MABARACIYAH Daga Bara Zuwa Firgitar Masu Iko by Auwal sadiya

Author :  Auwal sadiya Category :  Free Novels Online (Read & Download)

Chapter   29 / 33

84K to 87K   out of 96.8K words

har bakin ruwa na bayan gari.
Zuciyarsa ce ta sosu daya tuna har yanzu bata yarda dashi ba inaga.
Shiryawa yayi cikin kayansa normal irinna gida,babu kowa a farlo ummah tana ciki,dan haka babu bata lokaci ya fice daga gidan.
Tafiyah yake a mota zuciyarsa tana hasaso masa yanda zai ganta,finally bayan kusan wata guda yau zai ganta.
Kamar yanda ta faɗamasa kuwa tana zaune ta juya bayan ta daga inda yake tahowa,duk da yasan tana jin takun tahowarsa wajen..
"Deejah kunyar juyo da fuskarki kike gareni komai,dan nasan kinji zuwana"
"Abinda nakeji gameda kai ma har yafi kunya Eemran.
A duk abinda nake a rayuwata,nakan saje a wajene nayi abinda nakeso sannan na bar wajen tareda ajiye tunanina a cikin zuciyarsu,sannan bana waiwayarsu koda kuwa da kaɗanne.
Saidai kai......zuciyata ta gagara fitar dakai daga cikin raina,a tunanina idan na sauƙe fansata akan mahaifiyarka na tafi zan manta dakai,amma kuma ba haka bane,musamman daya kasance ina kallon shige da ficenka a kullum,na gagara mantawa..."
Samun waje yayi ya zauna a kusada ita yana kallon ruwan dayake gabansa.
"Hmmm wannan zancen dama nasan hakane,tunin sa kawai kike a cikin kunnena deejah,nariga nasani kina sona kaman yanda nake sonki,abinda na kasa sani shine yanda kika boye cikin duniyah,inda idanuwana bazasu iyah tsinkayoki ba.
Abubuwa kaɗan zafi sukemin tareda nauyi a zuciyata,saboda komai saina haɗa da tunaninki cikinsa deejah"
"Nasan hakan Eemran,a hakane a NAWA BANGAREN nima,inason tsayawa a gefenka,saidai kuma matsalar dazan jawo maka nake tunani.
Kaine babba a gidan sarauta,nan gaba kaɗan zaka zama sarkin garinnan idan da kwana,taya zaka nuni a matsayin matarka a haka Eemran?"
"Wannan kike tunawa,shiyasa kika gujeni akan haka,sadeeq ya tsayawa matarsa,itama tatsaya a gefensa amma kuma ke ko sau ɗaya kinkasa yarda dani deejah"
"Na yarda dakai,abinda nake gudu shine,saimun shaƙu da juna na tafi magarƙama na barka"
"Baki yarda dani ba,tunda bazaki tsaya tareda ni ba har Allah yayi nasa hukuncin,ina sonki deejah,guduwarki bazai sanja komai ba,face ƙaramana wahala"
"Shikenan idan hakan kakeso zan amshi soyayyarka Eemran,nima ganinka cikin wannan halin baso nake ba,saidai ina mai tabbatar maka dole mu shiryah mai zaizo ya tafi,duk da nasan ƴan uwanka dasu sadeeq baxasu ƙini sosai ba."
"Mai kike nufi da hakan"
Ƴar dariyah deejah tayi tareda kallon eemran ta jijjiga kai.
"Har yanzu baka sanniba,baka gama sanina,abinda ka sani ma na rayuwartawa bamai daɗin bada labarinsa bane,amma duk da haka ka yarda na kasance abar sonka?"
"Na yarda shi so halitta ne,sannan kuma daga Allah ne,mutum baya sanja kaɗɗararsa,sannan baya zabar wanda Allah zai jarabceshi da sonta.
Koma mai zakice ina ji a jikina ke Alkhairice a gareni,Addu'ar da nadaɗe inayiwa Allah kan ya haɗani da mace tagari bazata tafi a banza ba.
Nafaɗa nasake faɗa,yamda kike nunaw mutane suke aibataki,sannan kuma suke tsoronki ba haka kike ba,kinfi mata fiyeda dubu idan aka jerasu.
Kuma bana miki shakka cewar ka zan zaba a cikinsu deejah,inasonki har cikin raina,kuma bana nadamar hakan."
