MABARACIYAH Daga Bara Zuwa Firgitar Masu Iko by Auwal sadiya

Author :  Auwal sadiya Category :  Free Novels Online (Read & Download)

Chapter   13 / 33

36K to 39K   out of 96.8K words

yanda aka miki?"
Hannunta ta maye gurbi aka cikinnata lokacin da inno ta ɗauke nata hannun,kallon cikin take kaman wanda zataga ɗan a ciki kwance.
Kuka ta fashe dashi tareda matse hannun akan cikinnata,daga gani jitake ina ma mafarki take data farka daga baccin.
Cikin raunin muryah ta kalli inno tareda cewa
"Tambayar yanzu tayi tsauri nabada amsarta yanzu ina buƙatar lokacin,saboda barin cikin harda alaƙata da ammar zai shafa,dam haka ina buƙatar yin tunani idan zan samu dama"
Itama inno hawaye take kafin tace,
"Kinada damar yin tunani tsawon yanda kikeso,ina fatan kiyi zabin dazakiyi nadama ba,amma duk wanda kika zaba ni mai baki goyon baya ce"
Daga kai tayi da maganar innon kafin ta tashi tashige ɗakinta.
Sai a lokacin na kulada hawayen dayake zubomin akan kumatuna lokacin da anty juwairah tabar wajen.
Khmariyyah kuwa ko motsi batayi,da alama ta tafi duniyar tunani.
Tundaga inda abin yafaru a cikinmu babu wanda yasake tada maganar tamkar ba'ayi shi ba.
Saboda wannan ba kyakykyawan labari bane daza'a dunga watsashi ga mutane.
Wata biyu sun shige,zuwa lokacin cikin anty juwairah ya tafi wata biyar,yayi wata fitowa tamkar cikin wata bakwai,mudai yanda muke ganinta bamuga wani abin tashin hankali a gareta ba,muma sai muka kwantar da hankalin mu muke ƙoƙarin nuna mata komai ba komai bane.
Duk da bata samu inno ta faɗamata zabinta ba,amma kuma ganin an ɗebi lokaci batayi ƙoƙarin cutar da cikin ba ko kuma cutar da kanta hakan ya nuna ta zabi ta raini cikin akan ta zubar dashi.
Wanda hakan yasa inno ta jinjina mata da juriyarta,sannan ta zage dantsen kulada ita har zuwa lokacin dazata haife cikin.
A zaune nake a ƙasa kan tabarma,ita kuma anty juwairah tana zaune akan kujerar da kwanon ɗan sululu akan cinyarta wanda maman yara tayi mata. ƙafarta nake matsamata wacce tayi suntum kaman an hura baloo.
Mu kaɗaine a wajen khariyyah ta tafi shagon computer ogansu ya ƙirata,ita kuma khamriyyah tayi ficewar tata,a cewarta ta tafi isalamiyyah,wanda nasan ba can ta tafiba,kawai dan inno tayi shurune.
Magana nake tayi amma banji anty juwairah tace komai ba,ɗaga kai nayi naga ta tafi tunani,ga kwanon a cinyarta amma bata ciba.
Ta bata nayi a cinyarta wanda hakan yasa ta zaburah kaɗan.
"Anty juwairah wanann zurfin tunanin dakikeyi kinsan fa da matsala,dan allah ki daina.
Kuma yakamata ma kifara zuwa awu yanzu"
Ɗan murumushi tayi tareda saka ɗan sululun a bakinta.
