MABARACIYAH Daga Bara Zuwa Firgitar Masu Iko by Auwal sadiya

Author :  Auwal sadiya Category :  Free Novels Online (Read & Download)

Chapter   5 / 33

12K to 15K   out of 96.8K words

aikata wanann kisan ba,saboda tabar mana takarda akan gawar kan cewa ba aikinta bane,amma tana dabb da aikata nata,mukanmu mun kasa samun ko alama ɗayah dazamubi wanda yake aikata kisan"
"Tayaya Sadeeq zakace ba ita bace ta aikata kisan,dan kawai ta ajiye takarda tace ba ita bace sai a yarda da itah,to taya tasan an ajiye gawa a wajen dakuma mai ya faru inba itace ta aikata ba?,mai gadi da bakinsa yace muku tace mabaraciyah sunanta,kuma yanzu tace ba ita bace ta aikata,wannan zancen banzane zancen wofi,kawai kace ka gagara kamata kawai,kuna gani kun zuba ido tana kashe iyaye mutane kun kasa komai akai,to idan baxaku iya ba muzamu fara ɗaukanataki mu wanda abin yashafah,ya za'ayi ace ƙaramar yarinya mace ta dunga kashe manyan mutane amma ankasa yin komai akai,wannan ai zancen son kaine,kawai saboda kuna ƴaƴan manyan security an ɗaukoku an sakaku akan tsaron mutane,kuna yanda kuka ga dama,sukuma ƴan ƙasa ana ta kashesu......"
"Kai muhseen ya isah haka,dec. Sadeeq yayi iyah ƙoƙarinsa akai,amma abin kam babu adalci a ciki,ya za'ayi mutumin da yake taimako yakeyiwa mutane magani,wasu kyauta yake basu ƙodar yau shine kuma za'a cirewa tasa dan mugunta?"
Har dr. Muhseen ya buɗe baki zayyi magana khamriyyah tasha gabansa,dan takai maƙura wajen ɗaukar rainin hankalinsa,
"Dakata malam,ya muna iya ƙokarinmu wajen bincikar wanda yake aikatawa kai kuma kana cimana mutunci,an faɗa maka nan asibitine inda mahaifinnaka yake isada iko a wajen,zakace dan yana dan mai bincike,kaima duk wanda yaganka ai yasan baka kai matsayinka baka akayi dan ubanka yana da faɗa a ji,da kaje kayi wani aikin mana ba irinna ubanka ba,kowa yasan kana cikin zafin mutuwa,amma bai kamata ka huce akanmuba,muda muke bada rayuwarmu dan taku.
Da kake cewa wani zakaje ka ɗau mataki,to inka fasa,mu ai taimaka mana kayi idan ka kamota,kaga muma munhuta da tashin hankalin ace mana an ɗauke wani mutumin san........"
Saurin janyeta dec. Sadeeq yayi suka bar wajen,gashi asibitine har dun fara tara ƴan kallo a wajen.
Saida sukaje har bakin motarsu kafin ya sake hannunta yana kallon ta da mamaki,dama haka take da masifah da iyah ɗaukar bacin rai,abinda bai taba ganin tayiba tsawon kusan shekara ɗaya dasuke tareda ita.
"Menene haka khamriyyah,muda muke kwantar da tarzoma kekuma kina ƙoƙarin kunnota,bakisan a cikin aikinmu akwai haƙuri ba"
"Haba ogah baka ganin ɗan rainin hankaline ba"
"To ke bakya ganin rashin mahaifinsa yayi"
"To dan yayi rashin mahaifinsa sai....."
"Ya isa haka,ga nan ahmad zai kaiki gida yanzu,kije ki huta kafin gobe na nemeki,dole zamu fara bincike akan wanann takardar,inaga dole zan barmuku aiki ma na tafi ƙarin sabon salo kona wata shidane"