Rau rau da ido deejah tayi,tana maimaita abinda ya faɗa a cikin kanta,hakiƙa ita kanta tasan soyayyar dasuke ma junasu they deserve each other.
"Zan nuna maka wanda babu wanda na taba nunawa shi a tsawon rayuwata,zan bayyan maka hakanne saboda na nuna maka cewar na yadda dakai.......amma har yanzu zuciyata kokwanto take da alaƙarmu,ina jin tsoron......."
Katseta yayi ta hanyar cewa.
"Deejah yanzu babu sauran abinda ban sanar dake ba,nagameda soyayyata gareki,bazan tilastaki dole saikin amince ba a yanzu,nafara jin babu daɗi saboda roƙonki danake,nizan tafi magriba tayi,kikulada kanki sosai,sannan .....idan na ƙiraki nayi kewarki ne,ki taimaka min ki ɗaga"
Yana gama faɗin hakan ya juya zai bar wajen,har yafara yin nisa,yaji abinda ya zuƙe masa ruwan kai,mai zai ji muryar Khamriyyah.
"Dec. Khaleeeeeellllll,karka kujeni,ina faɗane dan banida zabi badan dan banasonka ba,komawata wajen aiki ma dominka ne,saboda na dunga kallonka ina kulada kai a koyaushe,yimaka hidima abune da bazan taba gajiya wa ba.
A da nakasance mai HARSHEN DAMO wajen kamanni,yanxu kam zuciyata takai maƙurah wajen boyewa."
A tsaye yake kyammm komai na jikinsa ya tsayah da aiki,ya dade a haka kafin ƙafafunsa suka taimakeshi suka maidashi zuwa inda deejah take durƙushe tana kunjin kuka.
Shima tsugunnawa yayi a gabanta tareda zuba mata ido,yarasa mai zaice,gabaɗaya harrufan bakinsa sun tafi yajin aiki.
"Kayi haƙuri khaleel,eemaran,junaid,komai ya farune da dalili,sannan babu yanda zanyine sai haka.
Wasu sunsha wuyah tareda deejah mabaraciyah,sai suke ɗaukar fansar su tareda ita.
Wasu kuma sunsha wahalane tareda khamriyyah V-lady,suma sai suke ɗaukar fansarsu tareda ita.
A tsawon rayuwata nayita yanda zan banbanta waɗannan mutane biyu,ta yanda wanda yasha wuyah da ɗaya kar abin ɗaya ya shefeshi. Kaine mutum na farko daka haɗa alaƙa da mabaraciyah,kuma khamriyyah ta bayyana kanta,badan komai ba sai dan.
Abinda mutane basu ganeba su mutane biyun zuciyarsu guda ɗaya ce ba biyu ba,ciwon kowacce da ƙalubalenta kan jiki guda yake faɗawa,haka feeling ɗin ta,walau bakin ciki ko kuma farin ciki.
Nima mutum ce,inada iyakata Khaleel,na daɗe da kaiwa iyakar amma bansan nakai ba,kaine ka taimakeni ka nunamin nakai wajen da bazan iya sake ɗaukaba,nima ina buƙatar na jingina a jikin wani,ba wai kullum na dunga jan wasu su jingina dani ba.
Abu ɗaya nake so kasani dec. Khaleel,kaman yanda deejah take sonka hakama ga khamriyyah,itama tana matuƙar son ka,Am sorry I love you!!!"""
Kuka tacigaba da rusawa khaleel yana saurarenta,gabaɗaya yarasa mai zayyi,tuno acting ɗin deejah yake da kuma khamriyyah,duk da ƙwarewasa a fannin bincike bai isa yace mutum ɗayace na,duk da yana ji a jikinsa yasan khamriyyan amma kuma bai tana kawo hakan a ransa ba.
Bude idonsa yayi akan fuskarta data jiƙe da hawaye,wanda yakan yasa fatar data saka tafara tasowa.
Hannunsa ya kai wanda yake rawa ya ɗaye ta daga kan fuskarta,take kuwa fuskar khmariyyah ta bayyana tamkar abin almara.
"Kenan wannan itace fuskarki ta ainihi,wato khamriyyah?"
Ɗaga masa kai kawai tayi,dan batasan ma mai zata ce ba.
"Tashi na kaiki gida dare yayi,karki faɗawa kowa wannan maganar,kicigaba da yanda kike,gobe idan kinje aiki zamuyi magana,inason nasan komai dan gane mutane biyun,karki boyemin komai,dannima na kai maƙura wajen sakani a duhu da kikeyi,idan har kin yardani zamuyi rayuwa tare,to bana son ko baoyemin komai"
"Inshaallah bazan boye maka ba,amma kar hakan yasaka ka cikin wani tunanin"
Ƴar dariyah yayi tareda cewa.