"Hmmm sabrah don na zabi cigaba da kulada cikinnan da kuma maida komai ba komai ba,wani abin bazan iya ba,taya zam iyah zuwa awu kaman yanda masu cikin sunnah suke zuwa,taya zan daina tunani na dunga murmushi kaman yanda masu miji da kuma cikin sunnah suke,kodah nace zanyi bazan iya ba,karki manta inafah da tabo a cikin zuciyata wanda har yau zubarda jini yakeyi bai warkeba,kodah na takura kaina wajen bashshi ya warke bazan iyaba sabrah"
Kukane yake son kubcemata amma taƙi bashi damar hakan,kallon cikin tayi tareda shafashi sanann tacigaba da cewa.
"Idan nace ban tsani uban cikinnan ba nayi ƙaryah,idan nace banasonsa kuma bana jin haushinsa a lokaci guda to kowa yasan ƙaryah nake.
Ina sonsa sosai,sannan inda burin riƙesu har lokacin da allah zai rabamu,amma bazan daina tunanin abinda ya faru dani ba"
Maikuma nake dashi dazan ce bayan naji abinda tafaɗa kuma,dole shuru nayi ina zullumin abun a raina.
A raina na cigaba da yimata fatan sauƙa lafiyah,sannan kuma dafatan sauƙi a lamuranta.
Tafiyah ta tafi,cikin anty juwairah yazama ƙato,duk wanda ya ganta sai ya sake waiwai yawa saboda girman cikin.
Komai yanzu yimata ake,duk da tana ƙoƙarin motsa jiki sosai,zuwa awu kam taƙi yarda taje,tunda ga dawowarta daga katsina zuwa shari'ar maryam bata sake fita waje ba har zuwa yau.
Dan haka inba mutum shigowa yake ba sosai bazai ganta ba ma.
Daff da haihuwarta sai ta fara kumburah sosai ,abin har ya wuce na lafiyah,ga ciwon kai da jiki datake fama dashi,amma kuma taƙi zuwa asibiti,idan an ce ta fita duk hankalinta sai ya tashi.
Haka muka zubamata ido babu yanda zamuyi.
Wataran mun dawo daga makaranta itakuma ta fito a banɗaki,babu zato babu tsammani sai ganin zubewarta mukayi akasa,jikinta ya ɗebi rawa kar kar kar.
Khariyyah ce ta ƙwalawa inno ƙira itada maman yarah,da gudu suka iso wajen suna dubawa.
Nida khamriyyah kuma muka fita da gudu neman mota a waje.
Kayan makarantar da bamu cireba kenan aka nufi asibitin tareda mu.
Tana kan cinyar inno a gidan baya itada maman yara,ina gaba wajen direba khamriyyha kuma tana gefensu.
Lokaci lokaci nakan leƙawa ina ganin yanda numfashin ta yake sama sama,ga ritsetsen ciki a jikinta kaman wanda zata haifo ƴaƴa biyar.
Gado suka turo da gudu aka ɗauketa sai cikin asibitin.
Sauri sauri suke ganin halin da take ciki,wata nurse ce naji tana cewa,
Wai jininta ne yayi mungun hawa saboda yawan tunani datakeyi,ga kuma ciki wanda hakan ya haifar da matsala babba.
Tambayar da nurse ɗin tayimin ita ta tsayar da fitar numfashi na cak,dan ban san mai zance da ita ba

