƙiftamin ido.
Wani numfashi naja na razana ganin waye sanye da kayan,khamriyyah ce tasha wata ɗamara ga baƙi tashafa a fuskarta ya maida itah baƙar dole,yaushe har tayi wannan shigar na faɗa a raina.
Dukkanmu sauke ido mukai akan khamriyyah wacce tashigo da kayan masu goge gogen a jikinta tana haki,
"Maza maza ku shiryah munada aiki babba,nagano anguwar dayake zaune,a yau basai gobeba nakeso mu gama dashi,saboda akwai abinda muke buƙata daga wajensa"
"Ke khamriyyah me kike faɗa,taya zamu gama dashi,tukunna ma ya akayi kika gano inda yake "
"Na'urar da khairiyyah ta haɗa a shagonsu ta bin diddigi nasaka masa a motarsa,sannan kuma riba biyune,naji yanacewa zaije sirrinsa,kunga zamu san inda yake,abinda muke buƙata shine motah"
Nuna deen tayi da yatsanta wanda yayi sororo yana kallonta,
"Mekikace,ni zan jaku zuwa inda za'a hallaka mu,inaaa bazan fara ba"
"Hmmm zakace haka mana,nasan zaka faɗi haka,shin kamanta abinda yayi mana ne,kuma har yanzu yake kan yiwa wasu,amma duk da haka mu barshi ya cibaga da yin abinda yake so,ku zaku iyah mantawa da abinda yayi ku cigaba da rayuwarku amma ni bazan iyaba,sannan bazan tirsasaku ku tayani ba,zanyi ni kaɗai a ƙashin raina"
Yanda take maganar kanaji kasam daga ƙasan zuciyarta maganar take fitowa,idonta ya ciko da hawaye amma da sauri ta mayar dashi kaman yanda ta saba.
"Ta wane bangare zan taimaka"
Khariyyah ta faɗa tana kallon khamriyyan,kuma yanda tayi magana babu alamar ja da baya.
"Ki taimaka mana da tracking ɗinsa,dama na saka masa na'urarki a motarsa"
Nima ganin hakan yasa na ce
"Toh bari mu gwada training ɗi aikinmu muga ko zaiyi aiki?"
Kowa murmushi yayi a cikinmu,da alamar aiki zai soma.
Inno kuwa tana kwance bata farfaɗoba,bamu da matsalar barinta,dan munsan zasu kulada itah tamkar muna nan.
Farawa mukayi da aron mota wacce zamu bisu,amma saida muka cire lambar motar tukunna.
Tafiyah muke muna bin danjar dake screen ɗin wayar khariyyah har muka fita daga gari.
Nidai zancen gaskiya tsoro yafara ɗarsuwa a raina,idan suka kamamu kuma fah ya zamuyi kenan.
Toh allah dai ya tsare shine addu'ar.
A bakin wani baƙin gida suka tsaya a dokar daji,tsittt kakeji babu kowa a wajen sai ƙarar tsayawar motarsu a can baya cikin bishiyoyi.
Wata riga naga khamriyyah ta ciro jaaa mai ɗan karamin hijab,dukkansu kallona sukayi ganin ta mikomin kayan,ni suke nufi wai zanje.
"Kije bayan bishiyar can kisaka kayannnan,a maganar dasuke naji za'a kawomasa wata yarinyah daga club,dan haka zakije a matsayin itace,basai na faɗamiki ba kinsan yanda zakiyi,ga takardar nan ki ɗan duba bamuda lokaci"
Ta ƙarisa maganar tana miƙomin wata ƴar kwalba,ko ban faɗaba nasan magani fitarda mutum a hayyacinsa ne.
Jikina yana rawa cikin dauriyah na karbi rigar da niyyar sakawa,yanda nake tunanin zan gwada basirata anya kuwa zan iya?.
Bayan na gama saka rigar mai shegen kyau,wanda itama a hanya muka ɗaukota a wani shago,ina mun gama saimu biyasu,kwalliyah tayimin sama sama,daga nan kuma na nufi hanyar gidan kirjina na dukan uku uku.
Kaina tsaye na nufi hanyar shiga wajen,a zato zasu tsareni sai kuma naga sun matsamin na wuce.
Yanda nake tunanin wajen ba haka yake ba ta ciki,wajen aljannar duniya,ga kuma lunguna kala kala kaman wani masana'anta,maganar da akayi min ne yasani zaburah na waiga bayana.
"Kece miss Suhailah?"
"Eh....eh nice"
"Ranki ya daɗe to nan zaki bi,zuwa sashen ogah"
Ɗaga kai nayi tareda binta ina rausayah kaman wata bishiyah lokacin damina.
