Author : Auwal sadiya Category : Free Novels Online (Read & Download)
bangaren eemran kuwa a zaune yake akan wani dutsi yana juya wani abu kaman ƙwallo ƙarama a hannunsa.
Tunda ɗazu yake zaune a wajen har rana tafara isoshi,sai yazo tashi yafara aikinsa,sai kuma yatuna da yayi mata alƙwarin zai jirata,duk da shima har ransa bawani jin zuwantan yake ba,amma yanajin babu daɗi ya saba mata alƙawarin daya ɗauka.
Jiyayi a jikinsa kamar ana kallonsa,wanda hakan yasa ya juya gefensa na dama,a tsaye take da goduwar riga a jikinta,saikuma mayafin datayi rolling a kanta..
Bugun zuciyarsa ne yaji ya ƙaru katt kafin ya koma yanda yake.
Yana mamakin irin wannan yanayin dayake ji a iya gareta baga kowaba,tunda yake yasan bai taba shiga wannan yanayin ba,tukunna ma bai shirya shigansa ba koda yanada buƙatar hakan.
Zuwa yanzu yafara tsoron tarayyarsu da deejan,kar a garin neman gira shiya rasa idonsa gabaɗaya fah.
Takowa take a hankali,idonta nakan fuskarsa wanda shima ya tsura mata ido..
Tausayinsa ne da kuma jin babu daɗi na tsayar dashi yana jira suka mamaye ranta.
Maida idonta tayi kan bakinsa wanda ya jajur,da alama matseshi yayi a cikin bakinsa yabada wannan kalar.
Ɗan runtse ido tayi tareda control ɗin zuciyarta dan karta kawo mata negetive thinking a wannan lokacin.
"Eemran ina kwana,duk da ina wuni ma yayi kusa,dan allah kayi haƙuri na tsaida ka,wani muhimmin aikine ya taso wanda nakeson yinsa a lokacin"
"Daga yanda kike bada labarin nasan yanada muhimmanci sosai a wajenki aikin"
"eh to kusan hakan,aikin dana faɗamaka hajiya fulani ta banine,alhamdulillah nagano amsar abinda yake damunsa yanzu.
Ta faɗa tana faɗaɗa murmushinta,ta wata fuskar kuma tana nazartar eemran ɗin,dan ganin wane yanayi zai nuna.
Dan murmushi kawai yayi tareda maida kallon wajen dawakan da suke ɗaure.
"Muna masa fatan allah ya bashi lafiya,ko domin wannan yaron ya daina ganin shine da mulkin garinnan,naji daɗi daya zamo yanzu kin fita a cikin barazanarta,yanzu dai tashi mu tafi bayin allah suna jiranki ki basu abinci"
Tayi mamaki da bai tambayeta abinda yake damunsa ba,saikuma tafara tunanin inaga zairginsa take a da leƙen asirin kawai,yanzu haka ba abinda yake nema a wajen.
Wasa da dariyah suka cigaba a wajen bawa dawakan abinci,deeejah ta ƙyar take kaiwa hannunta kusa da bakinsu,hakan ma sai anyi da gaske.
Wani dogarine yazo inda suke tareda cewa
"Ke deejah saƙo daga yariman masarauta wato mai girma jalal,yan ƙiranki zuwa sashensa akwai abinda zaku tattauna"
Kallon eemran take wanda shima dogarin yake kallon,hannunsa kuma a dunƙule da alama ransa ya baci da wannan maganar.
Har ya buɗe baki zayyi magana deejah ta rigashi tareda cewa.
"Ina nan zuwa amsa ƙiransa yanxu nan"
Bayan dogarin ya tafi ne ta juyar da kallonta wajen eemran ɗin,har sannan fuskarsa a haɗe,kaman bashine yake mata dariyah yanzu ba.
"Karka emran babu abinda zai faru,zanje na dawo lafiya kaman yanda na tafi,yin maganar ka zai iya jawo maka matsala ko a koreka"
Tafiyah tafarayi a hanyar dazata kaita sashen yarima jalal ɗin.
Batayi tsammanin zayyi magana ba sai taji yace.
"Idan kika wuce minti talatin baki dawo ba zaki ganni nazo ɗaukarki,ki kula dakanki,shine kaɗai zai kwantarmin da hankali"
Ɗaga kai tayi alamar taji kafin tabar wajen.