"Ina katin awunta kuje ku ɗauko,tana cikin mawuyacin hali,sannan idan babu shi to bazamu tabata ba saidai kuje asibitin kuɗi"
Shin cewa zan ce batada shi,saboda bata ta'ba zuwa awu ba,ko kuma haƙuri zan bata.
Taya zamu shawo kansu su dubata a halinda take ciki,ni bansan ma mai zanyi ba a lokacin,kai na yayi mungun yin murfi.
Wannan ita ake ƙira da rayuwa.
Idon khamriyyah nagani yanda ta zubawa nurse ɗin jan idonta,a raina sunan allah nake ƙira yayi mana tsarewarsa,dan kuwa da alama wani abu take shirin yiwa matar,wacce tazage sai magana take mana babu alamar imani a tareda itah.

Anan kam free ɗinku ya ƙare,duk mai buƙatar sanin mai zai wakana a littafinnan toh ya kasance dani ranar juma'a,a PAID group domin cigaba.
Karku manta naira 400 ne zai biyamuku buƙata.

3131951977
Auwal sadiya
First bank.



Taku
_sadi-sakhna_
Ƴar mutan jama'are.







*MABARACIYAH*


_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)





21••22


Tun kafin nayi wani yunƙuri khamriiyyah ta zari a wuƙa a wani faranta ta yankawa matar hannu.
Ihu ta fara ganin yanda jini yake bin hannunta,sanann kuma wajene da in ba'ayi da sauri ba zata iyah rasa jini dayawa.
Sauran nurse tahowa sukayi da sauri domin taimaka mata,saidai khmariyyah ta riƙe hannunta ta hanata barin wajen,ga jinin yana ta zuba,sanann ta riƙe wuƙar idan da mai buƙatar sake matsowa.
"Kusan allah in kunga na sauta kunyi mata magani to kun duba antynah dake halin mutuwa koh rayuwa,inkuma kuna ganin wasane to kucigaba da tsayuwa.
Munsan mun yi kuskure wajen rashin zuwa awu,amma kuma tanada babban dalilinta nayin hakan,wacece a cikinku wani zai shiga gidanta ya kashe iyayenta yayi mata fyaɗe,ta wayi gari ta ganta da ciki kuma tayi farinciki har ta samu damar zuwa awu,waye nace a cikinku takeda wannan ƙwarin gwiwar,na tabbata kusan dukkanku kashe cikin zakuyi daga sanda kuka sani.
Toh wallahi ban faɗi karya na indai rashin tabata yasake zawo wata matsalar,saina cinnawa wajennan wuta bayan na fatattaki duk marasa lafiyar wajen"
Dukkansu jikinsu rawa yakeyi,da sukaji abinda tace,ga yanayin ta ma daya nuna ba a hayyacinta take ba.
Magana mukaji a bayanmu ta wata mace,da alama ta ɗan manyanta a shekarunta.
"Mai ya faru a nan wajen haka?"
Zaro ido tayi ganin khmariyyah ta damƙe nurse ɗin ga kuma jini yana zuba a kasa.
Magana tafarayiwa matar dan ta taimaketa.
"Uhm.....mmetron ki taimaka wanann batada hankali"
Sauranne suka tsara mata mai yake faruwa,wanda yakan yasa maida kanta wajen khamriyyah.
"Saketa yarinyah,ni zan duba yayartaki yanzunnan,barta su gyaramata karki ɗorawa kanki laifi da yarintarki,naji abinda suka ce gameda ƴar uwarki,ina mai tabbatar miki zanyi iya ƙoƙarina,allah yakare gaba"
Babu kunya kuwa khamriyyah tasaki matar tareda tunkuɗata kana ta bita da harara,itadai ana sakinta tabar wajen da sauri.
Wacce aka ƙira da metron ɗinne ta nufi ɗakin da aka kwantar da anty juwairah,wanda hakan yasa nayi ajiyar zuciyah.
"Ke khmariyyha meyasa kika yi haka,kinsan fah hakan zai iyah jawomana wani tashin hankalin"
"Dama dan ayi tashin hankalin nayi ai,kuma wlh ba sakinta zanyi ba har sai ta suma,naga bakin ciwa mutane mutuncin"
"Uhm"shine kawai abinda nace,tareda komawa bakin ɗakin da anty juwairah take,inda sabo yakamata na saba da taurin ran khamriyyah.
Tun azahar muke asibitin har dare,ko abincin rana bamici ba bare yin wanka,gashi har yanzu tana ciki basu bamu damar shigaba,kawai dai sunce haihuwar bata zoba da saura,saidai a halin datake ciki mai hatsari bazasu barta ta tafi gidaba,dan har yanzu bata san inda kanta yake ba.
Allurar bacci suke ta ɗuramata daga ta farfaɗo,saboda a bawa ƙwaƙwalwarta hutu daga tunanin datake yi.
Nida khamriyya komawa gida mukayi aka bar iyah maman yara da inno a ca,khariyyah kuwa dama tana gida,saidai tayi mana ƙira a ƴar wayarta yafi sau a ƙirga.
A can dole su inno suka kwana saboda yanayin jikinnata,saidai kuma sun faɗamana ta fara naƙuda a lokacin.
Shiryah wa mukayi muka tafi asibitin,dan koda mune makarantar ma babu abinda zamuyi sai tunani.
Lokacin da muka isa asibitin har sanann likitocin suna kanta,amma ansamu nasarar sauƙar da jinin nata ba kaman jiyaba.
Muna nan zaune har wajen sha biyu kafin mukaji kukan jinjiri daga ɗakin,zumbur muka miƙe muna jiran muga wazai fito.
Duk da baƙin fentin da ubansu ya shafamusu,amma hakan bazai hana muyi marmarin yaranba,wanann ne karo na farko da haihuwar yaro akayi ba kawoshi ba.
Nurse ne guda buyi suka fito da jarirai a hannunsu,sororo muka tsayah muna kallonsu,dama ƴaƴa biyune,kuma hakane gasunan mace da namiji tufarkallah.
Nice na karbi mace inno kuma da karbi namijin,khmariyyah bata ko kalli yaranba,hankalinta yana kan ɗakin sai leƙawa take,ganin nurse ɗin batada niyyar yimata ƙarin bayani yasa ya tambayeta