Tafiyah muke waje daban daban,har muka isa waje dayafi ko ina kyau a ginin.
Murɗa kofar tayi nasaka kai a cikin falon,wowww aljannar duniyah kenan,wani turnuƙuƙin baƙin ciki naji yana cina,yayinda duk wani tsorona ya bace a cikin zuciyata,ya cutar da mutane ya kashe mutane yayinda wasu ya keta musu mutunci,shikuma yana nan a zaune babu abinda ya dameshi,harkar gabansa kawai yakeyi.
Kallonsa nake yana tsaye da riga marar hannu a jikinsa,sai three quater wando,murmushi yakeyi har dimple ɗinsa yana motsawa.
Mai kyan ɗan maciji kenan,dui yanda zanyi sai na bada gudunmawa wajen duomiyar da rayuwarsa shima,kaman yanda ya dulmiyar da ta wasu rayuwar shima.
Koni ko kuma shi!!!!........
Taku
_sadi-sakhna_
Ƴar mutan jama'are.
*MABARACIYAH*
_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)
25••26
Shu'umin murmushi nayi saurin yi tareda kashe ido ɗayah.
Ga mamakina kuwa saina ga ya narke wa kallon nawa,duk da ba wata kwalliya nayi na azo a gani ba,sannan kayana basu wani nuna tsaraici ba,abu ɗaya nasani shine inada kyau sosai.
"Barka da zuwa duniyar saifuddeeen ƴan mata,ki saki jikinki ko kawashi ɗaɗi da kuma daulah,allah ya kashe ya baki"
Ya faɗa cikin dashashshiyar murya irin ta ƴan bariki,jinayi kaman nayi amai saboda amon maganarsa,amma haka dole na daure tareda ƙaƙalo murmushin dole.
"Nagode da wannan damar daka bani,nima zanyi ƙolarin shayar dakai ruwan daɗi daga korama ta mai ɗanɗano"
"Hhhhh inajiran wanann daɗi baby"
Ya faɗa yana shafa gefen fuskata,juyawa yayi ya shiga wani ɗaki,babu yanda na iya haka na bishi,indai inason cimma burina to dole saina daure.
Sakin baki nayi ina kallon katafaren gadon dayake girke a tsakiyar ɗakin,badan komai aka sakashi ba sai dan sabon allah,kai azubillah.
Zama yayi a bakin gadon yana ƙaremin kallo.
"Babby ke kyakykyawace sosai,barina shiga banɗaki na dawo,kafinnan na yi oder a kawomiki abin motsa bakii.
Yana gama faɗa ya cire rigar saman tareda wurgata akan gadom yashige banɗaki dagashi sai ɗan wando.
Wata ajiyar zuciyah na sake daya bacewa ganina,anya kuwa zan iyah,tabbb ban taba ganin zingimemen mutum haka ba rigaba,yau gashi na gani ƙiri da muzu.
Wata matace ta shigo dauke da faranti da lemuka akai kala kala,ajiyewa tayi a gabana bayan ta gaisheni tareda ficewa da sauri,da alama tana tsoron kar ya shigo ya gantane,haka kawai naji ban yadda da zaman ta a wajen ba,daga gani dole akayi mata abubuwan datakeyi.
Saurin tsiyanya lemon nayi a kofi danaji motsin fitowarsa,hannuna yana rawa na zuba maganin tareda kaɗawa dan karya gani.
Tundaga fitowarsa da yanayin kallon dayake min ya nuna alamar akwai wani abu a ransa.
Ina nan zaune ya saka wata ƴar karamar riga fara da kuma farin wando,ƙaryah nake ma idan nace bayyi kyau ba,da haka suke yaudarar mata,nima kuma saina fara yimasa kallon na folawa halittatar tasa,duk da ta ciki kaman zan fashe dan tsoro.
Zuwa yayi gefena ya zauna,yayinda kamshin turarensa ya cika hancina..
Lemon dayake kan tiren na ɗauko tareda miƙamasa ina murmushi,yayin da nikuma na kai wanda yake hannuna baki.
Saurin riƙe hannuna yayi tareda karbar lemon,wanda na miƙa masa kuma ya kaishi saitin bakina,ɗan zaro ido nayi ganin mai yake ƙoƙarin shirin yi.
"Hmmm me kike zato,kina nufin bansan bake nayi booking ba,ina hankalinki ya shiga da kika kasa ganewa saida naga wacce na zaba kafin nayi booking,ke kuma saiki zo kawai kuma na yarda dake,hhhhh da haka nake da tuni an gama dani,saboda mutane bila adadin na barazanar ganin bayana.