"Baccin da banyi ba mai yawa na tsawon wata guda yau zanyishi cikin walwala,hankalina ya kwanta yanzu fiyeda yanda kike tunani. Nagode dakika yarda dani,ina fatan nakasance nine taki majinginar dakema yanzu zaki jingina deejah,tashi mu tafi na kaiki gida,yau a can ma zan ci abincin dare,gobe kuma zan koma gida"
Zaro ido khamriyyah tayi,amma bata ce komai ba sai ɗan murmushi da tayi kawai.
Tashi tayi suka nufi motar tasa,babu wanda yake cewa komai,kowa da abinda yake saƙawa a ransa.
Yana packing ɗin motar tayi nufi sashensu batareda ta kalleshi ba,shima murmushi yayi tareda bin bayan ta kawai.
Sallama ta ƙwallah amma babu wanda ya amsa mata,leƙa ko ina tayi amma babu kowa a cikin gidan.
Haka kawai jikinta ya bata babu lafiya.
Fitowa tayi da gudu zata je sashen hajiya saratu.
A hanya sukayi karo da khaleel wanda ya biyota zai bata wayarta data bari a mota.
"Lafiya naganki haka mai yake faruwa?"
"Uhm babu kowa a sashen,inaga ba lafiyaba gaskiya"
Tare suka nufi sashen hajiya saratun,saidai nan ma babu kowa sai masu aiki kaɗai.
Salaha ta kalla tazo wucewa,da gudu ta risketa tareda tambayrta mai yake faruwa.
"Uhm anty khamriyyah bakisan mai ya faruba?,anty sabrah ce ta sule a tile ɗazu da yamma ta faɗi,shine aka ɗauketa zuwa asibiti a sume jini yana zuba."
"Meeeeee kikacewa,faɗuwa kuma da wannan cikin ya Ilahi,Khaleel maza muwuce asiviti"
Da sauri suka koma motar sukaja da gudu sai general hospital,inda aka tafi da ita.
Khamriyyah sai kuka take a motar tana ƙiran sunan sabriyyan......!!!






Taku
_sadi-sakhna_
Ƴar mutan jama'are.








*MABARACIYAH*


_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)






57••58











Ko packing khamriyyah bata tsaya sun gama ba ta nufi cikin asibitin da gudu.
A bakin ɗakinnata ta haɗu tasu khairiyyah da sauran ƴaƴan gidan,idon khairiyyah yayi jawur dashi saboda kukan data sha.
"Khairi dagaskene ina take itaɗin"
"Uhm tana ciki,har yanzu wai jini take zubarwa,saidai kuma sunce wai zai tsayah,yana tsayawa kuma za'a shiga da ita ɗakin tiyata,domin tserar da abin cikinta"
"Huh alhamdulillah"
Khamriyyah ta faɗa cikin ajiyar zuciya,saidai duk da haka har yanzu hankalinta bai dawo kanta ba sosai.
Ganin magriba tayine yasa su amal da kuma sauran wanda suke wajen suka shiga motar jalal domin komawa gida.
Aka bar iyah su inno da hajiya saratu sai khamriyyah da khairiyyah,saikuma khaleel wanda ya tafi sallah zuwa masallaci.
Sai bayan isha tukunna khaleel ya dawo ɗakinda aka kwantar da sabran,hannunsa ɗauke da ledodin abinci da kuma wasu magungunan da ake nema.
Hajiya saratu ya miƙawa bayan ya tambayi jikin sabrah,wanda take ɗaki daban a gefensu.
"Da sauƙi junaid,ɗazu muka ganta,gobe inshaallah za'a mata aikin,ya za'ayi da tsautsayi yazo,hmm"
"Allah ya taƙaita ,ni barina tafi gida,zan dawo da safe kafin na tafi wajen aiki"
Duk abinda suke sadeeq yana zaune baice komaiba,ɗazu da hajiya deejah tazo babu yanda tayi su tafi amma ya kafe ba inda zaije
Kallon khamriyyah Khaleel yayi ta kasan ido tareda yin hanyar fita,ganin khamree bata biyoshi bane yasa yace..
