MABARACIYAH Daga Bara Zuwa Firgitar Masu Iko by Auwal sadiya

Author :  Auwal sadiya Category :  Free Novels Online (Read & Download)

Chapter   25 / 33

72K to 75K   out of 96.8K words

hakan bake kika sakani ba,idan kin yarda muhaɗu gobe"
"Eh na yarda,buƙata shine kiyi abinda nace,na warware wannan abinda kikayi"
"Ke wacece,da kikeson bada rayuwarki domin wasu daban,ki dawomin da abinda kika ɗauka,nikuma zan maidake abinda bakya zato a nigeria"
"Wannan kawai nake bukata,saboda soyayyar danake yiwa ɗanki"
"Uhm Allah kuwa ya tsinewa soyayay in hakane,shiyasa banga komai a cikinta ba sai wahala"
"Bazaki gani ba kam,tunda kika kasa jin son ƴaƴanki"
Daga haka deejah ta juya tafita a sashen,babu abinda taji a ranta,dan tasan babu abinda zata mata indai har akwatinnan yana hannunta.
"Hmmm zaki ɗanɗana kuɗarki,Allah ya kaimu goben,daga nan tarihinki ya ƙare a doron ƙasa,saina miki abinda zaki buƙaci mutuwa dashi"
Tana fita silver ta kalleta tareda cewa.
"Amma meyasa kika amince mata,bayan kinsan idan babu akwati saidai fah ki maida gubar dake jikin Junaid kanki,inba haka ba sai kinyi musu alƙawarin wani na jikinki dazasu ɗauka"
"Nafiki sani silver,nasan dodo bashida yafiyah.
Amma kisani na shiryah haɗa musu tuggu ne da bazasu iya tsallakewa ba daga ita har su
Nasan bazata iya samun wanda zai buɗe mata akwatinnan ba a mutane,dan haka zan wanke kaina a gabansu tamkar na tuba da abinda nayi musu,daga baya kuma bayan nacire abinda yakd jikinsu,zata dawomin da akwatin.
Nikuma saina kasheta itada sarkin garin,na bada jininsu ga dodo a matsayin yarjejeniyata batareda su junaid sun sani ba.
Kinga na dawo da yarda ƴaƴana ita kuma na kawar da ita,zan jefi tsuntsu biyu da dutse guda kenan"
"Amma kuma kaman suna soyayya da junaid fah"
"Hhhhh kaman kin mantani kennan,daga lokacin da na ɗorashi a mulki zan maidashi mutum mutumi ne,bazai san komai ba sai abinda na sanar dashi,ba zai ganiba saina nuna masa,bazai jiba saina faɗamasa.
Kede ki tsaya kiyi kallo gobe,deejah kuwa duk da ta taimakeni a plan ɗina tayi kuka da kanta,dan saina yi mata abinda ban taba yiwa wata halitta ba"
Junaid ta zubawa ido daga inda take zaune,zefi zefi yake ɗagowa ya kalleta,tun yana basarwa har abin yafara bashi mamaki.
"Deejah menene ya faru,idan naganki kinamin wannan kallon to da akwai abinda yake damunki,ko kin kwarewa soyayyatane kema amma kin rasa yanda zaki faɗamin?"
"Batun soyayayr ka dama na daɗe a ciki ai"
"To meyasa kika ƙi amincewa zuciyarki"
"Saboda batada ikoyin hakan koda kuwa tanada buƙata,in tayi ma zata cutar da kanta ne sannan kuma ta cutar da wanda yake son ta.
Idan hakane taya wannan zuciyar zatayi garajen wannan kasadar"
"Wace irin kasada kuma?"
"Kayi hakuri junaid da abinda na aikata maka a yau,na bayyanawa mahaifiyarka wanene kai"
Zaro ido yayi yana kallonta,bayyi tunanin hakan daga wajenta ba
"Hakan bazai haifar maka da kowacce matsala ba,hasalima nayi wata yarjejeniya ne da ita,in exchange zata cire gubar dake jikinka,daga nan komai zai daidai ta shikenan"
"Me zaki bata,nasan koma menene akwai illa a cikinsa"
"Kayimin uzuri bazan iya faɗaba,kona faɗamaka ma bazayyi amfani ba,tunda ta riga ta amince"
Shuru junaid yayi yana kallon deejah,duk da cewa daga nan bai sake cewa komai ba