Yanzu in kina so ki fanshi kanki to ki shanye wanann lemon yanzunnan"
Ya faɗa yana miƙamin na hannunsa,babu yanda na iyah haka na bashi nawa tareda karbar nasa mukayi musanye.
Ɗagawa nayi na sha kusan rabi kafin na ajiye,yayinda shikuma ya shanye wanda nake ƙoƙarin sha.
Shuru mukayi babu mai cewa komai can sai naga ya fara gyangyaɗi,aikin yayi kyau yanda ake so.
Kallon idonsa nayi ina dariyah,
"Mai kake nufi kaima,a zatonka dama sha zanyi,jira nake ka karbi nawa wanda shine mai sinadarin a ciki,wanda na baka da farko babu komai a ciki,dama na san kana zargina,sannan kuma nasan ka gane bani kayi booking ba,dayake ance rana dubu da barawo rana ɗaya ta mai kaya,shiyasa ka barni har nazo i yanzu a wasan,yanzun dai ka shirya ga baƙi nan shigowa"
Layi yake tayi amma yana ta iya ƙoƙarinsa wajen ganin bai bari abin ya cinyeshi ba.
Ɗaukar wayah nayi tareda bugawa su khamriyyah wayah.
"Kun gama shiryawa,toh na bashi yasha,yanda kikace kuwa haka ya kasance,yanzu zan kurma ihu sai ku shigo bayan minti biyar"
Inagama kashe wayar na kifta masa ido daidai lokacin dayake fadawa kan gadonnsa,nikuma nayi waje da gudu ina ihun ya faɗi.
"Wayyo jama'a kuyi sauri ya faɗi yana fitowa daga banɗaki,nakira motar asibiti ma suna kan hanya"
Muna cikin hakanne khamriyyya suka shigo itada khariyyah da kuma deen,sun sha uniform kaman ƴan asibitin,dan dama munyi shiri tun rana kafin muka zo wajen.
Da sauri suka kinkimeshi muka nufi waje dashi tareda sakashi a motar.
Securityn kuma suka nufi motarsu domin binmu a baya,danni ma ana sakashi na shiga da sauri ina kuka.
Dukkansu key sukayiwa motocin amma suka ƙi tashi,wannan aikin deen ne,kafin suyi wani abu tuni mun bace a cikin duhun daren,sai kurar motar kawai.
Tafiyah muke cikin gudu,duk da munsan bazasu iyah biyomu na amma saboda tsaro.
Sai wajen goshin asuba kafin muka tsaya a wani ƙauye nesa da garin katsina kaɗan.
Wata bukka muka shiga tareda daɗɗaureshi a ciki tamau..
A daren khairiyyah da deen suka koma cikin gari wajen inno,yayinda khamriyyah kuma dani muka zauna.
Kasa jure tashinsa khamriyyah tayi,hakan yasa ta ɗebo ruwa a wani masaki a gefen rafi ta shaƙa masa akansa.
Wata zabura yayi tareda jan numfashi yana ƙare mana kallo,tambaya ce cike fall a bakinsa amma ya gagara furtasu.
"Kana mamakine malam saifu,shari'ah ta gagara ɗaureka mukuma mun ɗaureka koh,wanann ba wani abin damuwa bane,yanzu dai abu ɗaya zuwa biyu muke so.
Na farko information akan dr bukar zaka bamu,na biyu kuma wannan akan ka ne,yanzu dai fara bamu na farkon.
Kuma karkayi gigigin ƙin bayarwa,wlh kasheka zamuyi mukashe banza mu bar wajennan."
Duk da yana ƙoƙarin dakewa amma daga gani warninng ɗin khamriyyah ya shiga kwanyarsa sosai."meyasa kuke buƙatar information akansa?"
"Kana tambaya ne dan karmu cutar dashi kaman yanda mukayi maka,toh illatashi zamuyi da mun samu da bamu samuba.
Mun riga munsan cewar yana amfani da jinyar talakawa yana cire musu ƙoda daya,sanann kaikuma idan ka ɗauko yara mata daga gidan marayu ta taimakon yaranka masu zuwa a matsayin ma'aurata marasa ƴaƴa,saika siyarmasa da tsada bayan ka gama lalatasu ta hanyar yimisu fyaɗe da sauransu,shikuma idan ya cire ƙododinsu saiya kashesu,ka faɗamin abinda nasani daya wuce wannan."
Diridiri ya farayi,dan bayyi zaton munsan har wanann kason daga cikin aikinsu ba.