"Am khamriyyah kizo akwai wata magana da zamuyi"
Tashi tayi tabi bayansa,suna tafe babu mai magana har suka iso bakin motarsa.
Kallonta yake kaman bazai ce komai ba saikuma ya buɗe bakinsa.
"Narasa mai ma zance,kawai so nake nasake ganinki,ki kulada kanki sosai,sannan ki rage damuwa,da ikon Allah zata samu lafiyah.
Gobe ba sai kinzo aikiba,saboda nasan ko kinzo babu abinda zaki iya"
"Nagode Yah khaleel"
Mamakin sunan data ƙirashi dashi yayi,itama ganin hakan yasata cewa.
"Zan dunga bin bakin sauran ƴan gidane,saboda gudun gane tsakanin mu,kaman yanda kace ya zama sirri..yakamata ka tafi gida yanzu,nasan ka gaji sosai"
Sallama sukayiwa junansu kafin suka rabu,kowa yanajin kaman karya rabu da rabin ransa.
Washagari misalin ƙarfe bakwai aka shiga tiyata da sabriyyah,dan dama tun dare aka gama shirye shirye.
Haka suma ƴan uwannnata kwana sukayi suna kaiwa kukansu ga Allah,domin nemawa ƴar uwartasu neman sauƙi.
Awa guda ta wuce,zuwa lokacin su khamriyyah sunyi cirko cirko a bakin ƙofar wajen.
"Inno har yanzu basu fito da ita ba"
"Ki haƙuri khairi,inashaallah babu abinda zai faru sai alkhairi"
Wata matace ta fito daga cikin thearter room ɗin,da kaya blue,da alama nurse ce irin masu taimakawa a ɗakin tiyatar,hannuta ɗauke da Tiren abinda ake buƙata a aikin.
Da dan gudu khamriyyah ta isa gareta tareda marairaice fuska.
"Sister ki taimaka,dan Allah ki faɗamin mai yafaru da ita"
Murmushi tayi tareda cewa
"Komai yazo yanda ake so,ga can likitan ma yashigo ki tambayeshi kiji"
Juyawa khamriyyah tayi tana kallon likitan wanda yake magana da su hajiya saratu.
Abinda ya faɗane ya ɗan kwantar mata hankali sannan ya jiyartar da farinciki cikin ranta.
"Congrat ma'am,munyi nasarar cire jariran dake cikinta mace da namiji,saidai kuma a yanayin wahalar da suka sha bazayyi yiyu ku gansu yanzu ba.
Ita kuma zamu riƙeta na tsawon kusan wata guda,saboda akwai haɗari ta tafi gida a yanayin da mahaifarta take"
Dukkanmu munji daɗi bayaninnasa,sannan a shirye muke mu zauna a asivitin domin tallafa mata.
Shikansa sadeeq jin labarin sai. Yanzu yayi magana tun sanda sabrah ta gamu da tsautsayin.
"Mashaallah,allah mun gode maka,Babu komai likita mun gode sosai"
Kwanan su sabrah hudu a asibiti kafin aka fara nunawa mutane yaran,kowa sai saka Albarka yake...
Ga zahiri nan kuwa ya fito,yaran kamar su ɗaya dasu amal,amal sai murna take idan aka ce da ita babyn take kama,namijin kuma yafi ɗauko babansa.
Har sannan sabriyyah tana kwance,amma jiki da sauƙi sosai,kawai hutune datake buƙata shiyasa aka sakata bedrest.
Khamriyyah ce ɗauke da file ta shiga cikin office din khaleel.
Sallama kawai tayi batareda neman izini ba ta shiga kai tsaye,tun jiya ta dawo aiki amma batayi aiki ba sai yau.
Idonta ne ya sauƙa akan wata budurwa tasha kaya matsatstsu masu tsada,ga wata karairaya datake kaman an zona mata battery..
Haɗe fuska khamriyyah tayi tamau,kana ganin fuskarta kasan matar batayi mata ba,saidai batace komai ba.
"Am ogah ga file ɗin dakace na kawo maka"
Matsawa wajen kujerar sa khamriyyah tayi tana nuna masa abinda tayi indicating a cikin file din.
Ƙarar buga tebur ne yasa su khamriyyah kallon wacce take zaune.
"Ke mekikeji dashi dazaki shigo wani kai tsaye ki wuce inda yake,bakya ganin magna muke,menene matsayin ki a wannan wajen.