"Allah yayi mana mai kyau,amma ban miki alƙawarin bazan bincika menene ba da kaina,tunda bazanji daga gareki ba"
"Nikuma dan allah ka taimakeni karka shiga sashennata da kanka,idan kayi hakan shikenan"

Kaman yanda ta faɗa kuwa,a ranar ta aika a ɗauko mata gimbiya khadija daga gidan aurenta,duk da cewar ita babu komai a jikinta,amma saidai tana son ta buga wasan a gabanta.
Dukkansu bude ido sukayi suka kallesu a wani a gida wanda basu wayeshi ba.
Junaid ne yafara juyawa ya kalli khadija,wacce itama kallonnasa take da mamaki.
"Kai kuma waye daga ina kake?"
"Kina nan da faɗanki da kuma taƙamarki kenan Kadidi"
Fuskarta ce ta nuna alamar mamaki,domin tasan sunan tun suna yara su junaid suke faɗamata.
"Ke addah khadija ina fah da hannunsa a ɗaukomu,banda haka mai mukayi,kuma kinga can yah mubarak ma a cikin akwatinsa,me yake faruwa"
Yar dariyah Junaid yayi,dan shi yasan mai yake faruwa,a yanda sukayi magana da deejah jiya yasan yanada alaƙa da wannan yanayin.
"Me kukeci na baka yana zuba,wanda ya kawomu wajen zai bayyana kansa ai,basai kunyi wahalar tambaya ba"
Har khadija ta bude baki zatace wani abu kalmar ta makale,ganin mahaifiyarsu ta fito daga wani ɗaki.
Zaro ido sukayi,dan inka ɗauke junaid da kuma deejah da take gefen ɗakin a zaune babu wanda yasan zai ganta a lokacin.
"Ummmah mai muke anan wajen kuma,wani kikayi mana?"
"Ko ɗaya ƴata babu abinda namiki,abinda nayi muku a bayane nayi nadama,shine nakeson gyara kura kuraina idan zaku bani dama"
Ta ƙarisa maganar cikin sigar tausayi da nuna nadama.
Itama khadijan cikin mamaki tace
"Ummah kece kuwa? Amma naji daɗi da hakan ta faru,koba komai farincikinmu ne mu ƴaƴanki"
Dan murmushi tayi tareda shafa fuskar khadijan,
"Hakane kam, na saka wani aljani dayake ɗaga darajarki fiyeda ta sauran yan gidan mijinki,harma da kishiyarki,zan janye na barki ki zauna lafiya,nasan yin hakan zai sa mai martaba ya daina jin haushinki na yin zalunci a gidan miji.
Kaima jalal na taka rawa wajen lalacewarka,domin in zaka gujemin kabi ra'ayin mahaifinka nina hanaka.
Haka kaima junaid na ajiye Guba ka sha,duk da bakai na ajiyewa ba,amma kuma ina sane na barka a wajen ranar dan kar nawa asirin ya tonu.
Saikuma mubarak,da kaina na bada rauhinsa saboda wata buƙata tawa,saidai zanyi iya koƙarina wajen gyara laifina.
Dafatan zaku fahimceni"
Fadawa jikinta khadija tayi tana kuka.