"Duk da cewa ina fargabar zuwanki wajen,amman na tabbatar daga yanayinki kin fi ƙarfin matan da yarima jalal zai iya juyawa,tundaga kallon mai hankali zai ga ƙarfin kwarjininki (aura),wanda zai tabbatar masa da cewa ke ɗin ba irin sauran mata bace.
Bakida jinin mulki a jikinki na ji hakan,amma kuma akwai halayyar tafiyar da mulki a tattareda ke,ko ban gani ba dole kin taba zuba mulki da jagoranci koda a kuwa a tsakanin iya mutum biyune.
Daga ni har ke dukkanmu munsan akwai dalilin dayasa kowa yake aikin dayake,saboda kowa a cikinmu yasan ɗan uwansa ya wuce matsayin aikin dayake.
Kowa a cikinmu yanada boyayyen kuɗuri a ransa,kaman yanda nasan kin ganni da daddare ina duba sashen hajiya fulani,nima na ganki lokacin da kike magana ke kaɗai ba kowa a gefenki cikin dare,sannan naji tatttaunawar maganin da kukayi,duk da dama nasan abinda yake damun yarima mubarak tun shekara goma sha huɗu baya"
.......toh fah..........waye eemran? Zasu shirya da mabaraciyah kuwa idan ta gano.
Taku
_sadi-sakhna_
Ƴar mutan jama'are.
*MABARACIYAH*
_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)
37••38
Tundaga bakin sashennasa take juyo hayaniyarsa shida muryoyin mata guda biyu..
Batayi kasa a gwiwa ba ta ƙarisa cikin falon.
Komai na wajen ja ne,kama daga kujerun table harda labulaye da kuma carpet.
Wata ƴar yarinya ce bazata wuce shekara sha takwas ba akan cinyarsa,ɗayar kuma tana gefensa yasaka hannunsa a cikin rigarta.
Dukkansu magana suke cikin maye,amma kuma bai kai ya gusar musu da hankali ba.
Kallon su deejah take idonta a tsaye,ɗaya bayan ɗaya kafin ta samu waje ta zauna a kujerar datake facing ɗinsu.
"Keee dana aika a ƙiraki sai yanzu kika ga damar zuwa koh?,wato rowar daɗinki kikemin dan kinga ina kwaɗayinsa koh,to barikiji na faɗamiki,duk wayonki saina moreki na kwashi romo,jiyama kwana nayi ina begenki"
Ɗayar ce da take kan cinyarsa ta bata fuska tareda hararar deejah,wacce tun ɗazu kallonsu take batace komai ba.
"Wannan kucakar ce dama kayi ta mana kukanta da daddare?,amma lallai ka bada mu,ni nayi zaton zanga wata ceelah,ashe wannan ce?"
"Ke diamond,ki kiyayayi zaginta fahhh,karki rainani dan kinga tauraruwarki ce take haskawa"
Har deejah tayi niyyar tashi ta tafi saikuma tayi wani murmushi tareda dawowa.
Idonta ta ƙanƙance tana kallon nasa tareda cije fatar bakinta ta kasa. Cikin kasalalliyar muryah tafara magana,wanda ko su daƙyar su iya wannan shu'umancin.
"Mai girma yareema,bansan mai yasa ka ƙirani ba,amma koma menene kamata yayi mushiga daga ɗaki tukunna,ko anan kakeson ganinnawa?"
"Ahah muje ciki na faɗamiki,dama nasan dan gaban wannan ƙazamin ne shiyasa kika ƙi nunamin nufinki a gameda tayina"
Ture wacce take kan cinyarsa yayi gefe tareda miƙawa deejah hannunsa.
Kawar da kanta tayi kaman bata ganshi ba,wanda hakan yasa dole ya miƙe da kansa.
Tafiyah yake yana layi har yashiga ɗakinnasa,ita binsa tayi tareda juyowa ta kashewa matan da suke zaune ido.
Zama yayi a bakin gado yana ƙaremata kallo,ita kuma ta riƙe bakin ƙofah tana kallonsa.
"Mai kike jira a tsaye,zo nan nabaki labari mai daɗiiiii"
"Zanyi farincikin zama a kusada kai na saurari labarinka,amma kafin sannan kaima saikayimin abinda nakeso,idan bakamin ba kaida........."
Ta kalli jikinta daga sama har ƙasa.