"Uhm uwar yaranfah tana nan ƙalau?"
"Eh toh da sauƙi dai za'ace,amma gaskiya abin babu daɗi,jikinta ya kumburah sosai,hatsarin kuma shine ba sacewa yake ba ƙaruwa yakeyi gaba,kucigaba da addu'a insha'alla komai zaizo da sauƙi."
Jikinmu ne yayi sanyi jin abinda tace gameda anty juwairan,dukkan bakinmu kowa sai motsi yake yana addu'ar da zai iyah wacce yasan tana buƙata.
A asibitin mukayi ta sintiri,wasu na komawa gida wasu na dawowa,tun nurse ɗin suna yawan dubamu akai akai har suka koma suna tsallake gadon anty juwairan,dan sunriga sun san matsalarta,kuma ba sauƙi yake ba bare suce an ga canji.
Ƙarshe dai yaran a asibitin suka ƙarbi sunan su,har suka shafe wata kusan guda da rabi.
Idan ta farfaɗo takan karbesu da basu nono,idan tana kwance kuma a basu madara.
Dayake babu abinda ya damesu suna ci suna ƙoshi sai girma sukeyi,ƙyawawane kam farare tamkar ubansu,wanda mukayi babban bincike akan sa,mun gano shi kaɗaine a wajen ubansa kuma bashida aure,shashanci yasaka a gaba kawai,abin takaicin kuma gashi ya bar mana da jininsa batareda yasani ba.
Kallom fadeelah nayi wacce take kan cinyata,yarinyar badai kuka ba kam,gata batada bacci sosai kaman fadeel ɗin.
Dawowa ta kenan daga gida na dawo daga makaranta.
Khmariyyah kuma dama bataje na yau,itace a wajen anty juwaira,inno kuma tana gida ciwom ciki yadameta,maman yara kuma ita ke kulada gidan.
Abubuwa dai duk sun kwabemana amma haka muke ta garawa,mun zubawa sarautar allah kallo muga yanda zayyi damu.
Tashi nayi daga corridon da fadeelah a hannuna na shiga cikin ɗakin da mahaifiyarsu take kwance,yanzu idonta biyu tana kallon silin,ƙarar kukanne yasakata juyowa ta kallemu muna shigowa,kasancewar bata magana sosai,sai dai binmu kawai take da ido.
Hannu ta ɗaga wanda yake rawa zuwa saitin yarinyar,alamar na bata ita.
Kwantarta nayi a gefenta tareda buɗe nonon,dayake shi take nema ba 'bata lokaci takama tafara sha.
Khamriyyah ce tashigo hannunta duk ruwa da goyon fadeel a bayanta yana bacci,da alama wankin kayan da anty juwairah ta bata tayi.
Hawayene yake gangorawa a idon anty juwairah lokacin data kallemu,nasan tunani take a ranta yanda muka tsaya a gefenta iya wuyah da tsanani.
Sallama mukaji ta anty shamsiyyah,dukknmu kowa ya tamke fuska yayi,dan iskancinta da cin kashinta ya ishemu haka.
Sai tazo tayi ta iyayi tana nuna ƙaryar kuɗi a gaban mai jinyah,ko kuma idan sunzo da wata saita nuna tamkar ba gida ɗayah muke da itaba,ta wuce sa'armu ashe tare muke.
Yanzu ma sallama tayi tashigo,zuwanta na uku kenan tun sanda aka kwantar da anty juwairah.
"Mai jinyah ya jikinnaki dai,naga jiki kam har yanzu jiya i yau,amma baza'a gwada kaiki asibitin katsina ba ko za'a dace"
Munajin ta faɗi haka khamriyyah tayi caraf tace.
"Gaskiyaa ke ta musamman ce anty shamsiyyah,da kin kyauta kuwa idan kika ɗauki nauyin kaita,barina karbo takardar izinin ina dawowa"
Dakatar da khamriyyah tayi tareda cewa
"Ahah bashshi zanyi masa maganar,ba yanxu ba tukunna"
Dawowa khamriyyah tayi tana sake tamke fuskarta,dama da gangan tayi dan taga yanda zatayi.
Cire fadeelah tayi a nono ta miƙamin ita ganin tayi bacci,kafin ta ɗaga anty juwairan domin cire mata rigar jikinta tayi datti da yawa.