Yana gama faɗa mata haka ya koma cikin asivitin,bata tsayah jiran ahmad ba takama hanyar gabanta,dan har cikin ranta taji haushin abinda muhseen ɗin yayi,haka kawai baka san abinda ubanka yayi ba,kadai tunda yana ciyar dakai da tufatar dakai babu ruwanka,sai wani abu ya sameshi bazasuyi bincikeba sai zakin mutane,ba gudu baza da baya,babu wanda ya isa yahana ta cikar burinta kaf cikin duniya kuwa saidai mutuwa tayi.
A bakin wani layi ta bayan wajen babu kowa wata mota ta tsayah ta ɗauketa.
Shiga tayi tareda miƙewa a gidam bayah,deen ne yakalleta ta cikin madubi tareda cewa
"Ran V-lady ya daɗe mai ya farune haka na kinyi jagwab dake,ko mutuminnamune ya birkita miki tunani"
"Kai deen i am not in joke mood,ka kaini wajen khairiyyah ina buƙatar ganinta,tunda naga ta ɗauke ƙafah dazuwa gida"
"Okay shikenan,hmmm mai kuma ya faru"
Bata kulashi ba saima rufe ido da tayi tana jin sanyin motar dayake ratsata a jikin jikinta,kafin su karisa wajen har bacci ya ɗauketa,sai jin deen tayi yana tashinta ashe har ya iso wajen khairiyyan.
Fitowa tayi tareda yimasa magana cikin ƙaramar muryah tashiga cikin cafe ɗin.
Zama tayi a kan wata kujerah batayi mata maganaba ganin tana yiwa wasu aiki,saida ta gama kafin ta tashi tashiga wani ɗan ɗaki a cikin wajen.
Tashi khamriyyah tayi ta bitah,wajen ɗan ƙaramin ɗakine mai ɗauke da computah guda uku,saikuma wasu abubuwan da wasu wayoyin.
"Anty khmariyyah ykk ya aiki"
"Cune baki khmariyyah tayi da alama sunan bayyi mata ba sam
"Ji wani sabon salo kuma wai anty,lafiya ƙalau ykk ya aiki,jiya baki dawo gida ba lafiya dai koh"
"Eh lafiyah kalau,wlh wani virus ne ya shigo mana,to kinga bazam tafi nabar su da aikiba,kwana mukayi muna aiki a wajennan,ya ayyuka suke tafiyah dai"
"Lafiyah ƙalau,amma daya kamata ki ƙira wayah,banason naga kina kwana a wajennan keba namiji,duk da muna aikin kasada hakan bai bamu damar yin yanda muka ga dama ba"
"Inshaallah mommy khamriyyah zam kiyaye"
"Kaimata duka khamriyyah tayi,da alama tafara ƙosawa da zolayar khairiyyan,wanda kaman halintane hakan,eh naji dai kunsan alhakin kuladaku dukka yana kaina ko kuso ko kuma ku ƙi,dan haka daga yau idan wani abu ya faru ki tabbatar kin faɗamin"
"Inshaallah kiyi haƙuri anty khamriyyah bazan sakeba nace ai,ina su maryam da su fareeda,ita batanan koh?"
"Eh tana wajen aikinta,amma wanann satin zata dawo daga service ɗinta itama ta fara aiki,wato kinfi missing ɗinta akan balki koh?,nasan sabriyyah kam kuna wayah ai"
"Uhm itama ba sosai ba,kinsan itah rashin ganinta yafi na kowa,baka isa ka ganta sanda kakeso ba,badan munsaka rai a wannan aikin ba dasai nace ni wlh na gaji,dandai zuciyata bazata samu nutsuwa ba idan banga mun cimma burinmu bane.
Yawwa naji labari a wajen deen wai mabaraciyah bata mutu ba,dagaskene kuwa?"
"Kai deen akwai gulma shiba mace ba,yaushe ya faɗamiki,keda baki fiyeson shiga sha'anin hakan ba"
"Hhhhh jiya yake faɗamin wai dasuka je ajiye gawar dr. Bukar sunga wata mata ta ajiye wani abu akan gawar,dasuka bita kuma basu sameta ba duk neman da sukayi"