"Haramiyarka,dan haka yakace toh"
Kana ganinsa kasan ya kwaɗaitun da jikinnata,musamman yanda take jijjiga da gangan a gabansa.
"Adadin wane kuɗi kike buƙata a wajena"
"Hhhhhhhh kuɗiiiii,nafi ƙarfin kuɗi jalal,bazaka iya sayen abinda kake so a wajena da kuɗi ba.
Saidai amma abinda nakeso inka yi yanda nace bai kai kuɗin ba ma.
"Ina buƙatar bayanai akan mahaifiyarka,kama daga na kuɗi da duk wani abinda kasani gameda ita.
Ba wanann ne babban ba,inaso ka ɗaukomin wani jan akwati a ƙarƙashin gadonta,idan kayi nasarar ɗaukomin akwatinnan toh ka faɗamin duk abinda kakeso"
Kallonta yake da mamaki kafin yace.
"Babu wani abu a wajen mahaifiyata sai kuɗi,idan kina so zan baki,mai zakiyi da wani akwati kuma?.
Akwaitinnan tamkar rayuwarta haka yake,kullum saita dubashi kafin ta kwanta,sannan idan har bata gidan toh shima baya nan,inaga dashi take tafiya ko ina"
"Eh dama idan ka ɗaukoshi zan baka wani kasaka a wajen,wanda zatayi ta ganin wancan ɗin a matsayin shine.
Karka min musun cewa bazakayi ba,dolene sai kayi jalal,saboda babu mai min idan bakai ba,idan kuma bazakayi ba toh,............saika zaba ko damar mulkinka a garinnan ko kuma ɗaukomin akwatinnan"
"Me kike nufi da hakan? Ke har kin isa ki tsoratar dani"
"Hahahahah namafi haka jalal,kasan wani abu.....duk matan daka kwanta dasu a satinnan na zuwana gidannan inada vedionku dasu,sannan nice mai kulada rashin lafiyar mubarak a yanzu,kuma kasan me? Nagano wace irin rashin lafiya yake ɗauke da itah,sannan zan iya nema masa magani da izinin Allah.
Idan har ya warke wa kake tunanin zai riƙe mulkin garinnan tsakanin kai dashi.?"
Zaro ido yayi tareda ɗauke ƙafafunsa ya maisu kan gadon.
"Idan fahimceki kinaso kicemin idan nayi miki wannan abin bazaki yimasa magani ya tashi ba harsai na karbi mulkin garinnan?"
"Kacanki amsar daidai abokina,idan kuma baka samomin ba,zan saki vedionka kuma bazaka moreni ba yanda kakeso .
Faɗawa wani kuma wannan maganar,..hmmmm...... Kayi hasashen cewa kaima ga naka gadon a gefensa kana baccin rashin jiran tsammani.
Dan kaima kwantar dakai zanyi kaman yanda yake kwance"
Jikin yarima jalal ne yafara rawa jin kashedin datayi masa,kuma idonta kawai ya kalla yasan zata iya,shi yanzu bai yadda cewar ita mutum ce bama.
"Yawwa yaron kirki,ka manta da mun haɗu anan wajen har sai ka kawomin abinda nakeda buƙata,gobe hajiya fulani zata dawo,dan haka gobe zaka ga akwaitin dazaka saka mata a ɗakinka da safe.
Aikinka sannan zai fara,saika shiryah"
Murmushin mugunta tayimasa bayan tagama faɗan hakan kafin tabar ɗakinnasa.
Har deejah tafita daga ɗakin bai saki ransa ba,gumi ya rufeshi shirkiff,shikansa yasan ya jawowa kansa tsiyah yana zaman zamansa,sunan wani littafi na yaƙi waishi GABA TSINI BAYA TSIYAKI.
___________________
A bangaren su dec. Sadeeq kuwa,ko yaushe yana hanyar gidan su sabriyyah,wani lokacin ma anan yake cin abincin dare.
Zuwa yanzu sun saba dasu kahriyyah sosai,musamman ma faɗansu da sabriyyah,gashi ɗakinsu ɗayah.
Yauma khariyyah ce da fareeda a kitchen suna abinci,sai sauri suke karsuyi dare,dan sun san uncle Sadeeq yana hanyar zuwa daga anyi magriba.
Dadduma aka shimfiɗa a tsakar madaidaicin falon,tareda jera abincin daren.
Duk wanda yagani sai abin yabashi sha'awa.