Anty shamsiyyha tana kallon ta bata tayata ba,har ta gama ta mayar da itah shimfiɗin.
Daga cikinmu babu wanda yasake kulata kaman bata wajen,muryar khariyyah mukaji tashigo hannunta ɗauke da kular abinci inji maman yara.
Bayan sati biyu da zuwan shamsiyyah sai jikin anty juwairah yafara sauƙi,dan yanzu tana magana sosai ba kaman da ba,har yaran take karba da basu nono daga kwance,wannna abin ba ƙaramin daɗi muka jiba.
Itama idan daga jin daɗinmu sai tayi ta murmushi.
Fadeelah ce a kan cinyarta ta gama bata nono,sai khamriyyah ta karbeta,dan har yanzu jikinnata bashida ƙarfi sosai.
"Ƙanne na haƙiƙa banida abinda zance muku sai allah yasaka da alkhairi,kuma allah yabaku mai yimuku kaman yanda kuke min...,"
"Dan allah anty juwairah kibar wannan godiyar,dama naga idanuwanki lokacin dakike kwance,kina buƙatar faɗin kalmominnan,babu komai,ganin zamu iyah yi miki mu shine kwanciyar hankalinmu"
"Khamriyyah ku karbomin takardar sallama inason komawa gida,idan wani abu ya faru inyaso saina dawo,nagaji da zaman wajennan,kuma nasan kun gaji sosai"
"Karki ce haka,kowa dama dayake zaman asibiti to zaman haƙuri yakeyi,abin farincikin shine da kika samu sauƙi har kika buƙaci tafiya gidan da kanki,barina gama gyara kayannan zanyi mata magana toh"
Suma da khamriyyah ta tambayesu basuyi musu ba,dan dama na kula sun gaji damu kaman.
Washagarin ranar maman yara tazo tayamu tattare kaya muka koma gida,ana ta murnar samun nasara,duk da bamai yawa bace amma dai an samu.
Ban taba sanin idan an ce ana samun sauƙin tafiyah da gaske bane sai a kan anty juwairah,lokacin da muke ta murnar samun sauƙinnata bamu saniba ashe na amsa ƙiran mahaliccinta ne,mutuwarta tafi ta duk sauran girgizamu,saboda bamu zata mata ba sai kawai ganin afkuwsrta mukayi.
Ranar da aka gama murnar dawowarta da daddare ciwo ta dawo ɗanye sharaf,da farko mun so nemo mota amaidata,amma ganin alamun rashin rayuwa a cikim idonta yasa dole muka haƙura jinkinmu ya saki muna tsimayin mummunan labarin dazamuji kuma mugani.
Mutuwa rigar kowa,idan tazo babu wanda bazai amsa kiranta ba,koda kuwa waye ya bari dole sai ya tafi.
Jijjiga jikinta yafara tana kikkifta ido,inno na gefenta tana shafa mata ruwa a fuska tareda yin salati.
Hannun khamriyya ta riƙo tana nuna mata yaran da suke gefenta da idonta,ko bata faɗaba tana rokon a kula mata da rayuwarsu ne,wanda batasan kobata fadaba mu masu riƙesune da basu kulawa.
Can bayan kaman wasu daƙiƙu dukkan wani motsi na jikinta ya tsaya,numfashinta ya daina shiga da fita,yayinda bugun zuciyarta shima ya tsaya cak dayi,rai yayi halinnasa daya saba a koyaushe.
Khamriyyah ce datake tsaye tafaɗi yaraff sai jin buguwarta mukai timm a ƙasa.
Kanta hankalinmu ya koma,a iya kwankinnan mun ɗanɗani mutuwa ba ɗayah ba ,ba biyu ba,saidai muyi fatan allah yasa muma tamu ta ɗaukemu muna kan turbar gaskiya.
Kafin wayewar asuba su inno sun gyarata a cikin kayanta na ƙarshe,kowa sai matsar hawaye yakeyi,dan anty juwairah mutum ce da bata cutar da kowa wajen zama da itah.
A masallacin anguwarmu aka sallaceta inda akayi nasu maryam da hajjah.