"Kutt to amma nibasu faɗamin wanann zancenba,yaushe suka fara rufemin abu toh,mun samu takardar kuwa,kuma daga mabaraciyar tafito kuwa"
"Tabbb to yanxu ya za'ayi,anya kuwa bazata kai farmaki kankiba,karki manta fah kece kika harbeta lokacin da ta yi ƙoƙarin kashe brr. Shehu,to amma meyema ya haɗata dashi,mungama target ɗin kamashi fah,kawai sai mukaga takamashi dakanta,nayi mamaki meyasa take bayyana idan zamuyi aiki?"
"Karki damu khairiyyah zanji da wanann,yanzudai abinda yafi shine inaso kimin wani aikine shiyasa ma nazo da kaina banmiki aika bah"
"Wane irin aiki kenan"
"Ke bakya tsayawa kici ribar zance,kibari mana na gama yimiki bayani.
So nake kiyimin hacking ɗin computar headquarter kisaka sunana a masu tafiyah ƙarin karatu a cikin wanann satin,zanje nacire paper zuwa gobe"
Kallonta khairiyyah take da mamaki,dan ba karamin kaɗata zancen yayi ba,ƙarin karatu kuma a cikin satinnna ma"
"Amma fah kinsan a ƙa'ida mutum sai ya tura takarda dakusan wata guda kafin a karbi takardar"
"Shiyasa nace kiyi hacking ɗin wajen kaman yanda kika saba ki sakani cikin wanda zasu tafi a satinnan,kinda nimber ID na kiyi amfani dashi"
"Okay angama anty khamriyyah,yanzu ina wani aikin,amma zuwa yamma zan miki,kafin na dawo gida"
"Ki tabbatar fah kin dawo gida da wuri idan ba haka ba zaki ganni nazo ɗaukarki,kuma saikinyi sati ban barki kin fita a gidaba,wannan shine punishment ɗinki"
"Baza'ayi haka ba ma,zan dawo inagama wannan aikin da'aka bani na wata masana'anta"
Daga nan ƴar hirarsu suka fara ta ƴan uwa yaushe gamo,kafin khamriyyah tafito ta nufi makarantar su fadeelah domin ɗaukosu a makaranta.
Tarar mai napep tayi tai masa kwatancen makarantar,har sannan kayanaikintane a jikinta,sai hijabai kawai data saka akai.
Kasancewar shabiyi ake tashinsu kuma a nursery 3 suke,har sun fito suna zaune a bakin wata bishiya suna jiran mai ɗaukan nasu har sannan bai zoba,fadeelah sai kuka take wai ita yunwa takeji lokacin data ga khamriyyah tazo ɗaukansu.
"Antyyyyyy....."
"Menene fadeelah,har yanxu wai bazaki daina kuka a makaranta ba,kina ganin fadeel bayayi saike koh"
"Ba shuraim ne ya kwacemin biscuit ɗina ba,babu abinda naci sai bredin da diddy tabamu da safe"
Ƴar dariyah tayi ganin yanda ta dage sai kuka take,wanda da batayiba saida ta ganta tukunna.
"To naji kiyi haƙuri tunda abokinku ne ina,kuma kema kirage tsokana da kuka,fadeel yana faɗamin irin tsokanarki ai a makarantar"
Harara ta zanbgawa fadeel ɗin wanda yake zaune a bakin bishiyar yana ganin tijarar datakeyi.
"Shima ai yana tsokanar zaice nikadai nakeyi,yau ma ai uncle saida yayi masa duka a aji"
"Ƙaryah takeyi ita aka duka suna faɗa da wata ƙawarta"
Kara kufulewa tayi musamman dataga khamriyyah ta yarda da zancensa,dan dama duk wata rigima ita takeyi
"Kai ni ya isheni haka,kutashi mutafi gida,dama ba yunwar kikejiba ai tunda kika tsaya tsare tsaren mai yake faruwa"
Wani mai adedetan taƙara tara suka tafi gida"