Dariya khamriyyah ta sheƙe da ita wacce banyi zaton ta iyata ba,
"Mungama da wanann zangon idan ka zayyano min yanzu da bakinka"
Ganin da gaske ba imani a cikin ƙalbinta yasa ya fara koro bayanai harda wanda bamu sani ba har ƙarshe.
"Yawwa to yanzu faɗamana lambobin asusun bankink"
Ƴar dariyah yayi tareda cewa
"Nidama nariga nasani kuɗine yasa kuke wanann wasan,tun farko nace muku ku faɗa,idan kidnapping ne da yanzu ankawo muku kudinku na tafi,neman ai harda saboda iriku muke tarawa"
"Eh duk naji mai kace,yanzu dai faɗamana asusun banki"
"Bazan faɗa muku lambobina ba,ku faɗi nawa kuke so na baku kawai,idan ba haka ba kuma ku rasa gabaɗaya,dannasan yanzu ana ta nemana,babu daɗewa za'a kamaku,zuwa sanann kuma ku ji tausayin kanku"
Wani drill khamriyyah ta dauko tareda sokashi a kan cinyarsa,dan tsabar tsoro nima saida na juyah,ga ihun sa ya cika wajen,banda jinin dayake ambaliya a cikin bukkar.
Fitar dashi tayi ta nufi maƙogaransa,da sauri ya riƙe hannunta yana jijjiga kai,har sannan ihu yake muryarsa har ta dushe.
"Zan.........zanfaɗa wlh zan faɗa"
"Yaron kirki,nayi zaton ai kaizaka fara rasa ranka kafin mu rasa namu muzama abin tausayin"
Numbobin yafara faɗa,daga ɗaya bangaren kuma khairiyyah tana jinsa har ya gama.
"Yawwa aiki na biyu ya kammala,saina ukun ka kashe kunnenka kaji mai zan faɗa,yanda harka mutu maganganun zasu dunga taroyowa a cikin kanka.
Bazan kasheka ba duk da inada muradin hakan,kasan dalili?....saboda ƴaƴanka danake matuƙar so a rayuwata,taya zan fuskancesu nace musu na kashe ubansu,duk da a wajensu kai mataceccene dan haka nake faɗamusu.
Saidai zanyi musu abu ɗayah,zan dakatar dakai daga yimusu ƴan uba,zan datse ƙarfinka na maza,sannan kuma da sake haihuwar wasu yaran,dan dama hakan shine hukuncinka a kotu wanda batayi maka ba"
Ihu ya fara jin furucin abinda ta faɗa,nima kaina na razana dajin abinda ta faɗa,duk da a cikin raina naji daɗin hakan,koba komai zuciyata zatayi sanyi da abinda yayi mana.
Gudumar da take gefenta ta ɗauka bai ankaraba ta sauƙe akan gabansa,dan azabar data jiyarceshi ko ihu kasawa yayi,sai tsayawa kawai yayi yana kallon yanda take murmushin daɗin ɗaukar fansa,kafin yayi yaraf akan kijerar sumamme.
Ƙarar wayar khariyyah mukaji,datake hannuna,
"Ke sabrah kuyi saurin barin wajennan dan angano motar nan ta taho,sanann kuma an sallami inno Ta tashi jiya da daddare,kuma babu matsala"
"Ya zancen kuɗin kin cire"
"Dukkama kuwa,na ciresu tass ban bar ko kwandala ba a ciki"
"Dakyau gamunan zuwa yanxunna toh"
Figar hannunta nayi muka fita da gudu karmuje su samemu a wajen.
Muna fitah muka samu mota mai zuwa cikin gari muka ɗale,bamu tsaya ko ina ba sai bakin asibitin.
A zaune muka samu inno khariyyah tana haɗa ɗan kayan da mukaxo dashi.
Ita kuma tana zaune akan gadon,turus mukayi tareda inda inda bamusan mai zamuce mata ba idan tace daga ina muke.
"Mukan muna shirin tafiya ai,da bakuyi sauri ba bazaku samemu ba,kunacan gidan ƙawarku"
Ajiyar zuciya nayi tareda dariyah danaji ashe khariyyah ta boyemu ma.
Mun fito zamu tafi gida,daidai lokacin kuma ake shigowa da saifuddeen a gadon asibitin,duk jikinsa jini ne babu inda kansa yake.
Kallon khamriyyah nayi wacce ta ɗaga min gira tareda yin murmushin gefen baki,suma su deen murmushin sukayi,ma'ana aiki yayi yanda ake so.