Ƴar dariyah deejah tayi babu wanda ya jita sai junaid da tun ɗazu ya kulada ita a wajen,amma kuma bai nuna ya ganta ba,haka kawai yakeji a jikinsa akwai wata a ƙasa na halayyar da uwar tasa take nunawa a yanxu.
Wajenda mubarak yake kwance ta nufah tareda ɗora hannunta akansa.
Wani abu takeyi na kusan minti biyar kafin ta ja wani numfashi,da alama aikinnasa ya bugeta.
"Zai iya tashi daga nan zuwa gobe,komai zai koma normal,saikai junaid "
"Ahah bana buƙata,inda gaske tuba kike bai kamata najiki kina ambaton sunan wasu aljanu ba,indai da shirka zaki warkarni to na ƙwammaci ciwom ya kasheni"
Wani kallo tayi masa kafin kuma gyara fusakrta zuwa abin tausayi,kafin yayi wani yunƙuri saiji yayi yana ƙoƙodon amai.
Kaman ana fizgar ƙirjinsa haka yakeji.
Deejah ce ta taho inda yake da gudu,saidai kafin takai ga isa inda yake ta tsayah tareda kallon su jalal.
"Ku tallafa masa,bazai ji daɗi ba idan na taba shi"
Riƙeshi sukayi yana ta kakarin amai,can wani baƙi abu kaman kwalta yafara fito wa daga bakinsa mai kauri.
Saida ya zubar yafi cikin jug kafin jini ya biyo baya,sai kuma aman ya tsaya.
"Hmmm nizakayiwa iyayin neman magani,kowanne magani da layinsa ake warkar dashi,duk maganin dakayi da kwantarshi kake,kuma koyaushe sake cin jikinka yake.
A da yawansa kaman mintin daka shane,yanxu kuma ka kalli yawansa a jikinka,da haka sai duk jikinka ya koma haka,shin zaka iya jurewa?"
Shuru yayi yana kallonta,shikaɗai yasan mai yakeji aransa.
"Shikenan nagama cire abinda nayi muku,yanzu kowa a cikin ku zai iya tafiya."
Wasu mutanene masu baƙaƙen kaya suka taimaka musu suka fita daga ɗakin,saura ita kaɗai da deejah kawai.
"Nagama abinda kika buƙata,yamzu sauran naki cika maganar"
"Hmmm wannan ai kanki nasaka kika yiwa,saboda kar abin yamiki yawa,amma ko kusa bazaki iya shafe laifin dakikayimin ba a raina.
Wai tukunna ma kinsan Malam AUDU Mai BARA,na garin KANKIA?"
Tafiya tunani hajiya fulani tayi sai daga baya ta kalli deejah da alamar razana.
"Keceeee?"
"Ƙwarai,kinyi zaton sun kasheni kenan,ahah shi zakaran da Alllah ya nufah da cara ko ana muzuru ana shaho ai sai yayi.
Bammmm Sumail kacewa malaminka yanzu zai iya fasa akwatin,lokaci yayi"
Wani gigitaccen ihu hajiya fulani tayi,amma kafin ta ƙarisa ihun Taji wata ƙara a cikim ƙoƙon kanta,da alama aikin gama yariga ya gama.
Ita kuwa deejah wata gigitacciyar dariyah tasaka,na ganin burinta da ta daɗe tana so yazo daf da cika.

