MABARACIYAH Daga Bara Zuwa Firgitar Masu Iko by Auwal sadiya

Author :  Auwal sadiya Category :  Free Novels Online (Read & Download)

Chapter   33 / 33

96K to 96.8K   out of 96.8K words

tareda zuwa kusada shi ta zauna bakin gadon.
"Yaushe kashigo,kenan na daɗe sosai?"
"Uhm ba sosai ba,ina kin iyo Alwala,yakamata muyi yanda ake a darennan,dan ya fi albarka,bamu tsayah sai wani lokacin ba"
Daga kanta tayi alamar tayi alwalar,daga nan ta dauki hijabinta ta saka,yajasu sallah raka'ah biyu.
Sun daɗe suna addu'oi,zuwa lokacin khamriyyah ta jera hamm sun fi a ƙirga.
Ganin hakan yasa ya dakata suka hau gadon.
Duk da baccin dayake cinta sosai,amma tanajinsa yana sarrafa jikinta ta kasa yunkurin hanashi,tausayinsane ya kamata,ganin ita kanta shaidace shi mutum ne mai gudun abinda yake haramun gareshi,ita wacece kuma dazata hanashi halal ɗinsa,bayan tsawon shekaru daya ɗauka yana jiran zuwan halal ɗin,yajure ɗauke kansa daga haram duk rintsi duk wuyah,irin wannan mutumin zata hana hakkinsa dan kawai bacci yana cinta,inaaa bata fatan takasance cikin wannan matan.
Ita macece marar tsoro,amma kuma mai matuƙar bin matakin yanda ya dace koda kuwa zata danne muradin nata zuciyar.
Sakin dukkan jikinta tayi,tareda miƙa masa dukka ragamar sirrinta da kuma akalar rayuwarta,har xuwa lokacin daya kai matakin maidasu abu ɗaya ita dashi.
(Wanda sukeda aure Allah ka zaunar dasu lafiya a gidajensu,ka albarkaci rayuwarsu data yayansu.
Wanda kuma har yanxu Allah baka basu damar yi ba,Allah yabasu miji nagari,wanda zaija ragamar rayuwarsu har zuwa ga matabbata mai kyau.)
_____________________________


_Bayan shekara ɗaya a china_

Khamriyyah ce a tsaye a bakin kofar ɗakinsu sai bubbuga kafa take tana sangartar gangan.
Tayi tuleliyah ta ita,tundaga kafatunta har zuwa fuskarta.
Tayi fari kam sosai,saboda tsohon cikin dayake jikinta.
Duk abinda takeyi Khaleel bai kulata ba,saima cigaba yayi ta ciro mata kayan ta daga cikin drawer ta.
"Wai ni yah khaleel nace maka lafiyata kalau,kalli fah yau har breakfast nayi mana,nayi excersice ɗina ma nasafe"
"Ban yarda dake ba,jiya kwana kike kina saƙƙowa kasa daga kan gado kina murƙususu,akwai abinda yake damun babyna kike boyemin,kima daina wannan gardamar kizo na shiryaki mutafi asibiti ehe.
Duk nasan wayonki bai wuce kice kin kalau kike ba,gobe mukama hanyar komawa gida,ba inda zan tafi dake cikin jirgi a haka,so kike haihuwa tazo miki a jirgi murasa yanda zamuyi?"
"Niba haihuwa zanyi ba,lokacin fab bai zoba tukunna,nina gaji da wannan kasar chanhu chanhu ɗin,mutafi gida kawai,khariyyah ma ta haihu banje ba nina gaji da wajennan.
Yanxun ma cikin rigima ta karishe maganar ,inda sabo ya saba,kullum tana cikin kuka da gardama,abinda batayi da ba shi cikin yasaka mata sosai.
Hannunta ya jawo suka nufi banɗaki,sai cuna baki take.
Sun kusa awa kafin suka fito da towel a jikinta,kayan yake bata tana sakawa,inda bata kai ba kaman zuge ziff yayi mata,har sannan taƙi sakin ranta.
Ɗaukar ta yayi ya kaita har mota ya ajiyeta,daganan yadawo ya kulle gidan suka tafi.
Tun a hanya take riƙe bayan ta tana yarfe hannu,shidai yana kallonta bai ce komai ba,sai waya dayayiwa midwife dij datake dubasu,akan gasunan zuwa,sanan ya kara gudun motar.
Suna zuwa aka wuce da ita labor room,shidama ya kula naƙuda takeyi da daddare,irin tsayawa tayi da safe,shiyasa tace masa kalau take,tayi zaton bai ganta ba.
Jijjiga kai kawai yayi yana murmushin halinnata,abin mamaki kuma a tsawon lokacin bai taba jin ya gaja da sauraranta ba,saidai in yan miskilancin suna na yayi mata shuru.
Yana cikin tunaninne yaji an tabashi ta baya..
Yana juyawa suka haɗa ido ta nurse ɗin da baby a hannunta cikin towel,zaro ido yayi yana tunanin karba,dan bai kawo a ransa nasa bane.
"Congratulation,you have beautiful baby daughter,you see the mommy if you like,she is in good condition"
Tun kafin tagama bayaninta ya nufi ɗakin da khamriyyah take ciki.
A zaune ya babu kowa a ɗakin sai nurse masu gyara wajen.
Zama yayi rungumeda babyn a hannunsa har khamriyyah ta fito daga banɗakin.
Kallonta yake cikeda tsantsar ƙauna har ta isa inda yake ta zauna tareda ɗora kanta akan kafadarsa.
"Nagode daka fini sanin kaina da kaina habeebty,ina kewar su inno sosai,nasan ka faɗamusu koh"
"Uhm na fadamusu,muma jibi zamu tafi a private jet na binciken nigeria dasuka zo,ina kin tabbatar bakyajin matsalar komai koh?"
Da sauri ta ɗaga masa kai tareda washe baki da murmushin jin daɗi.
"Nagode sosai my king"
"Ur welcome my queen,ummu zahrah"
Dagowa khamriyyah tayi daga rungumar da tayi masa tareda cewa.
"Sunan daka sama kenan? Sunan wa taci?"
"Ba sunan kowa ba,sunanta a sakamata saboda darajarsa"
"Allah ya rayata da imani,yabamu ikon rainon tarbiyyarta bisa turbar gaskiya"
"Ameen ya Arhamar Rahimeen"



Thammat bihamdullillah.

Anan na kawo karshen littafin mabaraciya,muna fatan Allah ya yafemana kuskuren da mukayi,wanda mukayi daidai kuma Allah ya bamu ladansa.
Ina fatan an fa'idantu sannan kuma an nishaɗantu da fasaha ta.

Allah ya hadamu da alkhairinsa a wani littafin inda kwananmu.


Masoya da ƴan uwa musulmai inayiwa kowa fatan Alkhairi,dan Allah a yafemin idan nayiwa wani laifi ko kuma na soki wani ta wani bangare na littafinnan,rashin sanine.



ALHAMDULILLAH.





Taku
_sadi-sakhna_
Ƴar mutan jama'are.




33 / 33