Kai kuma Honey kamata yayi kace ta tafi,narasa gane mai yasa ka sanja tunda ka bar china,nayi ta jiran zakazo gidanmu baka zo ba,yanzu kuma nazo nan kana basar dani why,you know i like to marry you"
"Honey. Marry. Gidanku?"
Kallon khamriyyah sukayi wanda tsagwaron bakin ciki da kishi suka turnuƙeta,kana ganinta kasan babu sauki an tabota.
"Khamreeee ki bamu waje,idan nagama da ita zan kiraki muyi magana kinji"
"Karkayi wannan kuskuren dec. Khaleel,inakaga na bar wajennna to wannan figeggiyar tabar nan wajen,idan kuwa ka tursasani saina bar wajennan kun cigaba da wannan wasan,toh ya nunamin ka zabeta ne sama dani,kuma bazan sake waiwayoka ba sai ankai ruwa rana"
Tana gama maganar tayi hanyar barin office ɗin.
Da sauri cikin zafin nama ya tari gabanta tareda hanata barin office ɗin. Cikin idanuwanta yake kallo tareda gane yanayin yawa bacin ran data shiga.
"Je ki zauna akan kujera yanzu nan,ke kuma Humairah zo ki bar office ɗinnan yanzu ,kuma karna sake ganin kinzo wajena da wannan maganar"
Cikin dakewa yayi maganar,wanda hakan yasasu yin abinda yace nan take,amma maganar bata hanasu aikawa junansu harara ba.
Bayan Humairah tabar office ɗin ya ƙarisa inda ruwa yake ya zuba a kofi,miƙamata yayi ta karba tasha kafin yafara magana.
"Badan gargaɗinki yasana na hanaki barin wajennan ba kokuma na sallameta.
Saboda har yanzu bake bace,kina buƙatar a koyar dake yanda zaki iya shanye abu ba tareda kin nuna ba.
Kin amince zaki jingina a rayuwata,kuma zaki kasance tareda ni,karki manta watarana zan iya karbar mulkin garinnan.
Bai dace ga sarauniya ta dunga bayyana kishinta irin haka ba,dole ki koyi hakuri,juriyah da kuma danne abu irin wannan,ta hakane rayuwa zata zomiki da sauƙi deejah.
Inaso ki dunga kwantar da hankalinki,nayi alƙwarin taimaka miki da kuma nunamiki hanyar dazata kaimu ga nasara,amma saikinyi min alkawarin zaki dunga yin duk abinda nace bstareda musuba.
Jiya naji lavarinki deejah,hakan yasa na ƙara jin ƙarfin gwiwar tallafa miki,nariga na zabeki a matsayin abokiyar rayuwata,bai kamata ki dunga tada hankalinki akan wannan irin abubuwan ba"
"Kayi haƙuri yah khaleel,ina sonka da yawa na kasa control ɗin kaina,musamman danaji tana zancen aure,jinayi kaman zuciyata zata faso ƙirjina"
"Uhm naji dadin hakan,amma duk da haka kidunga ragewa My Queen"
Blushing kumatunta yafara dataji sunan daya ambaceta dashi.
"Jiya naji kasako maganar case ɗinmu dasu sabrah,gashi ita kuma batada lafiyah"
"Karki damu mun tsara komai nida sadeeeq,sannan duk shaidun dakuka bamu na abinda sukayi yana wajenmu.
Case ɗin mabaraciyah kuma sai na gama dana wannan,saboda akwai plan ɗin danake son shiryawa akai,thank god babu wanda yadan kece ita"
"Na yarda dakai,duk abinda kace in ma zartarmin da hukuncin kisane daya dace dani zan karba da hannu biyu,saboda nasan bazaka yimin abinda bai daceba"
"Bazata kai haka bama,kedai ki zuba ido kawai.
Zamu miƙaku kotu da zarar sabrah ta warke an sallameta a asibiti,saboda kar hakan yashafi lafiyarta."
"Mun gode da bayyanar ku cikin rayuwarmu lokacin da bama tsamanni.
Ohh na manta ban fadamaka ba,zanje makarantar su fadeelah karfe shabiyu,akwai event da suka shiryawa yaran,to an gayyaci iyayen yara,zanje musu idan babu wani aikin"
Tana maganar ne tana kallon agogon office din,yayinda shikuma yake kallonta yanda take burgeshi saboda resposibility ɗinta.
"Kina burgeni sosai Jarumata,you are their savior khamriyyah,Allah ne kaɗai zai biyaki abinda kikayi,kuma ina mai tabbatar miki ubansu sai yayi nadamar abinda yayi.