........














Taku
_sadi-sakhna_
Ƴar mutan jama'are.







*MABARACIYAH*


_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)





47••48



"Me kika aikata min da akwatin,waya taimaka miki kika buɗeshi"
"Hurumin sanin waya taimaka min,kawai ya faru a lokacin da bakiyi zato ba kuma bakiyi tsammani ba.
Dama ance rana dubu ta barawo rana ɗaya ta mai kaya,sannan kuma dama akwai ranar ƙin dillanci,yau taki ranar tazo."
Kakarin amai hajiya fulani tayi tareda riƙe kanta,saboda barazanar ihun mutanen data kashe suke mata a kan.
"Da nasan ke wacece ta tuni bakizo wannan matakin ba,saboda yaron daya tashi da burin daukar fansa,yafi kowanne mutum hatsari"
"Gwanda da kika gane hakan,yanzu kiyi manage da wannan kafin nazo ɗaukar fansa ta a kanki gobe,babu makawa kuma saikin amshi hukuncina daidai da yanda kikayiwa mahaifina,ruwanki ne idan nayi miki ki jure ki rayu,ruwanki ne ki mutu bai dameni ba"
Kasa jura tsayawa hajiya fulani tayi,kafin wani lokaci tayi luuuuu ta faɗi
Tsallaketa tayi babu alamar tausayi ta nufi bakin ƙofah,mutanen wajen ta kalla tareda cewa.
"Ta faɗi me yiyuwa tana bukatar taimakonku a ciki"
Suna shigewa ita kuma tabar gidan gabaɗaya,tana fitowa ta tari adaidaita sahu sai gidan masarautar.
Saleem ta gani yana gode motah,kunnensa rufeda ear piece yana jin waƙar rara.
"Am saleem Eemran ya shigo ne?"
Shuru yayi bai jita ba saida ta maimaita tukunna ya zabura ya juyo.
"Ehhhh mekikace ne?"
"Nace eemran ya dawone?"
"Eh ya dawo,naganshi ɗazu ya wuce kansa a sunkuye,danayi masa magana ma bai kulani ba"
Bata bari ta gamajin abinda yake faɗaba ta wuce inda ɗakinnsu yake.
Sallama tayi amma yaƙi amsawa,kuma tana da yaƙinin yana jinta.
Dan haka tura ƙyuren ƙofar tayi ta shiga cikin ɗakin
A kwance yake rabinsa ya rufu ta bargo,yana jan numfashi a hankali.
"Amma bai kamata ka shigo nan kai kaɗai ka zauna ba,yakamata ka bari ƴan uwanka su taimaka maka yanzu,dan nasan suna nemanka,basu san ka taho nan ba"
"Bana buƙatarsu a yanzu,gabaɗaya abinda ya fari yau ya kullemin kai,ina jin zafi a raina da har yanzu nakasa samun matsayi a wajenki dakazaki iya faɗamin mai yake faruwa"
"Ba haka bane junaid,wani abun barinsa a duhu yafi fito dashi,saidai koma mene kayi haƙuri ,iya abinda zan iya kenan shiyasa.
Yakamata kaje suna buƙatar ka,sannan mahaifiyarku itama tana cikin halin neman taimako"
"Hmmm a tunaninki na yarda da wasan da kuka yi cewar ta tuba,nasan hakan yana daga cikin abinda ki buƙata a wajenta,duk da bansan wani abinba amma nasan fiyeda babu.
Dalilin faduwarta kuma nasan akwaitin sihiirin ta wanda tasaka sirrinta na tsafi a ciki kika buɗe,kuma wanann aljanin dayake miki aikine yayi wannan abin.
"Ba aiki yake min ba ,taimakona kawai yayi kaman yanda na taimakeshi a baya yakoma kan hanyar gaskiya"
"Eh to naji,yanzun suna ina su"
"Sun tafi asibiti inda take kwance,yakamata kaima muje a dubaka,dan Allah karka cemin a'a"
Har zayyi magana ta haɗa hannunta a fuskarta alamar roƙonsa.
Baice komai ba ya tashi daga kwancen tareda jawo bargon kan kirjinsa,kasancewar bashida riga.
Tashi tayi zata fita a ɗakin domin bashi waje,sai taji yayi mata magana.
"Ki faɗawa saleem ya ɗanzo idan kin fita"
Ɗaga masa kai tayi,daga nan ta fita.
Tana zuwa ɗakinsu ta tattara kayanta waje ɗaya.
Babu kowa a ɗakin,shiyasa ta samu damar yin duk abinda takeso.
Bayan ta gama tafito,sannan har sun shiga mota zasu nufi asibitin,a gidan baya junaid ya kwanta saboda ya mike,itakuma ta shiga gidan gaba itada saleem.
GENERAL HOSPITAL KATSINA.
suka nufa direct,inda aka kwantar da Hajiya fulani.
A raception aka basu bayanan inda take,dayake sunada Family register basusha wahalar neman inda suke ba.
A kwance take kaman matacciya har yanzu,Nana khadija a zaune a gabanta,shikuma jalal yana tsaye,gefensu kuma mubarak ne a kwance shima.
Dukkansu kallon Junaid yuyi wanda yake layi kaman zai faɗi a bayan Deejah,
"Doctor maza kuzo ga wani na buƙatar taimako"
Da sauri nurse ɗin wajen suka kwantar dashi a katafaren gadon asibitin shima,tareda bashi taimakon gaggawa.
Babu bata lokaci likitoci biyu suka rufu akansa domin bashi taimakon gaggawa
(Hmmm idan bakada kowa kuwa babu wanda zai kulada kai,saima a fara neman wasu dalilai dazasu hana a dubaka.
Nigeria kasarmu,Allah ya shirya mana ita)