Bayan sunyi salla zama sukayi suna jiran zuwan Sadeeq ɗin.
Khairiyyahce ta kalli sabrah wacce waya take hannunta,da alama basu daɗe dayin waya da shiba.
"Ke dallah ki faɗawa wancan mijinnaki yayi yazo muna jiransa,duk ni ta wajensa ce amma yaufah babu sauki,dan yunwa nakeji sosai ,tunda na dawo daga wajen aiki banci komai ba(aiki take a wata center ta conputer,Dec. Sadeeq ne ya sama mata,satinta guda kenan da farawa,ita kuma sabrah so take ta cigaba da karatu idan komai ya lafa na aika aikar da sukayi. Fareeda kuma tunda mutane basu san da itah ba ta koma aikinta na bincike).
"Kuttt ke khairi mijinnawa ne kike wannan maganar,bari yazo na fadamsa,daga yanzu ya daina kulaki,iya fadeelah zai dunga kulawa,koh fadunah?"
Tsalle fadeelah tayi jin an ce itah,gwaliyo tayiwa khariyyah wanda hakan ya ƙara ƙularta.
Dama ita ga shiriri ta,sai ta dunga abu kaman ƙaramar yarinya.
Tashi tayi zata duka fedeelan datake yimata dariyah,inno tana uhm uhm amma sunayi.
Dariyah sabrah takeci harda rike ciki,ƴar kara tayi daidai shigowar Dec. Sadeeq.
Da sauri ya isa wajenta akan kujera yana tambayar mai ya faru..
Ɗan zame jikinta tayi tana kallon su inno,wanda suma suka kawar da idonsu,da alama kunya taji.
"Babu komai hayatee,kawai dariya nakewa su fadeelah,sainaa ji cikina yaɗan kama."
"Ayyah amma ki dungayi a hankali,kinsan yanzu kin fara nauyi,gobema inshaallah zamu tafi gida,na faɗawa ummah halin da ake ciki"
Zaro ido sabrah tayi,tun kafin tayi magana umman su sadeeq ɗin tashigo falon da sallama,da alama kaman waya tatsaya yi.
"Salamu alaikum"
"Wa'alaikissalam"
Suka amsa mata,inno ta tashi tareda nuna mata kujera.
Kalon sadeeq tayi wanda yake manne ta sabrah,itakam kanta a ƙasa ta gaisheda umman,kunya duk ta isheta ta sadeeq ɗin,sai tureshi take amma ko a jikinsa.
"Inno nikam sai yau yake faɗamin abinda ya faru,kullum baya dawowa gida sai bayan isha,idan ya koma yace ya ƙoshi da abinci,sai nake tambayarsa ina yake cin abinci.
Ganin raina zai baci shine fah yake fadamin cewar,ashe nan yake zuwa kuke cin abincinku sai ya koma.
Kuma dayake yaga dama shine yake fadamin abinda yasa ta dawo gida,da nayi zaton faɗa sukayi,ashe abin gagarumine,banda sha'anin yaro ai sai ya faɗa tunda farko.
"Hakane kam hajiya abune gagarumi,ni kaina dakika ganni bansan da labarin ɗaukar wanann fansa tasu ba sai daga baya,su ganin wai shari'ah taƙi yimusu adalcine.
Amma komai yafi ƙarfinka ai saika barwa allah"
"Toh yanxu dai zanyiwa mahaifinsa magana akan lamarin,komai muka yanke zakuji daga garemu,amma uhmm abin akwai dubawa,tashi mutafi Abbakar zan je gidanmu zanyiwa hajiya saratu gaisuwa tunda ta dawo"
Tashi sadeeq yayi tareda yiwa su inno sallama,dukkansu kowa yayi jugum,dan kowa ya kalli fuskar umman yasan da wata a ƙasa,bazuwa tayi sasanto ba,tazone domin tabbatar da rashin amincewarta akan Abinda su khariyyah sukayi.
Shiga mota tayi ta hakimce tana jiran shigowar sadeeq,wanda kana ganinsa kasan baiji daɗin abinda tayiba.
"Wai zaka shigo motar kaja mujene ko kuwa sai dare yayi mana kai.
Banda sakarcinka duk da abinda sukayimaka harka samu damar zuwa wani gun ɗiyarsu,wacce tun farko danta cutar dakai ta aureka?.