A gajiye dec. Sadeeq yashiga gida yana sauƙe ajiyar zuciyah,kana ganinsa kasan ba ƙaramin abu bane yasashi haka.
Akan kujera ya jube yana kallon P.O.P ɗin dayake saman falon,motsin zaman amrah dayaji a kusada shine yasashi ɗagowa ya kalleta,
"Jarumina ya akayine naga ganka a gajiye,har yanxu akan case ɗin dr. Bukar ɗinne?"
"Hmmm wanann case ɗin ai an rufeshi amrah,shima an kasheshi kuma har yanxu babu wani abu dayake nuna alamar zamu samu mai kisan,shikam ma dan rashin imani ƙodarsa aka cire fah duka biyun,nikaina dana dade ina bincike idan naga kisan da ake saina razana,kuma abin mamakin ma wai macece takeyinsa,yaya take oho,menene dalilinta har yanxu bamu saniba,kuma kinsam menene,da alama tanada alaƙa da makarantar almajirai,koma ba itaba to da akwai wani acikin irin makarantun dayake taimaka mata.
Toh yanxu kuma mun sake binciko wai ba itah kaɗaice take kisan ba akwai wasu ma dasukeyi.
Ni narasa ma yazanyi da wanann abun kwata kwata,a da na raina case ɗin danaji ance macece, amma yanzu kuma abin yafara gagarata amrah,inaga nafara kasawa da wannan case ɗin"
"Karkace haka honey,inshaallah zaka iyah ka kwantar da hankalinka komai zai zo da sauƙi,kacigaba da jurewa jarumina"
Rungumeta yayi a kirjinsa,da alama daman neman wanda zaiji ƙorafinsa yakeyi.
"Nagode matata,yah babyn mu yake,naga yau jikinki da sauƙi sosai,ina fatan babu matsala ko"
"Babu komai muna nan kalau,barina ɗebo maka ruwa tukunna,kafin na haɗo abincin"
"Aha sannunki da aiki,nibanyi tunanin zakiyi bama yanda na fita na barki"
"Ahah nasamu sauƙi miye zanyi ta kwanciyah,bayan nasan zaka dawo,ko a gidan su mamah baka son cin abinci yanzu bare a waje.
"Maman ce ai yanxu ta daina girki sai masu aikine yanzu sukeyi,shiyasa na ajiye shafinsa a gefe guda"
Bayan ta kawo abincin ma zancensu suka cigaba dayi irinna mata da miji,bai san lokacin da nutsuwarsa ta dawo masa ya manta da duk wata damuwa daya kwaso.
A zaune suke yau ma da daddare suna cin abinci,saidai yau a hankali kwamce suke ci babu zancen wani da zasuje da daddaren.
Khairiyyah ce ta fito da wata takarda ta miƙawa khamriyyan.
Ƙarba tayi tareda buɗewa takallah.
"Eh yayi kyau,amma nayi mamaki dasuka yi approve a yau ɗin,banyi zaton abin zai faru nan da nan ba"
"Karki damu,kinsan niɗin bata wasa bance,sunan ki nasaka a jerij na huɗu,suna karbar biyar suka haɗa da sunanki,kinsan kaman banɗakina haka nake shiga wannan website ɗinnaku,babu abinda nake jin sauƙinsa kaman yimusu kutse a lamarinsu,na ɗauko bayanai.
Wai tsayah kin karbi takardar ƙarin karatu,shin tafiyah ƙarin karatun zakije ko wani abune daban kika saƙawa wanda dole saikin bar wajen?"
"Kai khairiyyah kin faye tambaya,ƙarin karatu zanje amma bata bangaren abinda ya shafi aikina bane,zanje sanin wani abune gameda wani lamari daya nake tunanin zai faru a gaba"
Dukkan shuru sukayi musamman su fadeel daina cin abincin sukayi.
"Anty tafiya zakiyi ki barmu?"
"Ahah fadeel ba tafiya zanyi na barku wani waje zanje zan dawo kaji"
Kallon dukkan matan wajen sukayi,khairyyah ce ta kasa hakuri saida tasake tambayarta.
"Anty khamriyyah zancen serious dama dagaske kikeyi,amma wata nawa zakiyi toh"
"Wata inaga zaikai shida zanyi,ya danganta da yanayin gama karatun,kafin na dawo kowa yayi normal rayuwarsa,nasan tunda ƙarin karatu zan tafi albashina zai dunga shiga,maryam ki dunga cirowa kuyi abinda yadace dashi,ku kula da kanku sosai"
Dukkansu jugum sukayi,musamman su fadeelah da khairyya,dan kaman sun fi shaƙuwa da itah,dr nawwarah ce ta kalli khamriyyan wanda itama ta gama cin abincin.