Ledar ruwa kusan biyar Junaid yasha kafin ya mike daga kan gadon,tsawon lokacin Gimbiya khadija bata bar asibitin ba.
Ranar satinsu guda a asibitin mubarak yafara motsawa,ba iya yan uwansa ba hatta sauran mutane saida hakan ya girgizasu.
Idonsa yafara buɗewa akan hasken silin ɗin asibitin,saurin mayarwa yayi ya rutsen idon,dan ji yayi tamkar an caka masa abu a ciki.
Hannunsa yajawo domin jin ko suna aiki,ga mamakinsa sai yaji sun motsa,tsawon lokacinnna yau yayi abinda ya daina mafarkin samun damar yi.
Sake bude idanuwan yayi domin adjusting din harken wajen,wanda duk da ya rufe idon ma yana jinsa a ciki.
Dusu dusu yake gani,amma duk da haka bai hanashi gane cewar,macece a zaune sai kuma wata a kwance a kan gadon.
Ɗan tarin daya bar bakinsa da niyyar yin magana ne yasa Gimbiya khadija juyowa inda yake.
"Ƙanina ƙanina,ka bude idonka kaine kake kallona,Oh Allah nah"
Kallonta yacigaba dayi,yayinda kunnuwansa suke ƙoƙarin karbar maganar datake aika masa,dan a kalmominnata kaɗanne yake mai take cewa.
Fita tayi da gudu ta ƙira likitan kwalkwalwar dayake dubashi,shima kansa yayi mamaki dayaga tashinnasa a dawuri,saboda basusan abinda hajiya fulani tayi ba akansa.
Kafin zuwa yamma mutane sun cika asibitin ana kallom mubarak,wanda yanzu a zaune yake an jinginashi da jikin bangon ɗakin.
Awa biyu kenan da farfadowarsa amma har yanzu babu abinda yace,saidai duk wanda zayyi magana ya juya ya kalleshi,da alama yanajin abinda suke faɗa kenan.
Sannan babu laifi yasha ruwan tea da hajiya saratu ta bashi,dan ita ma tazo asivitin tun jiya domin ta taimakawa Khadija kulada masu jijyar.
Itama madeena ranar da suka zo asibitin tazo dubasu,amma dayake washagari zasu fara jarabawa dole ta tafi.
Hajiya saratuce a zaune tana ƙoƙarin bawa mubarak abinci a cokali,kallonta yake da alama baya ganewa sosai,sai tayi tukunna shima ya kwaikwaya.
"Khadija yakamata a tuntubi likitannan yaushe zai fara magana koh?"
"Eh munyi maganar jiya,yace wai tsawon lokacin daya ɗauka a kwancene,dole sai a hankali ko zai tuna komai"
"Uhm to Allah ya kawo sauƙi,yayah hajiya fulanin itama bata motsaba,Allah yasa dai ba ita kuma wannan bacci rashin tsammanin ta faɗa ba"
"Ameen ummah,nima abinda nake tsoro kenan,kar ko nata rauhin ta bashi ita ta fadi"
Amal ce ta shigo da abinci a hannunta,a bayan ta kuma deejah ceh,wacce itama take riƙeda kula.
"Sannunku ya masu jiki"
"Da sauƙi amal,kema ya jikinki,naji labarin tsautsayin daya faru dake,toh Allah ya kiyaye gaba"
A hankali ta amsa tana kallon deejah wacce ta ɗauke kai tana gaisheda jikin mubarak ɗin.
Sunan zaune basu daɗe ba Mahaifiyar Su sadeeq ta shigo,shima yana biye a bayan ta.
Ta ƙasa deejah take ƙaremusu kallo har suka zauna a kujerun ɗakin.
Bayan an gaisa suka fara labarin duniyah.
"Ummah Deejah,ina yah khaleel ne har yanzu bai dawo ba?"
"Uhm au yayannaki,eh ya dawo amma baya garin"
"Kuma shine ko yazo a gaisa,yasan labarin mubarak ya tashi kuwa,ai yakamata yanzu kam ya shigo gidan koh?"
Shuru hajiya Deejah tayi,da alama bata son yin zancen saboda wani dalili.
Haka kawai daga yanda deejah take nazarinsu ta kula akwai wani abu a ƙasa.
Masu zuwa dubiyah sun ɗan ragu ba kaman da ba,shima mubarak da sauƙi sosai,dan yanzu yakan kama sunayen jalal,idan yana son abu kuma sai ya nuna da hannunsa,ko kuma ya fada a cikin kalmomi ƙalilan.
Yanzu zaman asibitin saboda hajiya fulani kawai suke zaune,ita yanzu takan buɗe ido,duk daga gani bata gane komai dayake faruwa.
Ganin abin bana asibiti bane yasa suka fara tunanin tafiya gida,zaman asibiti dama ai sai dole.