Hannunka mai sanda nayi musu ai idan sunada hankali,kuma aurene dole sai an tsinkeshi,babu yadda banyi dakai ba ka auri yar yayana mai martaba wato Madeena,ta gaji sarauta gaba da baya,ga gidan mutunci amma kayimin biris da zancen.
Kaje ka auro wacce ko asalinta bata ma saniba bareta bawa naka ƴaƴan,ga abin karin ma sheɗaniya makashiya masu kashe manyan gari.
Dan haka bakai babu ita daga yau,batun saki bazance saika saketa ba,idan ɗana yakama su ma aka zo zartar musu hukinci ai dole ka saketa idan kaga zata ƙare a gidan yari.
Hmmm ɗan cikinnata ma daya zama jininmu takaicinsa nakeji,ai wani abin ma sai babanka yaji labarin,ba ita ba har kai saika fuskanci fushinsa.
Kuma aure babu fashi yanzu,madeena tana gama karatunta a BUK za'a tsaida ranar aure,banason sakejin labarin wannan yarinyar a bakinka."
Masifah ummannasa ya dungayi har suka shiga cikin gidan masarautar katsinan bata daina,ta inda take shiga ba tanan take fitaba,shikansa yasan yau babu mai kwatarsa a wajenta.
Ta barshi yaji da abinda tayiwa dangin masoyiyar tasa mana,hmm dan basu san yanda yakeji akan sabrah bane shiyasa duke faɗan hakan.
Kuma yanda suka ɗauki su khairiyyah shiba haka yagansu ba,mutanennan cutar dasu akayi,amma kowa yimusu kallo yake kaman sune suka fara zaluncin,bayan kowa idan shine ba daɗi zaijiba..
Shikuma dec. Khaleel yace masa ya tafi daurah fara bincike daga farko akan labarin su sabrah,da kuma ya akayi suka haɗu da khamriyyah.
Shikamsa har yanxu bai gama yarda da itah ba,dan komai akayi itace ta shiryah,su aiwatarwa kawai sukayi,in hukunci ne ma ai ita yakamata a yiwa basu ba.
(Toh kaima ashe ka iya son kai ɗin.
Har ummah ya yi hanyar shiga sashen hakiya fulani sadeeq bayyi niyyar binta ba,yana jingine a jikin motarsa ya faɗa kogin tunani.
Kallonsa take cikeda takaici,don tasan zancen gizo baya wuce na ƙoƙi.
"Ni kaɗai zan shiga kai bazaka shigaba,kodan nayi maka faɗane matar yayannawa ma bazaka yimata gaisuwa ba"
"Kai ummah ni ban faɗaba,dama da kunzo keda meena ita so take ki barta tazo tayi hutu ma anan"
"Banga damar zuwa ta itaba dakai naga damar zuwa,a haka zata ganka a matsayin surukin da take tunani"
Bin bayanta yayi suka shiga sashen hajiya saratun.
A falo na biyu lami tayi musu iso suka shiga,dayake kowa yasan Hajiya Khadeejah,wacce ƴar hajiya fulani ta Nana khadija.
Ita ɗayace ƙanwar Mai martaba,wanda suke uwa ɗaya uba ɗaya,.
Sauran mata guda biyu dukkansu ba a garin suke aure ba,kuma su mahaifiyarsu daban,daboda halin hajiya fulani dakuma irin zaman da'akayi yasa basa zuwa garinma sosai.
Kasancewar salaha batada lafiyah tana ciwon mara na baƙon wata,yasa deejah zuwa a madadinta domin kawomusu ruwan sha.
Tsugunnawa tayi ta gaisheda Hajiya deejah wacce take mai sunanta,harma da saurayin data gani a gefenta,wanda ko kallonta bayyi ba hankalinsa yana kan waya.
Bayan hajiya saratu tazone suka fara gaisawa,cikin raha da sanin juna.
"Uhm ina kuwa Fulani ko yanzu ma bata nan kaman kullum"
"Hmmm Addah bata nan,tayi tafiya wai Singapore,amma gobe zata dawo inaga,haka naji a wajen hamman naki"
"Hmmm sai kuyita haƙuri,ya hakuri na rashin waziri da akayi kuma"
"Alhamdulillah Hajiyan yara,yazama dole hakuri kam ai,Babana kuma yanaga yana haɗe rai kaman ya haɗiyi kunama,daga gaisawa yayi shuru,ni rabona dashi ma na manta,inaga kuma babangida,wanda shi tun yana yaro rabona dashi,bakwason zumunci sosai"
"Hmm kema kya faɗa,dani yake wai na masa faɗa,mata yaje ya ɗakkota babu asali ba komai,sai jawo fitina a gari.