Bayan kwana biyu da dawowarmu jikin inno yayi sauƙi sosai,dan yanzu tunda babu yanda zamuyi munsan mai yasameta to munabin ƙa'idoji yanda ya kamata,har sanann bamuyi zancen kuɗin da muka kwaso a asusun saifuddeen ba,gashi sai neman wanda sukayi danyen aikin akeyi a gari.
A zaune muke dukkanmu a bayan gidannamu,ganin kowa yana nan yasa na taso maganar kuɗin da khamriyyah tace na mu kwaso.
"Khamriyyah bakice komai ba akan wanann kuɗaɗen har yanzu"
"Aikinsune bai zo ba shiyasa,nawane kuɗin duka duka"
"Miliyan Hamsin ne 50M"
Khariyyah ta faɗa.
"Iya kuɗinnasa kenan ma"
"Ahah ina tunanin ba iya nan yake ajiyewa ba,wannan ƙaramin asusu ne"
"Shege yana ganin taurarin mutuwa amma son kuɗin yana ransa,dama duk a nan suka hallaka ai.
Inaso mu gina gida a garin katsina,sannan muyi karatun daya kamata yanda zamu iyah tunkarar sauran,domin rashin ilimin bazai kaimu ba,sanann zan kulada rayuwar su fadeelah a cikin kuɗin,harma da karatunsu,idan nasamu aiki kuMa saina cigaba da kuladasu da kaina,ta haka zan biyashi kuɗinsa,dama na ubansu ne ai,gadone basuda shi amma sunada hakkinsa "
Ihu muka saka dan dama kowa yana son zuwa makarantar,maganinsu kenan adunga kwashe kuɗin
Sai a sanann na tuna ashe ina som zuwa Alqalam,makarantar tanayiMin a rayuwa,ita kuma khariyyah wai makarantar computer technology takeso,shikuma deen atbu,yanason Mechatonic Engneering.
Mai gayyar kuma karatun State security zatayi(SSS), saboda sajewa a cikin masu bincike.
Tun daga lokacin muka fara shirin abinda mukace zamuyi,dan har mun riga munce daga wannan babu abinda zamu sake,bayan dr bukar,kowa zayyi karatu yakama abinda yafi.
Wata rana muna tsaka da shirin tafiyah makaranta saiga wasu mutane daga katsina,sunzo nemanmu,babu bata lokaci aka saka ankwa a hannunmu nida khamriyyah,wai angano mune mukayi wa Asibitin dr bukar sharri,kallon kallon muke akan yaushe hakan ta faru,saidai babu wanda zai ji mu bare bamu amsa.
Inno tana kuka muma munayi sai kurku a garin katsina,abinda bamu saniba ashe angano cewar munsan mai yake faruwa a asibitin nasa,daga bakin wanann nurse ɗin,kuma ctv camera ta ɗauki khamriyyah lokacin datake saka kayan masu aiki zata shiga office ɗin dr bukar,saboda jin mai saifudddeen zaice,kuskuren damukayi kenan wanda muna ganin mun gudu ashe bamu tsiraba.
Sannan kuma shaidu sun nuna mun je asibitin Ali Maibara kan zancen.
Kai mutane dai ba'a iya musu a rayuwa.
Kwanan mu uku a kurku babu wanda ya waiwayemu,banda wuyah da ƙazanta babu abinda muke ciki.
Sai a kwana na ukunne aka shiga kotu kan sai mun amsa laifinmu a gaban alƙali.
Duk yanda aka kawo shaidun ƙaryah wai wani ne ya sakamu muke ƙoƙarin shafawa asibitin kashin kaji,dan haka dole mu amsa laifinmu.
Barr shehu ne ya fito tsakiyar kotun idonsa kyam akanmu.
"Malamai shin zaku iya faɗamana sunanku na gaskiyah?"
Har zanyi magana khamriyyah ta dakatar dani tareda cewa
"Sunana khadija ita kuma zainab,dukkan mu a gidan marayun daurah muka taso"
"Shin menene yasakaku yiwa asibitin dr bukar sharri,akan cewar yana kashe mutane,sanann an ganku a asibitin kuna bin diddigin ma'aikaciyar lafiyah,sannan kuma ke khadija kinyi baɗda kama zuwa cikin office ɗin shugaban aaibitin.
Bugu da ƙari kuma kun shiga ɗakuna da dama kuna yaɗa musu ƙaryar cewar kashe mutane ake a asibitin,bayan kuma ba iya jahar nan ba hatta nigeriyah kowa yasan karamci da kuma taimako irinna wanann asibitin"
Cikin ɗaga muryah khamriyyah tace.
"Wannan ƙaryane ba haka akayi ba,kawai sharri ake yimana"
Yana jin ta faɗi haka yayi murmushi,dama abinda yake