Domin yanzu nazama ubansu nima,kuma bazan bashi su ba koda yaso hakan.
Barina shiryah muje tareda,abbansu ma zaije yaga bajintarsu,sunyi sa'ar samun cute little parent"
Dariyah dukkansu sukayi cikeda jin dadin yanayin.
Ranar da ƴaƴan Sabriyyah suka cika kwana bakwai a duniyah aka raɗa musu suna.
Namijin MUHAMMAN BILYAMIN,sunan mai martaba,saikuma mace taci sunan inno wato ZAINAB,ana ƙiran su da SULTAN da kuma SULTANAH.
Yanda aka so yin gagarmin biki hakan bai samu ba,domin uwar gayyar tana kwance a asiviti,saidai duk da haka bikin sunan yasamu mutane ƴan uwa da abokan arziƙi sosai.
Bayan sati biyu da haihuwar sabrah tafara tashi tana yawonta ko ina,tsakaninta da yaran sai sunzo neman abincinsu tukunna.
Ga kulawa ta musamman datake samu daga wajen ƴan uwanta.
Duk ta dawo gida bayan sati biyu,amma su khaleel basu fara zancen shari'arsu ba saida sabrah tayi arba'in tukunna.
Hakan ma badan sunso ba saidan babu yanda zasuyi. Domin idan abin yayi nisa daga baya akaji dole zasu fuskanci matsla.
Bayan haka kuma aikin hukuma ba wasa ba,sunyi alƙawarin yin gaskiya da amana,taya soyayyya zata rufe musu ido su manta da hakan.
Duk wani abu da zai kasance sun riga sun tsarashi tass.
Tun jiya aka kai su khamriyyah dukkansu su kwana a can,saboda bin ka'idar shari'ah.
Khaleel ne sanye da kayansa normal,shikuma sadeeq da kayan aikinsa.
Hajiya saratu ce a gabansu sai matsar ƙwalla take akan su ceto mata ƴayanta,amal ce da sadeeq suke bata bakin kan ce babu abinda zai faru.
"Ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru,domin mun haɗa dukkan shaidun dazasu fito da masu laifin a fili"
"Toh nidai ku kula dasu,musamman sabrah,har yanzu fah bata dawo normal sosai ba"
"Kai ummee,wai mijinta ake cewa ya kulada ita,ki kwantar da hankalinki komai zaizo da sauƙi,sannan dan allah karfah kifara kifara kuka idan kika ga abinda bai miki ba"
Dukan wasa hajiya saratu ta kaiwa jalal wanda yake mata dariyah.
"Kai wato har bakin dariya ma ka samu a wannan lokacin?"
"Menene a ciki,nasan masoyansu zasu fiddasu ai,suda sukeda mai garin ma a gefensu,bakisan yah khaleel ya folawa ƴar ki bane?"
Wani kallo khaleel yabishi dashi akan yayi shuru,amma hakan baisa yayi shuru ba saida ya ƙarisa faɗin abinda yayi niyyah.
"Uhmm naji,mun riga mun sani ai tun a asibiti kawai munyi masa irinna iyayen gargajiyane,shikenan kuje muna zuwa Allah ya dafamuku"
Amsawa sukayi da ameen tareda yin hanyar sashen mai martaba.
"Wai dagaske ɗan uwa kayi zurfi a soyayyar khamriyyah,to amma deejah fah ya zakayi da ita kenan,koka daina sonta ne"
"Ban daina sonta ba,dukkansu ina sonsu sosai,sabida abinda yayi ɗayar shine yayi ɗayar"
"Mai kake nufi,kasakani a cikin duhu ban ganeba"
"Bazaka gane ba yanxu,bari a gama wannan case ɗin,case ɗin gaba zan warware maka zare da abawa,saboda muna buƙatar taimakonka akai"
Daga haka khaleel bai sake cewa komai ba har suka shiga wajen mahaifinnasu,dukkuwa da yanda sadeeq yake binsa da buƙatar ƙarin bayani.
Addu'ar fatan nasara yayi musu,tareda basu gudunmawar lauyoyi guda biyu daga fadar,saboda sukare masa ƴaƴannasa,wanda a hannun hukuma yanzu.
Lokacin da suka isa police station ɗin har ya gaji da jiransu,
"Ina kuka shiga yallabai ina ta jiranku,kotu ta buƙaci jin wanda ake

29 / 33