Bazan iya da rike matar nan tasa a matsayin suruka ta ba,duk waccar ja'irar kamriyyahrce ummul aba'isin.
Kizama cikin shiri hajiya saratu,domin madeena tana dawowa za'a saka ranar bikinsu,waccar matar kuwa ko yana yaso ko bayaso idan ya daina ganinta dole zai haƙura"
Ita dai hajiya saratu shuru tayi tana sauraran hajiya deejah,gabaɗaya bata fahimci komai ba na maganar,dayake babu ruwanta sai kawai ta zuba musu ido,har zuwa lokacim da jakadiya tasanar mata cewar mai martaba yana jiranta a falonsa idan ta gama.
Sallama tayiwa hajiya saratu kafin suka fice itada sadeeq.
Duk abinda suke deejah da take rakabe a bakin ƙofah tana jinsu har suka gama.
Lokacin da suka zo fitane ta koma can nesa kaman mai jiran wani.
Bayan fitarsu da minti biyar itama lami ta fito,dan dama ita take jira
Tafiya suke shuru babu mai cewa komai,sai deejah ce ta katse shurun ta hanyar cewa.
"Ni yadiko lami waɗannan ɗin suwaye suka zo?"
"Ohh ashe kefah baki dade anan ba,hajiya deejah sunanku ɗaya,ƙanwar mai martaba ce wacce take auren General muhammad Kareem. Shugaban masu harkar tsaro na garinnan.
Wannan dakike gani kuma Abbakar Sadeeq babban danta ne,yanada ƙanwa ɗaya mace Ameena,ana ƙiranta da meena.
Saikuma ɗan yayarta data mutu da take riƙo wato Ibrahim khaleel"
"Uhm allah ya jikanta,barina je na kwanta"
Daga haka deejah ta wuce sashensu tana jinina abin a ranta,dama dec. Sadeeq yanada alaƙa da gidannan,dolene ta zama cikin shiri kenan.
_______________
Sai wajen yamma kafin hajiya fulani ta dawo daga ƙasar data tafi.
Mutane sai shiga ake da fita kaman itace mai sarautar garin,dama ance yanzu kuɗine yake mulki bawai martaba ba.
Saida magriba tayi kafin mutane suka dauke ƙafa daga gidan.
Bayan deejah ta idar da sallah ne taji muryar zainabu a bakin sashennasu,shigowa tayi tareda zama a kasan ɗakin.
"Deejah idan kin gama hajiya fulani tana nemanki akan maganarku,kiyi gaggawar zuwa yanzu nnan"
Tana gama fadan hakan batace komai ba ta tashi tabar ɗakin
Kallon alamar tambaya salaha tayiwa deejah,saidai kuma ganin babu razana a fuskarta yasa ta bar zancen.
"Kinsamu aiki a sashennata ne,nayi mamaki sosai,dama tana ɗaukar hausawa ne a sashenta?"
"Ahah ba aikin abinci bane,wani aikine da ban,bari naje ina dawowa"
Daga haka ta fice ta nufi sashen hajiya fulanin.
A hakimce ta ganta a falonnata tasha wasu kaya baƙaƙe sai walwali suke da stone,ga kamshi yana tashi,da alama turakar mai martaba zataje.
"Uhm ina jiran amsarki,ance kinzo kin dubashi jiyah,mai kika fahimta gameda ciwonsa,idan kuma baki saniba ko kuma kika faɗamin abinda ba hakaba,keda sake ganin hasken rana sai a lahira idan ta fito"
"Ɗanki yareema mubarak babu wani ciwo a jikinsa.
Bashida kuruwa a jikinsa wato rauhunsa bayanan an kamashi a wani wajen,shiyasa yake kwance kaman mai bacci,tsawon wannan lokacin"
Ɗan murmushi hajiya fulani tayi tareda rausayar dakai,da alama dama tasan mai yake damunsa tun da.
"Kin samo amsar daidai,babu abinda yake damunsa face raahin kuruwa a jikinsa,nasan da hakan ,ina jiran mai maganin dayasan hakan,shiyasa na ajiyeshi domin ƙwato kuruwarsa.
Zan nemeki gobe yanzu akwai