Tashi Hajiya fulani tayi daga bacci,suna haɗa ido da deejah tayi saurin mayar da idonta ta rufe.
Ƴar dariyah tayi kasa kasa babu mai kulada ita,ita dama tasan babu abinda ya samu hajiyan na tabin hankali,fargaba ce a jikinta kawai na bata san yanda zasu ƙare da dodonsu ba,da kuma haɗuwarsu da deejan wacce ta barta ta warke.
Tattara kayan deejah suka fara itada salaha,dan dama dalilin zuwansu kenan dan su tayasu tattare kaya.
Kowa fita yayi aka bar su iya deejah da kuma hajiya fulani sai khadija.
Kallon hajiya fulani deejah tayi ta ƙasan idonta,kafin tayi mata alamar zatayi magana da ita.
Tana ganin hakan ita kuma ta nunawa khadija banɗaki,tana uhm uhm da bakinta.
Matsawa tayi tareda fita komawa gefe,ita kuma saita shige banɗakin.
Wayarta ce da take hannunta ake ta ƙira,wanda hakan yasa ta kalli deejah tareda cewa.
"Am deejah kike koh? Ki tsaya anan wajen har ta fito daga banɗakin sai ku fito,barina amsa wannan wayar a waje"
"Toh Ranki ya daɗe"
Deejah ta faɗa da sauri,dan dama haka take so.
Gaskiya allah yana taimakonta,ta faɗa a ranta.
Matsawa tayi kusada ƙofar banɗakin ta ƙwankwasa da ƙarfi.
"Zaki iya fitowa ƴarki ta tafi"
Buɗewa hajiya fulani tayi tana kallon deejah wacce ta kama kunkumi tana kallonta.
"Hmm bazaki taba tuba ba hajiya fulani,nasan bazaki taba canjawa,ina jinki da daddare jiya kina wayah data hannun damanki,akan yanda zakuyi plan ɗin kasheni.
Da nayi niyyar barinki kodan ƴaƴan ki,amma yanzu kin bata rawarki da tsalle.
Dama an ce mutum baya tsiya sai yayi wa kansa,a yanzu babu wanda yasan Bakida ƙarfin iko saini da dakum babban ɗanki,kinga kenan bana cikin masu tsoronki koh?
Biggy ku shigo yanzu nan"
Tana gama faɗan hakan ta fesa mata abu a fuska.
Kaman jira suke kuwa suka shigo ɗakin ɗauke da kwandon shara babba suna turawa.
Kinkimarta sukayi suka jefata a ciki tareda rufewa suka fita a ɗakin da sauri.
Deejah tana ganin sun fita, ita ma ta fito daga ɗakin da gudu tana ihu kan gari ya gari.
"Ranki ya daɗe ku kawo taimako ku taimaka,babu hajiya ta bace,wasu baƙaƙen halittu sun bace da ita yanxu nan"
Ko zazzzaro ido yayi su hajiya saratu da kuma su jalal,babu wanda ya musa abinda deejan tace,saima tsoro daya shiga ransu,dan sun san hakan dama zata iya faruwa tunda ta tuba.
Ita kuma hakan da tayi yabawa su biggy damar fita daga gidan cikin kwanciyar hankali,batareda kowa ya sani ba.
Shuru dukkansu sukayi aka rasa mai cewa komai, basu ma sam ya zasuyi ba,tunda kowa tunda yaji ance bacewa tayi,taya zasuyi yunƙurin nemota.
Mota suka shiga domin tafiyah gida,babu mai cewa komai a cikinsu.
A hanya saleem ya bugawa Junaid waya yake faɗamasa mai yake faruwa,dan duk cikinsu yanda sukayi tagumi babu mai cewa komai,suma bangaren hajiya fulani a tasu motar gwanda ma kowa dasu.
Kafin su iso labarin bacewar Hajiya fulanin yaje ko ina a cikin gidan,yan uwanta ma daga maiduguri wanda basuzo dubata ba suna hanyar tahowa.
Wanda suka san tsafin da take kuwa sun san ruwa baya tsami banza,wataƙil ta daba wanda suka fi ƙarfinta.
A bangaren junaid kuwa kafin su iso,yana ajiye wayar yaga mata a gabansa tana rarrraba ido.
"Am junaid,dama uhm dama Tsafin Mahaifiyarka ya karye lokacin data tuba sannan......."
"Ya karye saboda deejah ta buɗe akwatinta,uhm mai zakice faɗi ina jinki?"
"Uhm ba bacewa tayi ba,inaga deejah ce ta ɗauketa kaman yanda ta ɗauke amal wancan ranar"
Ɗan nazari ya tafi na wucin gadi kafin ya kalli wacce ake ƙira da Silver.
"Taya kika san hakan ke"
"Share baki tayi ta sanar dashi duk abinda

25 / 33