Har aka kaita safiyah tayi hantsi ya washe khamriyyah bata farkaba,har muna shirin kaita asibiti sai kuma mukaga alamar motsawarta,daga gani doguwar suma tayi amma ba mai tsayi ba .
"Sabrah ina anty juwairah take,dan allah kicemin mafarki nake kinji,karkice abinda nagani na bacewar numfashinta na ƙarshe da gaskene"
Shine abinda ta fara faɗa bayan tasowarta daga suman datayi.
Jijjiga kaina kawai nake ina share hawayen dayake zubowa a kuncina,wanda shikaɗai nasan ya isa ya faɗamata gaskiyar lamarin da take biɗar sani,dan da bakina bazan so na gaskata mata wannan labari mai ɗaci ba.
Hannunta ta dunƙule tareda mayar da hawayen dayake ƙoƙarin zuba akan fuskarta,kana ta cije baki tana kallon bangon ɗakin.
Da alama irin wanann yanayinnata ta shiga,wanda narasa menene yasaka ta a cikin halinnan.
"Khamriyyah meyasa idan abin kuka yasameki bazaki zubar da hawaye ba saidai ki mayar dashi hakan fah yanada illah"
"Sabrah bashida dalilinsa na sauƙowa a cikin idanuwana,bayan wanda yasakani na zubar ɗin shi bayyi ba"
"Kai khamriyyah,ki dunga yarda da kaddara mana,shi sanadi ne,amma maƙasudin faruwarsa yine na allah"
"Nasan wannan,amma shi bai saniba idan ba sanar dashi akayi ba,dan haka da ɗaɗɗai zan sanar dasu kuwa inshaallah"
Idanunta a soye suke,ga wani numfashi datake fitarwa kaman mai shirin yin kokuwa da 'bauna,nidai ɗaga kai nayi,dan komai zan je bazata saƙƙoba sai taga dama.
Bayan kwana uku da mutuwar anty juwairah wato ranar sadakar uku kenan,sai inno ta ƙira anty shamsiyyha daga cikin mutane zuwa ɗakinta.
Iya mu yamu ƴah gidan kenan.
Ɗanta wanda ya kusa shekara sai kuka yakeyi.
"Shamsiyya dama akwai maganar danake so nayi miki,kinga dai ƴar uwarki kuma ƙanwarki ta rigamu gidan gaskiya,gashi tabar ƴaƴa marayu masu shan nono,wanda ko bazasu sha nonon ba dole zasu buƙaci madara.
A halin yanzu bamuda kuɗin madarar dazamu shayar dasu,koda munada shi ma ni kinga ba lafiyace dani ba fama nake da ciwon ciki mai tsanani,ita kuma maman yara itama ɗanta a cikin satinnan zai ɗauketa dayaji mai yake faruwa a nan ɗin,dama ba da son ransa take zaune ba,kawai dai abune daya zama jiki.
Sukuma su khamriyyah makaranta suke,abin zai musu yawa ga rainon yara ga kuma na makarantarsu,inaga idan mijinki zai amince shamsiyyah ki ɗauki yaranann a wajenki,inaga hakan zai fi"
Saurin miƙewa tayi jumbur tareda zaro ido,
"Haba haba inno mai kike cewa haka,na riƙe ƴaƴa,babu jinin daya haɗani dasu na riƙesu hakan ma kuma shegun ƴaƴa,wlh bazan iyaba,nifah zuwan danake asibiti da kuma gidannan dan kar a zageni nake zuwa,abinda ya haɗamu daku dama ya raba,zamane nikuma yanzu nayi aure na samu rufin asirina,bazan iyah saka ƙazaman ƴaƴa akan nono na ba,ko kuma nakashe musu a kuɗi a banza na siyan madara,bazan iyah....."
Tasss kafin ta gama maganar inno ta ɗauketa da mari,danni kaina danake kusada khamriyyah saida na tsorita,dan ban taba ganin 'bacin ran inno ba irin na ranar.
"Kinada hankali kuwa shamsiyya,ni kike faɗawa wannan maganar,?"
"To wai dolene saina riƙe ƴaƴan da kowa yasan shegune,kuma daza'a tilastamin nima da'aka riƙeni ai ba'a banza aka riƙeni na,saidai gwamnati tabada albashi"
"Abashi!....albashi kike

13 / 33