"Duk da bansan mai zakiyi ba amma nasan abune mai muhimmanci,karki damu inshaallah komai zai tafi normal,sannan zancen albashinki kuma kema ai zaki buƙata,menene amfanin kuɗin danake dashi wanda a yanzu bana ganinsa a wani abu fashe ruɗi na duniyah,zan cigaba da kuladasu dukka,za'a ɗauko mai gadi ma saboda tsaro,kafin allah yayi mana ikonsa"
"Nagode sosai dr. Nawwarah da taimakonki,haƙiƙa bazanji dumuwar barmiki ahalina a hannunki ba"
"Nima yanzu sun zama nawa ahalin,yaushe ne zaki tafi"
"Jibi zan tafi ranar alhamis,idan gobe dec. Sadeeq yayimin sign,inkuma bai min ba dole saina jira ya amince"
Dukkansu dariya sukayi a hankali,suna kallonta taƙasa
"Da alama fah bawan allah nema yake ya fola fah,inkuwa hakane yana ruwa inya gano gaskiyah"
"Ke maryam,wato tunda bakiyi magana ba saida kikaji zamcen tsokana koh,da har zance ina fareedah ashe fah mijinta ya dawo ɗazu,sun tafi gida."
Ƴar dariyah khairiyyah tayi kafin tace,
"Bawan allah kenan,duk da yasan gaskiyah amma bai hanashi sonta ba,Gaskiya samun miji kaman Badulmajeed sai antona"
Kallonta balki tayi kafin tace,
"Jimin khairiyyah mai saurin afkawa abu kaɗan,gaskiyar mai yasani,bai san harda itah a kisan da'ake ba,baisan tsakanin ta da khamriyyah,kawai fah yasan marainiyace kuma a nan gidan aka riƙeta,ki gayamin mai yasani toh"
"Hakane kam,shiyasa daga yanzu nacireta koda wani abu zai taso,saboda kar a je ya shafi aurenta,zaman ta gidanta yafi wannan abin"
Fareeda ce ta mike tareda cewa
"Toh nikam saida safenku akwai abinda zanyi saina kwanta,fadeel maza tashi mutafi kwanciyah kaji mutumina"
Tashi yayi yabita da gudu yanayiwa su khamriyyah bye bye,itakam fadeelah ana hirah harta kwantar da kanta akan diddy tana shirin bacci.
Ƙwankwasa ƙofar office ɗin khamriyyah tayi dan tasan dole yana ciki,tunda lokaci yazo bata shigo da wuri
Izini taji ya bata daga ciki hakan ta murɗa ta shiga da takarda a hannunta.
"Ina kwana ogah"
"Lafiyah khamriyyah ya hidimar aiki,naga yau kin makara koh duk gajiyar aikinne"
"Eh to dama......wani abu na tsayah yi saboda akwai abinda nake shirin yi"
"Mene....."
Tun kafin ya gama tambayarta ta ajiye masa takarda a kan table,tareda kallon idonsa tana jira taji mai zaice.
Ɗaukar takardar yayi yana karantawa,tun daga farko yasan takardar menene amma saboda tabbatarwa yasashi karantawa.
"Me hakan yake nufi khamriyyah naga ya nuna cewar ƙarin ƙaratu,yaushe kika yanke wannan hukuncin haka"
"Dama yallabai so nake kasaka min hannu,buƙatar hakanne yataso,naji kana cewa zaka tafi ƙarin karatu,to inaga gwanda naje akan kai ka tafi,beside ma ga matarka tana ɗauke da ciki,nasan bazakaso kayi nesa da itah.
Kuma dama nayi shekara guda akan aiki,lokacin tafiyata ƙarin karatu yayi,musamman yanda muke ƙarbar case a watannin nan masu yawa"
Shuru yayi yana nazarin bayanan nata,tabbas abinda ta faɗa gaskiyane,amma a wannan lokacin tace zata tafi gaskiya....
"Toh naji ƙorafinki,khamriyyah kije zanyi nazari kafinnan saina ƙiraki "
"Amma yallabai wajen dazasu ƙarbeni yau suke buƙata na turamusu takardar tareda da takarduna,shiyasa na kawomaka,kayi hakuri ogah"
"Naji amma duk da haka zan ƙiraki dai"
Cikin sanyin jiki da alamar rashin samun nasara khamriyyah takama hanyar fita daga office ɗin,har taje bakin ƙofah taji yayi mata magana,wani murmushi tayi na sun nasara kafin ta juyo da sauri.
Miƙamata takardar yayi tareda yimata fatan alkhairi.
"Nagode nagode yallabai,allah yabaka abinda kake so"
"To saiki dage,bakije kiyi ta shirmeba,fatan alkhairi"
Da sauri ta fita daga office ɗin tana ƙafafa tareda farin cikin cikar burinta.
Washagari dasafe ta haɗa kayanta ta tafi,bayan tasaka khairiyyah ta tura information ɗinta makarantar data keso su ƙarbeta.

******

"Fareeda yau fah kwana uku kenan har yanzu banga khairiyyah ba,ko gida bata dawoba ,naje wajen aikinta ma bata nan fah"
"Mai kike faɗa maryam kin duba kuwa,mai yake faruwa"


_sadi-sakhna_



*(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)*

*MABARACIYAH*
(mai harshen damo)

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιε.


_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)



Paid book #400
3131951977
Auwal sadiya
First bank

Mai turo kati kuma ta wanann number MTN
09035784150

Mutanen niger su tuntubi wanann number
+227 97 21 16 15

Naƙara shafin free har zuwa page 20,zuwa lokacin inka shiryah kazo a fara dakai ranar juma'a.

_____________________
Assalamualaikum barkan mu da wannan lokaci *ABMAR COLLECTION* ina nan na kawo muku kayana masu kyau da sauki👌🏻
KAMAR SU:-
Atamfa, Atamfa Mai golden,💁‍♀️
Lace ,Shadda lace
Yadi, Shadda
Abayas💥
Kids wear
Takalmi, jaka, mayafai💥
Sleeping dress, kananan kaya na gayu🔥kayan kitchen,
DA DAI SAURANSU ina Sokoto ina tura kaya ko ina da izinin ubangiji mai son kayana pc ina maraba daku siyan daya ko sari👏🏻domin neman karin bayani sai ku neme ni ta wannan number waya👉08101521252
nagode kwarai da gaske💃💃







Free page
9••10



Daurah_____5:00pm


Mutanene guda biyu mace dana miji zaune a bakin rafi suna hira,gefen ƙafarsu kuma ruwa yana wucewa,daga kallon yanda suke kasan suna jin dadin yanayin sosai.
Kallon mutumin dayake zaune a gefenta tayi,kafin ta sau ɗan sansanyan murmushi.
Doguwar rigace a jikinta baƙa,sai kanta ma ta nannaɗeshi da baƙin mayafi.
Wanda hakan yafito da jar fatarta sosai irinta fulani.
"Yah muzzanbil nayi mamaki danaga yanda kamaida wajenann,gaskiya wajen yanada tarina ni'ima,amma hakan fah rani yana zuwa zaku bar garin fah ku koma gun daban koh.
Yaushe za'a daina wannan tashi tashin na almajiraine?inaga kuma lokaci yayi dazaku zamanta tsarin karatunku nan"
"Lallai ma deejah har yanxu kina nan da ƙorafinki,yanzu idan muntashin menene zai shafeki a ciki"
"Babu komai,kawai dai kasan bazan biku bane,kodah yake ni wani satin ma fah nake son shiga cikin garin katsina,wannan hutun jakin da kaya akai ya isheni haka"
"Hmmm wai ke ba namijiba amma kina birkita hankalin manyan gari,nayimiki magana kibar wanann aika aikar amma sam kin ƙiji sam"
"Bazan iyah dakatawa ba saina gama tukunna,a lokacin dana gama zan fito kowa yasan nice,kafin zuwan lokacin nashiryah kallon tsagwaron tsana a idanuwan wanda nayi sanadiyyar mutuwar masoyansu,nikaina nasan abin akwai babbar wuyah idan lokacin yazo"
"Kwanaki kincemin na faɗamiki idan yadiko lami tazo ganin gida,to tazo jiyah a satinnan zata koma,maiyasa kike buƙatar zuwanta,wani abin kike ƙoƙarin shiryawa ko"
"Hhhhh kai ya munzanbill mai ka maidani ne,kafin nan inaso ka ƙarisamin bayanin yanda ake laƙanin karshennan,saboda inada buƙatar sa a cikin shirina"
"Deejah ina jiyemiki kiyi abinda zai jawo hatsari ga rayuwarki fah,wanann abin yakamta ki tsayah iyah haka"
"Kayi haƙuri yah muzanbilu,nayi maka alkwari daga wannan nadaina bazan sakeba,amma matar sarkin katsina babu mai hanani illatata koda ban kasheta ba saita ƙwammaci a kashetan"
Saurin zaburah muzanbilu yayi ya tashi tsaye tareda sunkuyowa yana kallon deejan,wacce ko a jikinta kaman ba ita tafaɗa ba.
"Deejah!mai kika ce,naji kunnena yajiyo min wani gagarren aiki,mai kike nufi da hakan"
"Basai ka

5 / 33